su Dady ta koma tana zama tare da cewa, "ga ta nan fitowa."
"Bari in je in ɗan huta a ɗaki, sabida akwai aikin da nake so in yi."
"Amma Alhaji baka ci abincin ba zaka tafi?"
"Deeja ba na jin yunwa yanzu, sai dai zuwa dare, but ki haɗa min coffee sai ki kawo min in sha."
"To Shikenan."
Shi kuma Dadyn ya wuce zuwa sama
While Momy ta kalli Sadiq tace, "Sadiq zuba abincin mana ka ci, ka dena danna wayan nan haka."
"Ok Mom." Yayi maganar yana miƙewa tare da nufan dinning ɗin, chart yake yi yana sanar da Hanif auren SHAREEF ɗin da aka ɗaura yau, yana faɗa masa, "but kar ya sanar da SHAREEF tunda Dady sai da ya gargaɗe shi."
Fitowar Maryamu daga ɗakin, shiyasa Momyn bata tafi ba, ta bi ta da kallo tana cewa, "kin yi sallan daughter?"
"Eh nayi."
"To je ki wurin Sadiq ki zauna ki ci abincin ki, ki cika cikin ki fa ba na son ganin ki da yunwa, ina zuwa."
Murmushi Maryamu tayi tace, "to Momy." Sai ta nufi wurin Sadiq ɗin da saurin ta
Ita kuma Momy ta wuce kichen
Sadiq yana ganinta ya ajiye wayan yana dariya da cewa, "ƴar ƙanwata, wannan ɗigon a goshi fa?"
Itama dariyan tayi tace, "kwalliya mana, but i forgot ban shafa hoda bane, i like ɗigon goshin."
"Wow! Kin iya turanci ashe?"
Fari tayi da ido tana tallabo kumatun ta da hannayenta dukka, sai tace, "ƙwarai kuwa, I'm sure I learn."
Dariya ne ya suɓuce masa, sai yayi kamar ta burge sa ne, yace, "wow! Wow! My dear, I'm happy fa, gaskiya kin burge Ni, to me za ki ci in zuba miki?"
Kallon plate ɗin gaban sa tayi, sai ta wani yatsina fuska tana wurga ido da cewa, "anything ma zan ci. Amma ka zuba min irin naka."
"An gama ranki ya daɗe! Matar Yaya SHAREEF." Ya furta yana ƴar dariya tare da ƙoƙarin save nata
Sai ta ɗan rage murya tana matso da fuskarta, cikin murmusawa tace, "wai Yaya Sadiq, ina Mijin nawa yake? Na ga har yanzu ban ganshi bane, zan so in ganshi wlh."
"Oh! Kar ki damu, yanzu za ki ga ya dawo ma, time ɗin tashin sa a wurin aiki yayi, za ki ga ya shigo." Sai ya nuna mata hotunan da suke can bangon falon yace, "kin ganshi can Yaya SHAREEF ɗin."
A kan pictures ɗin su, su uku idanunta suka sauka, sai kuma ta kalle shi tace, "wanne daga ciki? Na ga duk kuna kama?"
"Wancan mana, wanda yayi murmushi kaɗan na hannun dama."
Baki ta washe tsaban murna, sai kuma tace, "wlh ya haɗu shima, kenan wannan shi ne Mijina Yaya Sadiq?" Tayi maganar tana dawo da idanunta a kansa
Murmushi yayi yace, "eh mana Maryam, Yaya SHAREEF kenan, shi ne babban Yayanmu, sai Yaya Hanif, but yanzu yana school a ƙasar waje, in ya dawo zaku haɗu ai."
Farin ciki ya cika Maryamu sai kallon fuskar SHAREEF take yi
"To ki ci abincin mana kar yayi sanyi."
"Wlh mamaki nake yi Yaya Sadiq, wai a ce wannan Baturen ne Mijin dana aura. Ashe gaskiya Nima mai Sa'a ce, yana da kyau sosai, ban taɓa ganin mai kyau irin sa ba wlh, har ya shiga raina nima ina son sa sosai."
