x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 11 - NA KASA JUREWA book 1

  • 30001 words
  • 33000 words
  • Out of 86738 words

Category: Love Stories

Views 125

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
basa wani iya riƙe aure ya kamata ki nutsufa, kuma kinga shi ba da wasa yakeyi ba"
Saudart ta tashi zaune tana sake duban Dady wanda bata ma san yana ɗakin ba,
Cikin ɓaci rai momy tace "hmm Alhji which tallahi zaka cutar da yarinyar nan, daga ƙarshe nadama ne zai biyo baya, saboda, yarinya da ƙuruciyarta ka ce zaka aurar da ita ga abokinka wanda a shekaru ma ya girme maka nesa ba kusa ba, tai maganar a hassale, Dady yayi murmishi, wanda daga ganin murmishin kasan ya tara ma'anoni da yawa, yace "wato Zainab har yanzu baki san me duniya take ciki ba, ya kamata ki nutsu ki san me kikeyi a duniya, kinsan Allah idan baki mori duniya ba, sai ki tashi jahili ma ya fiki muƙami, kinga kuwa Naira abar so ce ga kowanne halitta" yai maganar yana gimtse fuska,
Nidai na gaya maka bazan amince ba, tun yanzu ayita ƙirga mata ɗakin aure, wancan auren tayi maka biyayya, wannan ai sai ka bari ta zaɓi wanda takeso ko?"
Momy tai maganar tana bubbuga bayan Saudart,
"Wato Umarni kenan kike bani?, to bari kiji ko ƴan uwana ne suka shiga cikin lamarin aurannan wallahi zan iya ɓata wa dasu, saboda akan kuɗi babu abinda bazan iya yi ba, sosai ta jinjina kai, sabda sarai tasan halinsa, farin sani ma kuwa.
Shiru tayi bata ce dashi komai ba, har ya tashi ya fice,
BAYAN SATI ƊAYA.
Alhaji Alherin Allah bai sake kiranta ba har tsawon sati guda, kamar kullum idan ta ɗan taya momy aiyukan takan je ta kwanta barci, hakan ko tayi inda take ta mafarkai iri daban daban, guɗa takeji, tayi tunanin ma a farkin ne akeyi, sai tajiyo Muryar momy a kanta cikin condition na ɓaci rai tana ce mata, Saudart ki rungumi ƙaddara walhi mahaifinki har ya karɓi kuɗin aurenki miliyan huɗu, da sauri Saudart ta tashi zaune, tana jujuya hannaye ta kasa magana, sai wani irin yanayi takeyi, daga ƙarshe dai ta fashe da kuka, momy ta rungumeta tana cewa "bari inje kayan sa lalle suka kawo, wai bikin nan da two weeks," Saudart kam ta kasa magana, har momy ta fice, sai dai bin bayan momy da kallo da tayi, ganin maganar momyn takeyi kamar a mafarki, ta fara mutsike idanu domin tabbatarwa, "ba fa ƙarya bane tunda ga shi can anata surutu a parlo" tai maganar tana share hawaye,
Acan parlor kuwa akwatuna ne guda goma cif cike suke da kaya na gani na faɗa, masu kawo kayan ma cewa suke yi saura akwatiin ɗaurin aure" ita dai momy bata um bare u um, ko da suka zo tafiya, lokacin Dady ya dawo ya basu 100k, sukayi masa godiya suka wuce, kai tsaye parlorn ya shigo, inda ya samu momy da Saudart a zaune sun tasa akwatuna a gaba kowanne yayi tagumi...!
More comment more typing
Mom Islam 08141799224

*NA KASA JUREWA*
    🪻🪻🪻

Mom Islam


37-38

"Ku kuma mai ya faru kun wani yi tagumi kamar anyi muku rashi?"

