cike da damuwa a kan face ɗin ta, sai ta taho ta zauna a gefen Katifar su tana cewa, "don Allah ki yi haƙuri Amra, ba abun da zai iya miki, insha Allah zan ɗauki mataki a kansa Ni ko ƙaransa zan kai wurin Babansa, domin na gaji da wannan cin mutuncin nasa, ki dena kukan nan don bai da amfani yanzu, kar ki ja wa kanki ciwo."
Ɗago hannunta tayi tana mata bayani cikin kuka, tare da faɗa mata, "ita ta tsorata da Jabir, kar ya zo yayi mata wani abu, don Allah ta taimaka mata."
"Babu abun da zai miki wanda Allah bai miki ba Amra, bazai ci nasara a kanki ba ki kwantar da hankalin ki, yanzu ma zan je in sanar da Mahaifinsa komai, dole a yi mana iyaka dashi."
Sai ta mike ta fita ta koma ɗakin ta, mayafi ta ɗauka ta dawo ɗakin tana sake rarrashin Amra domin har yanzu kukan take yi
Su kansu su Afra hawaye suke yi sun gaza cewa komai jikinsu sai rawa yake yi
Sai da ta ja musu kunne a kan su yi shiru before ta fita, ta saka Salma ta biyo ta ta rufe gidan, idan ta buga sai ta buɗe mata
Amra kuma ta kasa yin shiru, domin ba abun da ta tsana sama da Jabir ɗan uwanta, gaba ɗaya ya takura mata a rayuwarta, nema yake yi ya haukata ta ya saka mata tsoron sa, ko kaɗan ba ta ƙaunar ta buɗe ido ta ga bawan Allan nan, wai a hakan sonta yake yi yayi ta muzguna mata,
Domin a baya ya sha zuwa gidan yana cin mata zarafi Allah kaɗai yake tsare ta, akwai kwanakin da ya zo lokacin Babansu bai jima da rasuwa ba, ya zo ya tarar da ita a gidan; ya kusa yin mata fyaɗe daƙyar ta tsira, sai ga su Afra sun dawo gidan, su suka je suka ƙanƙame ta Afra na dukan sa da kukan ya sakar musu ƴar uwa,
Dalilin da ya dawo hayyacinsa kenan ya haƙura ya tafi yana cizon yatsa, amma ba wai don ya haƙura da ƙudirin sa ba, don a yanda yake kwaɗayin Amra komai zai iya yi, bai da mutunci ko kaɗan, ga shaye-shaye ba ya ganin mutuncin kowa, tunda Babansu ya rasu ya soma addabar rayuwarsu, yayi ta zagin Amra yana kiranta da muggan sunaye a cewar sa, "tunda naƙasashshiya ce shi zai taimaka mata yayi maneji da ita ya aure ta."
Wannan dai lokacin har gida Mama ta je ta samu Mahaifinsa ta sanar mishi, kuma an ci Sa'a yana gida,
Bayan sun gaisa da Asabe mahaifiyar Jabir, sai ta nemi iso wurin Baba Jafaru mahaifinsa, kuma ƙani wurin Baban su Amra,
Asabe ta je har ɗaki ta sanar mishi; sannan yace, "ta shigo."
Zuwa tayi ta zayyane mishi abun da ke faruwa
Amma buɗan bakin Baba Jafaru, sai yace, "ƙazafi take yi wa ɗansa, ƙarya take yi, me zai yi da Kurma? Ya rasa wacce zai bibiya sai ita? Dama ya ga take-taken ta nema take yi ta ɗaura musu sharri tun ba yau ba, an gama na rabon gado, yanzu kuma abun da ta ɓullo dashi kenan, to wlh in ta saka wasa zai amshi Yaran gaba ɗaya tunda su yakamata su riƙe su ba ita ba, bazai bari ta ɓata tarbiyyar Yaran ɗan Uwansa ba, inyaso sai ta kama gabanta ta tafi."
Kuka Mama ta saka mishi, tana cewa, "yanzu duk halin da Jabir yake nuna mana; ban taɓa kawo ƙaransa ba sai a yau, amma nema kake yi ka mayar da laifin a kanmu, don kawai na zo na faɗa maka gaskiya amma maimakon ka tsawatar mishi gani kake yi kamar ƙage nayi mishi?"
