x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 18 - KUNDIN CINIKAYYA

  • 51001 words
  • 54000 words
  • Out of 96350 words

Category: Romance Story +18

Views 567

09 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
"Tabbas ni ce zan kawo sauyi cikin wannan masarautar saina tabbatar da na saita musu zama kafin na bar gidan nan, ba zan iya zuba ido na ga ire-iren waWan nan abubuwan na faruwa ba, ya zama dole na koya musu hankali".



Babu zato suka ji an banko ?ofar cikin Wakin. A zabure gaba Waya suka juya tareds sauke idanuwansu a kan matan da ke tsaye bakin ?ofa babu abin da suke ta faman yi sai tauna chewgum yayin da suka Wora hannuwansu kan ?ugu. Sanye kansu yake da gashin ?ari wanda ya sauko musu har gadon baya yayinda ko ina na jikin su ke sanye da azurfa masu kyau da she?i. Kallo Waya za ka musu ka tabbatar da cewa su ma ?a?an wannan masarauta ne.


?araso wa ciki mata ukun suka yi sannan suka buga tsaki. Daya daga cikin su ce ta ce. "Ke Mami me ya sa har yanzu baki je kin wanke min panties Wina ba?".


Kallon Mami Zahra ta yi kana ta ce. "Mami su waye kuma waWan nan almajiran?".


Kallonta Mami ta yi kana ta ce. "Su Win ba almajirai ba ne, ?a?an kishiyoyi na ne, Samira, Yusra, da Fasma".


A matu?ar fusa ce ?aramar cikin su ta dubi Zahra ta ce. "Su wane ne almajiran, nan Win gidan ubanki ne. Tsaya ma tukun nan ke Win wace ce daga wane duniyar ki ka zo nan". Cewar Fasma.


Yusra ce ta dubi Fasma ta ce. "Dalla ?yale ta Fasma zamu ji da ita daga baya. Yanzu wajan wannan banzar matar muka zo, ta zo ta wanke mana kayan mu, domin ni yau bana sha'awar saka kaya a cikin washing machine da hannu nake so a wanke mu".


Idan ran Zahra ya kai dubu to ya Saci. Cikin Sacin rai ta ce. "Kuna da hankali kuwa?, ku san da cewa wannan matar ba sa'ar iyayen ku mata ba ce, amma shi ne ku ke cewa ta zo ta wanke muku panties da kaya, lallai kamm banga ta zama ba a gidan nan domin daga yanzu ya kamata na soma aiki na".


Rai a Sace su ukun suka tunkari in da Zahra take kana suka ce. "Eh mun aike ta Win wace ce ke da za ki dakatar da mu?".


Nuna su gaba Waya Zahra ta yi kana ta ce. "Zai iya kasance wa kun daWe kuna yi mata abin da ranku ya gada ma, like mothers like daughters ko, to tun da na riga da sanya ?afafu na cikin wannan masarautar komai ya zo ?arshe domin kuwa ba zan bar koda iyayen ku mata su ?ara ci mata mutunci ba balle ku ?ananun ?wari".


Nan take Samira ta saka ?afarta wanda ke sanye da takalmi mai tsini ta taka ?afar Mami da shi. Nan take Mami ta saki wani irin azababbiyar ?ara!.



Nan take ran Zahra ya Saci yayin da ta kai hannu tare da fizge gashin dokin da ke kan Samira sannan ta kama ?wa?widon kan Samira kana ta kwashe ta da lafiyayyun maruka har guda biyu. Nan take su Yusra suka ja da baya.



Shafa kan Samira Zahra ta yi ta ce. "Wai dama ba gashin ku ba ne, ashe gashin doki ne, ji gashi kamar ammatar Wan iska". Ta faWa tana mai kwashe wa da dariya sannan ta maida kallon ta kan Mami ta ce. "Mami kada ki damu za ki riSanya hakan abinda ta yi miki kiyi mata times 2".


Girgiza kai Mami ta yi kana ta ce. "Ki rabu da ita Zahra, bana son matsala".


"A'a Mami ba zai yu ba, me ya sa koda yaushe waWan da suke da shiru-shiru su haka fi raina wa ne?, ke sa'ar su ce da za su wai ki wani wanke musu kaya da panties, idan ba rashin tarbiya ba wa ye zai faWi hakan?". Cewar Zahra.