Ganin yanda take maganar cikin gaskiyar ta, sai yace, "ai ke ma mai kyau ce Maryam, ko ba ki taɓa jin an ce miki kina da kyau bane? Musamman in kika yi murmushi dimples ɗin nan naki suka fito irin na Yaya SHAREEF, suna ƙara miki kyau, ga manyan idanu kamar irin na Momy."
Dariya tayi tace, "ai haka ƴan ƙauyen mu suke cewa, shiyasa nake tsula tsiyata wlh, na ƙi kowa sai ɗan birni mai waye wa."
"Sai ga shi kin samu kuwa." Ya faɗa yana dariya. Itama tana taya sa
Lokacin Momy ta fito daga kichen ɗin, tana cewa, "wai abincin kuke ci kuwa ko surutu? Ka zuba mata abincin Sadiq?"
"Eh Momy, ga shi nan zata ci."
"Ok to, bari in kai ma Dadyn ku coffee, Maryam ga Yayanki nan sai ku zauna tare ina zuwa."
"To Momy."
Tana tafiya sai Sadiq yace, "ki ci abincin mana ki dena surutu."
Dariya tayi, sai kuma ta saka cokalin ta soma cin abincin cike da farin ciki, tana yi tana kallon fuskar SHAREEF cike da wani irin tsagwaron annashuwa. Zuciyarta fari ƙal sabida ganin wane ne Mijin nata, ai ta more kuwa in dai wannan ne Mijinta, lokaci ɗaya ta ji ta kamu da sonsa har a cikin zuciyarta, irin Mijin da take mafarkin samu sai ga shi Allah ya bata, haƙiƙa Allah na sonta, to amma shi zai so ta? Allah yasa ya so ta shima kamar yanda take jin ƙaunar sa ya ɗarsu a cikin ƙalbin ta, babu mai raba su wlh.
[20/01, 8:16 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱
__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE12*
Daga hall da suka yi taro suka fito, kai tsaye hanyar office ya nufa cikin takunsa na ƙasaita a kuma natse. PA ɗin sa na biye da shi a baya har zuwa cikin office din sa
Shigan sa office din, sai ya kai duban sa kan agogon hannunsa yana jan tsaki, ganin har 7 ta kusa, kallon PA ɗin yayi, wanda yake ajiye masa documents a saman table. Guntun tsakin ya sake ja, cike da sanyin muryan sa yace, "What time will we have the meeting tomorrow?"
"Sir, by ten ne."
"Shikenan ku yi magana da Shuraihu a kan kayan nan, and ka sanar da Mr. Pitter by tomorrow zamu shiga meeting din."
"Ok sir, I will let him know."
Bai ce mishi komai ba ya matso bakin table ɗin, yana ɗaukar bairo ya buɗe da nufin yin sing
Shi yasa nan da nan PA ya buɗe mishi ɗaya daga cikin document din yayi sing a ciki. Yana gama wa sai ya rufe yayi masa sallama ya fice
Shi kuma SHAREEF ya tattara kayansa tare da ɗaukar ƙaramar jakarsa ya fito
Da sauri PA ya zo zai amshi jakar hannun nasa
"No leave it." Ya furta a yatsine yana yin gaba da saurin sa after ya jefa masa keys na office din sa. Kai tsaye bakin motan sa ya nufa ya buɗe ya jefa jakar, ya shiga ya ja cikin sauri sabida gaba ɗaya ya gama gajiya, yau bai tashi da wuri ba ga shi har 7 ya kusa, tun karfe 4 suke meeting a kan haɗakar kwangilar da zasu amsa da wasu Companonin, a kwanakin nan duk meeting suke yi sabida yanda zasu tafiyar da tsarin, gobe ma haka duk zasu haɗu da sauran Companyn da zasu yi haɗaka su tsayar da magana ɗaya. So yau kansa yayi zafi sosai shiyasa ko wani abu bai nema ya saka a cikin sa ba illa ruwa, shiyasa ransa duk a jagule yake
Yana isa bakin gate ɗin su, ya danna horn da ƙarfi kamar zai tashi gidan, akai-akai yake danna wa cikin sauri
In a hurry Mai gadi ya zuge mishi gate, sai ya ja motan a guje zuwa packing space. Bai ɓata lokaci ba ya fito daga motan riƙe da jakarsa yayi hanyar gidan. Kamar yanda ya saba yau ma bai yi sallama ba, tunda ba sabon shi bane sai ya ga dama, ko kuma yayi a ciki-ciki, yau kuma yanda yake jin sa a tsananin gajiye ya ƙosa ya huta. Yana shiga idanunsa suka sauka a kan su Maryamu da ke zaune a falon; ita da Sadiq suna ta hira suna dariya. Ɗan tsaya wa yayi yana kallon fuskar Maryamun cike da mamakin ganin baƙuwar fuska a gidan, ganin yanda take bin sa da kallon itama ko ƙyafta ido ba ta yi, sai ya turɓune fuska yana takowa zuwa ciki
Sadiq yace, "sannu da zuwa Yaya."
