x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 22 - KUNDIN CINIKAYYA

  • 63001 words
  • 66000 words
  • Out of 96350 words

Category: Romance Story +18

Views 575

09 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
tsananin ciwo Musa ya shiga Wakin nasa. Ganin yana kwance ya sa shi sakin murmushi ba tare da imani ko tausayawa ba ya samu pillow ya danne fuskar mahaifin nasa da shi. Haka Alhaji Muhammad ya dinga kuruwa har rai ya fita daga jikin shi. Musa bai sake shi ba saida ya tabbatar da baya da sauran numfashi. Hakan ya sa shi farin ciki a sa'inda ya dinga ganin kansa matsayin govnor domin kuwa tunda mahaifin nasa ya mutu babu wanda zai ana shi zama govnor.

Jama'a sun yi kuka na rashin Alhaji Muhammad da suka yi, yayin da ita ma Khadija ta ci kukan ta har ta gode wa Allah.

Musa ya fara neman takara shida babban Abokin sa wato Abdullahi wanda suka taso tun suna ?anana har izuwa girmansu tare suke. Hakan ya sa kowanensu yake da burin zama Wan siyasa. amma sai dai shi musa bai yi nasara ba domin babu wanda ya karSe sa hannu biyu. A yayin da Abdullahi ya zama babban Wan siyasa ya yi al?awarin gyara ?asar sa da mutanen cikin ta. Musa ya ji aushi sosai ganin abokin saya samu takara shi bai samu ba, hakan ya sa ya Wora tsanar duniya a kan abokin nasa, a yayin da yake zuwa wajan Abdullahi da fuska biyu na kirki da kuma na mugunta.

Umar yana da shekaru biyar a duniya Khadija ta kuma haifo santalelen Wanta saidai yaron bai zo da rai ba. Bayan wasu shekaru Khadija ta sake haifo namiji wanda ya ci suna Usman, Sannan Ramlat sai kuma ta ?arshe Khairiya wanda su ukun gaba Waya shekara WaWWaya ne a tsakani.


Haka rayuwa ta cigaba wataran da dad'i wataran kuma godiyar Allah. Ana tsaka da haka wata rana Khadija na gyara Wakin Mijin ta, nan ta tarar da wani caset. ?aukar caset Win ta yi sannan zuciyar ta tace da ita ta saka caset Win a tv ta ga ko film ne. Bayan ta saka caset Win ne a tv ta ga abin da ya yi matu?ar firgita tunaninta. Mijinta ta gani ya kashe mahaifin sa da hannunsa . Hakan ya sa ta ji dana sanin auran sa. A dai-dai wannan lokacin kuma Musa ya shigo ya tarar da ita a Wakin tana kuka. Nan dai ya gano cewa ta gano shi ne wanda ya kashe mahaifin sa. Ganin hakan ya sa Musa ya fara ro?on matar sa da ta rufa masa asiri. Amma ita kuma Khadija ta?i amincewa sannan ta ce dole ta sanar da ?an sanda ko wane ne mijinta domin ba za ta iya take gaskiya ba. Ganin dai ta?i bashi haWin kai ne ya sa ya Wauki glass cup sannan ya rotsa wa kanta. Nan take kanta ya fara fidda jini yayin da ta faWi ?asa mutacciya. A dai-dai wannan lokacin Umar ya dawo daga makaranta sannan ya shiga cikin Wakin nan ya tarar da gawar mahaifiyarsa a kwance. Hakan ya sashi sakin ?ara yayin da ya faWi ?asa sumamme.

Ganin hakan ya sa Musa ya goge kowane sheda da ?an sanda za su bi domin gano makashin.


Bayan nan ne ?an sanda suka zo suka yi ?araci binciken su basu samu komai ba. Hakan ya sa haka rufe case Win.


Bayan wasu kwanaki ne Umar ya dawo cikin hayyacinsa a yayin da yake mafarkin mahaifiyar sa sannan ya ?udiri niyar dole ya zamo jami'i, domin ya san wanda ya kashe mahaifiyar sa sannan kuma ya kare ?asar sa daga sheWanun mutane irin mahaifinsa. Umar ya fara jin tsanar mahaifinsa ne tun lokacin ya ga mahaifin sa da wasu karuwai a gidan su. Daga wannan rana Umar ya tsani mahaifin sa.