Kallonta Mami ta yi ta ce. "Zahra umarni nake baki ba shawara ba maza ki sake ta".


Jin hakan ya sa Zahra sakin gashin Samira tare da shinshina hannunta. Nan take ta ji wani mugun wari ya bugi hancin ta.


"Ya subha'anallahi!". Zahra ta furta kana ta ce. "Wannan kai ne ko kashin akuya?, ji wani wari da ke fita daga kan wannan Samira kamar mutacce alade. Chabb ashe duk gayun da iyayin na banza ne tun da ba'a iya tsaftace jiki".


Node Kai su ukun suka yi kana suka ce. "Za ki san mu ki ka taSa wallahi yau kin taSo wa kanki bala'i, kuma za ki gani". Suka faWa tare da fita daga cikin Wakin.



Duban su Zahra ta yi ta ce. "Zan ga alkhairy ba tsiyar ku ba, shegun yara kawai".


Su Samira na fita kuwa suka je suka sanar da su Gimbiya Saratu da Talatu duk abubuwan da Zahra ta yi musu. Nan take gaba Waya suka mi?e tsaye yayin da suka nufi kitchen daga mai Waukar wu?a saime Waukar chokali. Yayin da su Yusrah kuma suka Wauki wayar chaza suka nufi Wakin Mami.




"Ke Zahra, nan fa ba kamar gidan ku ba ne, za su ya cutar da lafiyar ki ni kuma ba zan bari hakan ta faru ba, tun da ki ka ji sun ce za ki gani to sun tafi ne su haWa dabar su za su iya cutar da ke, ya kamata ki bar masarautar nan yanzu".
Cewar Mami.


Murmushi Zahra ta yi kana ta ce. "Mami ki barsu su zo dai-dai nake da kowaccen su, nayi da wanda yafi su ma balle su ?ananun tantirai. Jira nake su ?araso a nan za su tabbatar da cewa Allah Waya ne, domin duk saina koya musu hankali".


Ta faWa tana mai hango dorina a ajiye kan table. Da sauri ta nufi in da dorinan take tare da Wauka ta ri?e a hannunta tana mai jiran shigowar su Samira.



********************
=؃?=؃?=؃?=؃?=؃?=؃?=؃?=؃?
*KAI ZAHRA KINA ?AMSHI MUNA BINKI DA UMRAH, INA YINKI OVER=??, MA ZA KIYI MANA MAGANIN SU. SU SAMIRA JIKIN KU ZAI FA?A MUKU DOMIN ZAHRA BA ABAR RAINA WA BACE. ALIYU DA KUMA UMAR FA SUN RIKICE, SUN KASA GANE SAFEERA DA AMRAH. KOYA ZA TA KASANCE MUJE DAI ZUWA=؃?=؃?=؃?.*


*KADA KU MANTA DA LIKING, SHARING DA KUMA COMMENTS FISABILILLAH???>???>?p?=؞?*


AL?ALAMIN
'?
A'ISHA M.B =؞?=؞?=؞?
(Zinariyar>???
@&?Jajirtattu)


Follow the









https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
=ت? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=ت?
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.'?

*DIAMOND =؎? STARP+*
*LADIES >???
@&?>??? @&?>???
@&?*
*(We stand together)*
>??>??>??

(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*
Da sunan Allah mai rahama mai jin?ai!

*=?%?KUNDIN CINIKAYYA* * *_________________________________________________*
Saida su Gimbiya Saratu suka zo dai-dai lokacin da za su shiga part Win Mami ne suka ci karo da Junaid.

Shan gabansu Junaid ya yi sannan ya dube su ya ce. "Mene ne ku ke shirin yi haka?". Maida kallonsa ya yi kan Gimbiya Saratu sannan ya ce. "Ammi what's going on?, kar dai wajan Mami za ku je?".


Kallonsa Gimbiya Saratu ta yi ta ce. "Koma wajan ta zamu je ina ruwan ka?, maza ka bamu hanya mu shiga. Har ma ta kai da har za ta kawo wata ?ar aiki cikin fadan nan kuma ta saka ?ar aikinta ta Waga hannu ta mari Samira saboda ta cika tangararriyar ?ar iska".


