x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 21 - KUNDIN CINIKAYYA

  • 60001 words
  • 63000 words
  • Out of 96350 words

Category: Romance Story +18

Views 563

09 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
yi sannan ya ce. "Shi na gadaman zuwa kai mene naka?".


"Bakomai ranka shi daWe ". Driver Win ya faWa.


Kai tsaye kasuwa ya nufa da su. Yayin da ya tarar da taru jama'a sun yi zagaye da alama wani abu ne ke faruwa.



?angaren Zahra kuwa babu abin da take sai surfa bala'i yayin da ta rikita kasuwar a lallai sai an fito da wannan kuWi.


Babu abin da mutane ke yi sai kallo.



Fitowa Yarima Sooraj ya yi daga cikin mota. Daga nesa su Samira suka hango shi. Nan take cikin su ya Wuri ruwa. A hankali suka silale daga wajan.



?arasawa wajan Sooraj ya yi. Nan idanuwan shi ya sauka a kan Zahra wanda sai faman masifa take ta inda take shiga ba ta nan take fita ba. Takaici ne ya kama Sooraj, dubanta ya yi ya ce. "Ke baki da hankali ne za ki zo ki tada wa mutane hayaniya a wajan nan". Ya faWa cikin Sacin rai.



Dubansa Zahra ta yi nan suka haWa ido a tare. take gaban kowanensu ya faWi!, yayin da suka fara jin wani irin yanayi na da ban.


Galla masa harara Zahra ta yi ta ce. "Kai malam waya gayyace ka nan?, shin ka zo ka biya kuWin da haka sace ne?, to maza ware daga nan".


Nan take ran Yarima Sooraj ya ?ara Saci. Take ya ji tsanarta ya shiga cikin ransa ya tsani mace mara kamun kai da rashin sanin darajar kai.



Juya wa Yarima Sooraj ya yi tare da barin wajan. Shiga cikin mota ya yi yayin da driver suka tada mota suka bar wajan.

Kai tsaye masarauta suka nufa.


Bayan tafiyar Sooraj ne Zahra ta ga kuWin a dun?ule s ?asa. Hamdala ta yi tare da bawa mutanen gurin ha?uri. Mi?a wa mai kayan kuWin ta yi tare da karSar abubuwan da ta siya.


Waige-waige ta fara yi domin gani su Samira amma ba ta gansu. Haka ta ci gaba da cigiyar tmds ta ga ba zata iya ba ta shiga cikin mota yayin da driver ya ja ta suka bar kasuwan.




Shiga ciki motocin su Sooraj ya yi cikin masarauta. Nan take dakarai da fadawa suka shiga dur?usawa suna kwasar gaisuwa tare da yi masa ?irari.



Fitowa Yarima Sooraj ya yi tare da amsa gaisuwar tasu.


Yayin da su Gimbiya Talatu suka sha jinin jikinsu. Gaishe da mai martaba Yarima Sooraj ya yi cikin girmama wa tare da gaidar da su Gimbiya Saratu. Sama-sama su Gimbiya Saratu suka amsa.


Part Win sa ya nufa tare da nufar Wakin ajiyar sa sannan ya saka thumbprint Win sa. Nan take ?ofar ta wangale gani ya yi an tsaftace Wakin an gyara shi ba kamar yadda yake ba. Mamaki ne ya bayyana kan fuskarsa. Da sauri ya fita daga cikin Wakin tare da fitowa harabar fada yana mai ?walla kiran kowa na wannan masarautar. Kan ka ce me mutane sun taru a fada.


Kallon kowanensu ya yi sannan ya ce. "Wane ne wanda ya shiga Wakin ajiya ta?". Shiru gaba Waya suka yi babu mai bakin magana. Dai-dai lokacin da Mami da su Samira ke ?arasowa wajan.



Daka musu tsawa ya yi yana mai faWin. "Na ce wane ne ya shiga Wakin ajiya ta?". Ya faWa rai a matu?ar Sace. Sannan ya ce. "Tabbas ko wace ce wannan ?ar le?en asiri ce kuma ba zan rabi da koma wane ne ba. babu wanda ya san password Win wannan Wakin sai ni kaWai, ta ya ya haka iya buWe wa bayan ni kaWai ne na san password Win?".


