x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 1 - KUNDIN CINIKAYYA

  • 1 words
  • 3000 words
  • Out of 96350 words

Category: Romance Story +18

Views 540

09 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
??ࡱ?>?? ?
????????????? ?
?
?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
, 

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Root Entry???????? ?F?
WordDocument????0Table????????2Data
???????????????????? P?@?KSKS? ????????tt????Ym?|
 T ??        $q?#*t??  ???? M?mM m Mm  ?m ?B`????BNormal$a$KHOJPJQJaJ ?6??1K?`l}??b?????????$|$?7f??J?_6x?????????F?l
?p4RR?d?i?xΉx?J???????????j???
|?+?<?J?VD`?i~t\z.?x?l????????F8((?3?D?N?Z?h?t?y(~Ή???0?????????(??()?3?CnQ?b?s?x????Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KhkWs8eY42GETnGLk2JC9G


*=?%?KUNDIN CINIKAYYA*ؐ?ؐ?.

WRITTEN & DIRECTED BY
'? A'ISHA M.B =؞?=؞?=؞?
(Zinariyar>???
@&?Jajirtattu)


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
=ت? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=ت?
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.'?

*DIAMOND =؎? STARP+*
*LADIES >???
@&?>??? @&?>???
@&?*
(We stand together)
>??>??>??

*Dedicated this page to you my one and only friends Mom muwadda and Pink darling Ina sonku sosai Allah ya bar mu tare>?p?=?
?>?p?*

*Maman ihsan da sauran members na Jajirtattu ina mika gaisuwata gare ku. Na gode da haWin kai da kuma gudunmawar da ku ka bani Allah ya ?ara haWa kawunan mu sannan ya bamu zaman lafiya mai Wore wa=?O?*

(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE
*BISSMILLAHI RAHAMANI RAHIM*

Da sunan Allah mai rahama mai jin?ai! Aminci ya tabbata ga shugaban fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.
Da sahabbansa da matayensa baki Waya.


Yau ma kamar kullum gani tafe da sabon littafi na mai suna.
*KUNDIN CINIKAYYA* wanda yake Wauke da ilimantar wa,wa'azantar wa, kayatar wa, da kuma nishadantar wa*

Daji
Magar?ama da kuma
Birni.
Three siblings from different part of the world


*Ban yarda a chanza min littafi ta ko wace tsiga ba Koh kuma s sayar min da littafi na tare da sani na bah Koh kuma s Wora min littafi a internet bah tareda izins bah toh idan kuwa mutum ya kuskure ya chanza min littafi, yaje na bar shi wa Allah*. *Kuma ba zan yafe masa bah*

Ban yi wannan littafin dan cin zarafin wani koh wata bah, nayi shi ne domin mutanen al'umma su amfana da darusukan dake cikin ta. Idan wannan littafin yayi dai-dai da rayuwar ka toh arashi nee


*=?%?KUNDIN CINIKAYYA* *
*________________________* *JIGAWA STATE*
*DUTSE >ب?*
*FEDERAL HIGH COURT*
*DUTSE*

*SHEKARA TA DUBU BIYU DA BIYAR *


__fitowa ta yi daga cikin Motar 'yan sanda yayin da hannayenta ke sanye da handcuf. Nan ?an sanda suka kalle ta tare da yi mata nuni da ta yi gaba. Tafiya ta fara yi cikin kasala da fauwala wa Allah lamuranta. Ta ke mutanen wajan suka fara tofa albarkacin bakinsu a kanta yayin da suke Allah wadai da halinta. Kare ta police Win wajan suka shiga yi gudun kar wani a cikin jama'ar wajan ya yi ?o?arin illatata.

shigar da ita cikin kotu suka yi mai matukar girman gaske.

Cikin kotun ya kasance mai matu?ar faWi gaske benci da wajan tsayawar shaida kake gani tare da kujeru, tebura, kofofi, lectern sai ?aramin tebur don wakilin kotu kusa da benci na alkali an rufe da magatakarda kotu, sai kuma katako shinge mai raba shari'a daga gallery.



gefe guda jama'a ne da ?an sanda yayin da lauyoyi suke tsaye tare da alkali.

Kallon su alkalin ya yi tare da basu damar zama. Zama kowanen su ya yi yayin da kotun ta yi shiru tamkar babu wani Wan adam dake cikin ta.