Bayan Umar ya yi karatun sa na boko da na addini ne ya shiga training school na jami'ai. Hakan ya sa ya fara gudanar da al'amuran sa shi Waya. A sa'inda duk abin da ?anensa suke da bu?ata shi yake musu. Kan kace me Umar ya zama babban jami'i wanda gaba Waya ?asa ke magana kan ?warewarsa domin kuwa duk wani mai laifi idan ya yi musu wahalan kama wa Umar shi ne wanda ake bawa wannan aikin kuma duk in da wannan mai laifi yake zai nemo shi sannan ya tabbatar da an hukunta shi. Aka ya cigaba da bincike domin gano makashin mahaifiyar sa, sai dai har izuwa wannan lokacin bai gano ko wane ne ba kuma bai san irin aikin mahaifin sa ba.

A Sangare guda kuma shima Musa ya zama Wan siyasa ba tare da an san ta wace hanya ya bi ya samu wannan takara ba.

*Amma idan ta yi tsami zamu ji ta yadda ya samu takara shiga siyasa*


Haka su Khairiya suma suka taso cike da ?aunar juna. Yanzu dai Usman ya gama karatun sa yana aiki a office. Sai kuma Ramlat wacce ke University level 300 tana karatun Optometrist. Da kuma Khairiya wacce ke 100 level tana karatun biology.


*Wannan dai shi ne takamaiman tarihin Umar*


___________________
Shigowa da motoci masu tsaron govnor Musa suka yi. Fitowa Gov. Musa ya yi daga cikin mota ganin babu motoci guda biyu a gidan hakan ya nuna masa alamun cewa tabbas Umar ya fita.



Kallon masu tsaron gidan ya yi ya ce. "Where's Umar?".

Amsa Waya daga cikin masu gadin ya bashi da cewa. "Yanzu suka fita".


Girgiza kai Gov. Musa ya yi ya ce. "Kun san in da suka je?".


Amsa suka ba shi da cewa. "A'a, amma mun ji kamar suna zancen za su je Kano".



"Kano!". Gov. Musa ya maimaita sunan. "Shi ke nen". Kawai ya ce sannan ya shiga part Win shi. Yana shiga ya yi saurin Waukar wayarsa sannan ya lalubo number Aliyu tare da danna mai kira.





______
Aliyu da ke zaune sai faman kallon Safira yake yana murmushi ne ya ji wayar sa na ruri. Maida kallonsa ya yi kan wayar. Ganin sunan wanda ke bayyane kan screen Win ne ya sa shi mi?e wa sannan ya bar cikin parlour Win daba bisani ya Waga kiran. Ya ce. "Salamu alaikum".


Daga Wayan Sangaren Gov. Musa ya amsa sallamar sannan ya ce. "Aliyu ina da bu?atar taimakon ka yanzu dan Allah, Wa na da ?annensa su tafi hanyar Kano, yanzu haka na san sun kusa isa chan, ina son ka bibiyar mun su bana son ya gano gaskiyar ko ni wane ne, sannan kuma bayan nan akwai yarinyar Mrs Laila a Kano ina son ka bincika min duk in da take ka sa a sace ta. Dan Allah ba dan ni ba Please, zan tura maka duk kuWin da ka ke da bu?ata".



?an jimm Aliyu ya yi sannan ya ce. "Shi ke nen naji, million goma shi ne kuWin aiki na, kuma cash nake so ba transfer ba".


"Shi ke nen Aliyu, ni zan ma ?ara maka ya zama twenty ni dai kawai buri na shi ne ka dakatar da su sannan ka nemo in da yarinyar Lailah take".



"Kada ka samu damuwa wannan abu ne mai sau?i, nan da sati Waya zan nemo duk in da take, kai dai kawai ka shirya min kuWaWe na". Cewar Aliyu.



"Angama". Gov. Musa ya faWa tare da katse wayar yana mai maida numfashi.