Dady yai maganar yana neman guri ya zauna,

Har yanzu babu wanda ya bashi amsa sai ma kuka da suke yi ita da momy,
Tsawa ya daka, musu tare da cewa "Saudart ki tabbatar da kin lallashi zuciyarki, domin kuwa aure babu fashi, sannan idan naji wata magana ta ɓullo ki kuka da kanki, yanzu ma dai duk ba wannan ba, zo nan"

Ta taso jiki babu ƙwari, nuni yayi mata da inda yake zaune, tazo ta zauna kusa dashi, ya ciro wayarsa kana ya shiga jiji app, wasu haɗaddun kayan furniture's ya nuno mata, kai da ganinsu ma kasan ba a Nigeria aka yi su ba, sunyi kyau sosai, sai dai a idanuwanta ne kayan suka birgeta a zuciyarta kuwa sam basu bata sha'awa ba ko kaɗan, "ki zaɓi wanda kikeso," Dady yai maganar yana sake nuno mata wasu, "ko wanne ka zaɓamin Dady sunyi"
Saudart tayi maganar  cikin rashin walwalah,
Ganin kar suyita jayayya yasa ya kashe datansa ya koma kan momy, "Zainab kafin biki nake son mu tashi daga gidannan mu koma wanda na siya" itakam momy ma bata da masaniyar ya siyi wani gida, sbda ada ne yake shawara da ita ban da yanzu da ya kama gashin kansa,
"Bata amsa masa ba, sai ma ce masa da tayi, "yaushe Anam zata dawo?" shiru yayi na ƴan wasu lokuta kafin yace "kwanan nan"
Kwata-kwata yanzu ta kasa yarda da Dady, ta kasa jure wasi wasinta sannan tana tunanin kar fa, ya je ya aikata wani abun da ƴarta, hankali a tashe tace "Habiby ka kira min ita mu gaisa koda yaushe bana samun ta a waya WhatsApp ma ta daɗe bata hau online ba"
"Haba Zainab da ba haka kike ba, yanzu kin sauya sosai, na ce miki tana nan lafiya ko? ki kwantar da hankalinki, ai basuyi hutu ba"
Gudun kar suyita jayaiyya a gaban Saudart yasa tai shiru.
Bayan kwana bakwai, biki ya rage saura sati biyu, babu abinda momy ta yiwa Saudart, sannan ko tattauna maganar bikin basayi, kowa harkar gabansa yakeyi, sai dai shi dadyn in ya shigo ya fara damunsu da maganar abubuwan da za'ayi shine suke ma tunawa da maganar wani buki,
Waye Alhji alherin Allah?,
Wani babban mutum ne, wanda ya gurmewa mahaifin Saudart ɗin nesa ba kusa ba, yana da dukiya ta ban mamaki, yanada mata ɗaya, da yara biyar a cikinsu huɗu sunyi aure uku mata ɗaya namiji yarinya ɗaya ce take gaban matarsa Hajiya Zaliha, Hajiya Zaliha ƴar asalin garin mai duguri ce, kirarin ta shine, bata zama da kishiya, wasu ma har sunayi mata kirari da wai shiga da alwalarka,
Matan su uku biyu sunyi aure a ƙasar waje, ɗaya kuma tana nan a Keffi anan tayi aure, tsakaninta da gidan iyayenta beyi 200 ba, sunanta Salma, tunda taji mahaifinta zeyi aure, tasa aka yiwa Hajiya Zaliha sabon furniture's da odar magungunan mata, a cewarta ƙarya ne amarta ta nuna mata wani abu, itama Hajiya Zalihan tana nan tana faɗi tashi gurin bokaye da ƴan bori, sabda taga an fasa auren, sai dai kash duk inda taje, sai suce mata wannan auren duk wanda yai shishigi a lamarin auren yana iya rasa rayuwarsa, ɗibarsu tayi ta watsar sbda ta dangana komai ga kanta, ita zata ji da komai, dama koda yaushe cikin ado da tsafta take, ya kasance ta ƙara a nada, duk da ta fara manyanta har gyaran jiki akeyi mata, ga gyaran gashi da ake turarashi da turaren mai duguri, tun kafin bikin kullum basa zama a gida ita da yarinyarta Salma, Salman bata taɓa aihuwa ba, sunyi neman magani har sun gaji, koda mijin yayi niyyar ƙaro aure, Salma na jin labari zasuje gurin boka a rufe masa baki, sai maganar ta shiririce.
