da ta ajiye a saman window."
Tana ɗago kai ta hangi Amra ta shigo gidan baki a washe ta nufo wurin ta,
Itama sai ta bi ta da kallo tana faɗin, "har kin dawo Amra?"
Kai tayi saurin ɗaga mata tana ƙarisowa wurin ta, cike da son fahimtar da ita samun nasaran ta; ta soma mata bayani da hannu bakin ta a washe kamar gonar adduga
Mama kuwa faɗi take yi, "Masha Allah! Alhamdulillah, an dace zasu dauke ki?"
Kai ta sake ɗaga mata tana ƙara bata tabbaci cikin farin ciki
Sai ga Afra da Salma sun fito daga ɗakin a tare tunda suka ji mai Mamansu take faɗa,
Afra na riƙe da Omon da ta ɗauko suka iso wurin, ita ta soma cewa, "wai Mama da gaske Aunty Amra ta samu aikin ne?"
"Eh, ta samu tace min, tace sun ɗauke ta, sai godiyar Allah, da alamu wahalar mu ta zo ƙarshe, alhamdulillah mun gode Allah."
Ta ƙare maganar tana ɗan share ƙwallan da suka fito mata da gefen zanin ta
Su kuma su Afra sai suka rungume Yayar tasu suna murna gaba ɗaya daya
Har ita Amran sai ɓashe baki take yi,
Sai da suka sake ta kuma ta samu wuri ta zauna a kan kujera ƴar zuƙuno da ke wurin
Mama ta dubi Salma tace, "ta je ta kawo mata abincin ta yanzu."
Wuce wa Salma tayi ta je ta dauko mata abincin; ta ajiye mata a gabanta,
Su ma duk suka samu wuri suka zauna a dakalin wurin suna sauraron Mamansu da take ƙara nuna farin cikin ta
Ta amshi Omon hannun Afra tana zazzagawa tare da cewa, "yanzu Amra to sai yaushe za ki fara zuwa? Yaushe suka ce za ki zo?"
Ta ƙare maganar tana duban ta don ganin amsar da zata bata
Ita kuma ta tsame hannunta tana musu bayanin komai yanda suka yi da Hanif,
Har tana faɗa musu, "da alamun yana da sauƙin kai ne shiyasa ya ɗauke ta aikin, amma ba don haka ba; ba ta tunanin zata samu."
Mama tace, "duk da haka har da roƙon Allah da muke yi, na tabbata ya fi kowa sanin halin da muke ciki domin kullum roƙon mu a gare sa ya kawo mana mafita. Insha Allahu da yardan Allah matsalar mu ta zo ƙarshe, komai zai tafi mana dai-dai ba tare da mun yi roƙo a wurin wasu ba bare a ga gazawar mu, da ikon Allah zan jajirce wurin ganin na taimaki rayuwarku har ranan da zan miƙa ku gidan Mazajen ku, ya Allah ka kawo mana sauyi da zai sa mu farin ciki gaba ɗaya, ya Allah ina roƙonka ka zaɓa wa Yaran nan Mazaje na gari waɗanda zasu ji tausayin ku su kula daku ko bayan raina."
