"duk wannan ba damuwata bane, indai ta shiga babu damuwa na shiryawa koma meye" daga nan ta ajiye masa 2 hundred.k kana ta bar gurin, boka ya kwashe da wata iriyar dariya mai sauti...
Abuja
A hankali tayi parking motarta a inda aka tanada na cikin company ɗin, kai tsaye office ɗin Ma'aruf ta wuce cike da yauƙi, nocking tayi ya bata izinin shiga, ta shige ranta fess, sallama tayi ya amsa kana ta ƙara sa ciki, yayi mata alama da hannunsa akan ta zauna, tunda ta shigo ya fara jin wani abu ga me da ita, shi kansa ya kasa fassarawa kansa shin me yake ji ne?" Bayan ta zauna tace "good morning my Honey" kasancewarsa miskili bata wani fahimci fara'arsa ko akasin hakan ba, "ya amsa mata da morning to o, tai murmishi kafin tace "wow Masha Allah honey kayi kyau sosai, dama dai daga gida sai mota, saboda bana son ƴan mata su gama kallemin kai" juyi yayi a saman kujerar kana ya lumshe idanunsa, wani sihirtaccen murmishi ya baiyana fuskarsa, kafin ya lashi pink lip ɗinsa na ƙasa, kana yace "da fatan dai kin tahomin da abinci"
Yah Subhanallah yafa birgeta, sai ta ji ta tamkar a wata duniya take, ko hira Mai tsayi basu taɓa yi a tsakaninsu ba, yau shi ne har da tambayar abinci?" Ta yi murmishi kafin tace "honey idan kana da buƙata ko nan da ina ne wlhi zan je in dafa maka, an sorry honey I love you wlhi" tayi maganar hawaye sun fara zubowa a idanunta, sosai yake kallon ƙwayar idanunta saboda tabbas ya hango tsagwaron soyayyar da takeyi masa, sai dai birgesa takeyi babu ƙaunarta a cikin zuciyarsa,
Murmishi yayi kafin yace Love You too, tayi ƴar dariya tana rufe fuska, kana ta tashi tana cewa "barin je inyi maka girki mai daɗi, yace "oky"
Matsalarta dashi sam baya iya yin magana Mai tsayi ko hira,
Haka dai ta wuce kai tsaye kasuwa tayi siyayyar kayan abinci, sboda tana son ta dafa masa jollof ɗin couscous da vegetables, daga kasuwa ta wuce gidan ƙawarta, bayan sun gaisa tace "kinga ba zama bane ya kawoni, sir Ma'aruf ne ya ce inyi masa girki shiyasa kika ganni yanzu, kai tsaye ta shige kitchen ta ɗora abinci, kasancewar bashi da wuyar dahiwa yasa nan da nan ta kammala girkin sai ƙamshi ke tashi, ƙawar Tata, ta bata sabuwa kula ta zuba a ciki, kana ta bata kunun aya wanda tayi mai daɗi, wanda yaji kwakwa da dabino da peakmilk, aka zuba a kyakkyawan jug, ta sanya su a wani basket mai kyau sosai.
A tukunya ta barwa matar gidan kana ta fito tace mata sauri takeyi, daga nan ta dawo company, yayi mamakin ganinta a wannan lokacin, sboda yayi tunanin zata ɗau lokaci mai yawa kafin ta kammala girkin, ko da ta shigo faɗaɗa fara'arta tayi kafin tace "your food is ready" shima murmishin yayi kafin yace "godiya nake, ya kamata ki wuce office I think akwai aiyuka acan" uhm..uhm gaskiya bazan iya zuwa ba har sai na baka abincin nan a baki" suka haɗa ido, tare da sakarwa junansu murmishi, cikin nutsuwa ta buɗe foodflaks ɗin tare da ɗaukar plate da spoon ta saka, kana ta ajiye a gabansa, cikin salon so take aikin kana ta fara bashi a baki, a hankali ya buɗe bakinsa tare da lumshe idanunsa, lokacin da yake tauna abincin, yana jin wani irin daɗi yana ratsa shi, "gaskiya kin iya girki Masha Allah, wato duk mijin da ya aureki ya more, wlhi"
Murmishin yaƙe tayi saboda wannan kalmar sam batayi mata daɗi ba, sai tace "ai kaine mijin" cikin suɓutar baki da tunanin me zai bata amsa,
Murmishi yayi yana amsar abincin, ta ƙara ɗibo abincin zata bashi kenan abokinsa Muhammad ya turo ƙofar bakinsa ɗauke da sallama hangame baki...!