Kallonsa Mami ta yi ta ce. "Eh wata sabuwar ?ar aikin mu ce sunanta Zahra. Laifi ta yi shi ne mai martaba ya ce za ta dinga share wannan Wakin kuma babu ranar da za ta tashi ta faWi ba ta share ba".


"Where is she?". Yarima Sooraj ya tambaya cikin tsananin Sacin rai.



Dai-dai lokacin da motar su Zahra ke shigowa. Parking motan ya yi yayin da ta fito tare da kayayyakin da ta je siya.


Maida kallonsu suka yi baki Waya kanta. "Yauwa ka ga ?ar halak ita ce wannan". Mami ta faWa tana mai nuna Zahra.



Take rab Yarima Sooraj ya ?ara Saci ganin yarinyar da ya gani a kasuwa. ?arasawa wajan Zahra ta yi ganin yadda gaba Waya suke binta da ido ya sa ta kawar da kanta gefe.



Nan take ta haWa ido da Sooraj. Take gabanta ya faWi!. Sakin kayan da ta ri?o ta yi gaba Waya suka faWi ?asa. Sannan ta fara tafa hannunta tare da ri?e haSarta ta ce. "Iyyeeh!, wato har gida ka biyo ni kenen, ?ara ta ka kawo ko me?, dama ina ganin fuskar ka na san kai ba na Allah ba ne. To maza zo ka fice daga cikin masarautar nan kada ka bari Yarima Sooraj ya shigo ya tarar da kai a nan domin ba za ka ji da dad'i ba".


Murmushi Yarima Sooraj ya yi ya ce. "Au aba da da gaske?".


Amsa Zahra ta bashi da cewa. "?warai da gaske nake ko zaci ?arya nake?. Idan ka bari Yarima Sooraj ya zo ya ganka a nan ba za ka ji da dad'i ba".


Kallonta Mami ta yi ta ce. "Wane Yarima Sooraj kuma bayan gashi nan a gaban ki".



Nan take gaban Zahra ya bada wani irin sauti. "Kambala'i, da gaske shi ne?".


Amsa Mami ta ba ta da cewa. "?warai da gaske shi ne".


HaWiye tsoron da ke ?o?arin bayyana Zahra ta yi ta ce. "Shi ke nen tawa ta ?are!".











*KUYI HA?URI DA RASHIN UPDATE DA WURI DAN ALLAH*.





LIKE, COMMENT AND SHARE FISABILILLAHI =?O? >?z? >?z? =?O?

AL?ALAMIN
'?
A'ISHA M.B=؞?=؞?=؞?
(ZINARIYAR JAJIRTATTU)


*=?%?KUNDIN CINIKAYYA*ؐ?ؐ?.
Daji Magar?ama Birni
WRITTEN & DIRECTED BY
'? A'ISHA M.B =؞?=؞?=؞?
(Zinariyar>???
@&?Ja???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?jirtattu)


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
=ت? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=ت?
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.'?

*DIAMOND =؎? STARP+*
*LADIES >???
@&?>??? @&?>???
@&?*
(We stand together)
>??>??>??

(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jin?ai!

*=?%?KUNDIN CINIKAYYA* * *___________________________________________*
Jiki a muce Zahra ta Wauki kayan da ta zube a ?asa sannan ta fara ?o?arin wuce wa ta gefen Sooraj, a sa'inda zuciyarta ke dukan uku-uku!.


Daga sama ta ji muryarsa. "Dakata!". Ta ji Sooraj ya furta.


Tsaya wa chak Zahra ta yi yayin da ta kasa motsa ko da Wan yatsarta ne saboda tsananin tsoron da ta shiga.


Zagayowa Yarima Sooraj ya yi har gabanta sannan ya tsaya yana mai fuskantar ta. Yayin da Sangaren guda idanuwan jama'a a kansu.


?ura mata idanuwansa ya yi masu matu?ar Waukar hankali sannan ya ce. "wace ce ke?".


Jin tambayar da ya yi mata, hakan ya sa Zahra ta bashi amsa da cewa. "Ni mutum ce mana".

Kallonta ya yi cike da mamaki ganin yadda babu wata alama na nuna jin tsoronsa a tattare da ita, hakan ya ?ara bashi aushi. "Ke haka na ce wace ce ke, me ya kawo ki wannan masarautar?, sannan daga ina ki ka fito?, da me ki ke takama?, sannan tambaya ta ?arshen ta ya ya ki ka iya buWe Wakin ajiyana bayan ni kaWai ne na san ma?ullin sirrin buWe wannan Wakin?".