Gaba ɗayansu sun yi shiru suna sauraron Mahaifiyar tasu, inda a ransu suke amsa mata da Amin zuciyoyinsu cike da damuwa, a kullum addu'ar Maman nasu kenan a kansu take ƙarewa, shiyasa wani lokacin sai su ga kamar itama zata tafi ta bar su ne, suna jin babu daɗi idan ta soma addu'ar nan tana nema musu zaɓin Allah tun kafin ƙasa ya rufe idanunta, sai su ga kamar itama zata tafi tabar su ne kamar yanda Babansu ya tafi; cikin faraɗ ɗaya ya gusa a duniyar ya bar su
Jikinsu yayi sanyi; wanda yasa Amra ta kasa cin abincin ma, sai ma tsame hannu da tayi tana nuna damuwarta kamar zata yi kuka
Mama ta fi tausaya wa Amra sabida ita ce a cikin lalura, tun farko soyayyarta ta fi tasiri a zuciyarsu sabida tun lokacin da aka haife ta ta soma wayau suka gano matsalar da take tattare da ita, daga wani ciwo da tayi tun tana ƙarama shine sanadi wanda har yanzu Amra ta kasa yin magana, suna matuƙar tausaya mata shiyasa suka nuna mata ƙauna mai ƙarfi, kuma suka jajirce wajen taimakon rayuwarta sabida gani suke yi idan sun bata ilmi tamkar shi ne Jigon da zai tafiyar da rayuwar ta, ko ina ta shiga muddin tana da ilimin ta baza ta taɓa gazawa ba, koda ta Allah ya kasance ita kaɗai ce ta rage babu su a duniyar; baza ta taɓa yin Bara ba kamar yanda masu lalura irin nata suke kasancewa,
Babansu sai da ya jajirce ya nemo mata makarantar Kurame tun tana ƙarama ta soma yi har zuwa girman ta, bayan ta gama secondary sai ya nema mata nan FCE ta ci gaba da karatun ta, da farko ya so ta karanci fannin su ne na Kurame special education
Amma sai Amra ta nuna mishi cewan, "ta fi son business; sabida nan ya fi burge ta, burin ta kawai ta karanci harkan kasuwanci."
Tabbas Amra ta fuskanci ƙalubale da dama a rayuwarta, musamman girman ta da fara karatun ta a Jami'a, amma tayi haƙuri ta jajirce tunda Mace ce mai hazaƙa, karatun kawai ta saka a gaba bata da buri a duniyar nan da ya wuce karatu, domin tana ganin kamar bata da sauran amfani a duniyar nan idan ba karatun ba, shine Abokin tafiyarta, bata da ƙawa ko saurayi; bata yarda tayi su ba tunda basu a gabanta, tana ganin kamar idan ta shigo da wasu a cikin rayuwarta zata samu matsaloli da dama wanda hakan zai kawo mata cikas a rayuwa, shiyasa ta zaɓi rayuwa ita kaɗai daga ita sai Ƙanninta da iyayenta da suke ɗebe mata kewa,
Sai kuma daga baya da tayi ƙawa A'isha wacce take anguwan su, sai da A'isha tayi naci sosai sannan Amra ta amshe ta a matsayin ƙawa har take kula ta, kuma dama abu ɗaya suke karanta a school shiyasa ƙawancen nasu har tayi tasiri suna taimaka wa juna
A wannan shekaran Amra ta gama karatun ta, kuma mahaifinsu kusan watanni uku kenan da rasuwar sa, inda ya bar su da tarin matsalolin ƴan uwansa da suka amshe musu komai wurin rabon gado, daƙyar suka tsira da wannan gidan da ya rage musu, kuma ba sa tallafa musu da komai sai dai cin zarafi da cin mutunci,
Karatun su ya tsaya cak har na islamiyya,
Gwara Amra ta gama school ɗin ta, yayinda take da burin ci gaba sai ga shi Allah ya dauke wanda suke dogaro dashi,
Afra tana SS 1 ne, inda Salma take JS 2, sai dai karatun nasu ya tsaya cak a yanzu tunda basu da kuɗin biya, wannan hutun da aka tafi basu da damar komawa yanzu ko an koma; sabida basu da kuɗin da zasu biya, tunda basu kai ga biyan schoolfees ba, a cewar Babansu, "zai biya musu idan sun shiga second time." tunda a wannan lokacin bai da kuɗi already ya biya kudin karatun Amra har da bashi ake bin sa, kuma yanzu bashin yake biya bazai samu damar biya musu ba since an matsa mishi. Ana haka ga shi har Allah ya dauke abun sa daga ciwon sati guda
Ganin yanda suka shiga damuwa dukkan su, sai Mama tayi ƙoƙarin kawar musu da halin da suke ciki, tace ma Amra, "ta ci abincin tayi sauri ta gama."
Dayake ɗumamen tuwo ne wanda suka ɗumama da safe, amma ita bata ci ba tsaban zumuɗi zata je wurin samun aiki, duk yanda Mama tayi nacin ta ci abincin kar ta tafi a haka, but ta ƙi tace mata, "sai ta je ta dawo."