Afuwan inasha Allah idan nakai page 50 da zarar mun fara 51 zaku samu more typing.
Mom Islam ce, 08141799224
*NA KASA JUREWA*
💋💋💋
💋💋
💋
_Mom Islam_
Page 57-58
Bayan ta gyara bedroom ɗin nata, ta koma ɗakin Alhji Abdullahi, yana kwance kamar inda ta barshi ɗazu, ya miƙe samɓal sai ta ga ya ƙara yi mata tsayi sosai, a hankali ta isa gareshi tare da kai tafin hannunta gurin hancinsa, yanayin da jikinta ya bata, sam ta kasa gasgata hakan, ta sake kai hannu a karo na biyu, a tsorace tace "baya numfashi?" ta fashe da kuka, saboda bata yarda da abinda zuciyarta ke gaya mata ba, da sauri ta koma ɗakinta, kana ta ɗauki wayarta ta danna number anty Asabe, bata ma san anty Asabe ta kirawo ba, murya babu daɗin saurare tace "Salima ya akayi?"
Cikin Muryar kuka Hajiya Salima tace "Anty Asabe dan Allah kizo, dan Allah" takai ƙarshen maganar tana sakin kuka mai sauti,
Daga can ɓangaren anty Asabe sauri ta farayi, adu'ar da takeyi bai wuce ta ji ance nata Alhaji Abdullahi ya mutu ba, a fili tace "baya motsi meye amfaninsa" ta fito harabar gidan sboda dama ita kaɗai ce a gidan sai yaron ƙanwarta da ta rasu ta bari tun yana jariri ga shi yanzu ya zama saurayi a halin yanzu shekarunsa 27yrs a duniya,
"Driver yi sauri kazo ka kaini gidan yayana, tai maganar cikin yanayi na nuna damuwa kai kace har a zuciya, bayan ta shiga mota driver ya tada mota suka fice, kasancewar mai gadi ya buɗe get tun kafin shigarta mota.
Driver na gudu tana yi masa masifa akan ya ƙara gudu ita kam taga yana driving sai kace wani mace, daga ƙarshe ma cewa tayi ya fito a motar ya dawo backside ta yarda ita zatayi driving, abin ya matuƙar bashi mamaki matuƙa, saboda driving ɗin ma bata iya ba, shi yake koya mata, masifarta ta hanata koya,
Ikon Allah ne ya kawosu gidan Alhaji, gida ya cika maƙil da mutane, saboda Hajiya Salima ta sanarwa da maƙota, sai koke-koke akeyi, tun da taga ƙofar gidan an cika, tai saurin fitowa daga mota ba tare da ta gama tsayawa ba, wata irin kururuwa takeyi marar daɗin ji, har ta isa ɗakin da alhajin yake, Hajiya Salima da maƙotansu da ƴan uwanta wanda suke kusa, mama dai har yanzu bata iso ba, sosai take ta gunjin kuka babu kauƙautawa, mutane sai bata haƙuri sukeyi, cikin Muryar kuka tace "Allah sarki Yaseen da Yusra, ko a wane hali suke ciki oho,
Hajiya Salima kam idanunta sun kumbura sosai, tsabar kuka, da jimamin yaranta, ta rasa su, daga shi har ƴaƴansa, sosai takejin rayuwar duniyar ma ta fitar mata a kai,
Bayan anyi masa wanka kana aka yi masa sutura, daga nan aka kaisa gidansa na gaskiya.
Alhmdllh Alhaji Abdullahi ya samu yabo daga bakunan al'umma, babu mai faɗar wani mugun abu sai alkairansa, yayi tashen arziƙi wanda har yanzu ma yana kai, sai kuma yabar duniya, ya gina manya manyan masallatai da makarantun islamiyya duk kyauta, kana yana yawan kaiwa gidan marayu ziyara duk lokacin da yake free, hakan yasa ya samu babbar shaida anan duniya.
Ana kaisa aka fara hada-hadar ɗora abinci, anty Asabe kam kai tsaye ɗakinsa ta wuce, ganin key a ƙofar ɗakin yasa ta kulle ƙofar ba tare da sanin kowa ba, a tunaninta Hajiya Salima ta iya zuwa ta kwashe dukiya ta barta a banza..
KEFFI
yau ta kasance sunday, washe garin biki kenan, sam hankalinta ya gaza kwanciya, gani takeyi kamar Hajiya Zaliha zata iya dawowa, duk da alhajin yana gida, zaune take a saman gado, tana sanye da shadda fara sol anyi mata stone work ɗinkin Abuja Bubu, tayi ɗauri mai kyau wanda ya daɗa ƙawata kwalliyar tata, Masha Allah.
