x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 18 - SHAREEF SEXY BOY BOOK 1

  • 51001 words
  • 54000 words
  • Out of 152447 words

Category: Romance Story +18

Views 387

25 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
her heart, halin da take ji a game da SHAREEF ɗin bazai iya misaltuwa ba, amma ta san cewa shi ne farin cikin ta a yanzu, komai zata iya yi domin shi. Yatsunta ta haɗa wuri ɗaya tana murɗa wa bata sake cewa komai ba, yayinda ta faɗa duniyar tunanin sa wadda lokaci guda murmushin fuskarta ya gushe, cus bata san ta ya zata iya saka soyayyarta a cikin zuciyarsa ba, tana cikin matsananciyar fargaba duk ranan da ya ƙi amince wa da ita, tana ga kamar baza ta iya rayuwa ba a lokacin, kuma a ɗan wannan kwanakin da tayi a gidan; ta ga alamun tsanarta ƙarara a fuskarsa, da yanda yake nuna mata ko kusa babu ɓurɓushin soyayyarta a zuciyarsa, illa ma ƙyama da ƙiyayya da yake nuna mata ƙarara babu ko shakkar su Momy, abun na mata ciwo, ga shi kuma kamar tana ganin raunin ta a tare da shi, tana jin kamar baza ta iya jure ƙiyayyarsa ba

Hannunta Sadiq ya rike. Hakan ne yasa ta ɗago manyan idanunta da suka ɗan canza kala, ta zuba masa su tana bin sa da kallo kamar tana neman wani abun a fuskarsa

"Mene ne Maryam? Ya na ga kamar kin canza?"

"Yaya Sadiq, gani nake yi kamar Yaya SHAREEF bazai so Ni ba, ya tsane Ni sosai fa, ban san me nayi masa ba, kuma ka ga ina yin duk abun da kace in yi, amma ba ya so na."

"Haba ke kuwa, meyasa za ki ɗaga hankalin ki a kan ƴar wannan matsalar? Halin Yaya SHAREEF ne haka, idan kika ce za ki ci gaba da damuwa za ki ja ma kanki wata matsalar ne, Yaya SHAREEF halin sa kenan, ki bi sa a sannu wata rana zai riƙa nuna miki kulawa kamar sauran ƴan gida, kar ki damu ƴar kyakykyawar ƙanwata, Clear this word and focus on studying, you will be a big girl. Har durƙusa miki zai yi wata rana."

Dariya tayi tace, "haba dai, ba dai Yaya SHAREEF ba, ai ya wuce hakan wlh."

"Ok wasa kike gani ko?"

Murmushi tayi bata iya cewa komai ba tsaban farin cikin maganar nasa

A lokacin ya karya kwana ya shiga layin makarantar nasu, sai da ya isa bakin gate ɗin ya dakatar da Motan, sannan ya dube ta yace, "yauwa Masha Allah! Mun iso, bamu yi latti ba." Ya ƙare maganar yana duban haraban wurin da ɗalibai suke ta taho wa suna shiga cikin makarantar

Itama kallon wajen tayi, sai kuma ta dube shi tana langaɓe kai da cewa, "to saura hoton."

"Kai little sister ba kya mantuwa? Oya to, gyara in yi miki." Yayi maganar yana ciro wayansa

Gyara wa tayi da sauri tana kallonsa ta tsaya ƙyam ko ƙyafta ido ba tayi

Dariya ta ba shi, sai dai bai ce komai ba ya soma ɗaukar ta hoton, guda biyu yayi mata, tayi kyau kuwa, bakin ta a washe kamar gonan adduga, shiyasa dimples ɗin ta suka bayyana suka sake ƙawata Black beauty face ɗin ta. "Wow! My dear kin yi kyau sosai, kin gani." Sai ya nuna mata pictures ɗin

Sai murna take yi da farin ciki. Then they said goodbye and she left in the car, ya ja motan ya tafi tana ɗaga mishi hannu, sai daga bisani ta shiga ciki ta bi ayarin dalibai da ta ga suna ta faman gudu zasu wuce wurin assembly,
Itama can ta nufa kasancewar ta ga ɗaliban sun taru a wurin, ta shiga wurin ta shige cikin su ba tare da ta tantance layin wanne aji bane