Mai da kallon sa alkali ya yi kan wanda hake tuhuma yayin da ya bata umarnin da ta fito gaban kotu domin jin hukuncin da haka yanke.

Jiki a sanyaye ta mi?e tsaye tare da nufar gaban kotu tana mai fuskantar jama'an dake cikin wajan.

Magana Alkalin ya fara yi kamar haka, "A bisa hujjoji da muka yi la'akari da su, bisa dogaro da abubuwan da haka bayyana tare da ?wa?warar bincike cewar Mrs Laila Abdullahi tana amfani da kamfanin ta da sunan tana taimakon talakawa bayan kuma safaran yara ta ke tare da aika mata ?asashen waje domin yin karuwanci suna samar mata da kuWaWe sannan tare da miyagun ?wayoyi da kayan maye wanda duk mun sani cewa doka ta haramta yin hakan".

" Don haka wannan kotun mai albarka ta yanke nan da sati Waya za'a mata hukuncin kisa ta hanyar rataya. Yana kaiwa nan. Kwamitin alkali ne suka mi?e tsaye tare faWin. "Court".

Jin hakan ya sa kowa fita daga cikin kotun yayin da kowa ke farin ciki tare da murnan hukuncin da kotu ta yanke mata.

Fitowa Mrs Laila Abdullahi ta yi hawaye na bin kan ?uncinta. Gefe guda kuma mutane ne a tsatsaye suna mata tofin Allah tsine.

Shigar da ita jami'ai suka yi cikin motan ?an sanda yayin da haka nufi can prison da ita. Bayan wasu kwanaki warders suka fito da ita jikinta sanye da kayan magar?ama tare da nufar inda za'a rataye ta. Kuka sosai ta ke tamkar ranta zai fita yayin da ta ke ji ina ma ta samu koda mutum Waya wanda zai yarda cewa bata aikata miyagun laifukan da haka tuhume ta dasu bah.

Sai da haka kaita har inda za'a rataye ta. Nan ta ke mai zartarwa ya fito da igiya yayin da haka Waure igiyar a sama. Sannan haka Wauki abin rufe fuska haka rufe mata fuska da baki. Sannan haka saka kanta saitin igiyar tana ihuu tana kururuwa.


A firgice ta farka daga mummunar mafarkin da ta ke, yayin da zufa suka fara ?eto mata ta ko wane sashi na jikinta yayin da damuwa da tashin hankali suka bi suka tunkushe guri guda a zuciyarta na halin da ta ke ciki na rashin mai taimakon ta. Nan da nan zuciyarta ya shiga bugawa da ?arfi-?arfi.

Dafe cikinta ta yi wanda ya kumburo sosai alamun cewa tana da juna biyu. Sosai taji gaba Waya jikinta sunyi mata nauyi yayin da ta kasa motsa koda Wan yatsarta saboda tsananin azaba da raWaWi na ciwon dake tattare da ita.

Jin alamun motsin mutum daga bayanta ya sa ta sauriin waigawa. Nan ta haWa idanu da gandirebas Win da ke tsaye ?e ?am a kanta. Ta ke zuciyarta ta ?ara faWuwa a karo na biyu!. Don ta tabbatar cewa sun zo ne domin tafiya da ita kotu. Kallon su ta yi hawaye na bin ?uncinta ta ce.

"Dan Allah kuyi min wata alfarma, ina son kafin ku kaini kotu a yanke min hukunci Waya daga cikin ku ya hara min waya na kira ?an uwana dan Allah".

Kallon juna gandirebas Win suka yi yayinda Waya daga cikin su ya kalle ta ya ce. "Kotu bata bamu damar yin hakan bah. dan haka kada ki ce zaki yi wani yin?uri a nan wajan idan ba haka bah zamu samu bindiga mu harbe miki kai dan haka obey the law".

Jiki a sanyaye ta mi?e. Jikinta sanye da tufafin ?an magar?ama. Yayin da ta mi?a hannunta gaba Waya a cikin su ya sanya mata handcuf a hannun sannan suka fice daga cikin wajan. Bangare guda kuma sauran matan cikin Magar?amar suka bita da kallo.

Cikin police van wato motar ?an sanda ta shiga yayin da suka nufi kotu da ita. Tun da suka fara tafiya ta ke ta istigifari tare da salati har suka isa kotun.

Parking police suka yi. Duk idanuwan jama'a a kansu yayin da suke jiran fitowar Mrs Laila Abdullahi.

