Hakan ne yasa Momyn tayi mata tsiya-tsiya, ta turɓune fuska tace mata, "tana yin komai ne sabida ita, tana son ta mayar da ita Macen da SHAREEF zai kalle ta bai raina ta ba, sannan ma idan ta zauna a nan a banza tunda shi auren sa zai yi; ƙarshe ita za a mayar Bora baza ta taɓa tasiri a gidan sa ba, in ta fi son hakan ya faru sai ta ci gaba da zama tana ƙunsan bakin ciki."
Sai kawai Maryamu ta fashe da kuka jikin ta na wani irin rawa kamar mazari, lokaci ɗaya ta zamo ƙasa ta dunƙule wuri ɗaya tana ihu
Gaba ɗaya Momy ta rikice, domin bata taɓa zaton Maryamun zata tayar da hankalin ta haka ba
Hanif da ke ɗaki kwance yana huce gajiyar makaranta, shiyasa ba ya fita ko'ina tunda ya dawo, babu kowa a gidan sai su kaɗai, yana ɗakin su sama-sama ya jiyo kamar kuka, shiyasa ya tashi ya fito ya ga Momy tana ta rarrashin Maryamu amma ta ƙi yin shiru. Da mamaki ya iso wurin yana tambayar me ke faruwa? Hankalin sa shima ya ɗan tashi sabida ganin yanda Maryamun take kuka sosai ta ƙi yin shiru, lokaci guda ta fita a hayyacin ta
Momy ta kalle sa ta faɗa masa abun da ke faruwa
Haka kawai ya ji tausayin Maryamu ya kama sa sosai, duk da basu fahimci dalilin da yasa take kukan ba, a tunanin su rashin son zuwa Abuja ne, sai ya zauna ya ɗago ta ta koma saman kujera ya soma rarrashinta cikin kwantar da murya
Daƙyar suka samu tayi shiru, amma hawaye sun ƙi tsaya wa a kan face ɗin ta, faɗi take yi, "don Allah Momy kar a yi masa aure, ina sonsa wlh, zan iya zama dashi a haka, ku faɗa masa ina son sa kar ya auri Wata, ina sonsa."
Abun sai ya zame mata kamar taɓin hankali, bata cikin hayyacin ta abun da take ta furta wa kenan
Shi yasa Momy ta soma mata addu'o'i cikin tashin hankali, domin a tunanin su Maryamu ta samu sauƙi daga ciwon da take fama dashi, sai ga shi lokaci guda ta rikice kamar mai aljanu tana surutai mara su kan gado,
To make hankali ai bazai yi wannan abun ba. hakan ya tabbatar wa da Momy har yanzu Maryamu bata samu sauƙi dukka ba,
Addu'o'i ta dinga mata tana tofa mata cikin tsananin tausayin ta, yayinda take salati a cikin ranta
Inda shima Hanif yake bin su da kallo damuwa kwance a saman kyakkyawar fuskarsa, wani irin tausayin ta ne yake ƙara ratsa mishi zuciya, wai yarinya kamar wannan har ta san soyayya? Wannan wanne irin son maso wani ne? Bazai so a ce wani abu ya same ta ba domin yana jin ta tamkar ƙanwarsa da suka fito ciki ɗaya gudan jinin sa, ya san waye SHAREEF. Ya san kuma yanda yake matuƙar ƙaunar Haseena. Haseena ta zama komai nasa a yanzu, tabbas a yanda take gabansa bazai taɓa kallon Maryamu ba, kai ba ma ita kaɗai ba, kowacce ɗiya Mace SHAREEF bazai taɓa kallonta ba a yanzu, amma zai so SHAREEF ya tausaya mata ko don halin da take ciki, kamar ya zubar mata da hawaye haka yake ji. Sai ya buga tagumi yana kallon yanda Momy take ta mata tofi
daƙyar ta samu ta dawo hayyacinta, amma duk da haka bata dena kuka da magiyan, "Momy kar ta bari yayi aure, tana sonshi! Ita kaɗai take son shi baza ta iya rayuwa babu shi ba, su taimaka su roƙa mata shi."