Afra ta soma miƙe wa a wurin tunda dama sharan ɗaki zata yi, sai ta wuce ta nufi ɗakin ta soma share wa
Ita kuma Mama ta ci gaba da yin wanke-wanken. Bayan Amra ta gama da kwanon tuwon, sai ta amsa ta haɗa dashi tace musu, "su shiga ɗaki su zauna tana zuwa."
Ɗaki suka wuce, sai sa'ilin Amra ta cire hijabin da ke jikinta tana ninke wa, ta ɗaura a kan Ghana-most go na kayanta, sannan ta zauna tana kallon Ƙannin nata tare da musu albishir, "idan har ta samu albashin ta na farko; su zasu fara koma wa makaranta su ci gaba, don ta fi son su ƙarisa karatun su zai fi."
Sai murna kuwa suke yi, sun tasa ta a gaba tana ta basu labarin abubuwan da zata siya musu in ta fara ɗaukar albashi, har islamiyya zasu koma, daga ƙarshe ta soma basu labarin girman Companin da ta samu aikin a can
Har Mama ta gama ayyukan ta; ta zo ta zauna aka ci gaba da hiran da ita,
Suna nan zaune har rana tayi, sai suka dauko garin kwaki suka tsuma suka sha haka nan babu sigar; tunda basu dashi,
Bayan sun gama suka je suka yi sallah
Daga baya Amra ta shige ɗakin su, wanda suke kwana a ciki ta kwanta sabida huce gajiya, ga kuma barci da take ji wanda bata samu tayi ba a daren jiya tsaban zullumin zata je neman aiki,
Ita kanta bata san iya adadin lokutan da ta ɗauka a kwance a wurin ba, sai jin murya sama- sama tayi a kanta, wanda lokaci guda ta wartsake sabida gane mamallakin muryan
Ilai kuwa shi ta gani a tsaye a kanta tamkar zai faɗo mata, yana kiran sunan ta kamar zai tsaga ɗakin,
"Lallai ma ƴar shilan nan; kin samu duniya kina nan kina raɓashe wa amma aka ce min ba kya gidan? Don tsaban munafurci ko?"
🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆
_____Around five o'clock suka tashi a aikin a tare,
Hanif shi ya soma zuwa office din SHAREEF ya jira sa har ya ƙarisa aikin nasa, sai suka fito a tare suka shiga Mota,
While wannan time ɗin ma Hanif ke tuƙa su,
Shi kuma Gogan yana hakimce a gefe ya ɗauki kiran Haseena wacce tayi masa a yanzu; suna shan soyayyarsu
Hanif tsam yayi yana sauraron ɗan uwan nasa cike da mamakin yanda ba ya jin kunyarsa muddin in yana waya da Haseena ne. Shiru yayi bai ce komai ba sai tuƙin da ya ci gaba da yi idanunsa a kan titi
Har sai da SHAREEF ya gama wayan before ya dubi Hanif ɗin; ganin yayi shiru kamar babu shi a motan, fahimtar da yayi kamar ma ba ya a cikin hayyacin sa ya faɗa tunani, sai ya taɓo sa yana cewa, "Mr. Man, lafiyar ka?"
Ɗago kai yayi ya zuba mishi ido, sai ya ɗan ɗage kafaɗa tare da furta, "mai ka gani?"
"Na ga ka tafi wata duniyar ne, me ke damun ka?"
"Nothing Bro."
Shiru SHAREEF yayi yana duban wayansa, sai kuma can ya sake cewa, "wai kai yaushe ne zaka kawo Budurwan ka kaima kayi aure ne?"
Kallonsa Hanif yayi, sai kuma ya taɓe baki da cewan, "aure kuma?"
"Yeah, aure. Ko maganar da ka taɓa faɗa min wasa ne?"
Murmushi Hanif yayi yace, "Nop, ba wasa bane, ai na so in riga ka yin aure fa, amma kuma yanzu tunda ka shawo kan Gimbiyyar taka i know zaka riga Ni, yanzu Ni ban ma da budurwan tunda Jamila ta yaudare Ni."
