x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 13 - NA KASA JUREWA book 1

  • 36001 words
  • 39000 words
  • Out of 86738 words

Category: Love Stories

Views 129

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ya wuce bedroom ɗinsa, sam bazai iya yin wanka ba, ya rage kayan jikinsa ya bar iya farar singileti, ya ciro white sleek jallabiya, ya sanya, kana ya ɗauki wayoyinsa, da eyepiece ya fito parlonsa, fridge ya buɗe yaga iya Hollandia da yoghurt da Five alive ne a ciki, sam bazasu yi masa maganin yunwar dake damunsa ba, badan ya so zuwa gidansu Hajiya ba, ya fito harabar gidan, kana ya buɗe get, jin ƙarar buɗe get ɗin yasa mai gadi fitowa da gudu, ganin uban gidan nasa yasa ya gaishe sa, yana komawa ciki, kai tsaye ya nufi gidan Hajiya, nocking yayi a bakin get ɗin, dama idan baku manta ba, abaya nayi muku bayanin katangar gidan Hajiya tana jinkin katangar gidan Ma'aruf, bayan an buɗe masa get, mai gadin ya gaishe sa ya amsa kana ya wuce ciki, kasancewar kafin mutum ya kai ga shiga cikin gidan akwai tafiya tunda gidan nada daɗi da tsayi sosai, yau kam tafiyar tayi masa nisa, sbda har ya fara tunanin dama ace da mota yazo ba da ƙafa ba, yana isowa ƙofar parlor yai sallama, Hajiya da anty Jamila suna zaune sun ta sa kuɗaɗe a gaba, sunata lissafi, ƙarasowa yayi kana ya zauna kusa da Anty Jamila, cikin marairaice murya yace "anty yunwa nakeji" yai maganar yana shafa cikinsa, ajiye kuɗaɗen hannunta anty Jamila tayi kana tace "Hajiya karki hada da waɗannan lissafinsu daban yake, anty Jamila ta miƙe kai tsaye sashen da ƴan aikin suke ta je, ko da yake Dija kam an koreta bayan tafiyar ta ma Hajiya sai da tayiwa anty Jamila faɗa, duk da hakan dai ba'a dawo da ita ba, hajjo ta ƙwalawa kira, cikin sauri ta zo tare da durƙusawa a gaban anty Jamila, kafin tace "Hajiya gani"
Please ki shiga kitchen ki dafawa Son indomie and vegetables, karkisa masa busashen kifi, saboda baya so, kawai ki ɗauko masa kunun aya mai sanyi, "to" ta amsawa anty Jamila, kai tsaye ta wuce kitchen, akwai ruwan zafi a flaks hakan yasa ta samu sauƙin girkin, ba wani long time ta ɗiba ba, ta kammala, kana ta juye a kula, kana ta buɗe fridge ta ɗibo kunun aya mai sanyi guda biyu, ta ɗauko fork da plate kana ta fito a kitchen ɗin ta nufo hanyar da zai sada ta da parlon Hajiya, sallama tayi daga bakin ƙofa su Hajiya suka amsa, shiko Ma'aruf ɗin yana daga kwance a saman kujera yana danne danne a wayarsa, ƙarasa shigowa hajjo tayi tare da ajiye abincin a saman table ɗin dake tsakiyar ɗakin, tace "anty an kammala" Hajiya tayi mata sannu" ta amsa da "yauwaa" kana ta wuce.
Saukowa yayi kana ya je ya ɗauko table ɗin cak ya ajiye a gabansa, ya zauna a saman kujera mai zaman mutum ɗaya, bayan ya buɗe kular yai bismillah kana ya fara cin abincin, har sai da ya cinye tass sannan ya kora da kunun aya mai sanyi.
"Abin kunya ace kamar ka, kana wuni da yunwa, ta hakan zaka gane cewar mata ma rahama ce a gareka, bai ce da ita komai ba ya ɗora ƙafafunsa a saman table ɗin yana shafa sumar kansa,
Anty Jamila tace "Hajiya kawai ki zuba idanu insha Allah yana nan da budurwarsa... Ya katse wa anty Jamila maganarta, kafin yace "anty Jamila har yanzu kun kasa ganewa, idan har mutum ya fara soyayya ya shiga uku, bashi da lokacin kansa ma bare na aikinsa, kinga hakan ko bazai yiwu ba sam, har yanzu kun kasa fahimtata".
