kula da kanta kasancewar ta Malamar jinya, tana kiyaye duk abubuwan da zai sa ta samu matsala
Shima Haruna yana taimaka mata sosai, duk abun da take so yana siyan mata, ko birni zai je sai ya nemo mata duk abun da tace tana so
Cikin ya kai watanni Bakwai aka yi auren sa da Jummai. Jummai ta tare a gidan Haruna tare da ƙudurin fitar da Hafsah saboda zugin ƴan uwa, tunda ba son Hafsan suke yi ba, suna baƙin ciki da ita kaf dangin nasu musamman da suka san ta fi su komai, ga ta wayayyiya a cikin su
Sai dai kuma Jummai bata samu Sa'a ba tunda Haruna yana matuƙar ƙaunar Hafsah, itama kuma Hafsah akwai iya zama da mutane, bata taɓa biye wa Jummai a kan shirmen ta ba, ta toshe kunnen ta da idanuwanta bata taɓa tanka mata a kan duk wasu rigingimu da take taƙalanta dashi ba, bare dama Haruna yana goyan bayanta shiyasa ta bar wa banza ajiyan ta, idan tana haushin karen ta tamkar bata san da ita take yi ba
A haka har Hafsan ta haihu, ta haifi ɗiya Mace aka sanya mata sunan mahaifiyarta, wato Samira suna kiranta da Ummita; kasancewar sunan da Hafsah take kiranta dashi ne shiyasa ya bi ta.
A wannan lokacin ne kuma aka yi bikin Ahmad; har Hafsah ta je bikin can Kano, tare da su Inna Samira suka tafi, kwanan su biyu suka dawo
Dayake itama yanzu Jummai tana da ciki shiyasa duk wasu abubuwan ta dena yi tunda tana shan wahala, Hafsan ne ma take kula da ita batare da ta duba irin zaman da suke yi da ita ba, sosai take bata taimako tunda kamar cikin ya zo da matsala ne, da rabon za a haife shi amma ta sha bak'ar wahala, kuma Hafsah ta amsar mata haihuwar
Shi yasa daga ranan ya zamana duk wacce zata haihu a ƙauyen ake kiran Hafsah, ko ciwo Mutum yake yi wurin ta yake zuwa tunda tana siyar da magunguna
Hakan ne yasa Haruna ya buɗe mata shago a kofar gidan su, duk da ba zama take yi ba amma idan an zo siyayya zata je ta ɗauko musu, kuma duk idan an kira ta zuwa gida zata je ta duba mutum. Da haka ne Mutanen karkaran suka rage tsanarta har ana zaman mutunci
Itama Jummai ta rage kishi da ita suna zaune lafiya sai dai idan tsiyan ya taso, wanda ba a raba kishiyoyi da shi. Yarinyar Jummai itama ta soma wayau sai suka taso kansu ɗaya da Ummita, itama sunan mahaifiyarta aka saka Aisha suna kiranta Indo
Kusan shekaru biyu da haihuwar su basu sake haihuwa ba
Fannin Ahmad kuma matarsa har ta haihu ɗa namiji, Yaron aka sanya mishi suna *SHAREEF*
Watan shi uku Hafsah ta sake haihuwar namiji, yaron ya ci suna Naziru. Daga nan ne bata sake haihuwa ba sai Jummai da ta sake haihuwar yara biyu Maza. A haihuwa ta biyun ne suka haihu tare da Jumman dukka Maza, daga nan kuma Hafsah ta ƙara Mace shikenan kuma haihuwar ta tsaya, yanzu yaranta huɗu, Ummita da Naziru, sai Bashir da Maryamu
Ita kuma Jummai; daga Indo sai Faisal da Ashiru, Halliru, Bintu sai Shatima
Yanzu Yaran Malam Haruna da suke kiransa da suna Baba; yaransa goma kenan. Ya aurar da Indo da Ummita duk a cikin garin, sai Yaya Faisal shima yayi aure, gidansa yana kusa da su babu nisa
Yanzu haka an saka wa Yaya Naziru rana shi da Yaya Ashiru, kuma su ne sukai karatu har matakin B8, yanzu ma suna ajin ƙarshe ne, bayan sun gama za a tsayar da lokacin a yi auren. Yaya Ashiru matarsa ƴar gaban ƙauyen su ne, shi kuma Yaya Naziru Matarsa ƴar cikin gari ne a Maɗachi. Wani lokacin Yaya Naziru shi yake zaman ma Innarsu a shagonta na Chemist, idan ba shi da lectures yana shagon tunda shima fannin likitanci yake karanta.