Kallon Sadiq ɗin yayi, kamar zai yi magana kuma sai ya dauke kansa ya sake mayar wa kan Maryamu. Da mamakin sa sai kuma ya ga ta washe mishi haƙora
"Sannu da zuwa Yaya SHAREEF." Ta furta cikin murna tana ɓashe baki, sai dimples ɗin ta dukka suka bayyana fili suka kara wa Black beauty face ɗin ta kyawu
"Wannan kuma daga ina?" Ya furta yana yatsina fuska
"Yaya, Maryam ce, tare muka taho da ita ƴar kanwar Dady ne."
"Oh God! what kind of frustrating is this? What will she do for us at home; and you bring her?" Sai ya ja tsaki yana yin gaba cikin sauri, har yana haɗa wa da gudu a kan matattaƙalan benen
Da kallo Maryamu ta bi bayansa dashi cikin farin ciki, har ya ƙule ta kasa ɗauke ido a kansa sabida yanda take jin tamkar ta bi bayansa, ya mugun tafiya da ruhin ta musamman yanda ta ga yana magana cikin aji da tsantsan wayewa, muryansa mai matuƙar sanyi da daɗin sauraro
Taɓo ta Sadiq yayi yace, "ai ya tafi ko?"
Kallon Sadiq ɗin tayi, sai kuma ta rufe idonta cikin kunya tace, "har ka bani kunya wlh, ban san ina kallonsa ba fa."
Dariya Sadiq yayi yace, "ikon Allah!"
"Amma fa ya haɗu Yaya Sadiq, ya fi kyau ma a fili, kuma ka ga ban san me yace ba ma da turancin."
Jin hakan sai Sadiq ya sake murmusa wa tare da cewa, "ba da ke yake yi ba ai."
Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta ɗan ɓata fuska da cewa, "yanzu shikenan bazan faɗa masa Ni Matarsa bace? Yanzu bai san Ni Matarsa bace ba ko?"
"Eh, kin san me Dady yace ai, kar ki sanar mishi kinji ko? But da alamu kina sonsa Because I see that in your eyes?"
Kanta ta ɗaga tana yin fuskar tausayi
"Yauwa sai ki dage ke ma ki saka sonki a zuciyarsa, hakan ne zai sa kawai Yaya SHAREEF ya riƙa kallonki yana kula ki, domin shi ba irin halin ƴan gidan nan ne dashi ba, yana da wuyan sha'ani, da sannu za ki fahimci ko wane ne shi kinga sai ki riƙa kiyaye abun da ba ya so kin ji?"
Dariya tayi tace, "to Yaya Sadiq, ai nima ka ce ina da kyau, kuma Nima na san haka, baka ga daga shigowar sa ba yana ta kallona ba? Shima ya ga na burge sa ne, ya ga ina da irin wannan lotsawar na kumatun sa, bare in na zama ƴar birni ina saka kaya masu kyau da tsada." Sai ta kaɗa harshen ta da cewa, "ka bari ka ga yanda zan nuna mishi kalan tawa soyayyar, shima sai ya riƙa bi na kamar sauran Samarina na ƙauye."
Kumatu Sadiq ya tallabo yana bin ta da kallo yana dariya, da alamu ya lura yarinyar tana da wauta da ƙauyanci irin na ƴan ƙauye. sai kuma yace, "I know za ki iya ai, Mijinki ne dama ya kamata ki yi ko mene ne, Ni nan zan ba ki satar amsa a kan abubuwan da yake so da wanda bai so, amma yanzu kinga time na sallan magriba ta gabato, Let me tell you some other time."