Ya ƙare maganar yana miƙewa alamun fita zeyi, Hajiya tace "Allah ya shiryeka" anty Jamila ta amsa da cewa "Amen"
******
Kwanci tashi asarar mai rai Talatu ta fara zuwa school an gama mata komai na shirye-shiryen zuwa, sabda komai Arman ne yayi, ya hana anty Tasneem ta bada ko nera biyar a cewarsa shima yana son ya samu lada, da safe drivern gidansu ne yake kaita, zuwa ƙarfe 5pm shi yake zuwa ya ɗaukota sabda a lokacin yake tashi daga gurin aiki,
A aji huɗu aka sata primary 4 next year sai ta rubuta jarabawar fita,
Yau ma kamar kullum, tana zaune ita kaɗai a harabar makarantar, saman wata kyakkyawar kujera tanata zuba idanu ta ina zai ɓullo, can dai taga mai gadi ya buɗe get, da sauri ta tashi ta fara takowa, cikin sa'a taga shine yake tahowa, har da ɗan gudunta, yana daga cikin mota yake ƙare mata kallo, tunda yake a duniya bai taɓa ganin ƴa macen da ta taɓa birgesa ba irin Aysha, komai nata birgeshi yakeyi, ƙaunarta har cikin ƙarƙashin zuciyarsa yake jinta, koda ta iso tana sanye da hijab guntu iya kafaɗa sai skirt iya guwaiwa, farar Safar da tasa ne ya kai mata har cinya, fuskarta ɗauke da murmishi lokacin da yake rage tsayin gilashin motar, tace "Yah Arman inata jiranka Allah yasa lafiya kowa ya tafi sai ni kaɗai"
"Ƙanwata lafiya lau, ina lunch box ɗin naki?"
Arman ya tambayeta yana buɗe mata gidan gaba,
Marairace murya tayi, wanda shagoɓa ta zame mata sa bo da yinta a rayuwarta, tace "Mun makara bamu tashi da wuri ba, shiyasa ko breakfast banyi ba, anty dai ta bani 1k gashi a hannuna ban siyi komai ba"
"Kai ƙanwata muje restaurant kici abinci, zama da yunwa fa babu daɗi" ya figi mota kana ya fice a makarantar, kai tsaye gurin cin abincin suka wuce kamar inda ya faɗa, bayan ya miƙa ATM ɗinsa aka miƙa masa list ya tambayeta ta bashi amsa, suka wuce wani guri mai kyau da kyawawan ciyayi masu ban sha'awa, wani sanyin ƙamshi ne yake kai wa Arman ziyara a hancinsa, in 1time ya fara jin kasala, idanunsa suka wani ƙankance, lokacin da aka kawo musu abincin tare da ice cream, Talatu tace "Yah Arman baka da lafiya ne, naga yanayinka duk ya sauya?"
"Lafiya ta ƙalau kawai ina cikin wani yanayi ne"
Yai maganar cikin cold voice ɗinsa,
Jinjina kai tayi, ta ɗauki ice cream ɗin kana ta buɗe robar ta sanya ɗan ƙaramin cokalin robar ta fara sha, lumshe idanu tayi, cikin zolaya tace "yah Arman kasan me?" Saboda yanzu tana iya zama tayi hira dashi,
Yace mata "sai kin faɗa"
"Wlhi ice cream ɗin gurinnan yafi na wancan ɗinnan daɗi, gaskiya zan kai wa anty tsaraba"
Arman yace "A'a, bazaki kai mata ba, kar ki sake ki gaya mata cewar munzo nan idan ba haka ba wlhi zata ɓata min rai, ko kuma kinason ɓacin rai na?"
