idan kana so kayi alfahari shi ne ka taimaki wurin da ka san kana samun gumin ka, a ce sun fi kowa ci gaba; ba wai ka bada goyan bayan durƙushe su ba."
Shuraihu dariya ya ɗan yi kaɗan yana cewa, "to ban da abun ka Mahmud ina ci gaba a nan? Ina maka zancen miliyoyin kuɗi ne fa wanda zamu samu a wannan aikin in mun taimaka musu su ma sun samu, kana ganin a nan zamu samu ne? Iyakan fa a biya mu albashin mu ne shikenan fa, ka ga idan zaka yi aikin nan kawai ka faɗa min mu san abun yi, tunda sai da taimakon ka zamu samu biyan buƙata cikin sauƙi, 15 millions dollars suka yi maka alƙawari in har zaka bamu haɗin kai."
Girgiza kansa ya soma yi tare da furta, "never, baza a yi wannan cin amanar da Ni ba, bazan iya taimaka wa ba MD."
"Baza ka iya taimaka wa ba?" Shuraihu ya maimaita zancen nasa cike da tsantsan mamakin jin furucin sa, tunda a tunanin sa da ya ji kuɗin da zai samu zai iya bayar da haɗin kai
Shi kuma sai ya ba shi tabbaci da cewa, "ƙwarai kuwa, bazan iya ba, a inda Allah ya ajiye Ni a nan zan zauna, tamkar cin amana ne wannan, bayan ka san cewa wannan Companin su suke da alhakin gudanar da ayyukan nan, amma kuma don son zuciya a ce mun ɓata komai domin wasu su samu? Ai nima ina son ci gaban wurin aiki na, bazai yiwu ba tunda ba dasu nake aiki ba, a nan nake aiki, don haka bazan so ganin durƙushewan ma'aikatan nan ba."
Shiru Shuraihu yayi yana mai mamakin maganganun Mahmud ɗin, ya san cewa shi ne Supervisor na companin gaba ɗaya, wanda sai da sahalewar sa ake shigowa da kaya kuma a fita da su, shi ne ja-gaba da in har suka saka shi a tafiyar nan, komai zai zo musu da sauƙi, zasu iya ɓata shirin ma'aikatan; su gurɓata ayyukan, amma kuma ga shi ya nuna bai amince musu ba
Mahmud wanda ya mayar da kansa ya ci gaba da latsa computern nasa, ba tare da ya sake bi ta kan Shuraihu ba, sai dai a ransa yana tunanin zancen Shuraihun da ya tsaya mishi a rai
Mike wa yayi yace, "Let me pass, but think again Mahmud, you still have a chance if you agree."
Ɗago kai yayi ya ɗan tsira masa ido, but bai ce mishi komai ba har ya fice yana faman bin sa da kallo, sai da ya rufe ƙofan before ya ja numfashi yana girgiza kansa, dole yayi wani abu a kai, tabbas bazai taɓa yarda su ci galaba a kan Companin nan ba, dole ne ya sanar da SHAREEF halin da ake ciki, amma kuma ba wai sanarwar bane, ta yanda SHAREEF zai amince da maganar yake tunani, tunda ya san yanda SHAREEF ya ɗauki Shuraihu a wannan ma'aikatan, suna ɗasawa sosai, kuma ya yarda da shi matuƙa, shi kansa yana mamakin meyasa Shuraihu yake son cin amanar SHAREEF ne, amma ko mene ne dole ya san abun yi, dole su canza taku a kan wannan aikin nasu, ya kamata ya san ta ina zai ɓullo.
***
Shi kansa Shuraihu ya shiga zullumi da tunanin abun da zai biyo baya kasancewar Mahmud bai basu goyon baya ba, tunda bai taɓa tunanin hakan ba, ga shi yanzu ya bayyana mishi ƙudurin su kuma ya ƙi basu go ahead, fargaban sa idan kuma ya sanar da SHAREEF ɗin fa? Wannan fa babban ganganci ne, idan ya sanar mishi tamkar ya gama rusa mishi mafarkin sa ne, shikenan zai rasa aikin sa, SHAREEF dole zai kore sa, ya ga samu ya ga rashi kenan, shi bai samu kuɗin su Alhaji Inuwa ba, sannan kuma ya rasa babban aikin sa, me zai yi? Hankalin sa ya tashi fa, don haka ya koma office ɗin sa ya kira numban Alhaji Inuwa ya zayyane mishi halin da ake ciki
Shi kansa ya ruɗe kuma ya shiga damuwa, "yanzu ya kake ganin zamu yi?"