Kaɗa masa kai tayi duk da bata fahimci mai yace a karshen ba
Sai ya miƙe yace mata, "bari ya je dakinsa zai yi alwala ne, idan Momy ta fito yana ɗaki." Sai ya kunna mata kallo yace, "ki yi kallo ya ɗebe miki kewa before a kira sallan ke ma sai ki je ki yi ko?"
"To Yaya Sadiq." Ta amsa mishi tana kallon TVn
While shi kuma ya wuce saman benen.
***
Momy kuma da takai ma Dady coffee din, lokacin har ya gama waya da su Baban Maryamu, har Iya Samira ya kira sun gaisa ya sanar mata, "sun sauka lafiya." Ya sauke wayan kenan Momy ta shigo. Shine yake sanar mata, "ya kira Zaria ne ya faɗa musu sun sauka lafiya, sun ce a gaishe ta."
Sai da ta zauna sannan ta amsa, tana cewa, "ai da ya bari ta zo sun gaisa tunda bata samu damar zuwa ba."
Dady yace, "kuma kinga shaf na manta, dayake ƙanwata Hafsah ita ta soma kira shiyasa, amma zuwa gobe sai ki kira su ku gaisa ki bama Maryam itama."
Momy tace, "to Allah ya kaimu.",
A nan kuma ta sauya alaƙar maganar nata da tambayar sa, "meyasa bazai bari Maryamu ta tare tun yanzu ba tunda yarinyar ba wata ƙarama bace sosai? Ta ishi SHAREEF su zauna lafiya a haka, saboda maganar ma Doctor da ya faɗa musu hakan zai fi, kar kuma a zo abun ya ci gaba daga baya ya fi ƙarfin sa ya faɗa halaka."
Numfashi Dady ya ja bayan da ya ajiye coffee din da ya kurɓa, tare da cewa, "nima nayi tunanin hakan, but kinga duk da haka Maryam ƙaramar yarinya ce, just she's 15years, kuma tana da son karatu sosai na kula da hakan, abun da yasa ma ta yarda ta biyo mu kenan, shi kuma auren da aka yi mata don Mahaifinta ya fi ƙaunar ta tafi da auren ta ne that's the reason da na yanke wannan hukuncin, duba da yanda doctor ya faɗa mana matsalar da ke damun SHAREEF, ba hakan kuma zai sa mu tauye wa yarinyar haƙƙin ta bane, Ni ina ga ta zauna a wurin mu ta soma fahimtar rayuwa da abun da ya kamata da ita before a kaita ɗakin Miji, yana da kyau ta samu ilmi since kinga yanda SHAREEF yake, zai iya bamu matsala musamman idan ya ganta ƴar ƙauye ce, kin san halin sa tunda mu muke zaune da shi, don haka gwara ta soma zama da mu for some time, ke ma ki riƙa koya mata wasu abubuwan da kuma abun da SHAREEF yake so, and kina kula da shi shima yanda ya ɗauki yarinyar, in kinga akwai kyakkyawar fahimta a tsakanin su fine, zamu iya ba shi Matarsa su zauna a gidan nan, before zuwa wani lokacin sai ya zaɓa gida daga cikin gidajena su koma."
Murmushi Momy tayi da cewa, "shawara mai kyau Dadyn mu."
Hakan ne yasa shima Dadyn yin murmushi yace, "yana da kyau ke ma ki bada taki gudummawar fa."
"Insha Allah, kar ka damu, Maryam ai ƴata ce, kuma a yanda nake neman ɗiya Mace Allah bai bani ba, sai ga ta a yanzu na same ta cikin sauƙi, dole zan riƙe ta kamar Ni na haife ta, don haka zuwa gobe ma zamu shiga kasuwa sai nayi mata siyayya, fatan mu dai Allah ya haɗa soyayyar su abun farin cikin kenan."
"To ai jini ba wasa ba, ko babu komai Maryam jinin sa ne bazai taɓa ƙin ta ba, nima ina ga zuwa jibi zan sa SHAREEF ɗin ya kaita school ɗin Doctor a yi mata komai a can, inyaso zuwa Monday ta fara karatu, zan kira Doctor ɗin ma muyi magana cuz makarantar ya fi min, ana koyarwa sosai, kuma kinga har da islamiyya a can."