Momy sai da ta zubar da hawayenta, ji take yi kamar ta kurma kuka sabida tsananin tausayin Maryamu, da tana da hali tabbas da ta cire soyayyar SHAREEF a zuciyar ƙaramar yarinyar nan; wadda bata gama sanin duniya ba amma wata mummunan ƙaddara tana shirin faruwa da ita, tabbas da tana da hali da ta canza Maryamu da Haseena a zuciyar SHAREEF; da ta saka shi ya so ta fiye da kowa a duniyar nan, yarinya ce bai kamata a ce ta san wannan soyayyar ba, babu yarinta ko wauta a irin yanda take ganin Maryamu tana ƙaunar SHAREEF, abun har mamaki yake bata,
Sai ta janyo ta jikinta tana sake rarrashinta tare da furta, "ki yi hakuri Maryam, ko so kike yi nima in yi kukan? Ai nayi miki alƙawari SHAREEF zai so ki wata rana; kuma SHAREEF naki ne har abada, auren shi ba shine zai sa bazai so ki ba amma ba na son ki shiga gidan sa ba ya ganin darajar ki kinji ko Maryamu na? Ki yi haƙuri ki dena damuwa da shi wata rana da ƙafafuwan sa zai zo gare ki, amma in kina wannan koke-koken zai raina ki ya ƙara wulaƙanta ki, ko ba haka ba Hanif?"
Kai ya ɗaga yana taso wa a inda yake zaune, ya zo ya kama hannun Maryamu yana cewa, "maza ki share hawayen ki ki dena wannan kukan, Momy ta rarrashe ki amma kin kasa yin shiru, share hawayen." Ya sakar mata hannun yana tsare ta da kallo
Ganin yanda yayi maganar babu wasa shiyasa ta share hawayen nan take, amma wasu ne suke ƙoƙarin fitowa, sai ta kalle sa da jajayen idanunta da suka kaɗa suka yi luhu-luhu, kamar zata fashe da kuka tace, "amma meyasa Yaya SHAREEF shi ba ya so na? Ku kuna so na amma ban dashi, me nayi masa da zafi haka? Kuma meyasa zai auri wata bayan gani Matarsa? Ka faɗa masa ina son sa, idan har bai so Ni ba mutuwa zan yi, zuciyata tana min zafi sosai, Momy don Allah ki taimaka min ki yi ceton rai."
Yanda take wani irin kuka shiyasa ta ƙarisa yin maganar tana kwantar da kanta a jikin Momy
Su kansu sun rasa yanda zasu yi da ita, abun ya soma basu tsoro, gani suke yi kamar Maryamu bata kai ta san wannan abun haka ba,
Dole sai dai Momy ta kira Dady ta sanar masa halin da ake ciki, domin wani irin zazzaɓi ne mai zafi ya kama Maryamun, sai da Momy ta nuna ɓacin ranta sannan ne suka samu tayi shiru, amma kuma sai jikinta ya rikice sun rasa gane kanta
Da sauri Hanif ya nufi ɗaki ya sauya kaya ya ɗauko key ya dawo, yace, "Momy mu je asibiti kawai a duba ta."
Momy ta girgiza kai tace, "ciwon Maryam ba na asibiti bane, ina ganin har da mutanen ɓoyen ta, babu yanda za a yi kamar Maryam ta riƙa wannan abun in har ba su bane, Ni ina kokwanto wlh, mu je kawai gidan Malamin da ke bata magani."
Hakan kuwa aka yi, shi ya ɗauke ta ya dire ta a cikin Mota,
Sanda suka tafi can sai ga kiran Dady,
Haka Momy ta ɗauka tace masa, "sun je gidan Malam ya biyo su can."
Da saurin sa ko zama bai yi ba ya fito suka wuce da drivern sa,
Lokacin da suka isa Malamin duk ya gama mata addu'o'i ya tofa mata, sai sannan suka samu natsuwarta ta dawo dai-dai duk da bata dena hawaye ba
Kiran sunan ta Malamin yayi, sai ta ɗago kai tana kallonsa, yace, "share hawayenki ki dena kuka kin ji Maryam?"