Inda yai maganar ya bata tausayi saboda yanayinsa ya mugun sauyawar ba kamar inda suka zo ba, ya ce mata "ba komai ne idan anyi ko na yi miki zaki gaya mata ba, yin hakan yana iya zamowa babban laifi ki kiyaye"
"Insha Allah" tace masa, sai kuma tace "ka sha mana"
"Uhm" ta tsinci kanta da cewa "in baka a baki?" Ya gyaɗa mata kai, karku manta Talatu bata san menene soyayya ba har yanzu, sabda haka ta faɗa hakan ne cikin tausaya masa ko bashi da lafiya ne,
Ɗaukan robar ice cream ɗin dake gabansa tayi, kana tasa cokalin ta fara bashi a hankali yana sha idanunsa a lumshe, Allah kaɗai yasa halin da yake ciki, ji yakeyi kamar ya janyota ya rungumeta ko zai rage raɗaɗin da yake ji a zuciyarsa, tabbas soyayyar Talatu tana neman haukatashi, amma yayi alƙawarin bazai taɓa nuna mata gaskiyar hakan ba har sai ta girma ta mallaki hankalin kanta tasan menene SO,
Abin mamaki ga dukkan tunaninta bazai iya shanyewa ba, sai ga shi ya shanye tass tasa Hankey ta share basa baki, shikam tuni ya kula duniyar tunani har wani ajiyar zuciya ya sauke, a hankali ya kai hannunsa saman nata, cikin sigar wasa yace "ƙanwata me yasa bakya yanke farce, kin fara zama ƴar gayu ko?" Ta cuno baki gami da cewa "anty ma ai bata yanke farce" dariya ma ta bashi, yace "wato kina koyi da ita kenan?" Tai murmishi, tashi mu tafi kar a ga kin daɗe" ta miƙe tsaye, a hankali ya matsa kusa da ita sun ɗan fara tafiya kafin su kai gurin motarsa, ya ɗagata ya goyata a baya, sai cewa take "yah Arman baka da lafiya dan Allah ka saukeni" shi kuma yana cewa "karki damu kin gaji da yawa"
Sai da suka zo bakin mota kana ya sauketa, suka shiga ya tada mota suka wuce gida, bayan an buɗe musu get ya shiga yayi parking suka shiga ciki, anty Tasneem tana zaune a parlor ita da ƙanwar Junaid kasancewar duk hutu idan sukayi suna zuwa, to yanzu ita ta fita daga makaranta tazo tayi kwana biyu, aiko suna haɗuwa da Talatu suka ƙulla ƙawance, kasancewar Talatun bata da duhun kai, tun daga ranar suka kasance ƙawaye gunin sha'awa, sunan yarinyar Umaimah, amma ta girmewa Talatu, sabda takai 18yrs dan har tanada waya, tunda ta gano Talatun tayi zaman ƙauye ta fara sake ƙoƙarin wayar mata da kai, duk da cewar kafin ma ta zamo hakan sai da anty Tasneem tasha fama sosai da sosai, suna kwance a saman bed lokacin ƙarfe 9:30pm, anty Tasneem ta kwanta kasancewar tana son gobe ta tashi da wuri zataje anguwa, sukuma sunata hira, Talatu ta bata labarinta from AtoZ Umaimah tayi dariya, tare da cewa "yanzu duk wanda ya ganki wlhi ba zai ce kinyi zaman ƙauye ba" tayi murmishi, labarin saurayin da suka haɗu dashi a gurin shan ice cream ta bata, sannan tacewa "Umaimah harda number waya ya bata, Umaimah tace "dalla ki wanki Gara kawo number in sa miki a kirashi, ringing ɗaya ta shiga ya ɗaga tare da cewa "hello waye?"....!
Alhmdllh hannu yayi sauƙi ga typing nan asha karatu lafiya da na yau dana gobe kinsan weekend bana posting sai aka samu matsala jiya banyi ba da shekaranjiya ciwon hannu nakeyi, masu Comments Nagode sosai mom Islam 08141799224

*NA KASA JUREWA*
💋💋💋
💋💋
💋

_Mom Islam_


Page 43-44

toshe bakinta tayi da tafin hannunta, Umaimah tayi mata nuni da tayi magana mana,
A hankali tace "ni ce Aysha" muryarta kaɗai ta isheshi, ba sai tayi masa dogon bayani ba, , a fili ya furta "godiya ga Allah da ya sake haɗani da kyakkyawar budurwa a karo na biyu, ya faɗaɗa murmishinsa kamar tana ganinsa, kafin yace "da fatan kina cikin ƙoshin lafiya, wlhi nayi kewar ganin kyakkyawar fuskarki, duk da dai gani na dake sau ɗaya ne, sai da na kasance a ko wane dare sai nayi mafarkinki, sannan sai na ɗauko hoton da nayi miki farkon haɗuwarmu, na rungume kana nake samun sassauci a zuciyata,
"A halin yanzu nafi buƙatar ganinki akan inji muryarki"
Umaimah ta raɗa mata, cewar "nima hakane"
Ta faɗi maganar da Umaimah ta gaya mata, daga can ɓangaren yace "yaushe kike ganin ya dace in zo?"
