babu daɗi, saboda Aysha sam bata da matsala a rayuwarta, sannan ta kasance mai barkwanci, kowa nata ne, yah Arman kam ko leƙowa beyi ba, shikam har ga Allah ya so ace zatayi ta rayuwa a gidan har lokacin aurensu yayi,
Suna fita a anguwar ta ciro wayarta, kunnawa tayi, kana ta fara lalubar number Zyd, kamar jiran kiran nata yakeyi, da sauri ya ɗaga tare da cewa "amincin Allah ya tabbata ga beautyna" ta lumshe idanu kamar yana kallonta kafin tace "tare da kai, muna hanyar zuwa Abuja" in Cold voice yace "Allah ya kaiku lafiya Beautyna Please idan kin sauka ki kirani" ta waro idanu tare da cewa "taɓɓ, so kakeyi a ƙwace wayar?"
"Toh shikenan ina dai jiran kiranki"
Ya faɗa a taƙaice, ba wata hira sukayi ba, ta katse kiran,
ABUJA
Gulma na cin Muhammad, sai da ya zo gidansu Ma'aruf ya gayawa Hajiya abinda idanunsa suka gane masa, tabbas daga Hajiya har anty Jamila babu wanda yaji daɗin labarin, sai dai sun ɗauki alwashin binciko gaskiyar lamari tunda har abin ya kasance haka,
Yau kwana uku kenan basu sanyashi a idanunsu ba, sai safiyar yau ya shigo musu, yayi shirin zuwa office, bayan ya gaishe da Hajiya ya gaida anty Jamila kafin ya miƙe zai fice, anty Jamila tace "Son ina san yin magana dakai"
"Anty Please ki bari idan na dawo sai in zo muyi maganar"
Ya faɗa yana fara tafiya,
Dakatar dashi tayi cikin bashi umarni kafin tace "son ka nemi guri ka zauna"
Dole ya zauna sboda yana girmama anty jamila sosai da sosai,
Ta fara magana...
"Ka sani Hajiya ta riga da ta zaɓa maka matar aure, nan bada jimawa ba, za'ayi bikinku"
Anty Jamila na gama magana yace "nidai inada wacce nakeso wlhi gara in aureta da in auri waccer village girl ɗin"
Buɗar bakin Hajiya tace "Jamila barshi ya auri wacce yakeso, ita kuma Aysha Allah ya fito mata da miji na gari wanda ya fishi"
anty jamila bataji daɗin, hukuncin da Hajiyar ta yanke ba, sai dai tasan cikin fushi ta yanke hukuncin, ransa fess ya miƙe yabar gidan.
Yana fita anty jamila tace "Hajiya mai yasa zaki yanke wannan hukuncin, bayan kina ƙoƙarin cika alƙawari?"
Hajiya ta sauke ajiyar zuciya kafin tace "Jamila tun ranar da Tasneem ta kirani tacemin Aysha ta kusa dawowa, nayi wani nazari, ina tunanin kar Aysha ta dawo ta samu labarin haɗin da zamuyi mata da ɗanmu taga kamar munso kanmu ne, kokuma da wata manufa muka ɗaukota, sannan duk ba wannan ba, Ma'aruf ba mutum mai sauƙin kai bane, idan har yace baya son abu, ko anyi masa baza'a zauna lafiya ba, Jamila bazan amince ya cutar da yarinyar nan ba, kawai dai abinda na gani shine, idan ta dawo a kaita makarantar kwana, tunda tayi ilimi sosai, sboda tanada basira, insha Allah bazamu sami matsala ba, kinga kafin nan ta sake girma sai mu jira Ubangiji ya fito mata da miji na gari"
Har yanzu dai anty jamila bataji daɗin maganar hajiyar ba, dole ta amsa da Amin tunda tana gaba da ita.
Acan company soyayya ce mai ƙarfi ta ƙullu a tsakanin Ma'aruf da Layl, ta samu abinda take so, ga shi duk abinda ta tambayeshi sai yayi ƙoƙarin yi mata, hakan ya fara bawa mutane mamaki, shi da kwata-kwata baya soyayya, bikin Muhammad ya rage saura kwana biyu, yayi musu anko iri ɗaya shi da ita na shadda mai tsadar gaske, duk wasu kayan ƙyale ƙyale wanda zata saka a ranar bikin, hidima yayi mata sosai, kai kace itace amaryar,
Ga shi yanzu bai cika zama a office ba, daga suyi nan sai suyi can yayita biye mata, sai da aka zauna meeting ma'aikata sukayi ta ƙorafi, tabbas bashi da bakin magana, dole ya karɓi laifinsa tunda har sun fara yi masa barazanar company ya fara samun matsala.
