x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 27 - NA KASA JUREWA book 1

  • 78001 words
  • 81000 words
  • Out of 86738 words

Category: Love Stories

Views 138

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
da juna biyu "kai haba, ya faɗa yana washe haƙora" dogon tsaki tayi "mtswww" sannan tace "au na ga kamar murna kakeyi?"
Ransa fess yace "nikam karki zubar min da ciki, ai ba shege bane da ubansa gani, ko a ina zan amsa ni ne ubansa"
Ta zaro ido saboda lamarin Sabeer ya fara bata tsoro ya daina bata mamaki,
"Kawai kizo mu haɗe zan baki gidana dake Tudun Wada karki wani damu, idan ta kasheki ai ni tayiwa asara" jin haka yasa ta ce "yanzu kana inane?"
"Ina hotel ɗin da kika barni, dama wlhi ina hungry ɗin..."
Ta katse kiran.
Mashin ta tare ko mayafi babu a kanta, kana ganinta tayi wuji wuji saboda ta fita a kamininta na ɗazu, wasu ma sun ɗauka Cristian ce, wanda suka santa kuma suyita yi mata adu'ar shiriya, tunda dama an daɗe ana bada labarinta, mahaifiyarta ce kawai bata sani ba.
Dan Allah iyaye mata mu kula, dan tayi wannan abin bai kamata, ace mahaifiyarta ta ɗauki alwashin kasheta ba, yanzu dai ga shi mai gari ya waya?, zata koma inda ake gudunta dashi, ya kamata da wani ƙwaƙwaran mataki ta ɗauka a kanta, duk da nasan tayi furucin cikin fushi ne, Allah Ubangiji ka tsare mana imaninmu ka kyautata farkonmu da ƙarshenmu ka bamu ikon riƙe amanar ƴa ƴanmu da ka bamu Amin.
Bayan sun iso ta kira Sabeer, ya fito ya bawa mai mashin kuɗinsa ya wuce,
Wani irin kallo yake mata wanda ya tabbatar mata da abinda ke cikin ransa, hannunta ya riƙe suka wuce room ɗin da yake, a ranar dai wuni yayi yana aikin Abu ɗaya, tabbas Ruqaiyya ta gane Allah ɗaya yake, a ranar yayi mata kyautar mota, mai kyau, sai dai bata kai tsadar tasa ba, sosai suka kasance manne da juna, kai kace yau ne rana na farko da suka taɓa haɗuwa, kokuma muce kamar wani sabon ango, siyan abinci ne kawai yake fitar dashi daga room ɗin, haka suka kasance babu sallahar azhar babu na la'asar bare na magriba da isha'i, koda dare yayi, haka ta shiga toilet ta dinga kwarara amai, cike da tausayinta ya taimaka mata har ta gama, sannan yace "akwai abinda take buƙata ne?"
"Babu tace masa lokacin da take mayar da numfashi"
Magunguna ya haɗo mata, tare da su peakmilk da moltina ya bata tasha ya ajiye mata na anjima dana gobe, fitar da yayi har boutique ya wuce, ya siyo mata kayayyaki masu tsada harda hijabai da takalmi, sosai soyayyarsa ta sake samun sabon mazauni a cikin zuciyarta, a ranar dai kwana sukayi farantawa junansu, can dare sosai barci ya ɗaukesu, koda aka kira sallahar asbha babu wanda yayiwa ɗan uwansa magana, basuyi ba, sai ma shiga wanka tare da sukayi suka dinga iskancinsu daga ƙarshe dai suka fito tsirara manne da juna, suka shafa mai suka saka kaya, da yake yau ne zai koma gidansa da yake zaune, suka shirya kayan su, kana suka bada key sannan suka wuce gidansa, tangamemen gidane, idan ka gansa sai ka rantse babu talauci a duniya, bayan mai gadi ya buɗe masa ya shiga, suka fito, tana sanye da dogon hijabi, bayan sun shiga cikin gidan, ta tsaya tana ƙarewa gidan kallo, saboda tunda take bata taɓa ganin gida irin wannan ba, saboda su ɗin bawai sunada hali irin sosai bane, dan kwananan ma momynta take cewa zata sallami mai gadin, tunda mahaifinta ya rasu komai sai yayi ƙasa, hakan yasa momyn ta nemi aikin gwamnati domin ta ci gaba da taimakon kansu..
Ko me ta gani sai ta ƙura masa ido kai kace makauniya, haka ta dinga kalle-kalle har ya kaita ɗakin da zata zauna, wani sassanyar ajiyar zuciya ta sauke, tare da rungumeshi tana murmishi tace "masa godiya nake"
Ya zauna saman bed tare da janyota ta faɗo jikinsa, sannan yace "Ruky anan zamu ci gaba da rayuwa babu mai takura mana, sannan inson kisa a ranki ni mijinki ne, ban taɓa son wata ƴa mace ba, bayan ke, wlhi tallahi duk wayar da kikaga inayi a gabanki kawai dan in gane kinaso na ko a'a ne, karkiji shayin yimin biyayya, ko kuma tambayata wani abun da kike da buƙata.. ta amsa da "to" tana sake ƙamƙameshi.
Waye Sabeer?
Sabeer ɗane ga Alhaji halliru, Alhji Halliru wani attajiri ne mai kuɗi sosai, matarsa ɗaya Hajiya Zainab, ba itace mahaifiyar Sabeer ba, saboda a gidan tazo ta sameshi kuma da wayonsa, sannan tun Sabeer yana ƙarami babu wanda ya isa ya ɗaga masa yatsa, hakan yasa, ko ke shayinsa, sannan mahaifinsa ba basa zabi akan ko ina yakeson rayuwa yayi, sai dai kar ya sake yayi kwana biyu basuyi waya ba, sannan idan har bashi da kuɗi, ko nawa yakeso zai bashi"
Wannan matar tasa a iya matsayinta kawai take zaune, tabbas idan har zata kawo wata magana akan Sabeer, to tabbas ranta in yayi dubu sai ya ɓaci, hakan yasa tayi haƙuri ta zauna, taƙi gani taƙi ji.
Bayan tafiyar Ruqaiyya Hajiya Lubabatu ta fara numfarfashi sama-sama, wata maƙociyarta da ta shigo suyi magana akan ankon bikin ƴar matar, tazo ta sameta rai a hannun Allah, kai tsaye taje ta samu mai gidanta, ya fito da mota suka wuce Hospital....!

