x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 30 - KUNDIN CINIKAYYA

  • 87001 words
  • 90000 words
  • Out of 96350 words

Category: Romance Story +18

Views 564

09 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
wajen Suraj, amma ina hakan ya ci tura. Fusgota suraj ya ?ara yi tare da nufar hanyar past Win sa da ita.


Yana isa part Win sa ya wurga ta ciki tare da nufara kan waydrop dansa sannan ya dauko bulala tare da igiya.


Ganin hakan ya sa Zara ta fara kuka wiwi tare da fara bashi hakuri ta ce mai. "Kayi ha?uri dan Allah, ba zan sake ba, na tuba, dan Allah kayi ha?uri, dan Allah kada ka dake ni na roke ka kada ka Waure ni". Tana faWa hawaye na bin ?uncinta, amma ina Suraj ya kada sauraran ta. Aka ya janyo ta ya daure ta a jikin gado sannan ya Wauki bulala bai yi wata wata ba ya Waga domin zabga mata sai wani tunanin ya sa ya dakata.



Furzar da iska ya yi waje tare da ?ura mata ido ganin gaba Waya hankalinta a tashe duk jikinta ya ji ?e da zufa ya sa shi kwashe wa da dariya tare da zama a kan gadon yana mai fuskantarta sannan ya ce. "Dama haka ki ke da tsor ai ni ban sani ba sai yau kenan ma dama duk waWan nan rashin kunyar da ki ke yi kenan duk baki ki ke da shi ba karfi gare ki ba?, ai na dauka ke irin jarumar nan cee ashe- ashe raguwa ce. To ni dai an dai ji kunya". Ya ?ara faWa yana mai kwashe wa da dariya.


Kallon Suraj ta yi ta ce. "wallahi ?arya ka ke yi, ni ba raguwa bace ba, ni da ka ke gani na nan sai da na taSa dukan Wan sanda kuma na sha ba tare da anyi min komai ba. Kaga tunda ma na iya dukan Wan sanda ba tare da anyi min komai ba ka ga ni jaruma ce kenan. dan haka ya kamata kayi hakuri ka manta da komai na riga na gaya ma cewar na tuba na koma ga Allah. Na riga dana canza".


Kallon ta Suraj ya yi sannan ya ce. "A hakan ne ki ka canza?, yanzu- yanzun nan naga kina yiwa gimbiyoyi rashin kunya sannan kuma kice min kin canza ba wani canza wanda ki ka yi". Yana kaiwa nan ya kunce ta, sannan ya ce ta mi?e ta zauna.


Mi?e wa tsaye Zahra ta yi tare da galla masa harara sannan ta ce. "Na gode Yahya Sooraj".







***************
*Umar pov.*

BuWe idanuwansu Umar da Amra suka yi, yayin da suka gansu cikin wani kango da sauri suka mi?e tsaye sannan suka fara wage-wage can suka hango wasu matasan mata cikin ?unci da bakin ciki suna a WaWWaure.



Da mamaki Umar ya kalle su sannan ya ce. "Me ku ke yi a nan wajen?, ta ya ya haka ta faru?, me ya same ku haka?, wane ne wannan mutumin ne wai da yake addabar mutane?, mene ne yake nema ga mutane?, me yake so?, me yake da bu?ata?, waye shi?". Tambayoyin da ya shiga yi kenan yayin da babu wanda ya Wago idanuwan sa. Nan suka ji watan budurwa ta kallesu ta ce. "Wani ne governor Musa Muhammad". Nan take gaban umar ya yanke ya faWi.


Kallonsu ya yi ya ce. "Govnor Musa Muhammad kuma?, kin san wane ne gwamna musa muhammad?, shi ne fa mahaifina, kuma shi din babban mutum ne wanda gaba Waya duniya ta san shi, ya za ki zo kiyi mai ?arya. Sam -sam bashi ba ne ba".