Sauke ajiyan zuciya Aliyu ya yi sannan ya shiga Wakin sa tare da haWa kayan sa cikin travel box. Bayan ya gama saka kayansa ne ya nufi Wakin su Grandpa sannan ya sanar da su yana son yin tafiya sainan da sati zai dawo. Addu'a suka yi mai. Daga bisani ya saka kayansa cikin mota. Babu abin da Safira kai ta faman yi sai satar kallonsa.


Babu zato suka haWa ido da Safira, saurin kawar da kanta Safira ta yi gefe. Murmushi Aliyu ya yi ya ce. "Kodai za ki je ne?".


TaSe baki Safira ta y ta ce. "Nop, ni kam babu in da zani". Ta faWa tare da shige wa ciki gidan.



Girgiza kai kawai Aliyu ya yi tare da tada mota sannan suka yi sallama da mutanen gidan gaba Waya daga bisani ya fice daga gidan. Bai zarce ko ina ba sai hanyar Kano.



_________________________
Zahra na fita ta hangi kuloli a jere kan dining hakan ya sa ta haWiye yawu. Da sauri ta je ta zauna kan table ganin zaman kujera ba zai finshe ta ba, ya sa ta kwashe gaba daya kulolin ta jera a ?asa sannan ta zauna a ?asa ta fara buWe kulolin. Take wani irin ?amshi ya bugi hancin ta hakan ya sa lumshe idanuwanta sannan ta sake buWe su. Tuwon shinkafa ne miyan taushe ya ji naman turkey yayin da bangare Waya kuma fried rice ne ya ji coslow da naman kaza. Sai Sangare Waya kuma kunun aya cikin jug da kuma lemo mai sanyi tare da Fruit salad.


Ganin ba za ta iya Wauke ido kan wannan abinci ba, ya sa ta cire duka chokulan kan trey Win abincin ta zubar a ?asa. Hakan ya sa ?aran chokulan suka bada wani irin ?ara.


Jin ?ara daga parlour ya sa su Gimbiya Saratu da Talatu tare da ?a?anta fitowa. Yayin da ita ma a dai-dai lokacin Mami ta fito daga cikin Wakin ta domin ganin meke faruwa. Dai-dai lokacin kuma Junaid ke dawo wa daga fadan mai martaba.


Fitowa Sooraj ya yi daga cikin Wakin sa. Tare da nufar hanyar parlour. Tsaya wa chakk gaba Waya suka yi ganin yadda Zahra ke Wura wa ciki ta abinci. Cin abinci ta take hankali kwance ba tare da tsoro ko wani tunani ba. Sai loma take ta kwara abincin da lemo tare da kunjn aya. Haka ta cigaba da cin abinta ba tare da ta kula da zuwansu Sooraj wajan ba.


Baki sake gaba Waya suke kallonta. Zahra kuwa sai da ta cinye Tuwon shinkafan tass sannan ta koma kan fried rice. Haka ta na ci tana sumbatu. "Wayyo dad'i kashe ni, da wahala gwanda dad'i ka kashe ni, dad'i kashe ni, da wahala gwanda dad'i ka kashe ni"

Sannan ta ?ara da cewa. "Gaskiya kuWi duniya ne, Allah kayi mu yadda muke so. Yoo ?an banza ba dole su dinga tumbi ba suna cin abinci mai daWi da gina jiki. DaWin ta ma ba za su ci ba, kinga kenen zanci sosai na ?oshi, naci na ci na bar na bari. Shi ya sa wannan Gimbiya Talatun bakinta yake wangalele kamar na akuya tunda tana cin abinci mai daWi dole, sai kuma waWan nan ?walaye ukun nan su Samira ko, dole su dinga yadda suka gadama tun da suna cin kayan dad'i. Yanzu ni duk ba wannan ba hanyar da zanbi na koya wa wannan mai ?aton kai hankali nake Sooraj yake ko, saina koya mai hankali, ba an ce ni ce zan dinga kula da shi ba, kawai idan Mami ta bani abinci shi na cinye sai in kai mai ragowa ya ci". Ta ?arashe tana mai bushe wa da dariya.