Cikin amincewar Ubangiji, sai ga su Aysha a cikin garin Abuja, hamdala tayi tare da sauke ajiyar zuciya, dambun naman da anty Tasneem tayi mata har ta kusa cinyewa a hanya, ragowar ta bawa driver, horn yayi a bakin get na gidan, mai gadi ya leƙo dan yaga waye, kana ya buɗe musu, bayan driver yai parking kafin ya kashe motar ta fito da gudu kai tsaye ta nufi cikin gidan, tana cewa "Hajiya anty Jamila..."
Aiko suka fito da sauri, fuskokinsu cike da murmishin ganinta, sai mamakin girmanta sukeyi, ga shi tayi jajir, dama ita ɗin fara ce sai ta sake gogewa sosai, anty jamila tace "ai na ɗauka jirgi kika biyo" Aysha tayi murmishi kafin tace "driver yana can ma gurin parking suna gaisawa da mai gadi"
Hajiya tayiwa Hajjo magana akan ta kai masa abinci, daga nan suka zauna aka fara hirar yaushe gamo,
Kana ganinsu kasan suna cikin farin ciki, "ga shi kinzo a daidai, gobe bikin Muhammad"
Anty Jamila tai maganar tana kallon Aysha,
Aysha tace "anty waye Muhammad?" Hajiya tace "abokin yayanki Ma'aruf mana"
Murmishi tayi, kafin tace "taɓɓ ni nama mance da shi tunda rabona da ganinsa tun lokacin da na cijeshi"
Suka kwashe da dariya, tana cewa "ai yanzu na girma.
Ƙarfe huɗu, ashe driver yayi gudu sosai, Aysha ta faɗa tana miƙewa zuwa yin alwalah,
Bayan tayi alwalah tayi sallolinta kana ta dawo parlor, lokacin an shigo da kayanta, tace Hajjo ta shigar mata dasu ciki, sallama sukaji na muryoyi biyu, Ma'aruf da Layla, Hajiya da anty Jamila suka amsa tare da kallon ƙofa dan ganin shi da waye, a tare suka shigo, Laylan tayi kyau babu laifi, ta sanya leshi coffee brown ya haskata sosai, tasa mayafi milk color tasa sarƙa da warwaro da agogon hannu, suka ƙara so ciki, Hajiya ta bata guri, suka zauna, ita da Ma'aruf ɗin nesa da juna, cike da kunya ta gaishe su suka amsa, Aysha kam ta ganeshi sarai, baya birgeta saboda bata taɓa tsayawa tayi masa kallon nutsuwa ba, shi kuma ya mance da ita, tunda kamanninta na da ya ɓace sosai, tayi haske tayi ƙiba ta cika sosai, kai kace ba ƴar 14yrs ba, "tace antynmu kinzo lafiya" cike da jin kunya Layla tace "lafiya lau" Aysha na dariya tace "ki riƙe mana yayanmu gam gam please, karki wasa fa" tana maganar ne tana dariya, daga Hajiya har anty Jamila babu wanda yayi ko da murmishi, har Ma'aruf ɗin ya lura da hakan, ya tashi yace zasu wuce, su Hajiya sukayi musu Allah ya kiyaye hanya, Aysha ma tace a gai da gida.
Kafin su mai ga fita daga gidan, Layla ta kwaɓe fuska tare da cewa "my hero sai naga kamar momynka bata farinciki dani?"
Ya ɗage kafaɗa gami da cewa "no karki damu, dani takeyi ba dake ba, gaskiya ko me za'ayi bazan iya rabuwa dake ba Layla" yai maganar cikin ƙarfafa mata guwaiwa, dama abinda take son ji kenan daga bakinsa, hakan yasa tayi murmishi mai kyau suka fice.
Suna fita Hajiya ta taɓe baki, kafin tace "hmm ayi dai mu gani" anty Jamila ta kasa ɓoye ɓacin ranta tace "wlhi tallahi kwata-kwata yarinyar nan bata kwanta min ba, yake wani rawar ƙafa a kanta"
Aysha tace "oh Allah Wlhi ga ta ƴar kyakkwa, zan dinga zuwa ina tayata aiki"
Anty Jamila ta kalleta kallo mai cike da ma'anoni masu yawa, kafin ta kawar da idonta a kanta.