kallon sa budurwar ta yi a karo na biyu sannan ta ce. "Kwarai da gaske mahaifinka shine wannan wanda yake yi mana barazana, yake mana duk abinda yake da bukata yake mana tozarci, ya samu cikin ba?in ciki, da wulakanci duk ya saka mu a cikin ?unci. Kuma shi ne wanda yake safaran mata, yake safaran miyagun ?wayoyi yake safarar miyagun laifuka sannan har izuwa halin yanzu babu wanda ya taSa sanin shi din babban mai laifi bane in ba mu ba. Ya kamata ka fahimce mu ya kamata ka saurare ni sannan kuma ya kamata ka yarda dani bansan wane hujja zan iya baka dangane da hakan ba amma tabbas mahaifinka masheki ne babba kuma criminal ne".


saurin dafe kansa wanda ke ?o?arin sara masa Umar ya yi dannan ya ce. " I can't believe this, mahaifi na shi yake duk waWan nan lefukan kuma ina matsayin Wanshi jami'in kuma shine ban san da hakan ba, tabbas na aikata babban kuskure, dama na daWe ina zargin shi da hakan, amma zuciya ta ta kasa aminta da haka sai kuma yanzu na zo na kara ji daga bakin ku, ban taSa tsammanin cewar mahaifina shi yake aikata duk laifukan da nake kokarin gano wane ne ainihin criminal Win ba ashe ma asalin criminal Win yana zaune a gida na ban sani ba. To wallahi ba zan bar shi ba ba zan duba ko shi Win mahaifina bane dole sai na kama shi na damka shi wa hukuma sannan an bi muku hakkin ku kum........


Maganarsa ce ta tsaya sakamakon ?arar da Amrah ta ?walla wanda ya cikashe ilahirin gidan kangon baki Waya.



Nan take suka ga ta fara laulayi tana mai dafe kanta.




?angaren su Aliyu, bai yi aune ba ya ga Safira ta buWe ?ofar mota tare da faWa wa cikin jeji. Nan take ta fara gangara wa cikin daji ba tare da ta tsaya ba. Da sauri Aliyu ya bi bayanta yayin da suka haWu su biyu suna gangarawa cikin daji.


*********
?angaren Sooraj kuwa, da mamakin sa ya ga jikin Zahra ya fara ?a??arwa.



A matu?ar tsora ce Sooraj ya mi?e tsaye tare da karanto duk wata addu'a da ta zo bakinsa.


Bai yi aune ba yaga Zahra ta tafi zata faWi da sauri ya isa gare ta tare da kare ta daga faWuwa. Nan ta faWa a jikinsa.


MANAGE PAGE PLS.


SHARE FISABILILLAH =?O?



AL?ALAMIN
'?
A'ISHA M.B=؞?=؞?=؞?
ZINARIYAR JAJIRTATTU



[12/7, 16:26] Ayeesher MB>?p?>?p?: https://whatsapp.com/channel/0029VaeK0CGLo4hfFWLtYL2g






https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
=ت? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=ت?
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.'?

*DIAMOND =؎? STARP+*
*LADIES >???
@&?>??? @&?>???
@&?*
(We stand together)
>??>??>??

(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jin?ai!

*=?%?KUNDIN CINIKAYYA* * _______________________
a tsora ce Suraj ya dube ta ya ce. "Zara me ke faruwa dake haka? me ya sa me ki haka?, ya kamata ki sanar dani me yake faruwa dan Allah ". Ya faWa a matu?ar razane.


A hankali Zahra ta buWe idanuwanta sannan ta cire jikinta daga na shi tare da ?walolo idanuwa waje tana mai yin gurnani.


Ganin hakan ya sa Sooraj razana sannan ya ja da baya, yana mai karanto duk wata addu'a da ta zo bakinsa.


"Zahra lafiyar ki ?alau kuwa?, ya kamata ki dawo yadda ki ke".



Girgiza kai Zahra ta yi sannan ta zauna a ?asa tare da sunkuyar da kanta.


Kallonta ya yi yana mai ?ura mata ido.


Nan take ya ga ta Wago idanunta tare da kwashe da dariya. Firgita Sooraj ya yi ganin yadda Zahra ta ?yal?yale da dariya.


Takawa ya fara yi tare da isa inda take ya ce. "Zahra kina lafiya kuwa?".



Fashe wa da dariya Zahra ta ?ara yi a karo na biyu tana mai faWin. "Dama kana da tsoro aka?, ai ban san aka ka ke da tsoro ba sai yau. Dama nayi hakan ne saboda na tsoratar da kai kamar yadda nima ka tsoratar dani".


