samosan tana zama gefen Maryamu wadda suka haɗa ido suka yi wa junan su murmushi
Sai kuma Aakifan ta ɗauki ɗaya cup da kanta ta zuba wa Maryamu drinks tana miƙa mata, tace, "Ammee wlh kyakkyawa ce, muna sonta zamu ji dadin zama da ita."
"Haka nake son ji ai." Cewar Ammee tana murmusawa, "ki zuba mata samosan itama ta ci, bari ina zuwa."
Sai ta miƙe ta nufi kitchen tunda ta ɗaura ferfesun kayan ciki da take musu
Su kuma su Yusaira sun saka Maryamun a tsakiya suna ta hira da su Hanif,
While Maryamu tana kurɓan juice ɗin tana haɗa wa da samosan, ta saki jikinta sosai tunda bata da baƙunta, musamman da ta ga su Yusaira suna janta a jiki suna mata surutu, sai yaba kyawunta suke yi suna ce mata, "tana kama da Kajol Agriwal, don dai ita Black beauty ne amma kamar su ta ɓaci, kuma ita ta fi Kajol ido."
Ita dai Maryamu bata ce komai ba tunda bata san wace ce Kajol Agriwal ɗin ba, amma a yanda suke ta zuzuta kamannin ta har su Hanif suna taya su shirmen, shiyasa take ta jin dadi a ranta tunda akwai ta da son a yaba ta
Hira sosai ta ɓarke a tsakanin su, har sanda Ammee ta dawo ta kammala komai ta kwaso food flakes tana jera wa a dining, sannan tace, "su taso su ci abincin."
Gaba dayansu suka nufi wurin har su Yusaira since su ma basu ci komai ba
Bayan sun kammala cin abincin, sai suka ja Maryamu suka wuce ɗakin kwanan su,
Ammee kuma ta nuna wa su Hanif ɗakin da zasu zauna,
Sannan ta fita ta saka Mai gadin su ya kwaso musu kayan su a Boot, da akwatin Maryamu da aka ciko su da kayanta har biyu,
Bayan ya ajiye a Falo, ita da kanta Ammee ta ja na Maryamu takai ɗakin su Yusaira,
Time ɗin ma Maryamu har ta soma sallah, shiyasa ta cewa su Aakifah, "su haɗu su gyara mata kayanta a wardrobe."
Suka amsa mata da to, sannan suka tashi kowacce ta ja akwati ɗaya suka fara aikin
While ita kuma ta fita ta ɗauki ƙaramar Jakar su Hanif; su ma takai musu dakin su,
Na'ilah na tare da Sadiq sai didima take yi a jikinsa ta samu abun da take so, dama jinta take yi kamar ƙaramar yarinya bare an sangarta ta
Hanif ya shiga wanka; sai Sadiq ɗin da ke kwance a saman gado Na'ilah na jikinsa
Ammee ta harare ta tana cewa, "ke fa ba kya jin magana dama, daga zuwan su kin samu abun da kike so baza ki bar su su huta ba ko? Common zo ki wuce ki barsu su huta ki koma ɗakin su Aakifah."
Kwaɓe fuska tayi tana shirin kuka
Sadiq da ke dariya yace, "Ammee ki barta kawai, doki nake mata but in na gama zata fito."
"Kai baka san halin yarinyar nan bane, haka take yi wa Abee ɗin su sam bata girma, in ka biye nata baza kayi abun da ke gabanka ba, zo ki wuce idan kun kammala kimtsa wa sai ta dawo, ga sallah ma baku yi ba."
Sai da ta tasa Na'ilan sannan ta ƙyale shi, don har kuka ta soma yi, ta ja hannunta suka fice
Sadiq kuma yana faɗa mata, "tayi shiru ya kawo mata tsaraba, idan ta ci gaba da kukan bazai bata ba."
Hakan ne yasa tayi shirun har ta dena turjiya a kan bin Ammeen.
***
_____Kwana ɗaya su Hanif suka so suyi, but Ammee ta hana su tafiya sai da suka ƙara kwanan, tace, "tunda ba Abee gwara su zauna su yi mata kwana biyu."
