x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 9 - NA KASA JUREWA book 1

  • 24001 words
  • 27000 words
  • Out of 86738 words

Category: Love Stories

Views 122

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
da doctor ya shigo ɗakin da aka kwantar da Talatu, ya ga jikin nata alhmdulilah, ya ce "anty Jamila ta biyo shi office,  bayan ta biyo shi, yayi mata ƴan bayanai kafin ya rubuta mata magunguna taje pharmacy ta siya, a take a gurin tayi masa transfer na kuɗin asibitin, bayan ta koma suka tattara kayan su ta kirawo driver ya zo ya ɗauke su suka koma gida, time ɗin Hajiya ta fito a wanka tana shiryawa zuwa Hospital ɗin sai ga su sun dawo.

Sosai ta samu kulawa a gurin Hajiya da anty Jamila kai kace ƴar da suka haifa a cikinsu,

Washe gari, kwana biyar da faruwar rashin lafiyarta.

Hajiya ce zaune a parlo  ko wanne da waya a hannunsa, kasancewar suna yin online business, ajiye wayar Hajiya tayi, kafin ta kai dubanta ga anty Jamila, kana tace "Jamila kinga dai Ma'aruf ya ƙauracewa gidannan ina tunanin duk wannan rigimar bazai wuce haɗa aurensa da A'isha da nace zanyi ba"

Itama anty Jamila ta ajiye wayarta, kafin tace "Hajiya nifa har yanzu na kasa gane wa son, kodai bashi da lafiya ne?"
Hajiya tai murmishin yaƙe kafin tace "Jamila kenan kin mance shekarun da suka wuce har Hospital ɗin London mun tafi, ƙaararrun likitoci suka tabbatar mana da lafiyarsa ƙalau,
Thinking anty Jamila ta farayi, ta ɗau few minutes kafin tace "am Hajiya inaga kawai ki tura ta Kano gurin Anty Tasleem wallahi Hajiya sai kin gode min da shawarar nan da zan baki, kinga Anty Tasleem  ƴar gayu ce, zata gogar da A'isha fiye da inda bakya zato, zata wayar da ita sannan ta sa ta a school, zamanta a nan Abuja bazai yiwu ba, sbda ma'aruf, tsoronsa zai dinga ɗauke mata hankali ta dinga tsorata ta kana samun nutsuwar"

Sai da Hajiya mama ta ɗau tsawon mintoci tana thinking kafin daga ƙarshe tace "wallahi Jamila na yarda da zancenki, amma fa ni ba zani Kano ba, sai next months sai dai ku tafi tare, amma zan gargaɗeki akan maganar alkawarin aurenta da ma'aruf da mukayi, inaso ya tsaya daga ni sai ke".

"Insha Allah" anty  Jamila tace tana danna wayarta ta fara lalubar number anty Tasneem, ringing ɗaya ta ɗaga tare da faɗaɗa murmishinta, kafin tace "Jamila manyan gari wato anty ta ɓoye ki ko? Kin dena kira waccan number taki ma bata tafiya"

Anty Jamila tayi dariya kana tace "yanzu dai duk ba wannan ba, insha Allah gobe ina hanyar zuwa Kano a airplane zan taho, anty Tasneem tace mata Allah ya kawota lafiya cike da farinciki,
Hajiya dake zaune gefen anty Jamila tace "yanzu me ya kamata a siya mata, kokuma kina ganin sai kunje kwa ƙare shawarwarin acan?"

"Eh Hajiya da zai fi, amma fa akwai buƙatar isassun kuɗaɗe wanda zasu isa kinga duk da haka nauyi za'a ɗora mata,
Hajiya tace "oh Allah aikin zumunci sai an daure, tun Ma'aruf yana ƙarami nake da burin in ga ya auri ƴar uwarsa amma burina bai cika ba"
Hajiya ta ƙare maganar cike da yanayi na damuwa,
"Hajiya ki kwantar da hankalinki ga ta an samu, A'isha ai rainon mu ce, sannan bazata cutar damu ba da izinin Ubangiji"
Hajiya tace "Allah ya yarda, zanyi miki transfer na one million a fara dashi, sai kuma kuɗin jirgi ko?" Anty Jamila tace"karki damu Hajiya nidai fatana in ga hankalinki ya kwanta sosai,
Jinginar da kanta tayi a saman kujera hawaye suka fara gangarowa a saman kumatunta, cikin muryar kuka tace "Allah sarki Alhji kafin rasuwarsa ya jaddada min aurar da A'isha ya barmin wasiyyar in kula da ita kamar ƴar cikina..
Ta sake fashewa da kuka, anty Jamila ta dafa kafaɗarta cikin raunin zuciya tace "insha Allah Hajiya zamuyi nasara ni kam na fara hangowa.