Babu musu ta share hawayen tana duƙar da kanta lokaci guda jikinta sai faman rawa yake yi
Sai ya kalli su Momy yace, "har yanzu mutanen nan suna nan kusa da ita basu rabu da ita ba, amma baza su taɓa cutar da ita ba, domin a bincike na na gane ƙaunar da ke tsakanin su da ita ne shiyasa har yanzu suke tare da ita, da suna son cutar da ita da tuni sun cutar da ita, amma kuyi haƙuri ku ci gaba da yin mata addu'o'i da magungunan da nake bata, itama kanta ku saka ta ta riƙa tsare jikinta da azkar, komai zai daidaita zata ga sauƙin abun, baza su taɓa cutar da ita ba, na tabbata su ne suke wannan haukan son ba ita ba, zaku iya tafiya yanzu ma babu wata matsala."
Godiya suka yi masa sosai, inda Dady ya basa abun sadaka sabida a yi wa Almajirai sadaka, sannan suka yi sallama suka tafi tare da maganar Malam da ya tsaya musu a rai
Har suka koma gida Maryamu bata sake magana ba, duk da jefi-jefi tana share hawaye a ɓoye,
Momy ta riƙo hannunta suka shiga ciki sannan suka zauna a saman kujera
Shima Hanif zuwa yayi ya zauna tare da Dady a kan two seater,
Dady da jikinsa yayi sanyi ya rasa me ke damunsa; sai ya kalli Momy yace, "Maryam ƴata ce da na ɗauko ta daga wani wuri domin ta zauna a tare da Ni, ba na son wani abu ya cutar da ita, sai dai ga shi Allah ya ɗaura mata wata lalura da nake ganin tamkar zai zama gazawata a nan gaba, bazan so a ce in sanar da Iyayenta halin da take ciki ba domin hankalin su zai tashi, yanzu me kika ce Khadija; ya zamu yi da ita?"
Shiru Momy tayi domin ta rasa me zata ce ma, illa kallon Maryamu da take faman yi har yanzu tana sharan hawaye jefi-jefi, sai can kuma bayan ta nisa tace, "duk da mu muka haifi SHAREEF amma bamu da ikon da zamu saka soyayyar Maryam a cikin zuciyarsa, amma mu Iyayensa ne muna da ikon da zamu zaɓa mishi abun da yake so, Maryam." Sai ta kira sunan Maryamun tana kallonta, bata bari ta amsa ba ta ci gaba da cewa, "idan kin fi son ki zauna da SHAREEF a haka ba ya ƙaunar ki kinga za ki iya; shikenan zamu tayar da bikin naku kwanan nan, sai a haɗa rana ɗaya da wacce zai aura, ko?" Ta ƙare tana ɗan shafa kanta
Shiru Maryamu tayi bata ce komai ba, sai dai kishi da baƙin cikin jin cewa zai haɗa su da wata shiyasa sam ba ta fahimtar me suke cewa, amma kuma idan zata zauna da SHAREEF shi ne cikan burin ta,
Shi yasa bayan Momy ta sake mata magana a kan, "ta amince zata tare a hakan?"
Sai ta ɗaga kanta tana faman share hawaye
"To shikenan, tashi ki je ki kwanta ki huta, saura kuma ki ci gaba da kukan naki kinji ko?"
Tashi tayi ta wuce ba tare da ta furta ko kalma ɗaya ba,
Suka bi ta da kallo; kallon tausayi har ta ɓace wa ganin su
Sai Dady ya ja numfashi yana kwantar da kansa jikin kujeran tare da zame hulan kansa
Hanif yace, "Momy gaskiya yarinyar ta bani tausayi, amma ina ganin kamar har da yarinta a lamarin ta, baku san yanda SHAREEF yake son Haseena bace, kuma kun fi kowa sanin wane ne SHAREEF da abun da zai aikata, wannan yarinyar ƙaramar yarinya ce, don Allah ku rarrashe ta kawai tayi karatun ta nan gaba sai ta tare, yanzu tayi ƙanƙanta sabida SHAREEF zai iya cutar da ita."