Mom Islam
*NA KASA JUREWA*
💋💋💋
💋💋
💋



_Mom Islam🍹_
Kuyi following ɗina Arewabook zaku samu more pages acan
https://arewabooks.com/u/momislam11


Page 73-74

sai da suka wuni a hospital ɗin ita da matar, saboda har test akayi mata, sannan aka saka mata drip, doctor ya tabbatar musu da damuwa ta saka a ranta shine ya haifar mata da wannan ciwon, ga shi ta kamu da hawan jini, zuwa yamma aka sallameta, mijin maƙociyarta ne ya biya komai, daga nan suka dawo gida, babu abinda take yi sai kuka, hakan yasa mutane suke ta cewa ƙila ta tuna da mutuwar baban Ruqaiyya ne, shiyasa take ta kuka,
Ita kaɗai tasan abinda ke damuta a cikin zuciya.
KD Ƙauye
Bayan sun dawo gida, malam yace "Najma ta miƙa niƙan masara ingi" suka wuce gona shi da Majeed da Haladu, malam na tafiya, cikin daka tsawa Inna tace "zoki miƙa kiƙannan dan ubanki akwai bayinki ne anan?"
Najma ta miƙe jiki a sanyaye ta wuce miƙa nika,
Acan a gona, zaune suke a gindin bishiyar ɗorawa Haladu da Majeed, Haladu yace "Majeed dan Allah ina neman wata alfarma a gurinka?" Majeed yayi shiru yana nazarin shi kuwa wace alfarma Haladu zai nema a gurinsa me yake dashi?" Majeed yace "Haladu insha Allah zan yi ƙoƙari gurin ganin na amsa maka tambayar da zakayimin?"
"Ina son Najma.."
Haladu yai maganar yana sunkuyar da kansa ƙasa, Majeed ya girgiza kai tare da cewa "Najma bata da iyaye taya zakuyi soyayya har takai ga kunyi aure?"
Haladu yace "Majeed ka fahimceni, amma inason ka sani iyayena ai sun zamo iyayenku, wai dai tsaya akwai wata tambaya da nakeson yi maka, sannan inason ka bani labarin asalinka, malam dake tsaye a kansu yace "Haladu abi komai a hankali, kasani fa har yanzu ban gama yi masa magani ba, saura kwana biyu mu kammala kuma insha Allah muna saka rai da alamun nasara daga shi har ƴar uwar tashi"
Majeed ya sunkuyar da kansa yana sake godewa Malam, daga nan suka ci gaba da aiki,
Mai motan da suka haɗu dashi ɗazu ne ya aika yaro gidansu Karima, a kirawo masa Najma, a kwatancen da yayiwa yaron yace farar yarinya, yaro ya shigo gidan tare da cewa "wai wannan baƙuwar tazo" Inna ta yatsina baki kafin tace "kace gata nan zuwa" lokacin har ta dawo daga kai niƙan tana gida a kwance sbda barci ma take yi, Inna tasa Karima ta shirya cikin kayan sallah tare da yin kwalliya ta fito kamar wata dodanniya, ta cika janbaki ja yayi mata yawa sosai, ta fito tana rangwaɗa tare da isa gurin mai motar, yana ganinta ya tuntsure da dariya kafin yace "kwalliya tayi kyau, amma ni ba ke nake nema ba, wannan yarinyar da na ganki da ita ɗazu ita nake nema" ta turo baki tare da cewa "to ai ta koma garinsu, kuma ni kaɗai ce a gidan" ya figi mota ya wuce ba tare da ya sake yi mata magana ba.
Da gudu ta shigo gidan nasu tana kuka mai sauti wanda har yasa Najma ta farka, kana ta fara sauraren dalilin kukan Karima, "uhm....um...hum... Inna wai dan nace masa tayi tafiya shine kawai ya wuce ya barni, wlhi Inna ya wulaƙantani" tai maganar tana share hawayen dake zubowa daga indanunta kamar an buɗe famfo,
Sai yanzu najma ta gane abinda sukayi, murmishi tayi ko me yasa oho.
Haka dai Najma taci gaba da rayuwa cikin tsngwamar Inna da kyarar da Karima take yi mata, tunda yanzu Karima ko cokali bata ɗagawa komai Najma ce take yi.
Bayan kwana biyu, malam ya kawo shinkafa mudu biyar wane mudu ɗaya, yasa aka daka yaji sannan yace a dafa masa shinkafar, bayan ta dahu, malam yasa aka zuzzuba a tray kamar guda biyar, ko wanne aka saka mai da yaji, yasa aka fitarwa da almajirai abincin.