Washe gari, ɗaya daga cikin dogayen rigunan da  anty Jamila ta siyawa Talatu ta sanya, pink color ce sai mayafinta light pink, kayan sun amshi jikinta, ta fito parlo ta zauna, har yanzu jikinta babu ƙarfi sosai, Dija da Hajjo suka fito domin ƙarasa aikace-aikacen gida, wata uwar harara Dija ta watsa wa Talatu, wanda karaf sukayi ido biyu, cike da masifa Talatu ta mike, ta fara nuna Dija da hannu tana cewa dama na daɗe ina tara ki, sai in fashe miki ƙaton baki, jibeta kamar wata kazar mayu"
Kukan kura Dija tayi, wanda ta mance ko da wa take faɗan idanunta sun rufe sosai, ta cakumo wuyan Talatu, suka fara kokawar dambe, Hajjo dake ƙoƙari rabasu Talatu ta ɗura mata zagi, dole ta ja gefe ta zuba musu idanu,

Jin hayaniyar tayi yawa sosai, ya sa anty Jamila fitowa tun daga ƙofar bedroom take cewa "wai meke faruwa ne?, tana maganar ne tana ɗaura agogo a tsintsiyar hannunta,
Rai a ɓace ta janyo Talatu tana cewa "Dija mai ya haɗaku?"
"Kafin Dija tayi magana Talatu ta ce Hajiyan binni wallashi ita ta fara wai cewa tayi, wannan Hajiyar nan farar nan wai muguntarta tayi yawa, wai bata biyansu albahi, bayan nan ta ce, wai ita ta gaji da zaman gidannan", Talatu ta ƙare maganar tana rushewa da kururuwar kuka, sosai maganar Talatu tayi tasiri a zuciyar anty Jamila, a duniya bata ƙaunar ɓacin ran Hajiya mama bata son abinda zai tunkareta na game da sauyawar yanayi fara'arta, Dija ko ta rungume hannaye a ƙirji tana mamakin bom ɗin da Talatu ta haɗa mata, cikin ladabi ta durƙusa har ƙasa, kafin tace "Hajiya wallahi ƙarya takeyi min"
Dija tai maganar tana fashewa da kuka, tasan in har anty Jamila ta koreta a gidansu Hajiya ma bazata barta ba, sannan makomarta ma ta fara tunowa, aikin da takeyi ne yake taimakawa ƙannenta da mahaifinta da mahaifiyarta, kasancewar mahaifin nata yana fama da ciwon ƙafa,
"Dija rashin mutuncin naki yayi yawa, ki tattara kayanki ki bar gidannan, yau wata saura kwana goma sha biyar ya ƙare ko?, barin baki kuɗinki, kiyi gaggawar fita tun kafin Hajiya ta fito dan zan ɗauki mummunan mataki a kanki, rashin godiyar Allah ne yasa kike wadannan maganganun.
Anty Jamila ta ƙare maganar tana miƙa mata 50k, kasancewar kuɗin aikin nata 30k ne, ya zama ta ƙara mata 20k, Dija na kuka ta karɓi kuɗin, jiki a sanyaye ta kalli Talatu, itama Talatun ita take kallo, tayi mata gwalo wanda ya daɗa sosawa Dija zuciya, Hajjo dake can gefe a raƙuɓe tai saurin bin bayan Dija, koda ta shiga samun Dija tayi tana rusa kuka gami da cewa "wayo Allah nashiga uku na lalace, Hajjo ta dafa kafaɗarta cikin sigar lallashi tace "Dija kinga banbancinmu da ita kenan, shiyasa na..."