"Gaskiya akwai matsala Alhaji, tunda har ya ƙi amince wa kuma ga shi ya san sirrin mu, duk abun da ya biyo baya dole mu zai zarga, kuma na tabbata Mahmud ba lallai ya bar zancen a iya cikin sa ba, dole zai fesar wa SHAREEF ya san halin da ake ciki."
"To in haka ne zamu ƙara mishi kuɗin ko zai amince mana, kayi masa tayin 20 millions domin samun amincewar sa."
Shiru Shuraihu yayi yana tunanin anya Mahmud zai amince? Amma sai yace, "shikenan Alhaji, ko me ke akwai zan sake tuntuɓar ku."
"And if he doesn't agree, then we know what to do."
"Ok Sir."
Daga nan yayi sallama da shi ya kashe wayan, tare da soma sintiri a cikin office ɗin nasa yana yi yana cizan yatsa.
🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆
Direct wurin Motan Maryamu ta nufa zuciyarta na ɗan bugawa da ƙarfi, duk da farin ciki da zumudin saka ran ganin SHAREEF ne ba wani ba. Ita dai a sanin ta wannan ne Motan da yake hawa, shiyasa da ta isa bakin motan sai ta saka hannu ta buɗe back door, nan idanunta suka sauka a kansa yana zaune ya ɗaura earphone a kunnen sa, babu hula a kansa sai wannan askin nasa mai tarin gashi a gaban ya sha gyara yayi baƙi siɗik, jikinsa sanye da white suite, komai na jikinsa whit color ne, inda ya ɗaura kansa a jikin kujerar ya lafe sosai kansa a sama idanu a lumshe
Jin an buɗe Motan; shi ne dalilin da yasa ya buɗe ɗan madaidaitan idanunsa da suke fari tarr gunun sha'awa. Ko kaɗan bai juyo ya kalli inda Maryamu take tsaye ba saboda ya san cewa bazai wuce ita ɗin bace, ba ya buƙatar kallon bak'ar fuskarta shiyasa ya tayar da Motan
Hakan ne yasa Maryamu tayi saurin shige wa ciki jikinta yana rawa, bata yi gigin zama mishi a kujera ba since he warned her from the beginning. A ƙasa ta zauna ta manne fuskarta a jikin kujerar gaban tana faman leƙan fuskarsa, zuciyarta na mata wani irin sanyi wanda take ji har can cikin ƙasan zuciyarta, a hankali duk wani kasala da damuwa ya soma gushe mata, ba ta ganin komai sai fuskar SHAREEF wanda take mata ƙawa da saka ta a nishaɗi da manta inda take a duniya, tunda ta kafa mishi ido bata ɗauke su a kansa ba sai faman haɗiyar yawu take yi tana lumshe ido kamar mai jin barci
Wanda shi SHAREEF bai san a halin da take ciki ba, domin tunda ya taka motan ya soma tafiya sai ya ƙure ƙaran waƙar da ya sa; yana kaɗa kansa a hankali, tare da son gusar da ɓacin ransa da ke cikin zuciyarsa, har a ransa haushi da takaicin dauko yarinyar yake yi, wanda daƙyar Dady ya tilasta mishi a kan dole sai ya dauko ta, shiyasa yake jin ɓacin rai a zuciyarsa, dalilin da yasa ya ɗaura earphone a kunnensa kenan yana sauraron waƙar da zai kwantar masa da hankali don manta halin da yake ciki. A cikin ƙanƙanin lokaci ya iso gida sabida gudun da ya sharara a kan kwalta. Ana buɗe masa gate ya harba motan ciki zuwa packing space. Dakatar da Motan yayi yana faman ajiyan zuciya a hankali, tare da lumshe idanunsa yana cije leɓe yana jiran yarinyar ta fita sannan shima ya fita
A sa'ilin itama Maryamu ta dawo hayyacin ta, bata san cewa an kawo ba sai da ta kalli haraban gidan; ta ga a inda suke. Sannan ne fa ta saka hannu tana buɗe motan da sauri ta fice, har tana sake waigen sa sannan ta rufe ƙofan, ta wuce cikin gidan tana harɗe ƙafafu kamar zata kifa don gajiya da nauyin Jakar da ke bayanta,