Bayan abincin sadakar ya ƙare, malam yace a yau ne ya kammala aikin da yake yiwa Majeed da Najma, dan haka ya bawa Majeed wani ruwan magani yayi wanka dashi har kansa, hakama Najma yace har tsarki tayi dashi, dukkansu sunyi yadda malamin yace, bayan sun sanya kaya ya kirasu dukansu zuwa ɗakinsa, suka zo suka zauna saman buhu, yayi bismillah tare da watsa musu wani ruwan magani kana ya fara karanto musu ayoyin Alkur'ani mai girma.
Ina one time suka wani sauya yanayi Najma ta sake fari sosai, wato farinta na da lokacin tana gidan mahaifinta ya dawo, shi kuma Majeed shima ya sake haske da fresh fatarsa ta da ta dawo,
Malam yayi hamdala tare da sake ɗaga hannu ya godewa Allah, kafin ya sake yin bismillah Sannan yace "ku suwaye?"
"Majeed ya fara kallon ɗakin yana waige waige, Najma kam kuka ta fara tana cewa "momyna wlhi karki sake yarda da mugaye" malam ya sake watsa mata adu'a kafin ta natsu, cikin nutsuwa Majeed yace ni ɗan PLATEAU ne, Jos mahaifina sunansa Alhji Abdullahi" malam yace "ko zaka iya bani lambar wayarsa?"
Majeed yace "eh malam"
Malam ya miƙawa Majeed waya yasa number mahaifinsa, sai dai a kashe, saboda tunda anty Asabe taji wannan maƙudan kuɗaɗen da ake bin bashi ta kashe wayar,
Ya saka number mahaifiyarsa Hajiya Salima, cikin sa'a ta ɗaga tare da cewa "waye?" Duk da Majeed ɗin yaso ya yi magana amma sai ya miƙawa malam saboda girmamawa.
Bayan Malam ya karɓi wayar cikin nutsuwa da Dattaku yace "sunana Malam Isyaka, ina zaune a garin Kaduna acan ƙauyen ƴan kifi, dalilina na kiranki wani yaro ne ana ce masa Majeed...
Hajiya Salima na jin an ambaci sunan Majeed ta zaro idanu tare da sake riƙe wayar da kyau, kana tace "malam ina jinka" yace "siyarsu nayi a gurin wani mutumi a matsayin dabbobi, da yake dai Allah ya bani ilimi dai-dai gwargwado yasa na dinga yi musu magani, har muka yi nasarar karya sihirin duka, yanzu dai inason in kawosu gareku ya za'ayi?"
Hajiya Salima tace "malam idan har kuɗi kakeji babu damuwa, ki taho dukkanku da mutanen gidan malam"
Malam yace "a'a, zan fara kawosu ni da yarona, daga baya mai ɗakina zata zo, ai kuma zumunci ya ƙullu"
Sukayi sallama da Hajiya Salima da niyyar gobe insha Allah zasu taho Jos,
Ko da mama taji labarin an ga su Najma har rawa sai da tayi, tare da yiwa Allah godiya, tun a ranar suka fara shirye-shiryen abubuwan da zasu tarbi Malam dashi...
MASARAUTAR MANDU
A wani ɗaki mai kyau tangameme akayi mata masauki, ɗaki ne wanda yake ɗauke da gado irin na zamani mai kyau, sannan gefe da gefen gadon akwai wani bedsite masu kyau, a gaban gadon kafin ka hau sai ka taka wani lallausan carpet mai taushi sosai, daga hannun hagu wata doguwar drowa ce mai kyau irin kwaliyar gadon ne a jikinta, sai dressing mirror dake can gefe da stool shima mai kyau,
Jakadiya tace "nan ne ɗakinki kafin ki koma ga iyayenki " Gudidi ta harareta tare da cewa "yasin baki isa ki koreni ba, zama a gidan nan daram ko mutum yana so ko baya so" ficewa jakadiya tayi ta barta tanata surutunta, saboda ta ga zatayi mata rashin kunya tunda dai a haife ta haifeta, da gudu tayi tsalle tare da hayewa saman haɗaɗɗen gadon, alamun buɗe ƙofa da taji ne yasa ta sauko da sauri tare da tsugunawa a ƙasa kamar mai karɓar gafara...!
Ayi haƙuri babu yawa