"Dakata Hajjo, a halin yanzu duk wata maganar da zakiyi ba zata yimin amfani ba, kawai ki ƙyaleni"
Dija tai maganar tana saɓo jakar kayanta kafin ta ɗora a kanta, Talatu kam ranta fess dan ko wata tambaya anty Jamila batayi mata ba.
SINGAPORE
Buland island
Dariya suka sheƙe da ita, tare da tafawa, oga ya kalli fuskarsa matar da suke magana wacce zata Kai shekaru hamsin a duniya,
"Mesha yaran nan zasu kai shekaru nawa?"
Da yaren su yake magana..
"Reed ina tunanin sunkai 20yrs gaskiya, akwai wata matsalar ne?"
Misha ta jefa masa tambaya,
Girgiza kai yayi, kafin ya ɗan latsa wayarsa sai kuma ya ce "akwai abin da suke bukata ne?"
"Misha tace "komai akwai sai dai bana son yawo da suke yi Reed"
Og Reed ya sheƙe da dariya kafin yace "Misha wannan yawon da suke yi ai shine zasu sami kwanciyar hankali suyi ƙiba suyi kyau, kinga bokana ya gayamin cewar inhar suna yawan yin sex da maza sunfi kawo kuɗi idan lokacin da zamu kaisu kasuwa yayi, amma fa akwai wani babban gargaɗi da zanyi miki, duk wani Muslim da ya kawo ƴarsa gurina, bana nunar masa da haka, kawai ina nunar musu da zamu fitar dasu daga Musulunci ne"
Murmishi tayi, kafin tace "haba Reed baka da matsala dani, sai dai motar da ka siya min ta fara tsufa ina buƙatar wata" hannun sa ya ɗora a saman kanta kafin yace "baki bani komai ba haka zaki wuce ?"
Sai da ta ɗan turo ƙirjinta wanda kana ganinta kasan ita ɗin ba yarinya bace ta girma, tace "karka damu yanzu zan koma gida gobe zan dawo zakayi farinciki sosai, tai maganar tana miƙewa tsaye kana ta saɓa jakarta tana yi masa kiss a kumatu ta ɗaga masa hannu cike da nuna kulawa, murmishi yayi kana ya ɗaga mata hannu,
Waye Reed
Reed babban matsafi ne anan ƙasar Singapore, ya kasance gagararre ga duk wani ɗan adam, baya shakka ko jin tsoro yayin da zai gudanar da aiyukansa, a halin yanzu akwai ƴan mata sunkai hamsin a hannunsa, wanda basu taɓa aure ba sai harkar karuwanci, a cikin ƴan mata hamsin ɗin nan akwai guda biyu waɗanda ya ware su, sune ƴan Nigeria, da Hussaina mai suna Nyrah, sai Iham mai suna Anjali, rayuwa suke yi ta gata da samun kulawa, ko wacce a cikinsu bata san da wani labarin talauci ba, kudade ne gasu nan su da kansu suke ɗiba suna bawa samarinsu.
Monday tushen aiki..
Katafaren gida ne mai hawa uku, gidan ya haɗu iya haɗuwa, komai nasa fari ƙal, ba ƙaramin mamayar guri akayi gurin gina wannan gidan ba, dan zamu iya kiran gidan da babban gida a hausance, amma sedai mutanen da suke cikin wannan gida idan ka gansu sai ka sake kallo, tsabar kyau da zubin halittar ko wacce, sannan ko wacce budurwa tanada ƴar aiki sai abinda ta zaɓa shi za'a kawo mata, rayuwarsu suke yi cike da gata, nasan zakuyi mamakin cewar mai yasa babu wacce take yunkurin guduwa?"..muje zuwa 👉
KANO
Suna isa Kano suka wuce anguwarsu Anty Tasleem dake Unguwa uku, masu gadi biyu ne a gidan, ba sai na tsaya fasalta muku irin tarin dukiyar da aka narka gurin gina gidan ba.
Wasu masu aiki dattijai guda biyu ne suka tari su anty Jamila sunata yi musu lale marhabun, abinda zai baka mamaki anan shine, Anty Tasleem bata ƙaunar kishiya bata ƙaunar abinda zai hada mijinta mu'amala da wata mace bayan ita, dalilin da yasa ƴan mata basa yi mata aiki kenan,
Anty Tasleem ce ta fito harabar gidan tana sanye da Black abaya mai adon golden stone ta yafa veil a kanta, Masha Allah tayi kyau sosai, Anty Tasleem baƙa ce ba sosai ba, tanada jiki ba mai muni ba, sannan tanada cikar halitta sai dai shekararsu biyar da aure ko ɓatan wata bata taɓa yi ba, cikin farinciki ta taresu suka shiga ciki, mutuwar tsaye Talatu tayi, sbda ganin ƙyale ƙyalen da aka ƙawata gidan dashi, ko ina gunin birgewa, bazata iya cewa gidansu Hajiya ya fi na Anty Tasleem ba, sai dai ya fishi kayan ƙyale ƙyale, zama sukayi a saman couch mai masifar kyau, wani sanyin AC ya ratsa jikin Talatu har wani lumshe idanu takeyi, ɗaya daga cikin ƴan aikin ne suka kawowa su anty Jamila food flaks kala biyu, ɗaya tuwon shinkafa miyar egusi sai ɗayar farfesun kifi, gefe kuma jug ne wanda aka zuba kunun aya wanda ya ji peakmilk mai sanyi sosai, Anty Tasleem ce ta zauna kusa da Anty Jamila cike da fara'a tace "Jamila kinyi wuyar gani" Anty Jamila tai murmishi kafin tace "ke da sai a shafe shekaru ma bazaki kawo mana ziyara ba?, Talatu tace "ina yini"  Anty Tasleem tace "lafiya lau Jamila wacece wannan?"...!