Basu ɗauki lokaci ba aka gama duk abin da za a gabatar musu, sannan suka basu damar wuce wa class

Since already an nuna mata ajin da zata je, don haka can ta nufa kanta tsaye,
A lokacin ma duk ƴan ajin sun gama shige wa kowa ya zauna a wurin sa suna ta hayaniya,
Raba idanu ta soma yi tana neman inda zata zauna,
Sai wata wacce ke layin farko ta hannun dama ita kaɗai, ta ɗago ido suka haɗa ido da Maryamun, murmushi tayi mata tace, "Are you new here? zo ki zauna mana."

Babu musu kuwa Maryamu ta nufe ta ta zauna a gefen ta, basu kai ga magana ba sai Auntyn su ta shigo class din,
Don haka suka yi shiru kowa ya tashi don gaishe ta

Ta amsa su tana basu umarnin zama. After kowa ya zauna sannan ta soma gabatar da abun da ya kawo ta

Ita dai Maryamu nata ido ne don ba komai take fahimta ba, dayake zallan turanci ake musu kuma kasancewar ƙwararriya ce Malamar ga shi Physics take yi, so ba ta fahimtar komai sai dalala mata waɗannan manyan idanun nata da take yi, sam ba ta gajiya da kallon Mutum in ta zuba masa ido, haka zata tsatstsare ka dasu there was no sign of fear with her,
Har Auntyn ta gama ta fice wani malamin ma ya shigo

Kwata-kwata basu samu hutu ba sai da aka kaɗa break, sannan ne fa suka samu damar magana, wacce ta bata wurin zama ta miƙa mata hannu tana murmusawa tace, "Suna na Amina Khabaeer, na ji daɗin haduwa da ke."

Hannunta ta saka a nata sannan tace, "Ni kuma Maryamu Haruna."

"Wow! Nice name, kin shiga raina, I hope we will be friends?"

Kai ta ɗaga mata bata ce komai ba

Sai Aminan tace, "ki tashi mu je break mu ɗan sha iska."

Babu musu Maryamu ta tashi tana goya Jakarta a baya, kasancewar yanda ta ga Aminan tayi itama ta ɗauki nata Jakar, kuma yawanci ƴan ajin duk ficewa suke yi da Jakar su

Hannunta ta riƙe suka fita suka nufi wurin wasa inda aka tanadar a makarantar, wurin manya daban na yara daban. Wani ɗan corridor suka samu suka zauna, Aminan ta ciro musu food flaks a jaka, ta saka musu spoon tace, "su ci."

Sai Maryamun ta girgiza kanta tana furta, "a'a, nima na zo da nawa."
Itama ta ciro Jakarta tana fito da manya-manyan biscuits da ta zo da su

"To ai naki daban nawa daban, mu ci tare please sabida bazan ji dadin ci Ni kadai ba, na saba ci da Feena amma yau bata zo ba." Ta ƙare maganar tana ɗan langaɓe kanta

Maryamu da ke duban ta tace, "wace ce Feena?"

Murmushi tayi mata tace, "Feena wacce muke zaune sit ɗaya da ita ne, ita yarinyar mai makarantar nan ne, tun last Friday ba ta zuwa cus bata da lafiya, I think ma yau zata zo sai na ji shiru, shiyasa nace ki zauna a kusa da Ni."

Shiru Maryamun tayi bata ce komai ba

Sai da Aminan ta matsa mata sai ta ci abincin, dole ta saka spoon suka ci tare, in wannan ta ci sai ta ba wannan, daga ƙarshe bayan ta gama sai itama ta bata biscuits ɗaya. Daƙyar Aminan ta amsa tayi mata godiya.
Sai da suka ji an kaɗa class sannan suka koma aji

Dayake ajin basu da wani yawa, kuma dukka Yaran masu kuɗi ne kowa ba ya shiga harkan kowa, sannan ma da rashin sabo tunda duk yawanci new students ne, shiyasa babu ruwan kowa, wasu ma basu gama sanin sunan ƴan ajin ba, Maza da Mata ne a haɗe. Layin Maza daban na Mata daban