Wunin ranar dai komai beyi musu daɗi ba, yau gashi sun ganewa idanunsu dama Muhammad ya faɗa, tabbas beyi ƙarya ba"
Lokacin da Hajiya ta shiga ciki, Aysha ta wuce ɗakinta, dan ta gyaggyara kayanta, sai da ta rufe ƙofa kafin ta kunna wayarta da ta kashe, number Zyd ta kira, yana ɗagawa tayi masa murmishi mai sauti, tare da cewa "na isa gida cikin ƙoshin lafiya"
"Beautyna wlhi NA KASA JURE rashin ganin kyakkyawar fuskarki"
Ta katse shi da cewa "ai Kanada hotona"
"Uhm na gaji da kallon hoto, kawai na yanke shawarar zuwa Abuja a satinnan zaki ganni, ko baki gayamin inda gidanku yake ba, tabbas zan bincika kuma zan gano, kawai ki tsumayi zuwana, wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa "dan Allah ka rufa min asiri..."
Hhh more comment more typing
Mom Islam ce 08141799224
*NA KASA JUREWA*
💋💋💋
💋💋
_Mom Islam🍹_
_Zakuga na canza tsarin page, kokuma wasu suce yashe akayi nisa haka basu sani ba, ada inayin mai page1 yanzu kuma nayi editing ɗin pages ɗin ya zamo mai 1-2 kin gane?_
Page 69-70
"Beautyna ban fahimceki ba?"
Tayi shiru tana nazarin maganarsa,
Murya a sanyaye yace "beautyna ina ganin kamar bakya sona shiyasa kike yimin rowar ganin kyakkyawar fuskarki?"
"Zayd yayi maganar yana jiran amsarta,
A shwagoɓe tace "kaima kasan ina sonka, amma ai na gaya maka idan har kazo Abuja akwai matsala sosai, saboda su Hajiya, zan iya fuskantar ɓacin rai, nikuma bana son abinda zai ɓata musu rai"
Sosai ya fahimceta, wannan ma gwaji ne, yanason ya daɗa jaddada soyayyarsa a gareta, sai da ya tabbatar da ta nutsu bata cikin fargabar da ya sa ta, sannan yayi mata sallama.
JOS
Kwanan Alhaji Abdullahi 3 da rasuwa, anty Asabe tace "kowa ya watse" dole suka tattara suka tafi, dangin Hajiya Salima, ya rage saura anty Asabe da Hajiya Salima, sosai Hajiya Salima ta kama kanta, saboda bata shiga shirginta, dan ɗaki ta kama musamman ta dawo gidan da zama, ɗakin ma na Alhaji Abdullahi, bayan kwana Bakwai da rasuwarsa, washe garin ranar, da safe, ta kira Hajiya Salima zuwa parlon ƙasa, bayan tazo sun gaisa tace "Salima ya kamata ki tattara kisan inda dare yayi miki, saboda baki da gadon Alhaji, sai tumunin takaba, tunda dai ba ƴaƴa ne dake ba"
Sosai maganar anty Asabe ta bawa Hajiya Salima mamaki, sai ta basar tare da cewa "naji tumunin takaba ne nawa, amma ai yarana sunada gadon mahaifinsu"
Anty Asabe ta taɓe baki, kana tace "ina yaran naki suke?, tun da suka tafi yawon duniya basu waiwayi ubansu ba, kinga kuwa idan har suka ji labari tabbas zasu ci gaba da sheƙe ayarsu, kinga kuwa basu da gado tunda ma, babu wanda ya tabbatar da suna raye ne kokuma suna mace?"
Rai a ɓace Hajiya Salima tace "au haka kikace?, wallhi tallahi Anty Asabe san duniya zai kaiki ya baro ki"
Anty Asabe ta dafe ƙirji tare da cewa "ni kike gayawa haka?, tabbas kin samu guri, amma ai abinda kike taƙama dashi babu shi a duniya, sai ki tattara ko fice dan wlhi idan baki fita ba, tsaf zansa a fitar dake.."
"Ba sai kinsa an fitar dani ba, anty Asabe, gidan duniya sai bana lahira ba, ki kwantar da hankalinki, zan yi takaba a gidanmu, amma ki sani wlhi sai na karɓarwa yarana gadonsu.."
Hajiya Salima tai maganar tana wucewa upstairs da sauri ta dinga hayewa idanunta cike da hawaye, har ɗaki ta bita, dan taga me dame zata ɗiba, ta fara ɓalle gado kenan anty Asabe tace "ai naga dai babu wani abu da kika zo dashi daga gidanku, dan haka kawai ki kwashi iya kayan sawa ki fice..."