Fannin Alhaji Ahmed wanda a yanzu yayi kuɗi sosai. Allah ya buɗa masa tunda yayi karatu mai zurfi, yanzu haka ya kai matakin professor. Yaransa uku dukka Maza, SHAREEF sai Hanif mai sunan Baba Sama'ila, wato mahaifin Alh. Ahmad. Sai Auta Sadiq
SHAREEF ya gama karatun sa yana aiki a companin Dadyn su, shi yake jagorantar companin gaba ɗaya
While Hanif kuma ya gama degree ɗin sa yanzu haka yana karatu a England inda SHAREEF ɗin yayi karatu
Haka Dadyn su ya tsara musu duk wanda zai yi masters can yake tafiya
Allah yayi ma Hajiya Bilkisu rasuwa wato Kakan su SHAREEF, bayan tayi dogon jinya Allah ya karɓi abun sa kusan watanni biyar kenan
Yaranta biyu da ta haifa da Mijinta, su ma sun yi aure dukkan su tunda Mata ne, kowacce tana garin da tayi auren.
To yanzu labarin zai fara, sai a gyara zama domin jin wane ne SHAREEF?
SHAREEF kyakkyawar matashi wanda kowacce Mace take fatan ya so ta, idan na tsaya faɗa muku yanda ya haɗu to kamar na rage mishi matsayi ne, Mutum ne mai matuƙar aji da tsantsan wayewa, ɗan boko ne zalla domin komai nasa da rayuwarsa gaba ɗaya irin na wayayyun ƴan boko yake yi, yana da son girma shiyasa ba kasafai yake da fara'a ba, idan baka fahimce shi ba za ka kira shi mai wulaƙanci da rashin son jama'a sabida ƙyanƙyamin sa da nuna shi ɗan masu kuɗi ne, ya tsani rayuwar talauci shiyasa ba kasafai yake ziyartan ƴan uwansu na ƙauye ba, zan iya cewa tunda yayi wayau bai taɓa zuwa ƙauye da sunan gaishe da ƴan uwan Dadyn shi ba, iyakansa cikin Zaria shima sai a shafe shekaru da dama bai leƙa su ba, sai idan Dadyn su yayi mishi faɗa sosai sannan yake zuwa, rayuwarsa yana yin abun sa shi kaɗai ne domin ba shi da wani Aboki sai iyayensa da ɗan uwansa Hanif, tunda sun taso tare basu da tazaran shekaru shiyasa suka zama kamar Abokai. Baya ga su babu wanda ya yarda da su a duniyar nan face Mace ɗaya, Macen da ya ƙwallafa rai a kanta yake sonta tamkar rayuwarsa, ba shi da buri sama da ya mallake ta a faɗin duniyar nan, bazan iya misalta muku irin ƙaunar da yake mata ba; amma zai iya bada ransa a kanta, komai zai iya mata saboda ƙaunar da yake mata, idan nace komai ina nufin komai.