"To ƙage ne mana Shafa, taya ya kike tunanin zan yarda da maganar ki? Ƙila ma ita yarinyar ce take bibiyan shi tunda itama ƴar taki yanzu yawon ta take yi, kina ce ban san me ke faruwa bane? Kurɗa-kurɗa yanda ƴarki take yawo a gari ina jin labari, to wlh bazan lamunta ba, mun kusa mu amshi Yaran sabida baza ki ɓata mana suna a gari ba, haka kawai don wulaƙanci ki zo kina son ɗaura wa ɗana laifi? Bayan naki yarinyar ne mai laifin, ai ta isa aure meyasa baza ki nema mata Miji ba? kun zaunar da ita a gida kuna haɗa kafaɗu da ita."
Kasa jure zantukan nasa tayi, shiyasa ta miƙe tana zubar da hawaye; ta dube shi da faɗin, "shikenan Allah na gani, kuma shi zai yi mana maganin dukkan matsalolin mu, wlh na rantse da Allah idan har baka ja kunnen ɗanka yabar zuwa mana gida ba; in har ya aikata muggan abu a kan ƴata, wlh tallahi sai inda ƙarfi na ya ƙare, bazan taɓa ƙyale wa ba, kuma Yarana babu inda zasu gusa daga kusa dani, sai dai duk abun da zaku yi ku yi."
Cikin tsananin mamaki yake kallonta, tare da furta, "haka kika ce Shafa?"
"Eh haka nace." Tayi maganar a zuciye ranta na ƙuna, idanunta jawur a kansa
Shima cikin ɓacin ran yace, "to zamu gani, tunda kin ce hanyar da za ki bi kenan, mu zuba mu ga wanda zai yi nasara."
Bata ce mishi komai ba ta juya tabar Falon nasa, ta fice tana sharan hawayen ta,
Ko kafin takai gida ta gyara fuskarta yanda Yaranta baza su gane halin da take ciki ba
Amma duk da haka sai da Amra ta fahimci akwai abun da ke faruwa, domin bata yarda da abun da Maman ta sanar musu ba a kan, "ta shawo matsalar komai."
Tana ji a jikinta dole akwai matsala, sai dai bata ce komai ba haka tabar abun a ranta ta kasa sakin jikinta, ko walwala ta kasa yi,
A haka ta kwana ranan cikin damuwa, domin har ga Allah tana tsananin tsoron Jabir da abun da zai aikata mata, ba ta son suna haɗuwa sabida yana cutar da ita
Kasancewar bata yi barci ishashshe ba sabida halin da take ciki, shiyasa bata koma barci ba tunda aka yi sallan asuba, tana zaune tana lazumi har gari ya soma haske,
Sai ta tashi ta je ɗakin Mama suka gaisa sannan ta fito ta soma aiki,
Tsintsiya ta ɗauka ta soma share tsakar gidan tunda akwai ta da gazar-gazar komai ita take musu, sai idan Mama ta sanya su Afra ne sannan take haƙura,
Amma yau bata da karsashi tunda barcin da bata yi ba ya saka mata weak a jikinta, tare da ciwon kai, kaɗan - kaɗan yake ratsa ta amma bata so Mama ta fahimta, kuma ga shi tana son fita wurin aiki da wuri gudun samun matsala
Mama kamar ta san halin da take ciki, sai tace, "tabar sharan kawai su zasu yi, gwara ta shirya da wuri kar tayi latti, daga fara wa kuma a samu matsala bata je da wuri ba."
Ce mata tayi, "ta hura wuta ta saka ruwan wanka, sai ta dama musu koko su sha."