"Kai kenan da kake ɗan uwansa kake faɗin hakan." Momy ta furta ranta babu daɗi, kawai jinjina kanta take yi zuciyarta na mata zafi a kan SHAREEF ɗin, Yaro ɗaya yana son gagaransu,
"SHAREEF bai gagare mu ba, kuma bazai taɓa gagaran mu ba, Maryam dai mu muka zaɓa mishi haka nan zai yi haƙuri ya zauna da ita, abun da yasa na sauko da zaɓin shi domin kar mu shiga haƙƙin sa da yawa, amma duk ranan da ya muzguna wa Maryam, wlh zan ba shi mamaki, don haka yanzu zamu ci gaba da shirye-shiryen tariyan ta a ranar da za a ɗaura mishi aure, tun da wancan Uwar gantalin ba tarewa zata yi ba, sannan ma babu inda zamu kaita a part ɗin ku zata zauna, muna nan tare babu yanda za a yi ya cutar mana da ƴa."
Dady ya gyaɗa kai da furta, "tabbas hakan yayi, nima abun da nake tunani kenan."
Sun ci gaba da tattauna matsalar, while shi kuma Hanif sai ya miƙe yace musu, "zai je ya dawo."
Direct sai ya wuce ya nufi Companin su ya je ya samu SHAREEF a can
Time ɗin yana cikin office din sa ba ya aikin komai sai waya suke yi da Haseena,
A lokacin shi kansa ya ɗan yi mamakin ganin Hanif ɗin, bare yanda ya gansa fuskarsa babu walwala, sai ya yi wa Haseenan sallama yace, "zai kira ta later."
Sai ya dube sa yana cewa, "ya dai na ga fuskarka a haka? Ko wani abun ne ya faru?"
Bai basa amsa ba sai da ya zauna shima ya mayar da idanunsa a kansa before yace, "lafiya ƙalau, kawai ina cikin wani yanayi ne sabida abun da ya faru da Maryam."
"Wace ce Maryam kuma?" Ya tambaye sa da mamaki sabida har ga Allah yana manta wa da Maryamu a lokaci guda idan ba ya ganta ba, kuma bai yi tunanin maganar nata bane Hanif zai yi masa a nan
Shi kansa Hanif baki ya buɗe yana kallon SHAREEF ɗin, amma duba da ya san wane ne SHAREEF kuma ya san me zai aikata; tabbas zai iya yin fiye da hakan ma, that's why yace, "kana bani mamaki wlh Brother, ina maka maganar ƙanwar mu Maryam amma kake nuna kamar baka santa ba?"
Sai kawai ya haɗe rai yana mayar da kansa jikin kujeran, yayinda ya sakar masa wani kallo ba tare da yace uffan ba
"Baka tambaye Ni me ya faru ba?"
Dogon tsaki yaja yana cewa, "to me kake so in ce maka? Ni fa bani da lokacin jin maganar yarinyar nan sabida ba ta gabana, kai baka san yanda na tsani yarinyar ba ko? Yarinyar da ta ƙulla min sharri abun da tunda nake ba a taɓa min ba, wlh I hate this girl, even in my heart I tell you this, I don't like to see her face, kuma duk ranan da na samu dama sai na ɗanɗana mata kuɗan ta." Sai ya kaɗa kansa yana jin ransa na ɓaci sabida tuna ta
Shi kansa Hanif bai san mai ya faru ba tunda ba a sanar masa ba, amma yana mamakin yanda SHAREEF ya tsani yarinyar yake ciccije baki a kanta; har yana tada jijiyar wuya, sai yace, "don Allah Brother ka sassauta mata a kan wannan ƙiyayyar da kake mata, ban yi tunanin maganar Sadiq gaskiya bane sai yanzu nake ƙara gasgata wa, Maryam yarinya ce ƙarama wacce yakamata mu jawo ta a jiki but kai ba haka ba, ko don sabida Haseena kake wannan abun?"