Girgiza kai Sooraj ya yi ya ce. "Kenen kina sane ki ka kurma ihuun nan?, tare da kakkarwar nan?".


Girgiza kai Zahra ta yi ta ce. "A'a, wannan bana sane naji kamar an buga min guduma a kaina shi ya sa na kurma ihuu, amma ka yarda dani iya wannan ne ba da sane nayi ba".


Shiru kawai Sooraj ya yi ya ce. "Fitar min daga Waki".


TaSe baki Zahra ta yi tare da shagwaSa fuska sannan ta ce. "Saboda za ka kore ni?".



Tashi tsaye Sooraj ya yi ya ce. "Idan baki fita ba zan miki dukan babban bargo yanzu nan".



Ba musu Zahra ta mi?e tsaye tare da fice wa daga Wakin. Ganin ta fita ya sa shi jan dogon tsaki, kana ya koma kan gado.







*******************
Chan cikin jeji Safira da Aliyu suka tsinci kansu.



Ganin kan Safira na fidda jini ya sa hankalin Aliyu ya tashi. Da sauri ya mi?e a hankali saboda shima yaji rauni sannan ya yi saurin isa gare ta.


Saurin Waga masa hannu ta yi ta ce. "Kada ka kuskure ka matso kusa da ni, bana ?aunar wani abu da zai haWa ni da kai, dan Allah kayi tafiyar ka".


Aliyu bai ko saurare ta ba ya ?arasa inda take, sannan ya samu ya yagi Wan ?arami daga jikin mayafin ta, tare Waure mata inda jinin yake fita.
Kana ya shafa kan fuskarta. Saurin ture shi ta yi daga inda take sannan ta ce . "Wai bana ce ka rabu da ni ba, me ne ne na ?ulle min ciwo?, dama ba so ka ke ka kashe ni ba, to ka barni na mutu Win mana. Wai kai jami'i ne ko?, kai sam baka cancanci zama jami'i ba ko kaWan, tunda har ka iya tauye ha??in wasu saboda son abin duniya, sannan ka iya manta da irin halin da iyayenka za su shiga samm baka cancanci kasance wa jami'i ba, Allah wadaran mutum irin k.........


Maganarta ne ya tsaya sakamakon tsawar da Aliyu ya daka mata.




******
?angaren su Umar kuwa, waWan da suka yi kidnapping Win su ne suka jiyo ?ara da Aliyu ya daka. Da sauri suka fita daga wajan tare da bindigogin su domin ganin wane ne.


Umar kuwa da sauri ya nufi inda Amrah take yana mai rungume ta a kirji tare da shafan lallausan gashin kanta.


A hankali Amrah ta buWe idanuwanta tana mai rungume Umar sannan ta ce. "Ina son zan faWa maka wani abu".


?aga ta Umar ya yi daga jikinta ya ce. "Mene ne?".


Furzar da iska waje Amrah ta yi ta ce. "Shin idan na faWa maka wani abu za ka yarda da ni?".


Girgiza kai Umar ya yi ya ce. "In sha Allah, ai na san bakya ?arya, ki faWa min ko mene ne zan yarda".


Shiru Amrah ta yi na Wan wasu lokaci, murya a raunace ta ce. "Mahaifin ka shi ne wanda ya kashe mahaifiyar ka".


Rass gaban Umar ya faWi!, yayin da mutanen wajan gaba Waya suka zaro idanuwa waje.


"Ban fahimta ba, ki fahimtar da ni, ta ya ya ki ka san da cewar mahaifi na ne ya kashe mahaifiyata?, samm hakan ba zai yu ba, duk rashin imani mahaifina ba zai iya kashe rai ba".



"Tabbas idan mahaifinka ne abinda ya fi hakan ma zai aikata". Umar ya ji wata ta faWa. Da sauri ya juya domin ganin wace ce.



Chan ya hango Nurse Nadiya a Waure kusada wani benching wanda mutanen gov. Musa ke zama a kai.