Duk abin da take a gaban idanunsa. A sa'inda Sangare Waya Gimbiya Talatu ta yi mugun ?ulu wa. Jin abin da Zahra ta faWa game da halittar bakinta. Sooraj kuwa mamaki kawai ya shiga yi ganin yadda take ta sumbatu tana cin abinci duk ba ga san suna tsaye a wajan ba.



Saida ta gama da komai da cikin kulan tass sannan ta kora da kunun aya da fruit salad. Ji ta yi cikin ta ya yi mugum cika. Gatsa ta yi ta ce. "Ya kamata ki kwanta Zahra domin abincin da ki ka ci su zazzage". Ta faWa tana mai kwanciya a ?asan wajan tana mai fuskantar saman silin. Gabanta ne ya bada wani rass!, yayin da zuciyarta ya fara dukan uku-uku ganin gaba ki Waya ?an gidan tsaye a kanta.



Zumbur ta mi?e tsaye tare da karkaWe jikin ta.


Kallonta Sooraj ya yi tare da kallon kulolin da ta cinye abincin ciki sannan ya girgiza kai ya ce. "Sannunki da aiki, yanzu mutum in banda dabba waye zai iya cinye uban abincin nan, to ki sani cewa baki ci a banza ba domin kuwa sai kin koma kasuwa kim siyo duk abin da ki ka ci sannan kin sake dafa irin shi komai da komai".



Rai a Sace Gimbiya Talatu ta ce. "In banda iskanci ?ar talakawa har ta samu matsayin da za ta ci abinci a kulan da muke cin abinci. Sannan kuma har ta samu damar ta ce wai ni mai wangalellen baki. Lallai kam wuyarki ya isa yanka".



"Madam za ki iya mana shiru a nan". Cewar Sooraj. Tsaki Gimbiya Talatu ta ja tare da wuce wa part Win ta ganin hakan ya sa Saratu ta bi bayanta. Sannan sauran ma suka watse ya rage Sooraj, Mami, da kuma Zahra.



Kallonsa Zahra ta yi bakin ta duk mai?on kaza ta ce. "Yarima wallahi ban iya girki ba, ban taSa yi ba, ta ya zan iya yin mai daWin wannan?, kayi ha?uri dan Allah".


Gyara tsayuwar sa Sooraj ya yi ya ce. "My wish is my command, dole ki sake girka irin wannan kuma taste Win dole ya zama iri Waya.


Zaro idanuwa waje Zahra ta yi jin kalmarsa ta ?arshe. "Ni na san ma sai dai nayi muku jagwab Win abinci don ban iya ba".



Bai ?ara cewa komai ba ya koma part Win sa.


Kallonta Mami ta yi ta ce. "Zahra kiyi abin da ya ce karki damu da wajan nan da ki ka Sata zan sa ?an aiki su gyara, maza kije ki siyo ingredient Win, domin ya ce ba za'a taSa na gida ba".



"Shi ke nen". Zahra ta faWa tare da shiga Waki ta saka saka hijabi. Fitowa ta yi yayin da Mami ta ba ta isashun kuWaWe domin siyan kayan abincin da ta ci. Bayan ta ba ta kuWin ne fita daga cikin harabar masarautar tare da tarar mai napep ya kaita kasuwa.



Bayan Aliyu ya isa Kano ne ya samu wani guri kusa da kasuwar kwari ya yi parking. Sannan ya fara waige-waige. Chan ya hango mai tallan tsire. Hakan ya sa ya tare shi tare da siyan na dubu Waya domin rage yunwar da take damun shi.


Zahra kuwa saida mai napep Win ya yi tafiya mai nisa sosai kafin nan ya isa kasuwar kwari. Chan ta hango tsayuwar Aliyu jikin motarsa. Tunani ta shiga yi kamar ta san wannan mutumin. "Wannan kamar wannan Wan sandan da ya so raina min hankali a magar?ama ne ko?". ?ara kura masa idanu ta yi. "Laa babu tantama kuwa shi ne". Dakatar da mai napep Win ta yi da ya tsaya. Ba tare da ta tsaya biyan mai napep kuWin sa ba ta tsallaka titi da gudu tare da nufar in da Aliyu yake tana mai faWin. "Malam Wan sanda mai Wagaggen wando kaine a garin Kano?".