Fashe wa da kuka Samira ta yi ta ce. "Wallahi yahya kome za ka yi ba zan rabu da ita ba, Waga hannu da ta yi ta mare ni kawai ka bamu hanya mu shiga don wallahi saina yi mata tsinannen duka".


Sauke ajiyan zuciya Junaid ya yi sannan ya ce. "Kun san dai mai martaba yana nan. Kuma idan har ya ji abin da ku ke shirin aikata wa to ran mu ne gaba Waya zai Saci. Hanyar zaman lafiya a bita da shekara. Yanzu me ku ke so ita ?ar aikin ta yi muku?".


Amsa Gimbiya Talatu ta bashi da cewa. "In dai tana so mu rabu da ita to dole ne ta zo ta dur?usawa har ?asan gwiwowinta ta bawa Samira ha?uri kuma bayan nan za ta wanke musu kayan su. Wannan shi ne". Ta ?arashe maganar hannunta ri?e da ?ugunta



Furzar da iska Junaid ya yi waje, sannan ya dube su ya ce. "Shi ke nen kuje ku zauna a parlour zan kira ta za ta zo ta baku ha?uri gaba Waya har da ma ita Samiran".


Ya faWa yana mai shige wa part Win Mami sallama ri?e a bakin sa.


Su Gimbiya Saratu kuwa jin abin da Junaid ya faWa ya sanya suka koma parlour tare da zaman jiran fitowar Zahra.


?arasawa ciki Junaid ya yo yayin da Zahra ta bishi da kallo. Murmushi Mami ta yi ta ce. "Junaid kaine a wannan lokacin".


Cikin jim kunya ya ce. "Eh Mami ni ne". Ya faWa yana mai maida kallonsa kan Zahra.


Mamaki ne ya kama shi ganin dorina kan hannun Zahra.


Baki sake ya bita da kallo sannan ya ce. "ke kuma me ki ke da dorina?, me za ki yi da shi?".


Kallonsa Zahra ta yi sannan ta bashi amsa da cewa. "Zan daki ?annen ka da shi ne, ko za ka rama musu?".


Kawar da kai Junaid ya yi gefe cikin jin haushin furucinta ya ce. "Ki fito babban parlour yanzu nan ko kuma ranki ya Saci". Yana kaiwa nan ya fice ya bar musu Wakin.



Dogon tsaki Zahra ta ja sannan ta ce. "Aikin banza, ni gaba Waya ma zaman magar?amar ma ya fi ?anci a kan nan wajan".


Binta da kallo Mami ta yi ta ce. "Kije Zahra zai iya yiwu wa sun kai ?arar ki wajan mai martaba".


Zama Zahra ta yi kan kujera ta ce. "Ni babu in da zani ina nan tare da ke".


Girgiza kai Mami ta yi ta ce. "Zahra kiyi ha?uri ki tashi ki je ko kuma mu je tare kinji ni".


"Shi ke nen Mami zanje ne kawai saboda ke, amma da ba dan haka ba babu abin da zai sa na Wau ?an matan ?afafuwa na naje wajan su".


Ta faWa tana mai mi?e wa tsaye sannan ta fita daga cikin Wakin. Ganin hakan ya sa ita ma Mami ta bin bayan Zahra.






***********************
Cikin rashin fahimta Safeera ta dubi Umar ta ce. "I don't understand what you are talking about, wace ce kuma mai green eyes?, ni a ina na sanka ma da za ka ce wai ni mai green eyes?. Kodai kana imagination ne?, ya kamata ka je asibiti a duba ka".


Ta faWa tare da juya wa ta yi tafiyar ta.


Baki sake Umar ya bita da kallo sannan ya ji zuciyar shi nayi masa zugi. Baiyi aune ba ya ga Safeera ta Sa ce masa daga gani.


?angaren Aliyu kuwa gaba Waya ya rasa me ke masa daWi yayin da ya rasa me zai yi domin tabbatar da cewa wannan Safeera ce ko ba ita ba ce. Yana tsaka da tunani ne kwatsam ya ji wayarsa ta fara ringing.