Zololo Zahra ta yi tana kallon shi. "Kai kuwa Yarima irin wannan tambayoyi haka sai ka ce google ake tambaya, ai sai kayi min tambayar Waya bayan Waya. To farko dai ni sunana Fatima ana kira na da Zahra, na rasa mahaifiya ta ne tun kafin na san ciwon kaina, yanzu haka bani da kowa sai iya Aunty Binta wacce ke kula da ni. Sannan batun me ya kawo ni masarautar nan babu ita domin ba ni ce na kawo kaina ba Mami ce ta bu?aci na zo nayi aiki domin tara kuWin motan da zan koma garin mu Jigawa. Sannan ka ce da me nake takama, to ni dai babu wanda nake takama da shi sai mahallici na bayan shi kuma babu, sannan sanin ta yadda na iya buWe wannan Wakin abu mai sau?i ne domin wani suna kawai na danna ya buWe, shi ke nen".


Ajiyan zuciya Sooraj ya sauke!, sannan ya ce. "Har yanzu baki bani amsa gamsashiya ba. zan ?ara tambayar ki a karo na uku ko. Wace ce ke?".


Furzar da iska mai zafi Zahra ta yi kana ta ce. "Kamar yadda na faWa maka tun fari, sunana Zahra, ni Win na taso ni cikin magar?ama tsakiyar masu laifi, hatta daga yin wayo na har izuwa girma na a magar?ama nayi".


Zaro idanuwa waje gaba ki Waya al'ummar masarautar suka yi.
Murmushi Sooraj ya yi sannan ya ce. "Kenen dai ke Win babbar mai laifi ce ko?".


Sauke ajiyan zuciya Zahra ta yi!, sannan ta ce. "A'a, mahaifiyata ce haka yi mata sharri shi ne aka kaita magar?ama bayan ta haife ni ne ta rasu, kuma ?an uwanta suka ?i ?arSa ta shi ne Hajiya Binta ta raine ni". Ta ?arashe maganar zuciyarta nayi mata zafi da ?una.



Murmushin mugunta Sooraj ya saki kana ya ce. "Kenen dai mamarki ita ce muguwa ko?, ita ce babbar mai laifi har aka kaita magar?ama. Ai dole ma ?an uwanta su yi rejecting Win ki saboda kar su zo suna dana sanin karSar ki, sai kuma gashi kema kin yo halin uwar taki".



Danne fushin da ke ?o?arin bayyana kan fuskar ta Zahra ta yi tare da kawar da kanta gefe sannan ta ce. "Yarima ka san me za ka faWa dan Allah, ka iya sarrafa harshen ka".


"Ba zan sarrafa harshen nawa ba". Sooraj ya faWa a matu?ar tsawa ce.


Nuna Zahra ta yi da yatsarsa sannan ya ce. "Na tabbatar da cewa ke ?ar le?en asiri ce, kuma idan ki ka kuskure na gano ko asalin wace ce ke to ba za ki sha ba". Yana kaiwa nan ya shige cikin fada sannan ya nufi part Win ta.



Sallamar kowa Junaid ya yi, yayin da jama'a suka watse saura mutanen cikin masarautar.


Kallon Zahra Mami ta yi sannan ta ce. "Zahra tawo mu shiga daga ciki".


Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Zahra ta yi ta ce. "Wallahi Mami nayi duba da irin mutunci da kuma kima da ki ke da shi ne a waje na. Hakan ya sa na rabu da yarima Sooraj, amma da ba dan haka ba wallahi sai ya san cewa Allah Waya ne, ba zan ji daWin a zagar wa wani mahaifiyarsa ba, haka zalika nima ba zan ji daWin a zagar min tawa mahaifiyar ba, da ka zagin uwa ta na gwammace ka kwana kana zagi na".


Tana kaiwa nan ta shige cikin fadan sannan ta shiga Wakin kwanan ta wanda haka ware mata a matsayin ?ar aiki.


Kallon Juna Gimbiya Saratu da Talatu suka yi tare da bushe wa da dariya yayin da suka ri?e hannun juna sannan suka shige part Win su.