Fitowa ta yi daga cikin motar. Ba zato taji saukar dutse a kanta. Dafe kanta ta yi cikin raWaWi hawaye na zarya bisa fuskarta. Nan da nan mutane suka fara jifar ta da duwatsu tare da fara Allah wadai da halinta. Ganin hakan ya sa jami'ai suka shiga kare ta. Har haka shigar da ita cikin kotun.



?an jarida da jama'a ne gaba Waya suka ?araWe gaban kotun high court yayin da koh ina ?an sanda da sojoji kake gani hannunsu ri?e da bindigogi don rike mutane a kan madafun iko.

*"Muna bu?atar adalci!muna bu?atar adalci!. Kalmomin da jama'ar wajan ke ta nanata wa kenen.

Daff da wani dattijo wasu ?an jarida suka nufa, tare da seta mike saitin bakinsa sannan suka ce. "Bawan Allah mene ne sunanka?". Amsa dattijon ya basu da cewa.


"Sunana Namadi". Tambayar sa ?an jaridan suka yi a karo na biyu da cewa. "Bisa wane laifi ne ku ke tuhumar wannan matar dashi, kuma me yasa kuke jifanta?".

Amsa dattijon ya fara bata kamar haka.

"Muna tuhumar ta da ?wamushe yaran mu tana safarar su. Dukkanmu muna bu?atar wannan kotu ta yi mana adalci hakan zalunta da yaudarar mu da ta yi. Ta Sata rayukan ?a?an mu mata, ta kashe mana yaran mu yayin da ta ke saka wasu yaranmu suna mata safaran miyagun ?wayoyi. Muna tunanin ce mun samu walihiya mai share kuka da ba?in cikin mu. ashe muguwa ce shigo-shigo bah zurfi ta yi mana.Ta yi mana al?awarin cewar zata horar da ?a?anmu kuma za ta ba su aiki a kamfaninta ashe ta ri?e ?a?an mu ne domin ta kai su wasu kasashen don samar mata da kuWaWe ta hanyar karuwanci.Dan haka muna son a bi mana hakkin mu a kan abin da haka aikata mana". Ya faWa yana mai fashe wa da kuka. Sannan ya ?ara da cewa. "Ta cuce mu ta zalunce mu, mu Wora mata yardar mu ta hanyar bata amanar ?a?an mu. Indai har kotu bata yanke mata hukunci bah toh tabbas sai mum kashe ta".


Mai da kallon ta Waya daga cikin ?an jaridar ta yi kan camera sannan ta ce. "Jama'a fatan kunji abin da wannan dattijon ya faWa kan cewar suna zargin Mrs Laila Abdullahi da aikata laifin safaran yara da safaran miyagun ?wayoyi. Neman gaskiya da amfanin jama'a, Bayyana zalunci, yi rahoto da gaskiya da daidaito. Kare yancin jama'a da mutuncin dan Adam duk a wannan kotu mai alfarma muke samunsa. Dan haka mu jira hukunci".


*Shigar su cikin kotu keda wuya Alkali shigo shi ma ciki Ma'aikacin ma'aikacin kotu yana sanar da lokacin da alkali ya bada umarnin da kowa ya zauna.

Umarni Alkali ya bada da Mrs Abdullahi Muhammad ta fito gaban kotu. Fitowa ta yi har inda masu laifi ke tsayuwa. Yayin da police suka tsaya daga bayanta.



BuWe littafi Alkali ya yi tare yin rubuce rubucen shi a ciki tare da bawa mgatakadda damar ya tashi.

Mi?e wa magatakadda ya yi tsaye sannan ya ce. "Assalamu alaikum Barka da safiya fatan kowa yana cikin ?oshin lafiya". ?aukar takarda da al?ali ya mi?a mai ya yi sannan ya ce. "A wannan rana ta Litinin Waya ga watan february, a wannan kotun tamu mai dumbin albarka zamu ci gaba da sauraran ?aran da wasu suka kawo bisa zargin aikata wannan laifi. Kuma a wannan rana za'a yi zama na ?arshe na sauraron shari'ar Mrs Laila Abdullahi wanda hake tuhuma da safarar yara da salwantar dasu".