__________
*BOOK1*
_______________ *FREE PAGE3*
Yana zaune a saman kujeran sa na office, inda ya ɗaura earphone a kunnensa yana faman latsa computern da ke gabansa a saman table, cikin ƙwarewa da zafin nama haka yake danna computern wanda da alamun aikin da yake yi mai muhimmanci ne a ciki. Sanye yake da farin suit daga na ciki har na wajen dukka fari ne, komai nasa fari ne in banda suman gashin sa da ya sha gyara yayi aski ya bar na gaban
Nocking ake yi a door ɗin; but bai san ma ana yi ba tunda already ya toshe kunnuwansa yana sauraron music, wani lokacin ma har kaɗa kansa yake yi
Sai da wanda yake nocking ɗin ya gaji before ya buɗe ƙofan ya shigo, PA ɗin sa ne riƙe da wasu files a hannunsa. Koda ya shigo ɗin ma bai san ya shigo ba tunda kacokan hankalinsa ba ya wurin, kuma bai ji ƙaran ƙofan ba, shi kuma PA ya san dama yana ciki bai wuce earphone ya saka a kunnensa ba since ba ya rabo dashi. Nufan wurin sa yayi tare da ɗan buga teburin
Hakan ne yasa ya ɗago ƴan madaidaitan idanunsa da suke fari tarr kamar madara; ya zuba masa su ba tare da yayi magana ba
Shi kuma PA ɗin sai yayi murmushi cikin girmama wa yace mishi, "Weldon sir."
A hankali ya zare hannunsa daga saman computern yana ɗaura wa a kunnensa tare da cire earphone ɗin ya sauke a wuyan sa, still ya bi PA ɗin da kallo yana jiran jin mai zai ce
Shi kuma sai yace, "sir ga files ɗin na gama dasu, and kuma akwai meeting mutane har sun taru amma na ji ka shiru ba ka fito ba."
Maimakon yayi magana sai ya ɗauke kansa yana azawa a saman wrist watch ɗin sa, nan take ya lumshe idonsa tare da buɗe wa yana jingina jikinsa sosai a saman kujeran, cikin yanayin gajiya da maganarsa mai fita da sanyi kasancewar sa mara hayaniya, yace dashi, "wlh i forgot." Sai kuma ya ɗan ja huci yana narai-narai da idanu kamar wanda yake jin barci, miƙewa yayi da zummar shiga toilet yake cewa, "za ka iya tafiya, ina zuwa."
"Ok." PA ya furta sannan ya ajiye files ɗin ya fice
Bai ɗauki lokaci ba ya fito yana nufan table ɗin sa tare da ɗaukar handkerchief da ke saman, ya share hannunsa sannan ya ajiye yana ƙoƙarin juya wa, wayansa ya ji ta soma tsiwa alamun kira ake yi, sai ya ɗan leƙa kansa; ɗan yatsan sa ɗaya na kan gemunsa yana faman sosawa. Lokaci ɗaya ya zuba murmushin da dukka dimples ɗin sa na gefe da gefen kumatun sa suka lotsa, ya zagaya ya ɗauki wayan a saman table tare da nufan bakin window yana mai amsa Call ɗin. Lokaci ɗaya ya lumshe idanu saboda jin sassanyan muryanta ya duki kunnensa. "Sweetheart." Ya furta a hankali wanda idan ba itan ba babu wanda zai iya ji, sai dai laɓɓansa da ya motsa alamun yayi magana... Shiru ya ɗan yi na daƙiƙu before ya sake magana, "I'm sorry, aiki ne yayi min yawa shiyasa ban kira ba." Sai ya sa hannu ya zage Curtain ɗin yana leƙa waje... "Ok meye labari?"... Taɓe baki yayi ba tare da ya sake cewa komai ba, ya ɗauki tsawon lokaci da alamu yana sauraron ta ne, sai kuma ya katse wayan bai sake furta wani kalma ba. Daga haka ya juya zai fice a office ɗin, kafin ma ya kai bakin ƙofan har wayan ta sake yin ƙaran kira, bai ɗauka ba sai ya sanya ta a silent tare da tusa wa a aljihu ya fice, yayin da fuskarsa babu walwala ko kaɗan, duk da dama shi ɗin ba wai mai fara'a bane; domin ba kowa yake ganin fara'an sa ba sai idan a gida, amma kuma na yanzu ya fi kowanne tunda kyakkyawar fuskar nan a haɗe take murtik, sai kuma yayi kyau ainun tunda yana da kwarjini matuƙa, Mutum ne mai cika ido da kamala, duk yanda ka kalle shi sai kwarjinin sa ya cika maka ido
Kai tsaye hole ɗin da suke yin taro ya nufa. A ƙalla ya kwashi fiye da mintuna talatin kafin ya dawo office, sai dai yana shigo wa ya sauke ido a kanta
Tana zaune a kujeran sa sanye da rigan suit ɗin sa da ya ajiye a jikin kujerar, jikinta kuma ta saka baƙin straight skirt da farar riga mai santsi, an yi shokin gefe da gefe yana da dogayen hannu, sai ta yafa farin Vail wanda ya yi wa kyakykyawar fuskarta kyau.