Sai da suka zagaya garin gaba ɗaya har su Yusaira sai jin dadi suke yi, tunda ba a barin su fita, basu da lokacin ma kansu kullum suna makaranta,
Sun ji daɗi sosai da suka fita yawon zagaya wa, ga shi Hanif duk ya kashe musu kuɗi ya siya musu kaya da su chocolates kala-kala yayi musu siyayya sosai
Ranan da zasu tafi ko damuwa Maryamu bata yi ba tunda tuni ta saki jikinta, ko lokacin tunani ma bata dashi tunda su Aakifah sun ɗauke mata kewa kodayaushe suna tare da ita suna mata surutu, shiyasa kamar sun jima da sanin juna sun ƙulle sosai bare kansu ɗaya
Bayan su Hanif sun isa gida sannan Momy ta kira Ammee ta sanar mata, sun daɗe suna waya suna sake tattaunawa a kan matsalar Maryamun, daga baya suka yi sallama
To kasancewar Hutu ake yi a wannan lokacin shiyasa Maryamu bata fara zuwa makaranta ba, amma tuni Ammee ta gama cike mata Form an saka ta makarantar haddan su Aakifah da suke zuwa asabar da Lahadi, sai yamma suke dawowa,
Zuwan Maryamun ne yasa Ammee ta nema musu wurin koyan computer, a ɗan lokacin da suke dashi bayan sun dawo hadda da karfe huɗu, zasu riƙa zuwa sai su dawo ƙarfe shida, driver zai riƙa dauko su,
Amma yanzu da ake hutu shiyasa suke zuwa kullum
Lokaci guda rayuwa ta sauya wa Maryamu, kulawa da komai Ammee tana musu, ba ta barin su lalaci tunda Mace ce mai zafin nama itama kamar Momy, komai na gidan su suke yi, ita take raba musu kowa yayi aikin sa, dayake itama ba zama take yi ba tunda tana aikin ta, shiyasa kafin ta dawo sai dai ta zo ta tarar duk sun yi girki sun gyara gidan, idan ta dawo su kuma sai su tafi wurin koyon computern su, har da Na'ilah suke zuwa tunda itama tana Hutu, kuma idan suka barta a gidan ita kaɗai take zaune, sai su tafi da ita ta zauna a can tana wasa, wani lokacin ma har da ita ake koya mata, don dai tayi ƙanƙanta ne da yawa
Shekara ɗaya ne ake koyon computern sai su yaye mutane, shiyasa Ammee tace, "da zaran sun gama zasu koma wurin koyon kwalliya."
Su Aakifah sai daɗi suke ji domin sun fi son haka, domin yanda suke ƙaunar kwalliya in har suna gida zaka ga sun cakare sun yi makeup a kan face ɗin su, shiyasa tayi musu alkawarin, "da zaran sun gama zata mayar da su can su koya kwalliyar."
Ita kanta Maryamu suna burge ta matuƙa, duk da ba kasafai take son kwalliya ba amma idan sun ce zasu yi mata; haka zata basu fuskarta su zana mata suyi ta yabon ta suna cewa, "tayi kyau sosai."