Mom Islam 08141799224
*NA KASA JUREWA*
💋💋💋
💋💋
💋 Mom Islam

Kuyi following ɗina Arewabook zaku samu more pages acan 👇
https://arewabooks.com/u/momislam11

Page 75-76

Gimbiya ce ta shigo, tana sanye da dakakken leshi mai kyau da tsada, leshin milk color ne, kwalliyar jikinsa sai ta kasance golden da duwatsu masu ɗaukar idanu, ta saka alkyabba a saman kayan,

"Tashi ki zauna" Gimbiya tace tana yi mata alama da hannu,

Inda kasan ruwa ya cinyeta haka tayi, bayan ta zauna Gimbiya tace "ke ƴar ina ce?"

Sam bata yiwa Gimbiya ƙarya ba, ta kwashe labarin dalilin da yasa ta fito daga ƙauyensu har zuwa gidansu Rukaiyya da tayi da kuma dalilin da yasa ta gudu,

Sosai Gimbiya ta jinjina kai tana dubansa, cike da nuna kulawa tace "ai nasan ƙauyenku saboda akwai wata yarinyar yayar mahaifiyata acan, kasancewar yanzu babu zumunci, wlhi iyayemu sunfimu zumunci, Gudidi tace "ahe ke ƴar garinmu ce?"

"Ai kuwa amman a Kano muke zaune, aure ne ya kawoni nan garin"