Haka kuwa Amra tayi,
Ko kafin bakwai ta gama komai har wanka tayi ta shirya cikin riga da skirt na atamfa, sai ta ɗauki baƙin Hijab ta sanya har ƙasa ba a ganin komai nata, since yanayin shiganta kenan, a rayuwa tana bala'in son baƙin abu, shiyasa yawanci hijabanta bakake ne har ƙasa, zaka ga ta saka ta rufe komi na jikinta, illa fuskarta da ake gani ko kuma idan ta fito da hannayenta, sau tari wasu da suka santa suna tunanin ƴar Shi'a ce, sabida a koyaushe da baƙin Hijab zaka ganta kuma different designs; balle kace guda ɗaya take saka wa,
Yanzu ma bayan ta gama shan kokon sai ta saka socks a ƙafarta tare da baƙin cover shoes,
Ta ɗauki Ƙaramar Jakarta na hammata ta maƙale ta, ta yi wa Mama sallama zata wuce
Mama tayi mata addu'a sosai,
Haka su ma su Afra sai murna suke yi suna mata a dawo lafiya
Naira ɗari Mama ta dauko mata ta miƙa mata,
Tace mata, "ta kula da kanta sosai tayi abun da ya kaita, Allah ya bada Sa'a."
Sai lokacin ta ɗan saki fuskarta tana kallon Maman, idanunta sun ɗan kumbura sun tasa har face ɗin ta, sallama ta sake musu sannan ta fice ta nufi hanyar titi,
Daƙyar ta samu abun hawa har hankalin ta ya soma tashi, ga shi ta fito da wuri kuma tana neman yin latti
Bayan ta isa Companin an sauke ta, sai ta biya kudin ta wuce ciki da sauri cikin rawan jiki,
Lokacin Companin ya cika sai hada-hada ake yi,
Kai tsaye office ɗin Hanif ta wuce tunda ba a nuna musu aikin da zasu yi ba bare a basu wurin zama, sai yau ne za a nuna musu offices ɗin su,
Tana zuwa kuwa ta tarar da sauran sabbin da aka ɗauka, su ma sun zauna a wurin suna jira, tunda Secretary yace, "su jira."
Itama sai ta bi sahun su bayan ta ɗaga musu hannu alamun gaisuwa
Wasu da yawa sun kalle ta amma basu ce mata komai ba, wasu kuma hankalin su ba a wurin yake ba, kowa yana harkan gabansa, itama wurin tsayuwa ta samu tana faman ayyana abubuwa a ranta
Jimawa kaɗan sai ga Secretaryn ya shigo wurin da Files a hannunsa, sai ya wuce su ya shiga office ɗin Hanif, ba a jima ba ya fito yana kallonsu, yace, "yanzu zamu wuce daku zan nuna muku inda zaku zauna, zaku fara aiki Insha Allahu."
Dukkan su sai da fara'a ya yalwata a kan face ɗin su
Sai ya sake duban su da faɗin, "wace ce Amra Abubakar?"
Da sauri ta ɗaga hannunta har jikinta na rawa jin an kira sunan ta
"Ok, ki shiga, Oga na kiran ki, ku kuma sai ku biyo NI ko?"
Ya wuce yana yin gaba; suka take mishi baya
Aka bar Amra tsaye a wurin cike da zullumi da fargaba, wanda hakan ya jawo ta kasa yin gaba bare ta shiga office ɗin, gaba ɗaya fuskarta ta nuna tashin hankali da tunanin abun da zai biyo baya; ƙila koron ta za a yi an fasa ɗaukan ta.
[10/03, 8:51 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱
__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE54*
_____Tura ƙofan tayi ta shiga ciki; sannan ta mayar da ƙofan ta rufe,
Hanif na kallonta har ta zo ta zauna sannan ta gaishe shi
Dayake bai san gaisuwar nasu ba, shi dai bai amsa ba illa murmushi da yayi mata yace, "kina lafiya?"