Kwanci tashi asarar mai rai, yau ta kasance Friday wato ranar sa lalle, momy kam bata gayyaci kowa ba, ta ɓangaren dady, kam yayi gaiyyata harda su gaiyyar soɗi, an cika gida sosai, 200k Dady ya mikawa Saudart, bayan kaya wanda zata sa daga yau har zuwa gobe ɗaurin Aure da yayi mata, dan ko na akwatin ma ba'a taɓa ba, har yanzu a cikin gasgata maganar auren takeyi, sbda ko kaɗan bata jinsa a ranta, ƙarfe 5:pm wayarta tayi ringing, lokacin suna zaune da Dady a ɗakinsa ita da momy, tai banza da kiran, wayar ta sake ringing, Dady ya lura da yanayinta, yace "amma kamar kiranki akeyi ko?"
"Eh...eh" Saudart ta amsa masa bakinta na rawa,
Wayarta ta sake yin ringing a karo na uku, dole ta ɗauka ba tare da ɓata lokaci ba, "Assalamu alaikum" ta faɗa tana cin ɗaci a ranta, daga can ɓangaren ya amsa da wa'alaikumussalam masoyiyata" gabaki ɗaya muryarsa bata yi mata daɗin sauraro, babu inda ta iya, dole ta ci gaba da jin me zai ce, "gani a ƙofar gidanku ki fito ina jiranki, Momy dai ta mayar da hankalinta a kan wayar da ke hannunta, bata ma san me Saudart ɗin take ciki ba, sai Dady da yake sa mata idanu, ɗagowa tayi ta kalli Dady wayar na ƙare a kunnenta, sai kuma ta juya ta kalli Momy da take ta murmishi ga dukkan alamu bata ma san wainar da ake toyawa ba,
"Idan wata matsala ta biyo baya walhi ki kuka da kanki"
Dady yai maganar cikin ɓacin rai, miƙewa tayi ba tare da ta sake magana a wayar ba, ta fice, kasancewar dama da hijabi a jikinta, bayan ta buɗe get ta hango motarsa a gefe, jiki a sanyaye ta ci gaba da takowa har zuwa gurinsa, tsayawa tayi cak, tare da rungume hannuwanta a ƙirji, yana daga cikin mota yana ƙare mata kallo, sai wani lashe baki yake kai kace maye, "innalillahi walhi zan more, kai kai dole in dinga bawa yarinyar nan kulawa ta musamman, da zarar ta shigo gidana zan nuna mata so da ƙauna" har ya kai ƙarshen zancen zuci da yake yi bata ƙara so ba, tana tsaye ta sunkuyar da kanta ƙasa, Allah sarki Saudart yarinya mai biyayya.
Rage gilashin motar yayi, kana yace "haba my wife ki ƙara so mana" cikin suɓutar baki tace "waye wife ɗin?" Cikin samun ƙwarin gwaiwa yace "ga ki tauraruwata" yai maganar yana nunota, "hmm" kawai tace, ya buɗe mata ɓangarensa yace ta shigo, "a'a" nan ma yayi, ta faɗa tana gyara tsayuwarta, "motsin buɗe get da taji ne ya sa ta yi saurin matsawa, ta fara ƙoƙarin shiga motar, murmishi yayi sabda hakan yayi masa daidai, koda ta shiga sai wani irin kallo yakeyi mata, kai kace yau ce rana ta farko da ya taɓa sanya mace a idonsa, ya ɗan matso kana yace "shekaran jiya nayi miki text message akan ki gayamin abubuwan da kike buƙata sannan kamar nawa ne zai isheki yin siyayya?"
"Bana buƙatar komai, saboda inada komai"
Tai maganar tana matsawa, saboda a inda ya matso suna iya jiyo numfashin juna,
"A matsayina na mijinki ya kamata ace mun fahimci juna kafin ki shigo gidana, amma naga kamar bakya wani mararin kasancewata a tare dake" kamar jira takeyi ya gama magana caraf ta karɓe da cewa "eh mana auren dole Dady zai yimin, kaima son ranka kabi, baka tunanin ya rayuwa zata kasance, ko kana tunanin auren da akayi shi ɗaya bayaso ana samun farinciki?, washe baki yayi, kafin yace "haba (SaudatatulBash) sunan da nayi miki laƙabi dashi kenan, ai duk wannan ba damuwa bane, zan sa ki soni sosai da sosai, sannan nayi miki alƙawari idan munyi aure da sati ɗaya zamu tafi yawon shakatawa acan zaki fi sakewa, sai ƙasar da kikeso nan zamuje" ita dai jinsa take, abu ɗaya wanda ta ƙudurewa zuciyarta shine, idan ma ta tayar da hankalinta ba fasa auren za'ayi ba, tasan halin Dady sarai idan har ya sawa zuciyarsa zai yi abu to babu makawa sai ya aiwatar yake jin daɗi, shi yasa ta ƙudurewa zuciyarta Tata ƙaddarar kenan babu inda zata yi, dole ta rungumi ƙaddara, koda ta gaji da surutansa, ta ce masa, "zan koma gida inada aiyyuka da yawa"