To itama ganin tana yin kyau shiyasa abun ya soma tasiri a ranta, ta ji tana son itama ta iya, dole ta matsa musu su riƙa koya mata tunda ita dai bata iya ba sai nasu na ƙauye,
Tana yawan yin waya da su Innarta tunda yanzu sun san tana Abuja da zama, yanzu ga shi har bikin su Bintu ya zo saura kwanaki, ta so ta je bikin amma Allah bai yi ba, bata da yanda zata yi, tunda su Aakifah ba sa riƙe waya sai dai ta ari na Ammee ta kira gida suyi ta waya, yawanci sun fi daɗewa da Bintu suna wayan tunda yanzu Mijin da zai aure ta ya siyan mata waya, Maryamu ta samu abun yi; tayi ta zama tana bata labarin Abuja tana gaya mata irin daɗin da take sha da kuma abubuwan da suke koya
Sai Bintu ta ji kamar ita, har so take yi dama ace itama a kaita a fasa auren nan, amma babu hali
Izuwa yanzu Maryamu ta koya wa kanta rayuwa babu SHAREEF, duk da bata taɓa tunanin zata iya rayuwa a wani wuri inda babu shi ba, amma zamanta cikin su Aakifah ta soma saba wa da hakan, duk da yana maƙale a ranta, in dai zata zauna ita kaɗai sai ya faɗo mata a rai, har kuka tana yi a ɓoye sabida a kullum soyayyarsa azalzalan ta yake yi, tana shan wahala matuƙa jurewa kawai take yi domin ta saka a ranta baza ta ƙara ɓata mishi rai ba, kamar yanda ba ya ƙaunar ganin ta a tare dashi itama dole zata yi nesa dashi, a yanzu fata take yi Allah ya cire mata soyayyarshi a ranta tunda gani take yi kamar baza ta iya doguwar rayuwa a inda babu shi ba
Kullum Momy sai ta kira ta itama ta ji lafiyar ta, tana jin daɗi yanda ta ga Maryamun ta saki ranta a yanzu, kuma bata taɓa yin mata maganar SHAREEF ba haka itama bata tambaya ba, iyakan su Yaya Hanif take tambaya, in suna nan ma suna yin wayan tare
Dayake tunda bikin nan ya zo ana gobe Dady yace zasu tafi Zaria,
SHAREEF ya so ya botsare a cewar sa bazai je ba, sabida ganin a ranan asabar Haseena zata dawo ranan bikin kenan, bazai so ya tafi ta dawo ba ya garin ba, amma Dady yayi mishi jan ido yace, "dole sai ya je wlh, sabida ko don auren sa da Maryam iyayenta su sake sanin sa, don haka ya shirya dole su tafi tare."
Ran SHAREEF ya ɓaci jin abun da Dady yace, ashe har yanzu suna nan da maganar basu sauya Shawara ba? Shi a ganin sa lokaci kadan yake jira su ce ya sake ta, ashe har yanzu suna ganin ta a matsayin Matarsa basu canza ra'ayi ba, ai kuwa a haka zasu gaji har su raba auren kamar yanda suka ƙulla, don yanzu lokaci kaɗan ya rage masa ya mallaki Haseenan sa, sanyin idanuwansa; wanda yake jin a duniyar nan ita kaɗai ce farin cikin sa, ita ce jin daɗin sa, a ƙagare yake ta dawo amma ga shi an yi masa cikas, tunda ko ta dawo suna can Zaria, since a gobe zata dawo.
***
_____A ranan juma'a misalin ƙarfe biyar suka isa cikin Zaria, a gidan Iya Samira suka sauka, murna wurin ta ba a magana, musamman yanda ta gansu dukkan su suka taho, ta rasa ma inda zata sanya su don murna da daɗi, sai kallon su Hanif take yi domin bata iya gane su ba sai da ta tambaya, "wane ne Mijin nata a ciki?"
Momy ta bata amsa tana nuna mata SHAREEF da kuma Hanif ɗin shine Mijinta
"Lallai! Idan a hanya ne na gansu bazan taɓa gane su ba wlh, ba kwa son zumunci ko kaɗan Yaran nan."
"Wlh kuwa Inna, SHAREEF ma bai so zuwa ba sai da nayi masa jan ido sannan ya biyo mu." A cewar Dady
Iya Samira ta sake kallon SHAREEF ɗin tana washe baki, wanda tuni ya duƙar da kansa yana ta faman latsa waya fuskarsa a ɗaure, tace, "yo ai kai ne zaka zo mu ganka tunda yanzu ka zama Mijin Meramun mu, ai mun yi kewarta wlh ba kaɗan ba, ashe bada ita za a zo ba?"
Murmushi duk suka yi,
Momy tace, "tana can Abuja tana karatu shiyasa, kuma bata daɗe da tafiya ba shi yasa bamu zo da ita ba."
"Ai hakan ma babu komai wlh, wata rana zata zo ai, komai lokaci ne."