Girgiza kai kawai Mami ta yi sannan ta ce. "Allah ya ganar da ku gaskiya". Ta faWa tare da shige wa part Win ta.


Rakiya Junaid ya yi wa mai martaba izuwa fadar sa. Gaba Waya gidan ya koma kaman gidan makoki. Babu wani hayaniya ko surutu. Abincin ma da aka jera kan dining babu wanda ya bi ta kansu.



Zahra na shiga Waki kuwa ta kwanta kan gado. Yayin da fuskar Sooraj ya fara yi mata gizo. Lokaci Waya ta ji tsanar sa ya mamaye zuciyar ta. "Aikin banza kawai, dan kawai yana matsayin Wan gidan sarauta shi ne zai zo ya dinga raina wa mutane hankali, ni Allah ya bani kuWi ma ni na haWa kuWin mota na tafi, na san kuWin motan ba za ta wuce dubu biyu zuwa dubu uku ba". Dafa cikinta ta yi jin yadda yake murWa mata alamun yunwa take ji.



"Kambala'i, ashe fa ban ci abincin safe ba na fita, chab Zahra me ki ke jira maza-maza tashi kije ki cika cikin ki". Ta faWa tana mai mi?e wa tsaye sannan ta nufo hanyar ?ofar Wakinta ta murWa handle Win ?ofar ta fita.






_________________________
"Dan Allah Amrah ki nutsu, ko daina kuka kinji, munyi miki al?awarin duk in da ?an uwanki suke zamu kai ki wajan su". Ramlat ta faWa damuwa bayyane kan fuskarta.


Girgiza kai Amrah ta yi cikin ?aramin muryarta ta ce. "Ni A'a, ku maida ni inda ku ka Wauko ni, ina son ganin ?an uwana". Ta ?arashe maganar tana mai rushe wa da kuka.



Dai-dai lokacin Umar ke ?araso wa wajan. Su Khairiya kuwa, ganin Umar ya ?araso ya sa su sakin ajiyan zuciya sannan suka ce. "Yauwa yahya barka da dawo wa, ka ga Amrah tun Wazu take kuka wai ita a mayar da ita in da aka Wauko ta".



Furzar da iska Umar ya yi waje sannan ya nufi in da Amrah take zaune kar?ashin bishiya ta yi ruff da ciki. ?arasawa ya yi wajan da take sannan ya dube ta ya ce. "Amrah, me ki ke so?".


?ago da rinannun idanuwanta Amrah ta yi ta ce. "Ina son ganin ?an uwa na".


Kallonta Umar ya yi a karo na biyu ya ce. "Shi ke nen, idan ki ka ga ?an uwan naki komai zai dawo dai-dai?".


Girgiza kai Amrah ta yi alamun eh.

Mi?e wa tsaye Umar ya yi ya ce. "Shi ke nen, zamu kaiki wajan na su".


Kallon Umar Usman ya yi ya ce. "Yahya me ka ke cewa haka?, ta ina zamu samo su?, basun riga sun mut......


"Shshiiiiiii!". Umar ya yi alama da hannu da ya yi shiru.


Shiru Usman ya yi yana mai jiran furucin da zai fito da baki yayan nasa.


Kallon Umar Khairiya ta yi ta ce. "To yahya a ina za'a samo su?".


Amsa Umar ya ba ta da cewa. "Wallahi nima ban sani ba, lokacin da Abba ya je ya saka mutanen sa suka je suna kashe dabbobin dajin ban sani ba sai daga baya naje na tarar da sun kashe duk dabbobin dajin. Ni yanzu ban san ya zan yi ba".




Kallon su Ramlat ta yi ta ce. "Yahya ina da shawara".



"Mene ne?". Suka furta a tare.


"Ku matso ku ji". Ramlat ta faWa. Matso wa suka yi kusa da ita tare da kasa kunnen su in da take.


Shiru ta yi kana daga bisani ta ce. "Me zai ana muje gidan Zoo na san dai akwai dabbobi a chan, mybe idan muka kaita ta ga dabbobin cikin wajan za ta yi farin ciki. Amma ya ku ka gani?".


Murmushi Khairiya ta yi ta ce. "Wow wannan shawara ce mai matu?ar kyau".