Hajiya Salima ta rufe ido tare da cewa "wallhi kibar gani ina ɗaga miki ƙafa, na rantse da Allah sai na tafi dasu harda kujerun parlor, idan ba haka ba, zaki jiki a kotu, tunda har takardar duk wani kaya da marigayi ya siya min mukeyi, idan kuma kina musu ki jirani "
Anty Asabe tace "to naji yi maza ki kwashe amma dai wannan gidan ya haramta a gareki wlhi" tai maganar tana nunata da yatsa.
Ba wani lokaci mai tsawo ta ɗauka ba, gurin tattara kayan nata guri ɗaya, sannan ta fito parlor ta samu anty Asabe tace mata, "Allah ya haɗa kowa da alkairi"
"Amin" tace tana Bin ta da kallon banza,
Hajiya Salima na fita, anty Asabe ta kulle ko ina na gidan, kana ta wuce kai tsaye ɗakin Alhajin ta fara bincike, sai dai ga mamakinta, babu ko sisi a ɗakin, hankali a tashe taci gaba da bincike amma shiru, har jakar kayansa ta zazzage babu komai, tunani ta farayi, na..
"Kuɗaɗen da yake bawa mutane masu zuwa neman alfarma a ina yake ajiye su oho?"
Ta zauna tayi jugum abin duniya ya isheta, ta fara tunanin a ina wayar marigayin take, ko wannan munafukar ta ɗauka ne?,
Da sauri ta buɗe ƙofar bedroom ɗin nasa, kana ta fito parlor ta buɗe ƙofar sannan ta fito harabar gidan tana ƙwalawa ma'aikatan gidan kira, mai gadi ne ya fito daga ɗakinsa, kana yace "Hajiya gani"
Anty Asabe tace "dan Allah ga wayata ka kirawo min lambar Alhajin gidannan, nikuma zan shiga ciki inji ko wayar tana ringing, kasan muna zargin kamar an saci wayar ne"
"To" kawai yace mata,
Ko da wayar ta fara ringing ta ruga da gudu zuwa cikin gidan, aiko tana shiga ta jiyo ringing ɗin wayar, hamdala tayi tare da sauke ajiyar zuciya, a fili tace "hmm da ace wannan shegiyar ta ɗauki wayar nan, na rantse da Allah da ta cutar dani"
Ta dawo gurin mai gadi tace masa ta gode,
Ta koma bedroom ɗin nasa, ta fara binciken inda wayar take.
Hamdala tayi, saboda taga wayar a cikin bedsite,
Kwananta biyu a gidan, tayi abinda ranta yakeso babu wanda ya shigo bare ya sani,"
A rana ta uku aka kira wayar Alhajin, da gudu ta fito harabar gidan ko nauyin tsufan da ta farayi bata ji, ta fara ƙwalawa driver kira, yazo da sauri yace mata "gani"
"Yauwa amsa min kiran nan, ɗazu sai na ji kamar Larabci sukeyi"
"Driver yace "Hajiya da dai Turanci ne, Larabci kam ban iya ba" mai gadi da ya jiyo maganar da sukeyi, yace "yanaji"
Aka miƙa masa wayar, bayan sun gaisa da wanda ya kira da Larabci, sukaga mai gadi ya zaro idanu yana jujuya hannaye, Allah -Allah, anty Asabe take yi ya gama waya ya gaya mata abinda wannan Balaraben yake cewa,
Sun jima suna zuba Larabci a tsakanin mai gadi da wancan Balaraben da yace daga ƙasar Egypt yake, sannan yace ta WhatsApp zai sake turo saƙon dan su tabbatar da gaskiyar magana"
Suna gama waya, mai gadi yace "Hajiya ki zauna inyi miki bayani"
Anty Asabe tace "kaga ni gayamin koma Meye, idan maganar akawin ne sai a tura musu ina dashi"
Mai gadi ya girgiza kai tare da cewa "Hajiya da dai kin zauna inyi miki bayani dalla-dalla"
Sai da taja tsaki mtswww kafin ta zauna tace "ina jinka"
Sai da ya sauke gauron numfashi kafin yace "Hajiya mutumin nan yana bayani ne akan bashin da ake bin Alhaji, kimanin biliyan goma" lokaci ɗaya zufa ya fara yanko mata, ta fara fifita da hannu, tare da cewa "kashemin wayar nagode, ta shige ciki da sauri, ƙara gudun fanka tayi, ga kuma sanyin AC, amma duk da haka ji take kamar an tsoma ta a cikin ruwan zafi.