Tsaki SHAREEF ya ja yana cewa, "wannan banzan yarinyar Sha-sha-sha? dama wa zai bari ka aure ta?"
Sai Hanif ya kwashe da dariya har da dukan sitiyarin Motan, yace, "wlh ka san abin da na tuna? Kai lokacin fa mun yi rayuwa a BUK; tamkar baza mu rabu da Jamcy ba."
"Shege, ai kaima ka taɓa iskancin ka, lokacin ma Ni ban ma san da wata soyayya ba, ka riga Ni fitsare wa." SHAREEF yayi maganar shima yana dariyan,
Domin ya tuna lokacin da suka yi karatun su a BUK ne, inda wata mayyar yarinya ta liƙe wa Hanif har kuka take mishi tsaban yanda take mutuwar sonsa,
Ya gwara kanta ba kaɗan ba; daga ƙarshe kuma kamar wasa suka soma soyayya, ashe Hanif duk na ƙarya ne kawai ya biye mata ne tsaban iskanci, don lokacin shima kansa yana hayaƙi,
Lokaci ɗaya ya ɗauke mata bayan ya tafi Masters ɗin sa England, sanadin rabuwar su kenan,
Har wannan lokacin bai ƙara ganin Jamila ba tunda ya katse alaƙar su gaba ɗaya, ita kuma bata san gidan su ba; itama asalin ta ba ƴar nan bace, tana Jahar Bauchi take karatu a nan
"Hmm! Rayuwa kenan! Har yanzu gani nake yi kamar alhakin Jamila zai bi Ni, wlh yarinyar nan ta so Ni fiye da tunani, Ni kuma na cuce ta, a yanda na nuna mata soyayya ko Romeo albarka; ashe duk ƙarya ne."
"Ita kuma Jakar bata gane ba." SHAREEF ya furta yana dariyan mugunta; tare da duba wayansa jin ƙaran saƙo
Numfashi Hanif ya ja lokaci guda yana tuna fuskar Amra, sai ga murmushi a kan face ɗin sa, ya kalli SHAREEF yace, "ka san wani abu?"
Girgiza masa kai yayi ba tare da ya dube sa ba, hankalin sa na a kan wayansa
"Wani abun mamaki na gani yau, waɗanda nayi musu interview har da Kurma a cikin su."
"Kurma kuma?" SHAREEF ya maimaita yana kallonsa
Shi kuma sai ya jinjina masa kai da murmushi a kan face ɗin sa yace, "wlh kuwa, abun ya bani mamaki, yarinya ce wacce a tunanina baza ta fi 20years to 21 ba. Ita na fara ma interview, ta burge Ni wlh sabida ban taɓa ganin wata Mace kamar ta ba, Naƙasa bai sa ta dagushe rayuwarta ba, tayi ilmi har tana neman aiki."
Taɓe baki SHAREEF yayi domin maganar bai burge sa ba, sai yace, "to meye amfanin karatun nata da neman aikin tunda bazai mata amfani ba? Babu inda za a ɗauke ta kuwa in har a haka ne."
"Ni kuma sai na ga hakan ba wata matsala bace, since yarinyar tana jin me ake cewa, magana ce dai bata yi, kuma ka ga hakan babu wata matsala, already ma na ɗauke ta."
"What..! A hakan ka ɗauke ta aikin?"
Kai ya gyaɗa masa da faɗin, "Yes, don ta cancanta ne, ba wai don wani abu ba."
Tsaki ya ja yace, "baka da hankali wlh, bazai yiwu tayi aiki a Companin mu ba, gwara ma tun wuri ka sallame ta since bata da gurbi a wurin. Kurma fa?".
[09/03, 9:39 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱
__________
*BOOK1*
_______________*FREE PAGE53*
_____"Itama ai Mutum ce kamar kowa Bro, bai kamata ace don tana Kurma mu ƙi ɗaukar ta aiki ba tunda ta cancanta..."
"Wanne cancanta kake faɗi a nan? A hakan ne zamu ɗauke ta bayan ba ta magana? Da me zata yi abun da ya dace? ko ka fi son ta jawo mana asara ne? Look Hanif, any thing that will bring us back in our company; mu yi asara a cikin Company, bazan yarda dashi ba."