Haka suka dinga hira bayan sun yi Sallah sun natsa
SHAREEF tun zuwan su Sallan Asar da yayi musu a hanya, sai yanzu suka samu suka yi, sai ya wuce ɗakin zauren da aka gyara musu yayi zaman sa a can, sai yatsina fuska yake yi kamar ya shiga cikin masai tsaban yanda yake nuna ƙyamatar sa da gidan, jinsa yake yi a takure kamar ya kurma ihu ko ya gudu ya koma gida, wlh ba don ɓacin ran Iyayensa ba babu yanda za a yi ya ci gaba da zama a gidan nan, bare kuma wancan ƙauyen da ya fi tsana
Su Hanif kuwa babu ruwansu suna can sun saki jikinsu ana ta hira, ƴan uwa ma sai zuwa suke yi suna gaisa wa tunda Iya Samira ta je ta sanar musu
Shima Dady yace, "da bata je ba tunda zasu shiga har babban gidan."
Da suka je yin Sallan magriba ne shine suka shiga Babban gidan su Iya Samira aka gaigaisa,
Itama Momy daga baya suka je ita da Iya Samira,
A can suka zauna har bayan sallan isha'i before suka dawo gidan,
Kuma suka sake dasa hira tunda an daɗe ba a haɗu ba,
Dama tuwo Iya Samira tayi, haka nan suka ci don Momy tace, "ba sai an musu wani abincin ba, gwara a ɗumama tunda su ma sun jima basu ci irin wannan tuwon ba."
SHAREEF dai ya ƙi ci, koda aka zuba mishi yace, "a ɗauke mishi a gabansa."
Sadiq ya dauka ya mayar ya sanar musu yace, "bazai ci ba."
Iya tace, "to ko dai a dafa mishi ko fara da mai ne ya ci? Tunda shi bazai iya ci ba don na ga alamun ɗan gayu ne Mijin Meramun tamu, dama haka tafi so ƴar tselan uwa." Ta ƙare maganar tana ɓaɓɓaka dariya
Momy tace, "a'a Iya kar ki wahalar da kanki, in dai a halin SHAREEF ne ko me aka ba shi in bai yi ninya ba bazai ci ba, don haka ki ƙyale sa cikin sa ne."
Shima Dady abun da yace kenan,
Shi yasa bata da yadda zatayi haka nan ta haƙura, amma bata ji dad'i ba duk da ta ga halin sa ya bambanta da sauran ƴan uwan nasa, da gani yana da ƙyanƙyami, amma ita hakan bai dame ta ba tunda sosai ta ji dadin ganin SHAREEF din a haka, a ganin ta Maryamu tayi dacen ɗan kyakkyawar saurayi kamar yanda take faɗa, wannan ai abun nuna wa ne da kwatance, ta san Iyayenta zasu ji daɗin ganin Surukin nasu na nuna wa Sa'a.
Zuwa washe gari tunda ranan bikin ne, kuma karfe 10 za a ɗaura auren, safe nayi suka shirya suka wuce ƙauyen; har da Iya Samira ta bi su a motan su.
[05/03, 8:27 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱
__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE49*
_____Sun isa ƙauyen; su Baba na ƙofar gida shi da wasu Abokansa suna ɗan tattaunawa,
Suka ga motan ta tsaya a ƙofar gidan, dayake Baba ya san da zuwan nasu shiyasa ya nufi wurin Motan tun kafin ma su fito
Dady ya soma fitowa shi da Hanif da suke baya, sai Momy da Iya Samira waɗanda su ma duk suna back sit; sabida Motan irin Jip ɗin nan ne ƙatuwa,
Sadiq ke tuƙa su; while SHAREEF na hakimce a front sit, ya ƙi ya fito bare ma ya ɗago kansa, wayansa na hannunsa yana chart da Haseena tana faɗa mishi, "yanzu haka ta hau jirgi zasu tashi."