Shiru Umar ya yi na Wan wasu lokaci sannan ya ce. "Kuma ganin wannan shawarar za ta yi aiki kuwa?".


"Me zai ana?, zai yi aiki mana, suma ai dabbobi ne a chan na san idan ta gansu za ta yi farin ciki".
Cewar Usman. Sannan ya ?ara da cewa. "Amma kamar babu gidan zoo a nan dutse ko?, ni dai ban sani ba ko akwai ko babu".


Kallonsa Umar ya yi ya ce. "Ko akwai ma, ba na wannan zamu je ba, ina son muje Kano daga nan zan yi bincike na a kan wanda nake nema mai safaran miyagun hayyuka".



"Shi ke nen bara muje mu haWa wasu kayan mu da wanda Amrah za ta saka". Khairiya ta faWa suna mai shige wa ciki. Lokaci ?alilan ya Wauke su suka gama shirya wa sannan Umar ya kalli Amrah ya ce .


"Tashi muje zamu kaiki in da ?an uwanki suke". Jin abin da Umar ya faWa, hakan ya sa Amrah saurin mi?e wa tare da sakin murmushi. Juyawa suka yi gaba Waya suka nufi wajan parking space, ganin hakan ya sa Amrah ta yi saurin bin bayansu. Shiga cikin motan Waya Usman da su Khairiya yayin da Usman ya tada mota, tare da fice wa daga gidan. BuWe wa Amrah ?ofa Umar ya yi ta shiga sannan ya sauke mata glass Win motan ?asa. Sannan ya tada motan tare da barin harabar gidan.


Daga bisani suka nufi hanyar garin Kano.


*To kafin mu cigaba dai muna son sani wane ne asalin Umar? sanann wane ne asalin gov. Musa Muhammad*.

Alhaji Muhammad shi ne asalin mahaifin Musa Muhammad. Alhaji Muhammad ya kasance mutum tawakali da kuma sanin ya kamata, ya kasance mutum bai bin ?a'ida. Matar sa Halima ta rasu ne a lokacin da take na?udan ?ar su ta biyu wacce ta ci suna A'isha. Musa ya kasance Wa na fari a wajan mahaifin sa sai kuma A'isha. Musa ya taso tun yana ?arami da burin zama Wan siyasa domin shi gaba Waya a tunanin shi babu komai a cikin yin harkar siyasa sai kuWi. Hakan ya sa ya ?udiri niyar zama Wan siyasa. Alhaji Muhammad ya tura musa karatu domin ya yi karatun Engineering, sai dai kuma abin da bai sani ba shi ne Musa ya chanza course Win da mahaifin nasa ya zaSa masa izuwa Political science. Musa ya gama diploma sa ne yana da shekaru talatin shif. A wannan lokacin A'isha ta kammala HND Win ta. yayin da ta fito da wanda take so wato Wan sarkin garin Kano. Bayan an Waura musu aure shima Musa ya auri matarsa Khadija wanda suka haWu da ita a University Win da ya yi.

Haka ya cigaba da sha'awar zama Wan siyasa ba tare da mahaifin ko matar sa ta sani ba.

Khadija ta kasance mace mai ri?o da addini, tana ?o?arin gujewa duk abin da zai Sata wa mijin ta rai. Bayan shekara Waya ta haifo santalelen Wanta wanda ya ci suna Umar.


Farin ciki wajan waWan nan ma'auratan ba zai misaltu ba.


Ana tsaka da aka, Musa ya je ya bayyana wa mahaifin sa abin da ya karanta a jami'a. Hakan ya sa ran mahaifin sa ya yi matu?ar Saci. Yayin da mahaifin sa ya ?udiri niyar cewa muddin yana da rai ba zai bari ya zama Wan siyasa ba. Jin furucin da ya fito daga bakin mahaifin nasa ya sa Musa ya tunzura sannan ya yi tafiyarsa sai bayan wasu lokaci ya dawo wajan mahaifin sa, sai dai a wannan karan bai dawo domin neman yafiyar mahaifin sa ba, ya dawi ne domin ya Wauki ran mahaifin sa.


Bayan isarsa chan ne ya tara ?an daba suka zagaye gidan a yayin da ya sa a Waukar masa video ta yadda zai kashe mahaifin na shi. Alhaji Muhammad na kwance cikin jinya da
End Ads