"Please, let's give her opportunity, if we find her wrong, we will send her away, har zuciyata ina jin tausayin ta bazan ji daɗi a kore ta ba; bayan nace mata mun ɗauke ta aiki, already yanzu tana can cikin farin ciki tana saka rai, yanzu kuma mu kore ta, i promise you idan bata yi abun da ya dace ba sai mu sallame ta."
Wani kallo SHAREEF ya watsa mishi, sai yace, "every day we find her guilty, kai zaka amshi laifin, tunda ka matsa."
Murmushi yayi yace, "yeah, na amince."
Daga nan basu sake maganar ba, har suka isa gida; don SHAREEF ya mayar da hankalinsa kacokan a kan wayansa bai da lokacin hiran da Hanif yake masa.
🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆
_____Da sauri Mama ta shigo cikin ɗakin, domin dama tana toilet ne ta jiyo muryan su Afra da Jabir suna faɗa mishi, "babu Amra a gidan," amma ya wuce su ya shige ciki yana faɗin, "idan ƙarya ne sai ya karya su."
Jin abinda yake faɗa ne shiyasa ta hanzarta ta fito don ta san ba mutunci ne dashi ba, ilai kuwa har ya shige ciki ya soma ƙunduma wa Amran zagi kamar yanda ya saba,
Tana shiga ta kira sunan sa tana cewa, "wai me kake yi ne haka Jabir? Kanka ɗaya kuwa?"
"Ke kai nawa kika gani a tare dani? In banda iskanci don na zo gun yarinyar nan ne har kuke min ƙarya ba ta ciki? To wannan wace ce?"
Ya nuna Amra da yatsa wacce take zaune duk ta tsorata da ganin sa
Tsaki Mama ta ja tace, "to wai meye haɗin ka da ita da kake son ka muzguna mata? Mu ji da wanne wai? Yarinyar nan lalura ce da ita amma tsaban rashin tausayi baza ka barta ta ji da abun da ke kanta ba, Ni fa wlh na gaji, idan baka ƙyale ta ba zan sanar da Mahaifinka don a yi mana tsakani."
Cikin rashin mutunci irin nasa ya karkace hanci da baki yana cewa, "to kin fasa mana. Tsoron sa nake ji ne? Yarinyar naki da take naƙasashshiya? Ba abun alfahari bace don na zo wurin ta na nuna ina son ta amma har wani jan aji kuke min, na rantse da Allah idan baku bi ni a sannu ba sai na farka yarinyar nan kowa ma ya huta, don wlh tunda na tashi da kwaɗayin ta sai na cika burina, ko ku bani ita in aura in yi maneji; ko kuma in karɓa ta ƙarfi, eh Allah wlh."
Ya ƙare maganar yana layi
Tuni hawaye sun soma sintiri a kan fuskar Amra, har jikinta ya soma rawa sabida jin abun da yake furta wa
While su Afra da gudu suka ƙarisa kusa da ita duk suka rungume ta; su ma cikin tsoro suka dunƙule wuri ɗaya
Ita kanta Maman ta tsorata da jin furucin Jabir, don ta san halin sa ba hankali ya cika ba, already shaye-shaye ya gusar masa da hankali komai zai iya yi, shiyasa cikin faɗa da karfin hali irin nata, ta nuna masa hanya tace, "zo ka wuce ka bamu wuri tunda ba gidan ku bane."
"Amma ai gidan Ubana ne ko? Babu wanda ya isa ya kore Ni, kuma Yaran nan Ƙannina ne ba mai raba mu, Amra tawa ce a haka nake sonta sai na ɗanɗana ta wlh, gwara ma tun wuri ki yanke hukunci kafin in sake juyo wa kanku."
Sai yakai duban sa wurin su Amra yana fito tare da turo bakin nan nasa da yayi baƙi tsaban jaraban shaye-shaye, "ke yar shila, zan tafi, ke ma ki yi tunani da kyau kwanan nan zan faɗa ma Babana a zo a sha biki dan ƙwal uban ku."
Ya tsitta miyau ya fice yana faman layi kamar zai tuntsire