HASEENA kenan. Yarinya ɗaya da duk duniya idan aka cire iyayen SHAREEF yake matuƙar ƙaunarta. Budurwa ce da aƙalla baza ta fi 22years ba, tabbas Haseena kyakykyawa ce kuma ta cika Macen da kowanne namiji ya ganta sai ya ƙyasa, tana da hasken skin but tana ƙara wa da mai kaɗan; wanda hakan ne yasa ta koma fara, tana da gata a wajen iyayenta duk da kasancewar su biyu suka haifa tare da ƙanwarta, amma sun ɗauki son duniya sun ɗaura mata shiyasa ta taso cikin gata da sangarta, abun da take so shi take yi. Sai ga shi kuma Allah ya haɗa ta da SHAREEF da ya shigo cikin rayuwarta suna matuƙar ƙaunar juna, iyayenta sun sani sai dai nashi iyayen basu sani ba, but yana da ninyar faɗa musu a nan kusa tunda yana bukatar aure
Tun shigowar sa ta washe baki tana miƙewa tare da cewa, "welcome my dear. I have been here waiting for you." Sai ta nufe sa tare da manne wa a jikinsa, a hankali tayi masa kissing a laɓɓansa
Bata kai ga janye bakin ba, sai ya matso da nasa ya haɗe bakunan nasu wuri ɗaya, take a nan ta lumshe idanu; while shi kuma ya sanya hannayensa ya kama ƙugunta tare da sake manne ta a jikinsa. Tsawon mintoci suna a haka before ya janye bakinsa yana bin ta da kallo; kallon soyayya
Daga ɓangaren ta itama hakan ne, sai dai tuni ta sake maida jikinta ta rungume sa sosai tana sauke ajiyan zuciya
A yanzu ɗaya hannunsa yana bayanta yana shafa mata tamkar ƙaramar yarinya, sai kuma ya janye jikinsa before ya kama hannunta ya nufi couch ya zaunar da ita, shima ya zauna a gefen ta yana facing ɗin ta, ƙura mata ido yayi bai iya cewa komai ba illa bin ta da kallo da yake ta faman yi
Ita kuma sai ta shagwaɓe fuska tare da cewa, "meyasa ka kashe min waya muna magana?"
Sai da ya saka hannunsa cikin nata ya haɗe yatsun yana kallo, yake furta, "I told you I don't want you to leave, meyasa baza ki bari ba sabida farin cikina?" Ya ƙare maganar yana sake tsira mata ido
Tura baki tayi tace, "don Allah ka bar ni Nidai, just two years ne fa zan yi karatun nan in gama, kuma na fi son can wlh bazan iya karatu a ƙasar nan ba, when I come back everything will come to an end; sai mu yi auren mu ko?"
Numfashi ya ja before yace, "Ni ba haka nake so ba, kin fi kowa sanin cewa ina matuƙar buƙatarki a halin yanzu, bazan iya jira har nan da two years bamu yi aure ba, ki canza wannan shawaran Please sweetheart?"