Tana shiga Falon babu kowa shiyasa kai tsaye ta wuce ɗakin ta, tare da zare Jakar daga bayanta tun kafin ta kai, sabida ba ƙaramin azaba kafaɗun ta suke mata ba tunda bata saba da wannan jibgegiyar Jakar da aka cika mata da Littafai ba
Tun fitan ta shi kuma SHAREEF ya ƙi fitowa a Motan bare ya buɗe idanunsa, sai da ya tabbatar ta daɗe da fice wa sannan ya buɗe ido ya zare earphone ɗin daga kunnen sa, wayansa ya cire yana buɗe Motan ya saka ƙafafuwan sa a waje, before ya zaro jikinsa ya fito gaba ɗaya yana riƙe da Jakar aikin sa, wayansa kuma a hannu ya nufi cikin gidan kansa tsaye, inda fuskarsa kaɗai zata nuna iya tsananin gajiyan da ya kwaso
Shigansa cikin Falon yayi dai-dai da fitowar Momy daga ɗakin ta; ta biyo steps tana sauko wa. Doguwar riga ce a jikinta mai sauƙin nauyi fara ƙal da ɗige-ɗigen kore, ƙafafunta sanye da slippers; kanta kuma ta ɗaura baƙin ɗankwali. Idanunta ta sauke a kan SHAREEF ɗin tana kallonsa ba tare da ta furta komai ba
Shima idanunsa a kanta yana ɗan narke ido tare da nufan inda take. "Mom barka." Ya furta sa'ilin da ya iso kusa da ita yana ɗan kawar da kansa daga kallon da take mishi
Ita kuma kallon tuhuma take mishi tare da cewa, "ban ji sallaman ka ba?"
"Mom nayi da na shigo."
Hararansa tayi tace, "kai ɗin? Dama ban san hali bane, ai da kayi tun daga nan zan ji."
"Mommy." Ya furta yana narke fuska ya kasa kallon cikin idonta
"Ka dena kira na tunda ba ka jin magana, baza ka dena wannan ɗabi'ar ba, sallama ya gagari ɗan musulmi bayan sarai ba ciwon baki kake yi ba, muryan da zaka ɗaga kawai ka buga sallama kowa ya ji amma kana ganin asara?" Sai ta ja tsaki cike da ɓacin rai
Sanyi jikin SHAREEF yayi, but ya gaza ɗago kai ya kalle ta sabida ba ya son su haɗa ido da ita
Wuce wa tayi zata nufi kichen, har ta gota sa sannan tace, "ina fatan ka ɗauko Maryam daga school?"
"Eh na ɗauko ta." Ya amsa yana bin bayanta da kallo
Bata ce mishi komai ba ta wuce kichen kai tsaye
Shi kuma sai ya kasa tafiya sabida yanda Momyn ta nuna masa, ya san ranta ya ɓaci, sai da ya ɗan ja lokaci a tsaye a wurin sannan ya wuce ɗakin sa since ya gaji sosai, wanka yake so yayi ya samu relief. Shiyasa yana shiga ya soma kwaɓe kayan sa ya faɗa wanka.
***
Maryamu kuwa tunda ta shiga ɗakin ta sai ta jefa Jakar a kan gadon ta, tare da hawa kai ta zauna tana sauke numfashin wahala, sai a yanzu ta ji wata muguwar yunwa tana ƙwaƙulan ta, miƙe wa tayi ta cire kayan jikinta dukka ta zuba a saman gadon, sannan ta duba closet ɗinta ta ciro Riga da wando ƴan kanti ta saka a jikinta bayan ta saka under dress. Kayan masu taushi ne kalan peach, sai rigan da aka yi mishi kwalliyan saƙar farar zare, kamar aiki a gaba ɗaya gaban rigan, kayan suna da kyau da tsada shiyasa suka yi mata kyau itama,
Hula ta ɗaura a cinkus ɗin gashin ta da bai samun gyara bare kitso, sai ta fita da sauri ko takalma babu a ƙafanta ta nufi Falo,
Har ta kalli dining kuma sai ta wuce kichen sabida jin ɓuruntu a ciki
Kamar yanda tayi tsammani kuwa Momy ne a ciki tana aikace-aikace zata ɗaura abincin dare,
Tana shigowa itama Momyn ta ɗago tana kallonta, fuskarta da yalwan murmushi tace, "ah ƴan makarantar Bokoko, har kin dawo ashe?"