Acan gidansu Hajiya Salima, mama na ganinta batayi mamaki ba, saboda tasan wacece Amru asabe, kasancewar a tsakar gida ta samu maman, ta ɗauko kujera zata zauna, mama tace "Salima kina takaba bai kamata ki zauna anan ba, suka shiga ciki, Hajiya Salima ta kwashe duk labarin ƙalubalen da ta fuskanta, har musayar yawu da sukayi da anty Asabe, mama tace "mai yasa ta kulata, karta sake duniya ai ba'a yi mata garaje,
Hajiya Salima tace "mama waɗannan ƙudaɗen da kike gani, sune a mazaunin dukiyar yarana, saboda Alhaji ya mallaki gidaje sunkai hamsin da filaye, sannan yana da wani Company ma a ƙasar waje, kinga kuwa babu wanda ya isa yace komai akai inhar ba kotu zamu kai ta ba".
Mama ta dakatar da ita, tare da cewa "kotu da kikace, babu inda za'a kaita, ki fita batun matar nan, waɗannan kuɗaɗe kuma kiyi shawarar abinda zai amfaneku keda yaranki, shikuma Allah ya gafarta masa" Hajiya Salima ta amsa da cewa "Amin" washe gari aka dinga zuwa ta'aziyya maza da mata manya da yara, kasancewar Hajiya Salima ta kowa da kowa ce, bata da duhun kai mace ce mai hankali da mayar da kowa nata...
KEFFI
Rabonsu da ganin anty Hadiza har sun mance, sabda takai kwana biyar, wayarta bata shiga ko sun kira, Salma taje gidanta ance wai tayi tafiya, abin ya bawa Hajiya Zaliha mamaki, anty Hadiza tayi tafiya ba tare da ta sanar mata ba, yanzu ita ya zatayi?,
Can gidan Saudart kuwa, a yau ne jirginsu zai tashi zuwa SINGAPORE daga nan kuma zasu wuce Saudiyya suyi Umrah tunda azumi saura kwana biyar, a safiyar yau ne ta mayar da simcard ɗinta kafin su wuce, ta kirawo momy ta sanar mata da cewar zasu je SINGAPORE daga nan zasu wuce Saudiyya, momy tace "me zaki yi a SINGAPORE? Saudart tace "kawai zamuje hutawa ne"
Momyn bata sake magana ba, sai dai tayi mata faɗa sosai akan kashe wayarta da take yi, sannan tace su dinga magana ta WhatsApp, sannan mommy ya ɗauki alwashin bazata sanarwa da Dady ga inda su Saudart sukaje ba, idan ba haka ba akwai babbar matsala.
Duk wasu abubuwa da zata buƙata ta shiryasu cikin wani kyakkyawan akwati, daga nan suka wuce airport driver ya dawo da motar, daga nan jirginsu ya ɗaga sai SINGAPORE.
Tunda suka sauka a airport, take ta rarraba idanu, duk da ƙasar waje na baƙon gurin zuwanta bane, amma guraren da suke wucewa ya birgeta sosai,
Mota suka shiga wacce ta kawosu, har Naumi hotel Singapore, bayan sunje reception ya gama duk wasu abubuwa da zasu buƙata, aka basu ɗaki, mai kyau sosai, kai kace gidane guda, saboda ɗakin 3bedroom ne, ga kitchen da guraren hutawa a ciki, sosai duniyar ta zame mata tamkar sabuwa, saboda ko makarantar da tayi a Singapore bata taɓa yawace yawace ba,
"Habibty da fatan dai ɗakin ya yi miki?"
Gyaɗa masa kai tayi tare da lumshe idanunta, wani irin sanyin ƙamshi na ratsata, sai taji yanayin gurin ya birgeta,
Ajiye keys da wayoyinsa yayi, kana yace "Habibty zan watsa ruwa"
"Tasan mai yake nufi dan haka ta yi lamo a lallausan gadon, tare da rufe idanu kamar mai yin barci, murmishi yayi Sannan ya matso kusa da ita, kafin ya fara cire mata, ɗan ƙaramin baby hijab ɗin dake wuyanta, a hankali ya ɗan mirgina ta duk tana jinsa, ya zuge mata zip na abayar dake jikinta, kasancewar zip ɗin yana a gaba ne, tana kwancen ya rabata da komai ma jikinta ya kasance daga ita sai vest da underwear, ko bra bata saka ba, ya Subhanallah "na shanunta sun mugun tsole masa idanu, kamar mai jin tsoro, ko kuma wani zai ƙamashi, ya kai hannunsa a hankali ya shafi na shanunta, kafin ya wani sauke ajiyar