Ita dai Maryamu har aka gama karatun bata fahimci me ake yi ba, har suka tafi break na biyu wanda suka gabatar da sallan azahar. Daga nan ne suka soma gabatar da karatun Arabia da litattafan Islamiyya, tunda makarantar tsarin su kenan, sai ƙarfe biyar ake tashi kullum ban da ranan Friday

Before a tashi ma har sun yi sabo da Amina tamkar sun san juna, tunda duk kusan Sa'anni ne haka suka saki jiki suna ta hira da dariya, ko'ina tare suke zuwa, Amina sai nuna mata wurare da dama take yi inda ya kamata ta sani,
Shi yasa Maryamu ta ɗan samu walwala a makarantar, karatu kuwa dama ba a magana tunda bata fahimta ba, ga shi ba a Hausa sai turanci da larabci, tsarin makarantar yayi mata matuƙa musamman yanda ta ganta cikin ƴaƴan masu kuɗi tsundum, dama Maryamu da rawan kai da nuna iyayi, shiyasa nan da nan ta saje da su tana nuna itama kamar ƴar masu kudin ne, domin babu wanda zai ganta yace ba daga ƙauye ta fito ba, sai ficchi da iyayi take yi, yau rana ɗaya daga zuwan ta sai da suka kusa dambe da wata yarinya

Bairo ne ya faɗi a ƙasa, sai yarinyar ta ɗauka tana ƙoƙarin saka wa a jaka. Maryamu kuma tana ƙilla ido ta ga lokacin da ta ɗauki bairon, bata tantance nata bane kawai ta ƙwace bairon tana hararan yarinyar

Ita kuma ta bi ta da kallon mamaki tana cewa, "ke lafiya za ki ƙwace min bairo?"

Wani hararan Maryamu ta maka mata tana cewa, "to ɓarausu, daga ganin bairo ya faɗi sai ki kama ki ɗauka za ki wani ƙaƙaba a Jaka? To Allah yasa na ganki balle ki ce naki ne."

"Nawa ne mana, yanzu fa na yar sai ya gangaro wurin nan na zo dauka."

"Karya kike yi wannan bairona ne, ki je wata ƙaryan ba wannan ba."

"Yau na ji ikon Allah! Ni da bairona ki ce ba nawa ba? Wlh sai kin bani."

"To zamu gani tunda uwar ki ta siyan min, daga zuwa da bairo yau har zai zama naki? A gidan uban wa ya zama naki?"

Jin zagin da Maryamun take liliyo wa, sai ƴan ajin suka saki baki suna kallonta

While Amina ta shiga tsakani tana kallon yarinyar tace, "Hafsah kin tabbatar naki ne?"

   

"Wlh nawa ne, yanzun nan ya faɗi shi ne na zo ɗauka kuma ta ƙwace."

"Kan Uba.. sannu sara mai baƙar ta kashi, na rantse da Allah ko kin fi uban wa maita a nan bazan ba ki Bairon nan ba, kaji min yarinya da shegen tsurfa a gidan uban wa Bairon zai zama naki? Bayan yanzu kika ɗauka a gefen ƙafa na? As for i, me hate lies and me hate those who make them." Tayi maganar tana tsuke ƴar ƙaramar fuskarta

Duk wurin sai suka yi shiru suna zuba mata ido da ganin ikon Allah, musamman yanda ta saka wannan shegen turancin nata. Nan fa wasu suka soma ƙumshe baki suna son yin dariya, amma kuma tsoro ya hana su saboda gani suke yi tsab Maryamun zata iya komawa kansu ganin yanda take da tsiwa sai wur-wurga idanu take yi tana fiƙi-fiƙi dasu alamun babu tsoro a tare da ita

Yayinda ita Hafsah tsaban takaici ne ya hana ta magana, ƙiris take jira tayi kuka musamman zagin da ta ji Maryamun na liliya mata

Amina ce ta kalli Maryamun, itama jikinta a sanyaye tace, "but sister ki duba Jakar ki mana, idan ba ki ga naki ba sai mu san abun yi ko?"