Kai ta ɗaga mishi itama tana Murmushin
Sai shiru ya ɗan gibta kaɗan, idanunsa a kanta suna kallon juna, mamakin yanda face ɗinta ta tasa yake yi; da kuma yanda idanunta suka kumbura suka canza launi kamar tana cikin damuwa, ko kuma tayi kuka,
Tabbas ya fahimci akwai abun da ke damunta don ba haka ya ganta jiya ba,
Amma sai bai ce komai ba ya ɗauke idanunsa a kanta ganin itama ta duƙar da kanta, sai da ya ɗan ɓata time wurin duba computern nasa ba tare da yayi magana ba bare ya kula ta
Yayinda Amra tayi tsumu har ta gaji ta ɗago tana kallon yanda yake aikin, murmushin sa a gare ta ya cire mata fargaban da take ciki, har zuciyarta ta ji sanyi domin ta sadaƙar cewan an fasa ɗaukar ta ne
"Kina jina?" Yayi maganar yana ɗago kai ya dube ta
Kai ta gyaɗa mishi da sauri tana gyara zaman ta
"A nan office ɗin za ki soma aiki Insha Allahu, idan Secretary ya zo zai nuna miki inda za ki zauna cuz za ki zama mataimakiyar sa ne, let's wait for him to come back and show you where to sit."
Smile tayi mai yalwa tana ɗaga hannunta tare da mishi godiya
Bai ce mata komai ba ya ɗauke kansa ya ci gaba da aikin gabansa,
Har sai sanda secretary ɗin sa ya shigo, sannan ya umarce sa da, "ya kaita wurin zamanta a office ɗin sa, zata zama mataimakiyar sa, since ba ta iya yin magana sai ya amshi numban wayanta ta haka zasu riƙa communicating, ya bi ya koya mata duk abun da ya dace ta sani."
Sai ya kalli Amran yace, "ta tashi ta bi shi."
Miƙe wa tayi suka fita tare da Secretary
While Hanif ya bi bayanta da kallo har sai da ta fice, sai ya ɗan sauke numfashi yana lumshe idanunsa; tare da ɗaura hannayensa saman table ya tallabo gemunsa; har a ransa ya damu da sanin halin da take ciki domin yana da tabbacin akwai wani abun da ya faru da ita, shi kansa yayi mamakin yanda yarinyar ta tsaya mishi a rai daga jiya zuwa yau,
Murmushi kawai yayi ya janye hannunsa ya ci gaba da abun da yake yi.
🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆
_____Sabuwar rayuwar Maryamu da ta tsinci kanta; ta soma sanjawa fiye da yanda take a baya, to ta zo wurin wayayyun mutane, shiyasa duk abun da suke yi shi take yi, duk da babu takura a cikin zamansu, amma basu da lokacin kansu sai na karatu, sai kuma idan sun fita zuwa koyon computer, duk abun da suke so ana musu
Ga shi yanzu har an shafe wasu satikai da zuwanta can,
A lokacin take jin labarin auren SHAREEF da za a yi a gobe; a bakin Ammee, duk da Ammeen ba zuwa zata yi ba kasancewar babu tariya,
Amma ta ji suna magana da Momy a waya, kuma ta ji su Aakifah suna zancen, tunda su basu san tana da auren SHAREEF a kanta ba,
Da farko ta soma manta wa dashi since bata da lokacin tunani, amma jin wannan maganar ya fama mata gyambon da ta rufe tana ƙoƙarin binne shi a ƙasan zuciyarta,
Lokaci ɗaya jikinta ya mace ta kasa yin komai, sai wani irin ciwon kai da ya kawo mata cafka, take ta haye saman gado ta rufe kanta zuciyarta na wani irin zafi kamar zata faso ƙirjinta, ta kasa jurewa sai ta fashe da kuka, kuka mai cin rai,
Shikenan tana ganin ta rasa SHAREEF na har abada; tunda ga shi zai auri wacce yake so yake ƙauna, zai yi rayuwa da wata ba ita ba, meyasa ya kasa fahimtar zuciyarta? Ko tana da laifi ne don ta so shi? Meyasa ba ya da tausayi bazai iya tausaya mata ba?
Shikenan yanzu ya kuɓuce mata ya zama na wata? Ba ta jin zata iya jurewa, mutuwa zata yi sabida tsananin kishin da ke taso mata a can ƙasar zuciyarta,
Kuka sosai take yi tunda ta samu dama babu kowa a ɗakin, daga ƙarshe sai jikinta ya rikice sabida kukan da ta dinga yi; ga kuma ciwon kai, nan da nan zazzaɓi ya sauka a jikinta,
Amma duk da haka bata sarara wa kanta ba, tana kukan baƙin ciki da tsananin kishin rasa SHAREEF, tana son ta cire sa a rai amma hakan bazai taɓa yiwuwa ba, abu ne mai matuƙar wahala ta manta SHAREEF a rayuwarta, ya zama jinin jikinta, shi zuciyarta take so, kuma tana ji a ranta sai dai ta mutu da soyayyarsa
Yusaira ta shigo dakin ta tarar da ita a haka tana gunjin kuka, sai ta taho wurin ta cikin tsananin tashin hankali tana kiran sunan ta, hannu ta sa ta yaye bargon tana cewa, "Maryam, kukan me kike yi? Ba ki da lafiya ne?"