Zaro idanu tayi tare da cewa "taɓɓ so kakeyi anty tayimin duka ko?" Yai dariya mai sauti, kana yace "anty bazata dukar min ke ba" suna tsaka da firar tace "sai anjima karmu cinyewa mai wayar kuɗi"
Babu komai, "ki tura min da account number zan sa miki kuɗi sai ki siyi waya."
Ƙirjinta ne ya bada rass, ta dafe ƙirjin tana kallon Umaimah, Umaimah ta gyaɗa mata kai,
Bayan sunyi sallama, Umaimah ta miƙa mata hannu suka tafa kafin tace "Aysha kin cika tsoro wallahi, ga dukkan alamu wannan guy ɗin yana sonki sosai, yanzu dai barin tura masa da account number idan ya turo sai muga wace irin waya ya kamata a siya"
Talatu dai har yanzu tana cike da jin tsoro har yanzu,
Bayan Umaimah ta tura masa da account numberta, tace "Aysha ki kwantar da hankalinki, idan har aka siya miki waya, zaki ƙara samun nutsuwa tare da farin ciki,
Talatu ta dafe ƙirji a karo na biyu kafin tace "hmm Umaimah Wlhi ban san haka soyayya take ba, in one time kawai guy ɗin nan ya fara shiga zuciyata" Umaimah tayi dariya kana tace hmm yarinya ai ba komai kikaji ba, Wlhi idan kika fara soyayya bazaki iya yin wuni ba tare da kinji Muryar saurayinki ba" suna cikin hirar suka ji alert na dubu ɗari biyu, Umaimah tace "wow yayinda take duba saƙon,
Nunawa Talatu tayi, kana tace "kinga gobe anty Tasneem zataje anguwa sai mu fita da wuri kafin ta dawo, Talatu ta dafe ƙirji sbda tana mamakin yan bariki basu damu da kashe kuɗi ba, idan da a ƙauyensu ne, duk wanda yake da dubu ɗari biyu ai yanada babban kuɗi, sai ta tuno lokacin da zasuyita faɗa ita da Gudidi akan Naira biyar, yau itace ta mallaki wadannan maƙudan kuɗaɗen?" Umaimah ta katse mata tunani sbda ta fahimci tunanin da takeyi, tace "ki kwantar da hankalinki, sannan ki tsarkake zuciyarki, soyayya babu abinda bata sawa a bayar Wlhi zuwa gaba ma zai iya yi miki kyautar da tafi wannan, to inaga ƴan matan da samari suke siya musu motoci Masu tsada kuma basu da tabbacin auransu zasuyi?, da wannan shawarar suka kwanta barci ya ɗauke su, bayan sunyi adu'oin kwanciya barci,
Acan ɓangaren anty Tasneem ƙarfe 12:am ta farka daga barci, kasancewar ta kwanta da wuri, alƙawari ne ma koda yaushe idan har Junaid baya gida sai ta farka a dai dai lokacin, a hankali haske yake fitowa a jikin wayarta, tana mutsike idanu ta janyo wayar tare da karawa a kunnenta cikin sanyin murya irin ta mai barci tace,
"Babyna, Kaine wanda ka dace da sarautar zuciya ta don haka na baka ita kyauta,
Zan iya aiwatar da komai har idan ina jin kalaman ka masu sanyaya zuciya, Na yarda da kai na aminta da kai don haka na mallaka maka kaina"
Daga can ɓangaren Junaid ya lumshe idanunsa in Cold voice ya fara magana
"Ina fatan zaki ci gaba da kula min da kan ki har zuwa lokacin da zan dawo gida. Allah ya tsare min ke matata,
ina son ki. Sonki kamar numfashine a gareni, taya zan dai na?
Cike da shaukin SO ta janyo heart pillow ta rungume idanunta a lumshe ta, wani marairaice masa murya, tana shagoɓa tana cewa "gaskiya baby bazan iya sake jure muyi nesa da juna ba, NA KASA JUREWA, tai maganar hawaye na kwaranyowa a idanunta, sheshekar kukanta ne ya tayar masa da hankali, cikin tausasa harshe yace "Please ki hau online ina WhatsApp" yana faɗar haka ya katse kiran,
Kai tsaye ta kunna data ta hau WhatsApp, yana online ɗin kamar inda ya faɗa,
"Baby kin jefani cikin damuwa gami da tashin hankali, kin sani bana son jin sautin kukanki, amma kika fara whay?"