Haɗe fuska yayi yana aika masa da wani banzan kallo yace, "me ya sako sunanta kuma a cikin wannan zancen?"
"Sabida a kanta kake ƙin Maryam mana, Dady ya aura maka ita but ba ka son zama da ita, kuma yarinyar tana matuƙar ƙaunar ka kai baka san me ya faru da ita bane yanzu, daga an ce zata koma Abuja wajen Ammee ta zauna a can duk ta tashi hankalin ta; har sai da muka kaita wurin Malamin da ke duba ta, duk saboda kai ne fa."
"And so what? Sabida Ni take wannan haukan? Kana ganin Ni ya dace in so yarinyar nan? Har abada! Wlh never Hanif, tun kafin raina ya ɓaci ma kabar min maganar ta." Yayi maganar da tsananin ɓacin rai yana buɗe idanunsa a kan Hanif ɗin
Sai shi kuma yayi murmushi, murmushin takaici sabida har ga Allah SHAREEF ya soma ba shi haushi, ya ƙara faɗin, "taya ya zan dena maka maganar ta bayan Matarka ce? Kuma a yanzu ma haka su Momy zasu baka Matarka ka zauna da ita, don Allah Brother Maryam yarinya ce duk da na san yarinta na ɗiban ta, amma bata rasa komai ba, yarinya ce kyakkyawa komai tana dashi; and ga ta karamar yarinya, da me Haseena ta fi ta?"
"Ya ishe ka dalla, ba na son jin zancen banzan ka." Ya daka masa tsawa da faɗin haka yana firfito masa da idanuwansa da suka soma kaɗa wa
Sai Hanif yayi dariya tare da furta, "oh! Ba ka son gaskiya ko? Soyayyar Haseena ta rufe maka ido, amma abun da ka kasa gane wa Maryam ta fita komai wlh, kuma nan gaba zaka ce na faɗa maka; but dole dai ko kana so ko ba ka so sai ka zauna da ita tunda already ta zama Matarka."
"Hanif." Ya kira sunan sa cikin tsananin takaici; yana buga teburin gaban sa
Sai shi kuma ya ja tsaki yana miƙe wa, "wlh ban san irin ka ba SHAREEF, ba ka son gaskiya, kana da wani irin zuciya da babu imani a cikin ta, babu tausayi."
Da sauri SHAREEF ya miƙe ya nufo sa, sai ya shaƙo wuyansa yana ƙara zare masa ido yace, "Ni kake faɗa ma haka Hanif? A kan wannan matsiyaciyar yarinyar?"
Zagin ya shige sa ba kaɗan ba, shima haka nan ransa ya ɓaci yace, "matsiyaciya SHAREEF?"
"Eh matsiyaciya nace, ko zaka rama mata ne? Nace ko zaka rama mata ne?" Yayi maganar cikin hargagi yana ƙara shaƙo sa kamar zai kashe sa
Sai shima Hanif ya sanya hannu ya shaƙo nasa wuyan ransa a mugun ɓace yake cewa, "don baka son a faɗa maka gaskiya? Na sha ce maka halin ka ba shi da kyau SHAREEF, ka sauya hali, ban taɓa biye maka ba sabida ba na son in nuna rashin kunya a matsayin ka na Yayana, amma baka da kirki ko kaɗan; baka da mutunci, ko babu komai yarinyar ƴar uwanka ce, idan wani abu ya faru da ita..."
Bai bari ya ƙarisa maganar ba ya kwashe sa da mari, ji kake fass ya kifa masa wani bahagon marin da sai da ya fitar masa da jini a hancinsa.
[28/02, 9:13 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱
__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE44to45*
_____Shi kansa Hanif bai taɓa tunanin SHAREEF zai saka hannunsa ya mare sa ba, sabida hakan bai taɓa faruwa da su bane, basu taɓa sa'insan da yakai har da cin kwala ba, ya san SHAREEF yana da zafi da saurin fushi, kuma jefi-jefi koda cacan baki ya haɗa su bai taɓa biye wa Hanif don yana faɗa masa gaskiya a kan halayyar sa