Juyawa Aliyu ya yi ganin waye wannan mai furta wannan kalma. Nan take ya haWa ido da Zahra. Take gabansa ya yi mummunar faWuwa!. Nuna ta ya yi ya ce. "Safira!".


Kallonsa Zahra ta yi ta ce. "Wace ce kuma haka?, wai Safira, kai ni ce fa baka gane ni ba a magar?ama da ka zagar min uwa na so nayi maka duka ka tuna?. Ba kai ne wannan Wan sandan mai Wagaggen wando ba?".


Dafe kansa Aliyu ya yi jin yadda kansa ke ?o?arin sara masa. Ri?e kansa sosai ya yi domin yin tunanin a ina ya santa. ?aga kansa ya yi ya kalle ta ya ce. "Kenen ba ke ba ce Safira ba?".


HaWe giran ta Zahra ta yi tare da turnu?e fuska ta ce. "Wace ce kuma Safira?, ni fa malam sunana Zahra ba Safira ba".



"I am totally confused, what's going on?". Aliyu ya tambayi kansa. Nan take ya fara tuna wan can ta magar?amar. Rass gabansa ya faWi. Cikin ransa ya ce. "Tabbas wannan ita ce wanda na gani a magar?ama kwanaki mai brown eyes, sannan Safira ma tana kama da ita, ga kuma ranar nan na ga wata mai kama da Safira mai grey eyes. Kenen hakan yana nufin su uku ne?, idan kuwa hakan ta kasance to tabbas hasashen Mom gaskiya ne, kenen hakan yana nufin yaran Mrs Laila ne?!".







COMMENTS & SHARE FISABILILLAHI =?O? =?O?
AL?ALAMIN
'?
A'ISHA M.B=؞?=؞?=؞?
(Zinariyar Jajirtattu)




Follow the

*=?%?KUNDIN CINIKAYYA*ؐ?ؐ?.
Daji Magar?ama Birni
WRITTEN & DIRECTED BY
'? A'ISHA M.B =؞?=؞?=؞?
(Zinariyar>???
@&?Jajirtattu)


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
=ت? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=ت?
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.'?

*DIAMOND =؎? STARP+*
*LADIES >???
@&?>??? @&?>???
@&?*
(We stand together)
>??>??>??

(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jin?ai!

*=?%?KUNDIN CINIKAYYA* * *___________________________________________*
"Wai tunani me ka ke yi ne malam Wan sanda?". Cewar Zahra.

Murmushi Aliyu ya saki sannan ya ce. "Babu komai kawai dai ina mamaki ne, masha Allah gaskiya naji daWin haWuwa da ke. Idan babu damuwa shin zamu iya zama abokai?".


Harara Zahra ta galla mai sannan ta ce. "Ta ina ka taSa jin ana aboki tsakani mace da namiji?, ni bana son wanda zamu fara abota ya kawo min zancen soyayya, atohh dai, dan na san yawancin ku daga abota za ku fara sai a zarce soyayya".

Dariya Aliyu ya yi ya ce. "Aba dai karki damu ni ina da ma wacce zan aura, sunanta Safira".


TaSe baki Zahra ta yi sannan ta ce. "To Allah ya bar soyayya".

Amsa wa Aliyu ya yi da "Ameen".


"Shi ke nen, ni zan tafi, zanje in siyo abu ne a wannan kasuwan kada na daWe kuma wan can yariman ya zo ya fara balbale ni da masifa, ni bai san ma Waga mai ?afa kawai nake ba".
Zahra ta faWa tana mai ?o?arin tafiya.



Saurin dakatar da ita Aliyu ya yi sannan ya ce. "A'a karki tafi bari nayi miki rakiya, ai yanzu mum zama abokai ko, don haka duk abin da ki ka siya ni nan zan ri?e".


Dariya Zahra ta yi ta ce. "Kai kuwa ka san me zan siyo?, ba za ka iya ri?e wa ba, idan na ce zan baka duk abin da zan siya sai dai ma na saka kuka domin ba za ka iya ba, kawai dai kayi tafiyarka".


Girgiza kai Aliyu ya yi ya ce. "Aba dai, ni fa ba ragon namiji
End Ads