Mamaki ne ya kama Umar ganin nurse Win kwanaki da ya taSa kai Amrah wajanta lokacin da ta suma.
"Kamar ke ce wannan Nurse Win ko wanda na baki amanar Amrah a asibiti lokacin muna Jigawa?". Umar ya tambaya.


Amsa nurse Nadiya ta bashi da cewa. "?warai da gaske ni ce nan ba wata ba, Mahaifin ka ya yi sanadiyar tarwatsa rayukan mutane babu adadi, shi ya yi sanadiyar rabuwar uwa da yaranta duk dan saboda abin duniya. Mahaifin ka ya kasance ya na aikata laifuka ne tun kafin ya zama Govnor, shi Win babban mara imani ne, ya ?ala wa baiwar Allah sharri wacce bata ji ba bata gani ba, ya sa kuma iyayen ta sun tsane ta dangint mijinta duk sun ?i ta, sannan kuma duk da hakan bai rabu da ita ba, yana neman dukiyarta wanda ke a Soyayyen, wanda babu mai zuwa sai ita ko yaranta, gashi ya kashe ta, yaran ma bamu san inda suke ba. Shin mahaifinka baya tunanin shima wata rana zai koma ga ubangijin sa?, baya tunanin ta yadda zai fara sauke nauyin ha??in mutane da ya ci bayan ya mutu?".



Shiru Umar ya yi yayin da ya rasa ta cewa. Ji yake dama ba ta hanyar mahaifin shi ya zo duniya ba, nan take ya ji tsanar mahaifin na shi ya cikashe zuciyarsa baki Waya.





*********
"Safira ya ishe ki aka, kina ta tsawatar min ina yin shiru, na riga na gaya miki cewa zan faWa miki komai daga baya amma kin ?i saurare na, me ki ke so nayi miki. Kin san dai ina sonki kuma ina ?aunar ki, ta ya ya zan iya cutar da wanda nake so har cikin raina?, ya kamata ki fahimce ni, duk abinda ki ka ga ina yi, to ina yi ne ba dan komai ba sai dan saboda ke, ina san na bayyana miki wata gaskiya, kuma bana don na bayyana miki wannan gaskiyar ta baki na fison na bayyana miki ki gani da kanki".



Tashi tsaye Safira ta yi ta ce. "Bana da bu?ata, ni kawai ka mayar da ni gida. Kai Win macuci ne, da a ganka a ga maciji, gwanda a fara kashe ka kafin a kashe wannan macijin, domin kai kafi maciji cutarwa".



Jin takum takalman mutane ya sanya Aliyu saurin ri?e hannun Safira sannan ya fara gudu da ita. ?o?arin wafce hannunta take amma hakan ya cutura.



Kuka Safira ta fara yi ganin yadda Aliyu ya matse mata hannu yana gudu da ita.



Aliyu bai tsaya ba saida ya isa bayan kangon babban gidan da su Umar suke sannan ya dakata yayin da ya ja hannunta tare da shigar da su domin su Suya.



****
Mutanen Gov. Musa kuwa suna zuwa wajan, suka tarar ba kowa, hakan ya sanya su koma wa inda suke.



Ajiyan zuciya Safira ta shiga jera wa tana mai kallon hannunta da Aliyu ya ri?e. Gani ta yi guri ya kaWa ya yi jajir. Nan da nan hawaye suka fara bin ?uncinta.


"Yi ha?uri Safira duk abinda ki ka ga ina yi duk saboda ke ne". Aliyu ya faWa murya a ?asa.





*************
?aki mai num105 na hango hajiya Binta ta yi tagumi idanuwanta a kan littafin da mrs Lailah ta bata, yayin da take tunano maganar da Mrs Lailah ta faWa mata kafin su rabu. "Ga amanar ?ata na baki ki kularmin da ita tamkar ?ar cikin ki sannan kada ki taSa faWa mata cewar ke Win bah mahafiyarta bace, har sai ta kai munzalin sanin hakan. ina son ki nemi ta gano inda mahaifinta ya ke".


Share hawayen da ke shirin zubo mata Hajiya Binta ta yi sannan ta ce. "Yanzu Zahra ta kai minzalin sanin wace ce ita tare da sanin inda mahaifinta yake, na san dai ba iya ita Waya Lailah ta haifa ba. Ina son na bawa Zahra wannan littafin amma ban san ta ya ya zan bata ba".