Nan hankalin sa ya Wauke daga kan Amrah izuwa wayarsa. ?aukar wayar sa ya yi ganin sunan wanda ke bayyane kan screen Win wayar ya sa shi saurin Waga wayar.



Juya wa Amrah ta yi tare da barin wajan sannan ta nufi Wayan sashen da Umar yake. Dai-dai lokacin da Safeera ke yowa wajan. Kai tsaye in da Aliyu yake ta nufa ba tare da sun haWu da Amrah ba.




"Hello your excellence fatan komai lafiya".
Cewar Aliyu wanda waya ke ma?ale kan kunnensa alamun yana waya.


Daga Wayan Sangaren Gov. Musa Muhammad ya ce. "Aliyu ina so kayi min wani aiki".


"Okay". Aliyu ya ce yana mai jiran mai Gov. Musa zai fada masa.


Magana Gov. Musa ya fara yi kamar haka. "Ina son ka bincika min wane ne ya kuSutar da Lailah harta gudu daga asibiti a wannan lokacin".


Cikin rashin fahimta Aliyu ya ce. "Ban fahimci me ka ke faWa ba yallaSai, kamar ya na bincika waye ya taimaka mata. Ita Win fa ta riga da ta bar wannan duniya, kuma ko ba komai ita Win kamar ?ar uwa take a waje na ko kuma na ce tamkar uwa take a waje na a kan me ya sa za ka ce na bincika waye ya taimaka mata. Gaskiya ba zan iya yin wannan aikin ba sai dai ka saka wani ya yi maka". Yana kaiwa nan ya katse wayar.



?angaren Gov. Musa Muhammad kuwa idan ranshi ya kai dubu to ya Saci!, cikin hassala ya ce. "Lallai ma aliyu, mun daWe cikin harkar nan tare da kai shi ne kuma yanzu ka ke ?o?arin juya min baya na san ta yadda zan Sullo maka".


Kiran wasu daga cikin body guards Winsa ya yi tare da faWa musu cewa su binciko wacce ta taimaka wa Laila ta gudu a asibiti.



Kamar yadda ya umarce su haka suka fice suka fara yawo a gari domin neman wace ce ta taimaka wa mrs Laila Abdullahi.



***************
Bayan Aliyu ya sauke wayan ne ya ci karo da Safeera a tsaye sai binshi da idanuwa take.


Binta ya yi da kallo sannan ya ce. "Wato yanzu ma kin kuma sauya shiga kenen kuma ?wayar idanunki kin mayar da su yadda suke da sannu da ?okari kinji".


Cikin rashin fahimta Safira ta dube shi ta ce. "Ni fa ban gane abin da ka ke magana a kai ba".


"Koma dai mene ne ke ki ka sani, maza tawo mu tafi idan kuma baki gama ba ni na tafi na barki a nan". Ya ?arashe maganar yana mai fice wa daga wajan. Ganin yana ?o?arin ya tafi ya barta ne ya sa ta yi saurin bin bayansa.


Suna isa waje suka tadda jami'ai zagaye ta ko ina. Mamaki ne ya kama su. Simi-simi Aliyu ya nufi in da ya ajiye motar sa tare da shiga ciki nan ita ma Safeera ta shiga cikin mota. Tada mota Aliyu ya yi sannan suka bar harabar wajan.




?angaren Amrah kuwa kai tsaye wajan Umar ta nufa. Nan Umar ya shiga binta da kallo yayin da ya rasa a mafarki yake ko zahiri. Ya shiga cikin ruWani. Su Khairiya kuwa bayan sun gama siyayya ne suka nufi wajan su Umar.


Kallon Umar suka yi ganin gaba ki Waya yanayin shi ya chanza ya sa Ramlat faWin. "Yahya meya faru?". Ta faWa da alamar tambaya.


Girgiza kai kawai Umar ya yi sannan ya ce. "Babu komai mu tafi". Ya faWa yana mai jan hannun Amrah suka fice daga cikin wajan.

Nan ya ga jami'an da ya kira har sun iso harabar wajan. Sara masa jami'an suka shiga yi a sa'inda suka buWe musu kofofin mota suka shiga. Gaba Waya yanayin Umar ya sauya ba kamar yadda suka sanshi ba. Binsa da kallo kawai Amrah ke yi ganin dan murmushin nan da yake mata baya yi hakan ya sa ta cikin wani irin yanayi na damuwa.