Maryamu duban ta tayi, sai tace, "to ai na san a nan na ciro nawa, in ba fiffike ne dashi ba taya zai koma cikin Jakana? A nan na ajiye shi tun lokacin da Teacher ɗin nan ya fita."

Shiru suka yi suna zuba mata ido babu mai magana

One of the class members, da alamun shi ne Monitor ma, sai ya dubi Maryamu yace, "ke meyasa baza ki duba Jakar naki a gani ba? Ki duba mu gani in kin saka naki."

Yatsina fuska tayi tana ɗauke kanta a kansa, sai ta sake tsuke fuskarta ta ɗage kai alamun baza tayi abun da yace ba

Cikin rarrashi Amina ta ƙara matsowa kusa da ita tana cewa, "Please Maryamu miƙa mata Bairon, ina da wani sai in ba ki."

"Allah bazan bayar ba, tunda ba ita ta siya min ba, bazan taɓa bata bairon nan ba, haka kawai daga zuwa da abu yau sai ta sace min? Tunda ɓarauniya ce ita."

Kuka Hafsah ta saka saboda jin sunan da Maryamu ta kira ta dashi

Yayinda ƴan class din su kuma suka soma hayaniya, wata da friend ɗin Hafsan ne tace, "sai ta je ta faɗa ma Uncle tunda Maryamu ta kira Hafsah da ɓarauniya."

Ana haka sai aka kaɗa bell alamun an tashi,
Miƙe wa Maryamu tayi ta tusa Bairon a Jaka tana rufe wa, sai ga wani ya faɗo daga jikinta alamun ya maƙale ne a rigan ta

Da sauri Amina ta ɗauka tana cewa, "yauwa Maryamu ga naki nan fa, kin gani ko, ga shi ya faɗo a jikin ki."

Shiru Maryamun tayi tana kallon Bairon

Ƙawar Hafsah mai suna Luwaisa tace, "ashe ke ce ma big Thief bamu sani ba? Amma kin zo kina ma mutane rashin kunya daga zuwan ki yau kin soma fitsara da rashin kunya, wlh kamar a kunnen Uncle Allah ya kaimu gobe sai mun kai ƙaran ki."

Ko kaɗan Maryamu bata nuna tsoron ta a fili ba, duk da jikinta yayi sanyi sabida yanda ta haƙiƙance tana surfa tijara, sai ga shi ita ce da laifin. Shiyasa ta jefa wa Hafsan Bairon tana cewa, "kin daɗe ba ki kai ƙaran nawa ba, inyaso kar a bar Ni da rai kin ji ko?" Ta ja tsaki tana ƙwace Baironta daga hannun Amina tare da zura wa a Jaka, ta goya Jakar a baya tana jan jiki ta wuce ba tare da ta kula kowa ba,
Duk da hayaniyar da class din suka ɗauka suna surutu a kan abun da Maryamun tayi,
Wasu kuma suna bama Hafsah haƙuri a kan abun da tayi mata, ciki kuwa har da Amina wacce take cike da mamakin Maryamun, daga zuwa yau ta soma neman rigima, ko tsoro ba ta ji a ɗauki mataki a kanta

Ita kuwa Maryamu kai tsaye hanyar fita makarantar ta nufa kamar yanda ɗaliban school ɗin suke ta tururuwan fice wa zuwa haraban wajen gate, since ba a barin Motoci su shigo ciki in har ba na teachers bane, kowa a bakin gate yake faka wa tunda akwai fili mai yalwa, sai su ɗauki yaran su daga nan,
Maryamu na fita ta hangi Motan SHAREEF a waje a fake, duk da a ranta tayi mamakin ganin Motan sak irin nasa, kuma ta tabbata shi din ne, shiyasa har ranta ta ji wani irin sanyi ya mamaye mata zuciya, lokaci ɗaya ta manta da komai da ya wakana nan farin ciki ya bayyana a kan fuskarta, da sauri ta nufi wurin a zuciyarta tana fatan a ce shi ɗin ne ba wani mai kama da Motansa ba, since ba a ganin na cikin Motan.
[01/02, 9:57 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱

      *SHAREEF*
          _SexyBoy_
🌱🌱🌱🌱🌱


_Writer: Nafisat Isma'il Lawal_
_Wattpad: UmmuDahirah_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.