Bai san ma mai ake yi ba sabida su Dady suna can ana gaigaisawa; har su Yaya Naziru sun fito daga gidan
Gidan suka nufa bayan sun gama gaisuwar, Baba da Dady suka fara yin gaba su Iya suka bi bayansu
Yaya Naziru da Yaya Ashiru suka ce ma su Hanif, "su shiga cikin gidan," tunda suna gefe ne sun gaisa tamkar sun saba da juna sabida yanda suka gaisa faram-faram, duk da dama an daɗe ba a haɗu bane, musamman ma Hanif dashi da SHAREEF
Hanif ne ya kula kamar babu SHAREEF, shi ne ya juya yana duban wurin Motan before yace ma Sadiq, "ina Bro ne wai?"
Sadiq shima ya bi motan da ido yana cewa, "bai fito ba fa."
Hanif kallon su Yaya Ashiru yayi yana musu murmushi yace, "bari in kira bro sai mu shiga tare."
Su ma tsaya wa suka yi suna kallonsa ya nufi wurin Motan, duk da sun fahimci maybe SHAREEF ne Mijin Maryamun su, dukkan su sai suka zaƙu da su ganshi suna ta kallon wurin Motan
Hanif ƙwanƙwasa side din sa yayi yana jiran ya buɗe mishi
Sai lokacin ma ya dawo da hankalin sa jikinsa; ya ɗago yana duban inda Hanif yake tsaye, hannu ya sanya ya zuge glass din yana faman kallonsa fuskarsa babu wata walwala, da ido yayi masa alamun mene ne? yana tsare sa da idanun
"Ka zauna duk mun fita kai ka ƙi fitowa, ko baka san mun kawo bane?"
Yatsina face ɗin sa yayi yana ɗan juya wa ya bi inda suke da kallo, har ya sauke idanunsa kan su Yaya Ashiru da suke gefe sun kafo musu ido, kallon kallo suka yi wa junan su while tuni SHAREEF ya ɗauke idanunsa a kansu, ya wani yanƙwane fuska da furta, "and so what?"
"Ka fito mana, su Momy har sun shiga ciki, kuma ka san Dady zai tambaye ka."
Gajeren tsaki ya ja yana wani haɗe fuska
Shi kuma Hanif bai bi ta kansa ba ya sanya hannu ya buɗe masa ƙofan
Kamar bazai fita ba sai wani haɗe fuska yake yi yana sake bin garin da kallo ta cikin Motan, wai ji be ƙauyen da aka kawo su haka kawai an takura masa, to taya ya zai iya zama na mintoci a wannan bahagon garin? Wani dogon tsakin ya ja yana zuro ƙafafunsa a waje, kana ya fito cike da ƙyanƙyami yana wani hura hanci
Sadiq da ya dubi su Yaya Naziru ya ga sun zuba wa SHAREEF ido, sai ya ɗan yi murmushi yana ce musu, "ga Yayanmu nan ya fito Mijin Maryam."
Murmushi suka yi su dukkan su, duk da sun san shi amma an jima rabon su dashi, don haka ba ƙaramin sauya musu yayi ba, tabbas su kansu SHAREEF ya burge su sosai, gani suke yi kamar ya fi ƙarfin Maryamu sabida yanda suka ganshi ɗan Gaye, duk da basu da bambanci da Hanif amma SHAREEF ya fi shi wayewa da hasken fata, kuma bai da sakewar fuska koda gani yanda suka ga ya fito face ɗin sa a haɗe babu annuri yana wani hura hanci; daga gani zai yi jijji da kai ne, duk wanda ya kalle sa ma zai gane hakan
Hanif ne ma yace mishi, "ga su Nazir nan baku gaisa ba Bro."
Kallo ɗaya yayi musu ya wani ɗauke kansa yana saka hannaye a cikin aljihun wando
Naziru ne ya soma ba shi hannu yana cewa, "aslm alaikum ɗan uwa, fatan kun zo lafiya?"
Kamar bazai ba shi hannun ba don har wani jan lokaci yayi, sai kuma ya ciro hannun tare da miƙa masa suka gaisa
Ko kusa basu damu da abun da yayi musu ba tunda tun farko sun soma fahimtar