08141799224

Mom Islam

*NA KASA JUREWA*
     🪻🪻🪻

    Mom Islam

Page 31-32

Anty Jamila tace "walhi yarinyar ƙanwar Alhji ce, kinsan kafin ya rasu ya bar wasiyya akan ko bayan ransa Hajiya ta kula da danginsa, shine take ta ƙoƙari, gurin taga ta kyautata musu, cike da kallon tausayi anty Tasleem ta bi Talatu, kafin tace "yanzu ya ake ciki?"

Kafin Anty Jamila ta miƙa buƙatarta ga anty Tasneem sai da ta jinjina, cikin ƙarawa kanta ƙwarin gwaiwa tace "Anty Tasneem dama na kawota ne ta sami ko da 2months ne a gidanki kiɗan wayar mata da kai, sbda daga ƙauye tazo wallahi idan kinga inda suke rayuwa abin ba daɗi"
Sosai anty Tasneem ta fara tattauna amsar da zata bawa Anty Jamila, can dai tace "shikenan dama nan da wata biyun zamu tafi Dubai kinga shikenan"
Anty Tasneem tai maganar cikin fara'a, kunun aya kawai anty Jamila ta ɗan sha, ta miƙe tana cewa "anty Tasneem zamuyi waya, wlhi kinsan sana'ar tamu babu lokaci"  anty  Tasneem ta miƙe tana ce mata "ba dai tafiya zakiyi ba?"
"Ai kuwa wlhi zan wuce, "am ki bani account number ɗinki zan tura miki da wasu kuɗi da Hajiya tace ayi wa yarinyar siyayya"
Anty Tasneem ta karanto mata, a take a gurin taji alert na 1million tace "ya shigo", daga nan sukayi sallama anty Jamila ta wuce.

Ko da anty Tasneem ta dawo ta samu Talatu a durƙushe a gaban fridge tana ta ƙare masa kallo, sai tayi kamar zata buɗe sai kuma ta fasa, haka ta dingayi,
Anty Tasneem tace "karki damu zan nuna miki komai da kuma amfaninsa, amma meye sunanki?"
Talatu ta washe haƙora kana tace "Talatu" Anty Tasneem tace "Talatu ba suna bane, daga yau duk wanda ya tambayeki sunanki ki gaya masa na gaskiya meye sunanki na gaskiyar."
"Sunana A'i hya" dariya ma Talatu ta bawa anty Tasneem, tana dariya tace "gaskiya daga yau zamu fara, kice Aisha" Talatu tace "A'i, hya" sai da anty Tasneem ta maimaita mata sau biyar, anty Tasneem na faɗa Talatu tana nanatawa, da haka ta fara faɗa dai-dai,
"Tashi muje in nuna miki ɗaki wanda zaki dinga kwana,"
Talatu ta miƙe tana bin bayan Anty Tasneem tana tafiya tana waige waige, koda anty Tasneem ta murɗa handle na ƙofar Talatu tayi mutuwar tsaye tare da dafe ƙirji tace "na higa uku inaga dai Allah ne ya yanke min wahala wannan irin daula haka?"
Tana maganar tana jinjina kai.
Wani haɗaden gado anty Tasneem ta nuna mata, tace "anan zaki dinga kwana, ta nuna mata TV dake manne a jikin bango, tace "wannan kinga inda ake kunnashi, sannan ta kirata suka shiga toilet, ta nuna mata gurin yin kashi da fitsari da bahon wanka da duk wasu abubuwan amfani, kasancewarta yarinya mai ƙwaƙwalwa yasa komai aka gaya mata yake zama daram a cikin ƙwaƙwalwarta, zuwa can yamma anty Tasneem ta sake yin wanka, ta sa Talatu itama tayi, lokacin da ake kiraye-kirayen sallahar magriba, suna kitchen ita da anty Tasneem, kasancewar anty Tasneem ƙwararriya ce gurin iya girki, dan har madia sunada labarinta, ta kasance mace mai baiwa gurin sarrafa girke-girke iri-iri, bayan sun fito daga kitchen Talatu ta hau yin tsalle, anty Tasneem ta haɗe rai, cikin rashin jin daɗin bata nutsuba, tace "A'isha ya kamata ki nutsu ki rage rawar kai bana jin daɗin ganinki haka"
Talatu ta sunkuyar da kai, saboda a duniya bata taɓa tsoron wata halitta ba, kwatsam sai ga shi anty Tasneem tana yi mata kwarjini, tsawa ɗaya tayi mata sai ta daidaita nutsuwarta, a round 10:pm suna zaune a parlor suna kallo a makeken TV wanda kamar zaka yiwa mutum magana ya amsa,
Alamar shigowa sukaji.
A hankali ya murɗa handle na ƙofar cikin izza da kamala yai sallama tare da ƙarasowa cikin parlon, anty Tasneem ta miƙe cike da kewarsa taje cikin yanga ta rungumeshi, kafin tace "baby I miss you walhi, ƙwayar idanunta yake kallo itama shi ɗin take kallo cikin cold voice ɗinsa yace miss you too my, hannunsa na a ƙugunta itama irin riƙon da yayi mata tayi masa, sai wani marairaice masa takeyi, kai kace ƙaramar yarinya, Talatu kam kunya ce ta kamata, sai ta juya fuskarta jikin bango tv ma ta kasa kallo, shikam bai ma san da akwai wata bayan anty Tasneem a gidan ba, a rungume da juna suka wuce bedroom ɗinsa, sai da ta taimaka masa ya rage kayan jikinsa kana taje ta haɗa masa ruwan wanka, wanda ya ji turaruka masu sanyin ƙamshi, "Baby na gama haɗa maka ruwan" anty Tasneem tai magana cike da shagwaɓa, "zonan" Junaid yace, yana lumshe eyes ɗinsa, kasancewar ya zauna a bed ita kuma tana tsaye, ta tako a hankali tare da ɗan zama saman cinyarsa, "na gaji sosai baby" Junaid yayi maganar ne cike da yanayi na gajiya" cike da nuna kulawa tace "baby idan kayi wanka Zaka ji daɗin jikinka, duk da bata jima da yin wanka ba, sai da ya sa ta yin wani wankan.
Bayan ta tayashi shiryawa, ta ce masa "baby mun yi baƙuwa fa" janyota jikinsa yayi kafin yace "wacece?"
Anty Tasneem tace A'isha amma daga ƙauye take, anty Jamilan Abuja ce ta kawota, tayi masa cikakken bayani, ya gamsu, kana yai na'am, sannan ta roƙeshi alfarmar ya samo mata me koya mata lesson kafin ya yi tafiya...!