Washe haƙora yayi kana yace "eh lallai kam nasan kinada aiyuka sabda gobe I War haka kina gidana" wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokareta, ta fito ba tare da ta jira maganar da zai ƙara yi ba,
"Lokacin da ta ji alamun buɗe get tayi tunanin Dady ne yake shirin fitowa, sai taga babu kowa,
Da sauri ta buɗe get ta shige, koda ta shiga masu aikace-aikace dangin Dady sai guɗa suke yi mata, sam baya mata daɗi sai takejin inama Allah zai ɗauki rayuwarta ta huta tsabar takaici, ko da ta dawo kai tsaye ɗakinta ta wuce, acan ta sami Momy tana ta kuka, duk a tunaninta ita kaɗai ce wannan auren be yiwa daɗi ba, ashe har da mahaifiyarta, cikin raunin zuciya tace "Momy kwata-kwata bana ganin Anam ko a WhatsApp ne fa, Anam ɗin da ko kwana ɗaya bamayi bamuyi magana ba, cikin suɓutar baki Momy tace "shikenan na rasa ki Anam, shikenan Anam" tai maganar tana sake rushewa da kuka mai tsuma zuciya, da sauri Saudart ta riƙe hannun Momy, itama ta fara kuka, cikin muryar kuka tace "Momy me kike nufi? mutuwa tayi ko me?" Momy ta toshe bakinta da hannunta sabda bata so Saudart ta fahimci komai ba, bata son ta banƙaɗo ɓoyayyen sirrin da suka birneshi tun shekaru ashirin da biyar da suka wuce, ko momy ta hau girgiza kai alamar "a'a" Saudart kam kuka ya ci ƙarfinta, ta sake cewa "Momy idan na rasa Anam shikenan bani da wata abokiyar shawara Momy acan kenan ta mutu, "Saudart kiyi hakuri Please Anam tana nan kuma cikin ƙoshin lafiya babu abinda ya sameta, nidai ina roƙonki kiyi ta yi mata adu'ar kariya daga azzalumai nima ina nan inayi mata, sannan wannan auren da mahaifinki yake shirin yi miki kiyi hakuri, babu inda zanyi, ƴan uwana ma basu isa suyi wani abu ba, shiyasa babu wanda na sanarwa walhi, duk da nasan yin hakan babban laifi na jawo wa kaina, amma idan na gaya musu komai yana iya faruwa, idan kika riƙe addini walhi bazaki taɓe ba, Ubangiji zai ci gaba da duba lamuranki" Saudart ta rungume Momy suka sake fashewa da kuka, sallamar Dady ne ya katse musu kukan nasu, kowacce tsoro ya shige ta, cikin nuna bai ma damu da kukan da suke yi ba, yace "Zainab bazan dai na gaya miki ba, idan har Saudart ta tafi gidan mijinta batayi masa biyayya ba, to akwai sa hannunki"
Momy ta zaro idanu, lokaci ɗaya ta ji gidan nasa ma ya fitar mata a kai, tunda ya siyarda farincikinsa, to me zata zauna tayi, ya nuna kuɗi sun fiye masa matarsa da ƴa'ƴansa da komai ma, baya kallon komai sai dukiya,
Wannan karon ne First time da Momy ta mike tsaye cike da ruwan masifa tace "nagaji da cin mutuncin da kake yi min, wallahi wannan karon kam bazan jure ba, ka sauwwaƙe min kawai, kaga idan na koma garinmu, sai ka sauya mata layi saboda kar in kashe mata aure, idan har da ban so tayi maka biyayya ba, ko kallon wannan tsohon ma zatayi ne?"
Momy ta fice masa a giya, ta nunar masa da fushinta fiye da tunaninsa, sanin kansa ne, idan har Momy ta cire abu a ranta, ta cire kenan cikin sigar lallashi ya fara magana "ke Saudart jeki ɗakin momynki zamuyi magana..
Mom Islam 08141799224