"Shin koh lawyer Mrs Lailah Abdullahi yana nan? da kuma lauya da ke kare wanda suke tuhumar Mrs Lailah Abdullahi yana nan? Idan gaba Waya kuna kusa muna bukatar ku Mi?e tsaye. Mi?e wa lawyer dake kare Mrs Lailah Abdullahi ya yi tare da bashi amsa da cewa, "Eh ina nan". Yayin da Waya tsagin shima ya mi?e tsaye.


Magana magatakadda ya fara yi kamar haka.
"Bayan hujjoji da haka gabatar a gaban kotu cikin zama da ya gabata na Waya na biyu dana uku kotu zata bayyana matsayinta hakan wannan shari'ar". Yana kaiwa nan ya zauna.


Kallon lauyoyin dake kare kowane Sari yayi sannan ya ce. "Shin akwai wata hujja da zaku gabatar koh A'a?".

Amsa wa suka yi da "babu".

?aukar littafin dake kan tebur Winsa al?ali ya yi sannan ya ce. "Bisa la'akari da hujjoji da suka bayyana a gaban kotu waWan da hujjojin duk suna nuna cewa abin da hake tuhuman Mrs Lailah Abdullahi, laifin ta ruga ta aikata kuma ba bu wata da lauyarta ya bayar ?wa?wara da zata gamsar da kotu cewa bah ita ta aikata wannan laifin bah. Don haka wannan kotun mai alfarma ta zata yanke mata hukunci kamar haka".

"Bisa dogaro da duba da haka yi da halin yana yin da ki ke ciki na juna biyu. Wannan kotun ta bada umarnin cewa ba za'a rataye ta ba har sai ta haifa abin ke cikinta, sannan wannan kotu mai alfarma ta bada umarnin cewa Mrs Lailah Abdullahi ta samu kulawa daga likitoci da kuma cikin magar?ama tare da bata abinci masu kyau har lokacin da za ta haifi abin da ke cikin ta, sannan nan da shekaru biyar masu zuwa za'a rataye ta. Wannan shi ne".
Kwamitin alkali ne suka tashi tare da cewa. "COURT".

Mi?e wa jama'a suka yi. Yayin da babu wanda yaji daWin hukuncin da Alkali ya yanke sunso nan ta ke zai bada order da a rataye ta sai kuma suka ji hakasarin hakan sakamakon cikin dake cikinta.

Fita jama'a suka yi daga cikin kotun, yayin da jami'ai suka fito da Mrs Lailah Abdullahi tare da nufar inda motar police ke a fa ke.

Bah zato ta ji saukar mari kan fuskarta. Saurin dafa ?uncinta Mrs Lailah Abdullahi ta yi sannan ta kalli matar hawaye ni bin kan ?uncin ta.

"Allah ya tsine miki albarka, muna fuka maciya amanar ?asa, dole ki gurbi abin da kika shuka". Cewar wata dattijuwa.

Ganin suna tunkaran inda Mrs Lailah Abdullahi ta ke ya sa jami'ai suka fara kare ta yayin da suka shigar da ita cikin mota. Nan ta ke suka ji saukar talkalma kan jikinsu yayin da suka fara bubbuga jikin motar da Mrs Lailah Abdullahi ke ciki. Ruff da ciki Mrs Lailah ta yi tare da fara rusa kuka. Kukan da ta ke yi ba saboda cin mutuncin da jama'a suka yi mata bah. Tana kuka ne bisa ga nadama da kuma takaicin abin da ya sa ta yarda da mutum. Ha?ika yardar da ta baiwa mutane shi ne ya yi silar tarwatse war rayuwarta, shi ne mafarin kuma ?arshe na rugujewar rayuwarta, tabbas ta aikata babbar dana sani a rayuwarta.

Tun da suka fara tafiya ba abin da ta ke sai kuka har suka isa harabar magar?amar da ita.

Parking daya daga cikin police Win ya yi kafin daga bisani gaba daya suka fito daga cikin motar yayin da warders mata suka nufo motar tare da buWe wa suka fito da Mrs Lailah Abdullahi waje tare da shigar da ita cikin magar?amar mata wato Sangaren mata sannan suka shigar da ita cikin kurkuku tare da ?ulle ?ofar wajan.

Guri Mrs Lailah Abdullahi ta samu ta zauna yayin da ta shiga yin tunanin koh a wane hali ?an uwa ta suke ciki a yanzu. Motsi tajiyo daga bayanta. Saurin waigawa ta yi tareda zuba idanuwanta hakan matar da ba za ta wuce shekaru arba'in zuwa sama bah a duniya.