Murmushi itama Maryamun tayi cike da farin ciki tace, "eh Momy, sannu da aiki."
"Yauwa, ya karatun? Ina fata an mayar da hankali sosai?"
Ɗaga kanta tayi tana murmusawa
"Masha Allah, yanzu ki je kan dining ki zuba abincin yana can."
"To." Ta amsa tana ƙoƙarin juya wa ta fice
Momy tace, "ina takalman ki kika fito haka nan?"
Tsaya wa tayi tana juya wa ga Momyn, sai kuma ta kalli ƙafanta tare da bata amsa da faɗin, "Momy na bar su a ɗaki."
"Kar in ƙara ganin kin fito babu takalma kin ji ko? Ko sanyin teyes ma ai zai dame ki, ki fara zuwa ki saka takalman first before ki dawo."
Cikin girmamawa ta amsa wa Momyn tana juya wa da sauri ta fice. Kai tsaye dakin ta koma ta ɗauki slippers ta zura a ƙafafunta, kana ta wuce saman dining ta zauna tana buɗe babban coolern da ke wurin, shinkafa mai man gyaɗa ne da wake a ciki, kaɗan ne ma a ciki don ya kusa ƙare wa. Sai ta ɗauki plate ta shaƙe shi da abincin, sannan ta zuba salad a sama ta saka spoon ta soma haɗiya cikin sauri; sabida yunwar da ke addabar ta, ga daɗin abincin da yake motsa mata har kunne tsaban yanda testing ɗin yake kai mata,
Kamar daga sama ta hango SHAREEF yana sauko wa daga matattaƙalan benen, lokacin dai-dai ta saka wani ƙaton loma suka haɗa ido dashi,
Lokaci ɗaya ta shaƙe sabida wata uwar harara da ya jefa mata idanunta na shiga cikin nasa,
Lokaci ɗaya ta kasa riƙe kanta, nan da nan ta ƙware da abincin kamar zata shiƙa, har hawaye sun taru mata a idanun sun kaɗa sun yi ja, daƙyar ta haɗiye tana ɗaukar ruwa ta soma kwankwaɗa
SHAREEF tun wannan kallon da yayi mata ya ɗauke ido a kanta, yayinda haushi da tsanar yarinyar ya sake diran masa a rai musamman yanda ya ga tana zuba wannan uban loman. Lokaci ɗaya ya saki wani siririn tsaki yana wuce wa kichen cike da takunsa na isa kamar bazai yi ba. Sanye yake da three quartern wando pencil maroon color, sai farar t.shirt mai gajeren hannu da ta matse shi gam ta fito masa da surar jikinsa, ƙafansa kuma sanye da wasu slippers masu shegen taushi baƙaƙe,
Ya zura kai cikin kichen ɗin yana kallon Momy. A hankali ya furta, "sannu da aiki Momy."
Itama tuni ta san da zuwan shi tunda turaren sa mai shegen ƙamshi da shiga ƙwaƙwalwa ya gama baibaye ilahirin kichen ɗin. Amsa mishi tayi ba tare da ta ɗago ta kalle shi ba
Ganin haka yasa ya gane har yanzu tana fushi dashi ne, a hankali cikin sanyin muryan sa yace, "Mom I'm sorry."
"For what?"
Shiru yayi ya kasa magana sai kallonta yake yi
"Ka je ka zuba abinci ka ci, kayi min rumfa a nan ba na samun iska."
"Mom..."
"Mene ne?" Ta faɗa tana tsare shi da waɗannan manya-manyan idanunta da suke shiga jikinsa sosai
A hankali ya sauke ƙwayar idanunsa a ƙasa yana cewa, "Dady fa?"