"Lallai ƴata ƴar gata ce, I enjoyed this topic, Allah yasa hakan shi ya fi alkhairi."
Dady ya amsa mata cikin fara'a yana ƙoƙarin rufe jaridan hannunsa, sabida jin ana kiran sallah
Ita kuma sai ta dauki farantin da ta daura masa coffee a sama, duk da bai shanye ba kurɓa biyu kacal yayi, sai ta fice dashi a ɗakin ganin yace mata, "bari ya shiga toilet yayi alwala, ta wuce dashi kawai ya gama."
Tana sauka ƙasa ta ga Maryamu kwance a kan kujerar tana ta kallo, "ah ah daughter, ke kaɗai ce? Ina Sadiq ɗin ya tafi?"
Da sauri Maryamun ta tashi zaune, tana kallon Momyn da cewa, "Momy ya shiga ɗaki zai je yin alwala."
"To shikenan, ke ma taso ki je kiyi sallan tunda an kira, ki je ɗakin naki da na nuna miki ki yi sallan a can."
Tashi Maryamun tayi after ta amsa mata, sai ta nufi ɗakin da saurin ta
While Momy ta bi ta da kallo tana murmusawa, sai kuma ta juya ta nufi kitchen zuciyarta tana bijiro mata wasu tunanin na daban.
*** ***
Tunda ya shiga ɗaki, kwanciya yayi a saman gadon ko cumbas ɗin ƙafafunsa ya kasa cire wa, idanunsa a lumshe sai sauke ajiyar zuciya yake. Ya ɗauki good 10mint a haka before ya ɗago yana faman yatsina fuska da taɓe baki, alamun gajiya ce tsantsa da yunwa da ya ci ya cinye sa, shiyasa har yana jin gefen cikin sa ya soma ƙulle wa yana mishi ciwo kaɗan-kaɗan. Hakan ne yasa yayi ƙarfin halin soma yunkurin zare cumbas ɗin daga ƙafafun sa, sai da ya cire su gaba ɗaya sannan ya zuge necktie na wuyan sa ya zazzago da shi, sai da ya kwance agogon hannunsa sannan ya cire suit ɗin yana mike wa ya nufi toilet, takalman da ke bakin ƙofan ya zura a Zara-zaran ƙafafuwan sa farare ƙal kamar zasu tsillo jini don haske da tsafta, ya shiga cikin toilet ɗin ya soma kwarara ruwa daga saman sa har ƙasa batare da ya cire sauran rigunan jikinsa ba, sai da ya jiƙa kansa da ruwan sanyi ya ji sanyi ya ratsa mishi ƙwaƙwalwa da jikinsa, wanda har tsigan jikinsa tashi suke yi tsaban sanyin ruwan, yayinda shi kuma sai faman cije laɓɓa yake yi idanunsa a lumshe. Ya ɗauki like 5mint a haka before ya tuɓe ya silla wanka kamar zai canza halitta, ko kaɗan bai damu da lokacin Sallah da ta shiga ba. Sai da ya gama tsab sannan ya yi alwala ya fito ɗaure da towel, ɗaya kuma a kansa yana goge suman kansa. A bakin mirror ya dakata yana kallon kansa yana goge jikinsa, sai da ya tabbatar ya tsane jikinsa sannan ya ɗibi lotion a hannunsa ya soma shafa wa, after ya gama ya feshe lungu da saƙo na jikinsa da turaren jiki masu sanyin ƙamshi. Ya ɓata lokaci yana abu ɗaya wajen gyara suman kansa tare da ƙalƙale jikinsa kamar bazai taka ƙasa ba, don ma wai cikin sauri yake yin komai kasancewar ya ji har an fito sallah, shiyasa ya dakata ya koma ya ciro farar jallabiya ya saka a jikinsa, itama ya feshe ta da turaren sa me shegen ƙamshi, wanda ta game ɗakin gaba ɗaya, komai nasa irin ƙamshin ne already ya bi jikinsa da komai nasa, sai da