*NA KASA JUREWA*
      🪻🪻🪻

    Mom Islam

Domin samun more pages kuyi following ɗina a Arewabook danna blue link👇
https://arewabooks.com/u/momislam11


Page 39-40

Saudart tana fita, Momy ta miƙe, cikin ɓacin rai tace "walhi tun wuri ka gayamin gaskiyar magana, ina Anam ko itama ka siyar da ita ne?"
Cikin siyasa da tausasa harshe yace "ai shine nace ki zauna inyi miki bayani"
Badan zata karɓi uzirinsa ba ta zauna tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, tana karkaɗawa, 
Ya fara magana yana wani marairaice murya kamar almajiri, kai kace ba shine yanzu ya dinga surfa bala'i ba,
"Zainab kin tambayeni Anam nace miki tana can makaranta sai sunyi hutu zata dawo"
Momy ta taɓe baki tare da cewa "hmm, to mai yasa wayarta baya shiga?" Dady yayi gyaran murya kafin yace "wannan kuma ina tunanin wayar ce ta samu matsala" cikin ɗaga murya Momy tace "kafin ku tafi ai sabuwar waya ce a hannunta, kana tunanin wayar 1 million har ta lalace?"
Cikin sassauta murya yace "na gaya miki ki daina ɗaga murya mutane zasu ji maganar da muke yi" yana maganar ne zufa na karyo masa, "kin gane ne?, ai lokacin da muka sauka sai aka samu matsala wayar tata sai ta faɗi mota tabi ta kai, to shine kika ga bakyasamunta"
Gabaki ɗaya yanayinsa da inda yake furta magana sam beyi kama da mai gaskiya ba,
Ta gaji da sauraron labarin ƙanzon kuregen da yake bata, bata jira ya sake magana ba tai ficewarta, kai tsaye ɗakinta ta wuce, nan ta samu Saudart tana ta rusa kuka har idanunta sun kumbura sosai, da kallon tausayi ta bita, kana ta jingina da bango tana nazarin inda zatayi ta samowa rayuwarta mafita, ta sani idan har danginta sukaji wannan labarin babu makawa sai sun ɗauki hukunci mai tsauri, sannan ranta zai yi matuƙar ɓaci, sabda harda laifinta, idan da ace tun da tariga da ta ɗauki mataki da duk hakan bata faruba, kukan ta take ƙoƙarin tarewa da rafin hannunta ne ya kufce mata, lokaci ɗaya ta saki wani numfashi mai tattare da tsantsar tashin hankali, sosai Saudart ta tsorata, ga shi bata son dangin Dady su san halin da suke ciki, da sauri ta buɗe ƙaramin fridge ta ɗauko ruwan gora mai sanyi ta yayyafa mata, cikin hukuncin Ubangiji sai ga shi ta farfaɗo, tare da sake nisawa kamar inda tayi lokacin da zata suma,
Murmishi Saudart tayi, wanda hawaye kuma yake zuba a idanunta, gefe ɗaya tana murmishin momynta ta farfaɗo, gefe guda kuma tana kukan auren dolen da Dady zai yi mata,
Wunin ranar dai a ɗaki suka yi shi, sallah ne kawai yake tayar dasu, acan harabar gidan kuwa dangin Dady da suka zo kwanansu biyar sai gulmar Momy suke yi, wasu suce tana yiwa yarinyarta baƙinciki da shiga gidan daula, wasu suce zasuyi saki na dafe, shiyasa kaf dangin Dady da suka karanci halin da ake ciki, suka kama part ɗin su da ban a cikin gidan, itama momyn bata shiga sabgarsu,
Ƙarfe 9:pm Dady sai juyi yake yi a gado tunani iri iri, har ya fara zargin kansa, yasan bai kyautawa Saudart ba, amma babu inda ya iya, dole ya amince ta auri abokinsa idan ba haka ba, shi kansa zai iya shiga tashin hankali sosai,
Gefe guda kuma lamarin Momy ya fara bashi tsoro, saboda tana gaf da ƙure masa gudu, duk wasu kalamai da zai yi mata sun ƙare ya rasa da wacce kalma zai yi mata magana domin ya kare kansa, har zuwa ƙarfe 10:30pm yanata juyi, tashi yayi ya nufi bedroom ɗin Momy, koda ya shiga babu kowa, yayi tunanin ma tana toilet ne, har ya zauna ya kai kusan 30 mints baiji motsin kowa ba, daga ƙarshe dai ya fito, tsayawa yayi tare da rungume hannayensa a ƙriji, kana ya fara tunanin inda zai dubota, dan yasan idan ma ya kirata ba ɗagawa zatayi ba, tunanin ya duba ɗakin Saudart ne
End Ads