Tada mota jami'ai suka yi tare da barin wajan baji Waya.





*****************
Zahra da Mami na fita kuwa suka tarar da ?an aiki tare da su Gimbiya Saratu da Talatu tare da su Samira a zazzau ne gaba Waya sun Wora ?afa Waya kan Waya.


?arasawa wajan su Zahra ta yi sannan ta ce. "Gani na zo me ya faru?". Ta faWa idanunta a kan Junaid.

Sauke ajiyan zuciya Junaid ya sauke!, kana ya ce. "Maza ki dur?usa ki bawa Samira ha?uri tare da sauran domin yin hakan ne kaWai zai sa ki zauna lafiya a cikin masarautar nan".


Jin maganar Zahra ta yi tamkar saukar aradu. ?asa da kai ta yi yayin da ta ji wani zuciyan ya ce mata kawai ta bawa Gimbiya Saratu da Talatu ha?uri domin a haifa sun haife ta.


Dubansu ta yi kana ta ce. "Shi ke nen tun da abin da ku ke bu?ata kenen zan yi. Amma Gimbiya Saratu da Talatu kawai zan bawa ha?uri Samira kuwa laifi ta yi don haka ba zan iya ba ta ha?uri ba".


Mi?e wa tsaye Gimbiya Talatu ta yi sannan ta ce. "To idan ba za ki iya ba ta ha?uri ba muma bamua da bu?atar ha?urin ki, in dai kina son mu yafe miki kuma keda wannan matsiyaciyar Mamin ku zauna lafiya cikin fadan nan to dole sai Mami ta dur?usa har ?asa ta bawa Samira ha?uri".


Nan take jinin Zahra ya fara tafarfasa yayin da ta ji wani irin Sacin rai ya ziyarce ta. Nan take ta dubi Gimbiya Talatu ta ce. "A kan me ya sa za ta ba ta ha?uri?, ni ce da laifi ba ita ba, kuma ita ta kawo ni masarauta nan ba ku ba, ya kamata ku san irin furucin da za ku dinga furta wa domin ita Win ba sa'ar ku ba ce ba".



Duban Zahra Mami ta yi sannan ta ce. "Aba ke kuwa Zahra wannan ba shi ba ne karo na farko da zan fara basu ha?uri ba wannan abu mai sauki ne. Ki bari kawai na ba ta ha?uri ". Ta faWa hawaye na gangaro wa kan fuskarta yayin da ta fara yin?urin dur?usa wa kan gwiwowinta.



Da sauri Zahra ta ri?e ta sannan ta ce. "Aba Mami, sai dai idan bani da rai shi ne kawai zan barki ki dur?usa a wajan nan amma muddin da numfashi na to babu abin da zai sa ki dur?usa mata".


Maida kallonta ta yi kansu sannan ta ce. "Na san Mai martaba bai san duk abin da ku ke yiwa Mami ba to a yau duk zan tona muku asiri domin saina faWa masa komai". Ta faWa tana mai yin?urin fita.


Take suka ci karo da mai martaba a hanyar ta na fita. Hamdala Zahra ta yi kana ta ce. "Mai martaba dama ina so na faWa maka abu ne sai kuma gashi Allah ya kawo ka, dama.......


Zahra ba ya kai ga ta idda maganarta ba suka ji Gimbiya Saratu da Talatu sun fashe da kuka.


Maida kallonsa Mai martaba ya yi kansu Gimbiya Saratu sannan ya ce. "Me ya faru?".


Cikin kuka Gimbiya Talatu ta ce. "Mai martaba uwar gidan ka ce ta kawo sabuwar ?ar aiki take yi mana rashin kunya harda zagin uwata. Sannan kuma uwar gidan ka ta saka ?ar aiki ta mari Samira sannan kuma ta zage mu".


Zaro idanuwa waje Zahra ta yi tana mai faWin. "Innalilahi wa innahilahir rajihun, wannan wane irin sharri ne, ku sani cewa ramin ?arya ?urarre ne".


Kallon Mami Kai martaba ya yi sannan ya ce. "A'isha maganar su Talatu gaskiya ne?".


Sunkuyar da kai Mami ta
End Ads