Sai da ta ɗan ja seconni tuni ta mayar da hankalin ta a kan yankan albasan da take yi, ta ba shi amsa da faɗin, "ka duba sa ɗakin sa."
"Momy wlh nayi sallama dazu, nayi a zuciya ne kiyi haƙuri."
"Tunda ka ce baza ka ji maganata ba ba shikenan ba? Ka tafi Please kana ɓata min lokaci a nan."
Juya wa yayi ya fice cike da sanyin jiki. Yana fita ya sake haɗa ido da Maryamu wacce har yanzu tura abincin a baki take yi, sai dai a yanzu ta rage cin abincin da sauri; tana ci ne a natse gudun kar ya sake kama ta tana wannan uban loman, don ita kanta ta ji kunyar kama ta da yayi,
Yawu ya haɗiye yana ɗauke kansa, tare da ɗaure fuskarsa tamau ya nufi wurin fridge kai tsaye. Kwalin Holandia ya zura hannu ya ɗauka sannan ya juya ya haye saman
Maryamu ta bi sa da kallo kamar zata haɗiye shi, sai da ya ƙule sannan ta samu damar sauke ajiyan zuciya tana ƙarisa cin abincin, kafin ta tashi ta koma kichen
Momy tace, "har kin gama?"
"Eh Momy."
"SHAREEF yana wurin ne ko ya tafi?"
"Ai bai zauna ba, ya dauki kwalin Holandia a fridge sai ya hau sama."
"Ok, je ki tattaro min kayan wurin; ki zo ki wanke su."
"To Momy." Ta furta tana bin umarnin ta ta fice, kai tsaye kayan ta kwaso ta dawo kichen ɗin ta soma wanke-wanke,
Bayan ta gama suka ƙarisa girkin da Momy sannan suka kai saman dining suka jera
Lokacin ma an kira Magriba shiyasa Momy tayi mata umarnin, "ta je tayi sallah."
Tana tafiya Sadiq ya fito daga daki, shima yayi alwalan ne yana ƙoƙarin warware hannun rigan sa da ya nannaɗe
Duban sa Momy tayi tace, "sai yanzu ka tashi barcin kenan?"
Langaɓe kai yayi yace, "No Momy, na jima da tashi fa."
"Eh na ga alama, tunda ga idanunka nan sun yi ja."
Dariya yayi yace, "Allah Momy da gaske ba yanzu na tashi ba, nayi kusan minti talatin ma ina zaune ne ban fito ba."
"Ok, ka kira SHAREEF yana ɗaki don na san bazai fito ba sai an kira shi." Tayi maganar tana wuce wa ta haye steps din zuwa ɗakin ta
Hakan yasa Sadiq ya bi bayanta shima yana wuce wa ɗakin SHAREEF ɗin.
[02/02, 9:30 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱
__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE22*
Sadiq ya fara dawowa daga masallaci sallan magriba da suka fita. A nan Falo ya tarar da Maryamu ita kaɗai ta tasa TV a gaba tana kallo, shigowar sa yasa ta gyara zama tana kallonsa da murmushi a face ɗin ta
Shima zama yayi gefen ta yana cewa, "har kin yi sallan ne My Ƙanwa?"
"Eh Yaya, ban ganka ba da na dawo makaranta?"
"Ina ɗaki My Ƙanwa, yau na dawo a gajiye shiyasa na shiga na kwanta after nayi sallan asar, to ya school ɗin ina fata kin yi enjoy?"
Ɗan tura baki tayi gaba, cike da sakarci tace, "wlh ba dad'i Yaya, kwata-kwata ban fahimci komai ba yau."
"Haba dai? Sabida me to?"
Ɗan yatsina fuskarta tayi tace, "to Ni dai karatun ne ba sa yi yanda zan gane, turancin ma babu dad'i."
Smile yayi yace, "kar ki damu na san rashin sabo ne My Ƙanwa, but zan riƙa koya miki in muka samu interval a hankali za ki riƙa fahimta."
Momy wacce ta sauko daga matattaƙalan benen, jin abun da Sadiq yake cewa, sai tayi murmushi tana cewa, "ai