__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE21*
               "Are you still here, baka tafi ba?". Shuraihu said that when he entered the office, he saw Mahmud working

Kallonsa Mahmud yayi yana faɗin, "eh har yanzu ina nan, ina son in kammala wannan lissafin ne, cus chief accountant yana jiran in tura mishi, that's why na zauna ina son in ƙarisa."

Samun wuri Shuraihu yayi ya zauna yana duban sa, tare da cewa, "There is something I want to talk about, that's why I'm following you here."

Ɗago kai Mahmud yayi yana dakata wa daga latsan computern da yake yi, tare da kallon Shuraihun yace, "ok Ina jin ka, Allah yasa lafiya?"

Smile Shuraihu yayi yace, "lafiya lau sai Alheri." Sai ya gyara zaman sa sosai a kan chair ɗin da ya zauna, tare da faɗin, "ina son ka fahimci maganata Mahmud, na san zaka ji maganar tawa ta zo maka wata iriya, amma kuma Ni a ganina ƙaruwar mu ne sosai, abun da zamu samu a Companin nan kaɗan ne da wannan aikin da zamu yi." Sai ya ɗan ja numfashi yana ƙoƙarin kamo bakin zaren ta inda zai fara sanar da Mahmud ya fahimce sa

Yayinda shima ya natsu sosai ya zuba masa ido yana jiran me zai ce

"Na san abubuwan da ke faruwa a game da wannan kwangilar da muka amsa na su Mr. Pitter, kuma ka san a halin da su Alhaji Inuwa suke ciki a game da son dole sai sun samu hannun jari a cikin companin nan, to shi ne muke so mu haɗu mu taimaka musu kamar yanda suke buƙata, they promised us more money than we will get in this job, ka san cewa dai idan mun yi aiki a wannan Companin ba wani abun kirki zamu samu ba, kawai zamu haɓaka Companin ne amma ba wai don mu ƙaru ba, shiyasa suka yi mana tayin nan mu samu mu taimaka musu aikin nan ya lalace ko kuma su samu wata shiyya a ciki, don muma mu ƙaru."

Mahmud wanda yayi kasaƙe yana kallon Sharaihu da ke koro bayani, mamaki sosai ne ya cika sa wanda yasa ya kasa magana sai buɗe baki da hanci da yayi yana bin sa da kallo kamar ya samu TV, a yanda ya fahimci maganar Sharaihun abun ya ɗaure masa kai matuƙa, bai taɓa tunanin Shuraihu yana ɗaya daga cikin waɗanda zasu ga sun durƙusar da wannan Companin don kawai son abun duniya ba, duba da yanda ya ga SHAREEF ya taimaka masa a rayuwa, abun mamakin lokaci guda Shuraihu ya zo ya samu aiki a wannan Companin aka ba shi muƙamin Manager, kuma amma wai yau da shi ake son haɗa baki domin a durƙusar da companin; after all ya san cewa muddin suka yi wannan aikin ba ƙaramin ci gaba Companin zata samu ba, kuma ba ƙaramin maƙudan kuɗi za a samu ba, zata yi suna fiye da nan ƙasa Nigeria ma, tunda aikin da zasu yi haɗaka ne da sauran ƙasashe na ƙetare. Har a cikin ransa ya ji babu dad'i da jin zancen Shuraihun, wanda yana jin cewa bazai taɓa cin amanar wannan Companin domin ya haɗa hannu da wasu don ganin bayan su ba, ko me zai samu kuwa ba ya jin zai iya taimaka wa wannan zaluncin, shiyasa ya buɗe baki yace, "MD ban taɓa tunanin waɗannan maganganun zasu fito daga bakin ka ba wlh, haba kai kuwa, ko ma me zaka samu ai ina ganin bai kai ya wannan Companin ba, kar ka manta a ƙarƙashin ta kake aiki, idan kuma ka ƙi ci gaban su mene ne amfanin zaman ka a ciki? Ai
End Ads