Sbda kar ku jini shiru yasa nayi muku wannan, kuyi hakuri yayi kaɗan sosai, walhi aiki ne yasha kaina barkanmu da Sallah.

Mom Islam

*NA KASA JUREWA*
        🪻🪻🪻

       Mom Islam

Page 33-34

Sai da ta tabbatar da Junaid ya amince kafin tayi murmishi, a hankali ta tura hannunta cikin nashi, cikin cold voice tace "Baby please ka tashi muje ka ci abinci"
Tayi maganar tana kashe masa ido,
Bayan ya tashi, kai tsaye dinning area suka wuce, kunun tsamiya da ƙosai kawai ya sha, yace ya ƙoshi, kwaɓe fuska tayi, cikin shagoɓa tace "haba baby gaskiya nikam ban yarda ba, shikenan abincin da zaka ci?" irin maganarta ya kwaikwaya kafin yace "kema ai banga kin ci ba" "to...to...to" tace tana yin raurau da idanu, sai kuma ta miƙe da sauri tabar gurin,
Sarai ya san halin abarsa ya miƙe yana murmishi, wayoyinsa ya ɗauka ya wuce bedroom ɗinta, bata nan, ya fito ya nufi bedroom ɗinsa, acan ya sameta ta kwanta ta rungume pillow siraran hawaye na zubowa a kumatunta, zama yayi a gefenta, kafin ya tallafo kanta kana ya ɗora a saman cinyarsa, cikin sigar lallashi yace "baby  mai ya faru, ko duk akan maganar cin abincin nawa ne?, yai maganar yana tura hannunsa cikin rigarta,
Ƙara sakar masa kukan shagoɓa tayi tana wani juyi tare da cino baki, sai kuma ta lumshe idanunta, "am sorry my lovely dan Allah karki hukuntani da hakan, wlhi na ƙoshi kafin in dawo gida na biya ta gidansu Umma na ci waina",
Yai maganar yana kama kunnensa ɗaya, ɗayan hannun nasa yana cikin rigar, "shikenan ya wuce?" nayi tunanin gurin wata kaje"
Dariya ma ta bashi, sai ya gimtse gudun kar ya sake yin lefi, a hankali ya zuge zip na rigarta tare da tura kansa cikin rigar, ya Subhanallah wani daddaɗan
End Ads