"But I don't have any advice kuma, Abbana yake son in je in yi karatu na a can bazan iya bijire masa ba, tun farko na baka kaina amma ka ƙi amince wa, to me kake so in yi maka? Tunda muna son juna why not baza ka amince mu ji daɗin rayuwar mu kafin auren mu ba? Please dear nima ina buƙatar ka a rayuwa domin ji nake yi kamar idan na tafi bazan dawo ba, don Allah ka fahimce Ni." Ta ƙare maganar kamar zata yi kuka tana sake shige masa
"Haseena." Ya furta sunanta ƴan madaidaitan idanunsa suna a kanta
Kasa amsa wa tayi sabida bata saba jin yana kiran sunanta ba, but sai dai tuni ƙwalla sun tarun mata a idanu tana shirin kuka
Girgiza mata kai yayi tare da cewa, "I don't want you to cry please sweetheart, Ni mai ƙaunarki ne ba maƙiyin ki ba, ba na son wani abu ya shiga tsakanin mu ba tare da aure ba, ko kin fi son mu aikata Zina ne?"
Kanta itama ta girgiza hawayen cikin idonta suna sauka, sai tace, "but amma ai muna ƙaunar juna, kai ne fa za ka aure Ni, meyasa baza ka fahimce Ni ba?"
"Shiiiii!" Ya furta yana ɗaura hannayensa biyu a saman face ɗin ta tare da share mata hawayen, sai ya sauya maganar tare da cewa, "yaushe ne tafiyar naki?"
"Later than ten o'clock at night."
Murmushi yayi mata mai yalwa wanda kyawawan dimples ɗin sa suka fito
Sai ita kuma ta sanya hannunta a cikin guda ɗaya; while itama tana murmushin cike da tsantsan ƙaunarsa
"I love you sweetheart." Ya furta tare da kama hannunta zuwa bakinsa yayi kissing ɗin ta, sai ya zuba mata idanunsa a cikin nata tare da ƙara faɗin, "zan yi kewarki matuƙa a cikin raina, zuciyata zata azabtu da rashin ki, but I will wait until you come back, two years is like two days, zamu kasance a tare a kodayaushe. Zuwa anjima zan zo gidan in raka ki zuwa airport."
Da sauri ta ɗago ta faɗa kansa tare da furta, "i love you so much dear, ina sonka sosai a raina, don Allah kar ka ci amanata bazan taɓa iya jurewa ba."
Bayanta yake shafa wa a hankali a yanzu ɗin cikin rarrashi, tare da ɗaura bakinsa setting kunnenta yana raɗa mata maganganu masu kwantar da hankali da zauta ta. Sai dariya take yi cikin fari ciki tana ƙara manne mishi. Hakan ne yasa a hankali ya soma romance ɗin ta cikin ƙwarewa da tsantsan soyayya, sun shiga wani irin yanayin da baki ma bazai iya furta wa ba
Daƙyar SHAREEF ya janye ta a jikinsa lokacin duk jikinsu yayi laƙwas, sai jaraba da tsantsan feelings da ke gudana a idanuwansu, yanda take manne mishi tana shirin mishi kuka shiyasa ya soma lallaɓa ta cikin ƙaunarta yace, "ta je gida idan ya gama aiki zai zo ya same ta."
Ba ya son irin hakan na faruwa dasu saboda matuƙa yana cutuwa, yana buƙatar Mace a rayuwarsa but bazai iya kusantar kowace ce ba idan har ba ta hanyar aure bane, yana tsoron Allansa a kan Zina. Ita kaɗai ce Macen da ya san ya iya haɗa jiki da ita, kuma ƙaunar da yake mata ne shiyasa bazai iya jurewa ya kasa taɓa ta ba, komai yana yi da Haseena sai dai kusantar ta ne bai taɓa yi ba, Allah yana kare sa a wannan wurin duk da ita ta sha faɗa masa, "ta gama mallaka masa komai nata, yayi abun da yake so da ita tunda aure zasu yi." Sai dai ya ƙi amincewa ya bar wannan ranan a matsayin Babban ranansu da zata kasance bayan auren su, wanda fatansa kenan ranan ta zo, sai ga shi kuma zata tafi karatu bayan ba haka ya so ba, ya so nan da ɗan lokaci kaɗan ya sanar da iyayensa don su je nema mishi auren ta, amma kuma yanzu haka nan zai jira har ta dawo tunda yana son abun da take so, ko mene ne zai iya haƙura dashi a kan ƙaunar da yake mata, ciki kuwa har da jiran dawowarta daga karatun ta.