Murmushi matar dake gefenta ta yi sannan ta ce. "Kada ki ji tsoro sunana Hajiya Binta nima kamar ke haka lokacin da haka kawo ni magar?ama na dinga kuka bah tare da aika ta wani laifi bah sa'anan ina ji ina gani na kasa aiwatar da komai saboda fito da gaskiya lamari. Kuma abin takaicin ma kina da juna biyu. Karki damu zan kula da ke tamkar ?ar uwa har ki sauka lafiya kinji?".

Murmushi wanda ya fi kuka ciwo Mrs Lailah Abdullahi ta yi sannan ta ce. "Nagode sosai ?ar uwa". Ta faWa tare da zaro wani babban littafi a cikin jakarda haka kama ta dashi. Sannan ta mi?a ma hajiya Binta littafin ta ce. "A gaba Waya magar?amar nan ke kaWai ce wacce na gani naji hankalina ya kwanta da ita, dan haka Ina son ki hadana min wannan littafin saboda yardar da miki domin na san duk abin da ya yi ?arshe akwai mafarin faruwar sa, ina son ki hadana min shi".

Mi?a hannun Hajiya Binta ta yi tare da karSar littafin wanda ya ke da matukar girman gaske. Juya littafin Hajiya Binta ta yi a hannunta sannan ta ce. "Wannan littafin fah mene ne a ciki?".

Murmushi Mrs Lailah Abdullahi ta yi sannan ta bata amsa da cewa. "Tarihi na da mafarin lamarin duk abin da ya shafi rayuwata da kuma abubuwa da dama wanda baki ba zai gama faWar su bah duk sune a ciki. Ina son ki hadana min shi koh bayan raina idan ina da rabon haihuwa a duniya ki bawa Wan da na haifa wannan littafin domin ya san wane ne shi, idan ma mace ce ki bata domin sanin wace ce mahafiyarta da kuma ita kanta".


"Kai maza ku taso kuyi aiki". Cewar wata warder a cikin magar?amar.

Mi?e wa suka yi yayin da Hajiya Binta ta Soye littafin a ?ar?ashin pillow Winta. Tana saka wa suka fice daga cikin Wakin da suke.

*BAYAN WATANNI UKU*
kwance ta ke yayin da ta ke jin bayan ta nayi mata ciwo ga wata iriyar azababbiyar ciwon mara da ta bi ta addabe ta. Yayin da cikin wanda ya yi tartsotso a gaba yake ta faman motsi.


Nan ta ke ta saki wata iriyar razananniyar ?ara!. A firgice matan dake cikin magar?amar suka nufi inda ta ke yayin da suka shiga bata taimakon gaggawa. ta ke suka haWa rufi da tsumma tare da zagaye wajan. Nan da nan mutane suka cunkushe guri Waya.

Cikin tsananin azaba na na?uda take nishi tare da furzar da iska mai zafi yayin da numfashinta ya ke ?o?arin sar?ewa.

Ganin hakan ya sa Hajiya binta ta fara danna mata cikin tana ihuu yayin da saura matan suka shiga yi mata addu'ar sauka lafiya.


Ganin tana ?o?arin rufe idanuwanta ya sa hajiya binta ta yayyafa mata ruwa tare da tattaSa fuskarta. Gani ta yi gaba Waya ?arfin ta ya ?are yayin da Wan dake cikin ya kasa fitowa.

Ba zato suka ji kukan jaririya ta fito. Nan ta ke farin ciki ya lulluSe fuskokin su yayin da suka shiga yi wa Allah godiya. ?aukar jaririyar Hajiya Binta ta yi sannan ta ce. "Masha Allah, ubangiji ya albarkaci rayuwarki". Ta faWa tare da mi?a wa Waya daga cikin matan magarkama suka sanya jaririyar a cikin tsumma tare da rufe ta. Sannan hajiya Binta ta Wauki placentar yarinyar wanda haka yanke ta ha?a rami a can bayan magar?amar ta bunne.



Mai da kallon ta kan Mrs Lailah Hajiya Binta ta yi. Nan ta ke Lailah ta kuma fashe wa da wani irin azababbiyar ?ara mai matu?ar razanarwa.

Cikin kiWima da firgici kowanennsu ya mai da kallon sa kanta. Yayin da suka ga Lailah ta ci-gaba da na?uWa.

Zaro idanuwa waje Hajiya Binta ta yi cikin farin ciki
End Ads