Daga nesa ta hango wata warder. Nan ta mi?e tsaye kana ta fara takawa izuwa inda wannan warder Win take.

Kallonta warder Win ta yi ta ce. "Ya aka yi?, me ya sa baki ke kinyi cutting grass Win da aka sanya ki ba".


Shiru Hajiya Binta ta yi ta ce. "Taimako nake so kiyi min, maganar cutting grass, zanyi shi, dan Allah wannan littafin nake son ki bawa DPO, kice idan ya ga MK ya ba shi wannan littafin, na san Mk zai iya sanin inda Zahra take. Ya bata littafin, gaba Waya tarihin mahaifiyar su yana ciki".




Turnu?e fuska warder Win ta yi ta ce. "Ba zan kaiba maxa kije kiyi aikin ki".


"Dan Allah kiyi ha?uri ki karSa, dan Allah". Ta faWa hawaye kan fuskarta.


Ganin hakan ya sa warder Win karSar littafin sannan ta jaddada mata cewa zata bawa DPO. Jin hakan ya sanya Hajiya Binta yin farin ciki sannan ta koma inda take.







***********************
Bayan fitar Zahra ne ta saki murmushi yayin da ta fara jin son Sooraj ya fara shiga zuciyarta.


Chan ta hango Mami zaune tana shan lemo a parlour.


Da sauri Zahra ta yi fuska tare da ?o?arin wuce wa dan kada Mami ta ganta.


Cikin rashin sa'a ta ji Mami ta ce. "Zahra zo nan".


A kunya ce Zahra ta ?arasa inda take tare da gaishe ta.


Amsa wa Mami ta yi murmushi kan fuskarta ta ce. "Zahra kenen, da fuska za ki yi ki wuce ko?".


Sosa kai Zahra ta yi ta ce. "A'a Mami, ai ban isa ba".


Girgiza kai Mami ta yi ta ce. "Wai me ke tsakanin ki keda Sooraj, naga yanzu kuna shiri ba kamar da ba, sannan naga har fita kunyi tare, yanzu ma naga kin fito daga Wakin sa, faWa min meke faruwa, kodai akwai wata a ?asa" .


A kunya ce Zahra ta sa hijabin ta tana mai rufe fuska sannan ta girgiza.



Murmushi Mami ta yi ta ce. "Mene kuma na jin kunya, ki faWa min gaskiya, nimai sa sarki ne ya je a neman miki auren ki wajan iyayen ki".


?ago kai Zahra ta yi sannan ta ce. "Ni bani uwa ko uba, amma ina da Hajiya Binta wacce ta maye min gurbin uwa".


"Ohh Allah sarki, ban san baki da iyaye ba, Allah y a ji?an su ya yi musu rahama".


Amsa wa Zahra ta yi da "Ameen". Sannan ta ?ara da cewa. "Ni bani nake nani ?ewa yahya Sooraj ba, shi yake nani?e min kinga kuwa shine yake sona, kuma nima na san yana sona kawai Soye min yake, bai san na sani ba". Ta faWa tana mai yin dariya.



Girgiza kai Mami ta yi tare da mi?e wa sannan ta ce. "Na manta ban baki kyautar da na siyo miki ba, bara naje na dauko min, ki jire min lemo na".



GyaWa kai Zahra ta yi ta ce. "Tom zan jire miki".


Jin hakan ya sa Mami barin parlourn tare da shiga part Win ta.



Duk abinda suke yi a gaban idanuwansu Gimbiya saratu da yaransu.

Tashi Zahra ta yi jin wani ?ishin ruwa ya dame ta ya sata nufar hanyar kitchen domin samo ruwa.





Mi?a wa Samira ?ullin magani Gimbiya saratu ta yi ta ce. "Kije ki zuba wannan garin maganin a cikin lemon nan kafin wan can sheWaniyar yarinyar ta dawo daga kitchen, maza-maza, ina son A'isha ta mutu idan ta sha maganin nan.



Da sauri Samira ta karSa tare da zuwa inda lemon Mami yake sannan ta fara zazzaga maganin a ciki.


Dai-dai lokacin Junaid ya shigo da sauri ya
End Ads