imbiya tace "zanyi bincike game da labarin da kika bani, idan har aka tabbatar min da gaskiya kika faɗa, tabbas zan roƙi iyayenki su bani ke sai in saki a makaranta" kamar wacce aka jefo daga sama ta wuntsulo tare da cewa "haba Hajiya, ai sun amince ma" Gimbiya tayi murmishi tare da fita daga ɗakin,
Bayan fitar Gimbiya, Jakadiya ta shigo mata da wasu kaya masu kyau, kana tace "kije kiyi wanka" idan da akwai abinda ta tsana a duniya bai wuce maganar wanka ba, turo baki tayi, tare da cewa "toh naji"
Jakadiya ta fice ba tare da ta sake bi ta kanta ba,
Miƙewa tsaye tayi, tare da taɓe baki kafin tace "uhm komai iyayi mtsw, ni yanzu ina zani in watsa ruwan mtswww komai a takurawa mutum mtswww, ta dinga maganganunta ita kaɗai, wata ƙofa ta gani, ta tafi da sauri, kasancewar ta iya buɗe ƙofar tun a gidan Hajiya mama, tana buɗe kofar tayi mutuwar tsayi, wasu na'urori ta hango wanda ake amfani dasu gurin wanka da busar da gashi, harda su turaren wanka da towel masu kyau an rataye su, dube-dube ta farayi, a ina zata samu kofi ta ɗibi ruwan daɗi, cikin ƙasa da murya tace "ahe dai zamu sake haɗuwa da kai" cikin sa'a ta hango wani cup mai kyau, ga dukkan alamu watsa ruwa akeyi dashi ko meye oho, da sauri ta isa gurin cup ɗin ta ɗaukoshi tare da buɗe murfin, can dai ta hango sabulun wanka mai masifar ƙamshi ga shi pink color, ƙarisawa gurin sabulun wankan tayi tare da ɗaukoshi, kafin ta jujuyashi, kana tace "wlhi ƴan binni almubazzarancin su yayi yawa, wato biskiti ma a banɗaki, wlhi cinyewa zanyi idan har wacce aka ajiye wa tazo ita ta sani, saboda ba zanga samu inga rashi ba"
Cikin gaggawa takai sabulun baki, ta gutsiri babba, sai da ta tauna sosai, ta tabbatar da ai ba abin ci bane, ta yamutsa fuska gami da furzarwa tana shirin yin kuka, tace "yasin Allah ya isa, ko meye oho, "to dame zan hyahe baki na?"
Tai saurin ɗauko wata ƙatuwar mai coconut oil ta kurɓa, wani tsaro idanu tayi tare da haɗiyewa ba tare da ta shirya Ba, ji kake maƙwattt.. ta riƙe baki, tace "Allah yasa ba guba naci ba" kofin dake hannunta ta kalla, tare da buɗe p-toilet ta dumbulo ruwan tana cigaba da runtse idanuwanta, tana cewa "da nasani tun farko ruwan gaɗi na ɗiba da duk hakan bata faru ba" bayan ta gama magana ta kurɓa tare da lumshe idanunta, tace "Amincin Allah ya tabbata ga wanda ya haƙa rijiyar daɗi, billahi da ruwan zanyi kwaskwarima, tayi maganar tana sake dumbulowa tana shafawa a jikinta, daga ƙarshe ta fito bayan ta ajiye cup ɗin a inda ta ɗauka, samu tayi an ajiye mata wani kyakkyawan tray an jere kulolin abinci, gyara ɗaurin zanin dake jikin ta tayi kafin ta durƙusa fara buɗe foodflaks ɗin, na farkon da ta buɗe faten doya ne da wake, yaji hanta da busashen kifi, ɗayar foodflaks ɗin kuma, farfesun kan rago ne, wanda yaji kayan ƙamshi sai tashin ƙamshi yake yi, "rufe waccar kular tayi, ta ɗauki cokali tace "wlhi romo zan fara warɓa" tai maganar tana ɗibar romon a cokali, "wayo daɗi" ta faɗa lokacin da tayi cokali ɗaya, duk yawan romon sai da ta shanye shi tass, kafin ta fara cin naman, inda kasan kura haka ta koma, saboda ko kaɗan bata rage ba,
Bayan ta gama ci ta miƙe tsaye tare da fara taka rawa, tana cewa...

"Inci farfesu Sannan inhya ruwan garɗi"
Tana faɗa tana rawa, har sai da ta gaji, ɗaurin bandejin dake goshinta ta fama garin yin rawa, da sauri ta haye gado ta kintsu, sai yanzu ma ta tuna da ledar maganin ta, an nuna mata amma bata sha ba..
Fulani part
Zaune take a saman lallausar couch mai kyau, babban parlor ne kamar na Gimbiya wato Umma, sai dai ko kusa bai kamo kafar na Gimbiya a kyau ba, amman shima ɗin yayi babu laifi, domin a hakan ma Naira ta raina kanta, Ruma ce zaune a kujerar da take kallon tata, cikin shiga ta alfarma, idan baku manta ba, da Mai martaba mahaifin Prince Murad da mijin Fulani uwarsu ɗaya ubansu ɗaya sai dai mahaifin Prince Murad shine babba,
" Ruma tace "Momy yanzu haka zamu zubawa yaya Murad idanu, ko tani da bayayi, ita kuma Uwar tasa ta zuba masa idanu kuma tasan alƙawarin da mai martaba yayi akan maganar aurenmu, Fulani ta taɓe baki kafin tace "akwai shirin da nake yi a kansu, tabba bazan barsu haka kawai ba, gara ma su samawa kansu lafiya su yi maganar tun kafin lokaci ya ƙure musu"
Fulani ta ƙarashe maganar tana yin wani irin murmishi mai wuyar
End Ads