But ina Maryamu ta kasa amsa mata, ƙoƙari take yi ta tsayar da kukan nata amma ta gaza, wani irin sabon kuka ne ya taho mata ta sake shi lokaci guda tana sake ƙanƙame idanunta, domin a lokacin wani irin azababben ciwon kai da yake kawo mata cafka ko buɗe idon bata son tayi
Yusaira kuma sai ta tsorata da halin da take ciki, da gudu ta juya ta fita ta je ta sanar da Ammee dake zaune a falo su da su Aakifah
Hakan ne yasa itama ta taso hankalin ta a tashe jin abun da Yusaira take cewa,
Tare gaba dayansu suka yo cikin ɗakin suka shiga,
Sun tarar da ita a wannan yanayin tana ta kuka tana kiran kanta
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!" Kalman da Ammee ta furta kenan tana zama tare da tallabo ta jikinta, yanayin yanda ta ga jikin nata hankalin ta yayi ƙololuwar tashi, faɗi take yi, "Maryam me ke miki ciwo? Me ya faru da ke ne? Yanzu fa kika shiga ɗakin lafiyar ki lau."
Su ma su Aakifah sai ga hawaye, sun yi tsumu sun kasa kataɓus sai kallonta suke yi cikin tsananin tausaya mata, don ko da gani tana jin azaba yanda take ta juya kai
"Yusaira, maza je ki ɗakina ki ɗauko min first eid box."
Juya wa tayi da sauri bayan ta amsa mata, ta nufi dakin Ammee ta ɗauko ɗan akwatin magungunan su
"Buɗe min ki ɗaura a kan gadon, ke kuma Aakifah dauko ruwa."
Itama Aakifah da gudu ta juya ta fita Falo
While Na'ilah tuni ta haye saman gadon tana kukan itama, ganin yanda Maryamu take kuka duk hankalin ta ya tashi; abun ka da ƙaramar yarinya
"Yi shiru Maryam, ki dena wannan kukan shi zai ƙara miki ciwo, kan kaɗai ke miki ciwo ko har da wani abun?"
Ta tambaye ta tana sake tallabo ta jikinta
But Maryamu ta kasa magana sai gunjin kukan da ta kasa bari, tana faman jujjuya kai kamar wacce zata hau iska
Bayan an kawo ruwan; lallaɓa ta Ammee tayi ta bata maganin ta sha, daƙyar ta rarrashe ta ta dena kukan,
Sai tace, "ta koma ta kwanta Insha Allahu jikin nata zai yi sauƙi."
Tunda a ganin ta zazzaɓi ne kawai ya rufe ta
Ita kuma sai ta kwanta tayi lamo sai shashsheƙan kuka take yi, ta rufe jikinta gaba ɗaya idanunta a rufe tana sauke nimfarfashi,
Yayinda wasu siraran hawaye ke ɗiga mata suna bi ta gefe da gefen kunnuwan ta,
SHAREEF kawai take iya tuna wa a halin da take ciki, fuskarsa ne a idanunta yayinda take jin wani taƙuƙi gami da kishi na ƙara hudo mata ƙirji, shikenan ta rasa sa? Idan tayi tunanin wannan kalman ji take yi kamar zata mutu, sai kuma ta kama kuka wi-wi
Dayake Ammee ta kaɗa su sun koma Falo, basu san halin da take ciki ba, amma sun tausaya mata gaba dayansu, sun gaza yin aikin ma da ke gabansu,
Sai da Ammee tace, "su je su ci gaba da aikin su kar a kira Magriba."
Sannan suka tafi jiki a sanyaye, sun rasa me