In voice yake mata maganar, tayi masa video call idanunta sun jiƙe da hawaye, sosai yake ji a ransa kamar ya biyo jirgi ya dawo gobe, saboda ya rarrashi farincikin ransa, ya wani gyara zama dama yana sanye da sleeping dress ne, itama hakan, wando ne iya guwaiwa sai riga mai botir, "baby kaje ka kwanta sai da safe" tai maganar tana gyara gyalen da ta ɗaura a kanta, ina.. bazan iya koda runtsawa ba, matsawar ban ga kinyi murmishi ba" kodan hankalinsa ya kwanta, tayi masa murmishi tare da cewa "i love You baby" shima yace "love You too babyn baby"
"Zuciya ta na cike da kewarki, zan samu sassauci ne kawai idan na ji ki a kusa da ni. Ki kula min da kanki har zuwa lokacin da zan dawo kulawarki ta dawo hannu na. Ina Son Ki" kana ya sauka online badan ya gaji da jin muryarta ba.
Cikin farinciki ta kwanta tare da yin adu'ar kariya daga dukkan sharri, lokaci ɗaya barci ya ɗauketa,
WASHE GARI
Kiraye-kirayen sallahar asbha da ake yi ne ya sanya ta farka, tare da karanto adu'oi kamar kullum, tashi tayi ta ɗauro alwalah tayi raka'atanil fijir kafin ta kabbara sallah lokacin har an fara kiran shiga.
Bayan ta idar ta yi adu'oi kana ta ninke prayer mat ɗin ta fito zuwa ɗakinsu Talatu, samunsu tayi suna sallah, tayi hamdala tare da wucewa kitchen, har masu aikin gidan su fito, suka gaisa ta ci gaba da aikinta, indomie tayi da ƙwai kana ta ɗibo dankalin turawa tana shirin ferewa, sai ga Talatu da Umaimah sun shigo kitchen ɗin, "anty good morning" suka faɗa cikin haɗin baki, "morning too" da fatan kun tashi lpy, suka amsa da lafiya lau anty, Talatu ta ɗauko dankalin Umaimah ta ɗibo musu wuƙa, da ruwa suka fara ferewa, bayan sun kammala suka miƙa mata, tayi musu godiya tana murmishi, a ƙa idar anty Tasneem bata taba bari ƴan aiki suyi mata girki, ko ya kai kala nawa ne,
Bayan sun koma ɗaki suka fara planing ɗin anty Tasneem na fita suka zasu fice, da wannan shawarar sukayi wanka, Umaimah ce ta fara shiga toilet bayan ta fito Talatu ta shiga, ko da suka shafa mai Talatu ta ɗauko powder zata shafa, Umaimah ta karɓe tana cewa "ni zan yi miki makeup kinsan na karanci tsara kwalliya sosai" Talatu tayi murmushi cikin sigar zolaya tace "shikenan kin huta idan bikinki ya zo" suka kwashe da dariya, ƙarfe 8:30am, anty Tasneem ta shigo ɗakinsu tare da cewa "breakfast yana dinning ni zan wuce Please ku kula da gidan, "anty sai kin dawo"
Suka faɗa cikin haɗin baki,
Tana fita Umaimah ta ƙwalawa Talatu kira, kasancewar anty Tasneem ta bar mata sallahun ta miƙawa su Inna mai aiki abincinsu, bayan ta miƙa musu ta dawo ta samu Umaimah tana searching a jiji app, Umaimah taga Infinix hot 12 kuɗinta dubu ɗari da sittin da biyar 165.000, basu wani ɗau lokaci mai tsawo ba gurin shiryawa, dukkansu abayar suka saka, Talatu ta sanya baƙa mai adon duwatsu masu ɗaukar idanu golden, itakuma Umaimah ta coffee brown sleek itama mai adon duwatsu, veil ɗin sukayi rolling nashi, wow Masha Allah, sunyi kyau sosai, ko wacce ta ɗauki hand bag ɗinta, hand bag ɗin Talatu babu komai a ciki daga abin share fuska sai lipstick da powder shikenan, suka fito cike da salo da ƴan mata masu tashen budurci, har Talatu ta so tafi Umaimah iya taku, sai da suka je gurin su Inna masu aiki suka ce musu zasu je siyan kati, kana suka wuce harabar gidan, mai gadi ma yana ɗakinsa, motsin buɗe get ne yasa shi fitowa, yana ganin sune yayi musu Allah ya kiyaye suka wuce, basa son hawa motar gidan, sbda suna tsoron kar bincike ya biyo ta kansu wataran, shiyasa suka yanke shawarar hawa napep.
Sai da suka isa bakin
End Ads