Danne-danne takeyi a wayarta, bata tunanin kiran iyayenta, saboda sune suka yi sanadiyar rusa mata farinciki, tunda akayi bikin bata kirasu ba, sboda ta ajiye simcard ɗin ta a ƙasa, a hankali Alhajin ya murɗa handle na ƙofar kana yai sallama tare da ƙarasowa cikin shiga ta alfarma, yana sanye da shadda milk color sleek sai sheƙi takeyi, a hannu ya riƙo babbar rigar tasa, ta amsa sallamar tare da sunkuyar da kanta, "Habibty gaskiya kinyi kyau" yai maganar yana ƙarasowa inda take, bata ɗago kanta ba, bare ta nuna ta ji abinda ya faɗa, zamansa a kusa da ita ne yasa ta ɗago fararen idanuwanta tare da ɗora su a nata, yai amfani da hakan wajen rungumeta, cikin Muryar tarairaya yace "Habibty nasan kina jin yunwa, idan har drinks ɗin da suke gidannan basuyi miki ba, ki tashi muje restaurant muci abinci"
Tabbas zaman kaɗaici ya dameta, duk da alhajin yana wuni a gida, amma bata wani sakewa suyi hira, ita har yanzu bataji tana sonsa ba, sai dai ta gano yana tsananin sonta sosai, tana son ta koyawa zuciyarta sonsa ya zatayi?"
Amsar ta maƙale mata a ƙasan maƙoshinta,
Rungumeta yayi sosai, kana ya ɗan sunƙuyo da fuskarsa gurin tata fuskar kafin yace "Habibty mai kikace game da fitar?"
"Uhm to"
Saudart ta amsa masa, saboda bata da zaɓi,
Ta zame a jikinsa tare da buɗe drowa ta ɗauki mayafi, ta ɗauko sabon takalminta da Hand bag, da wayarta, wacce babu simcard a ciki, kana ta fito parlor, har yanzu yana mamakin Saudart, duk irin soyayyar da yake nuna mata har yanzu ta kasa fahimtarsa, mai yasa take yi masa haka?" murmishi kawai yayi, kana ya fita a bedroom ɗin nata, kai tsaye ya wuce bedroom ɗinsa, car key da ATM ya ɗauka, kana ya sanya takalmi cover shoe sannan ya fito parlor, tana zaune a ɗaya daga cikin kujerun da suka ƙawata parlorn, tayi nisa a tunani sosai, "Habibty tashi mu tafi.." jin bata ce komai ba, sannan bata motsa ba, yasa shi ɗan risinawa a gabanta bai kai ƙasa ba, yace "Habibty nace tashi mu tafi"
Firgit ta miƙe saboda tayi zurfi cikin tunanin nata, drivernsu na ganin fitowarsu ya fara shirin shiga mota, alhajin ya dakatar dashi tare da cewa "kayi zamanka yanzu zamu dawo"
Driver yayi musu Allah ya tsare, bayan an buɗe musu get securities ɗin suka buɗewa Alhji Murfin mota gurin zaman driver, already Alhji ya buɗe wa Saudart kusa dashi, kai tsaye yayiwa motar key suka bar anguwar,
Driving yakeyi time to time yana kallon fuskar Saudart, cikin rashin sa'a go slow ya haɗu, wata ƙawar Salma ta hango Saudart dake zaune cikin motar Alhji, abin ya bawa ƙawar Salma mamaki, dan bata san yayi aure ba, sbda har hannunsa ya ɗora a saman Saudart, kana ya zuba mata idanu, da sauri ƙawar Salman ta danna number Salma, ringing ɗaya ta ɗaga, tare da cewa "Aminiya ya akayi ne?"
"Ke na rantse da Allah idanuna sun ganemin wani abu, Salma Dad ɗinki tare da wata kyakkyawar budurwa har yana kissing ɗinta a mota gashi go slow ya haɗamu, nikam basu gama isata kallo ba" Salma ta miƙe a zabure, kana ta kalli mahaifiyarta, kafin tace "momy wlhi tallahi Dady ya gama damu, ashe ma yawo yakeyi da amaryar tasa, yanzu fa ƙawata ta kirani" Salma tayi maganar tana fashewa da kuka, tare da ɗora hannu a kai,
Hajiya Zaliha tace "shikenan, wlhi shikenan, mun kaɗe, daga mu har ganyenmu, Hajiya Zaliha tace "barin kira Hadiza inji ya akayi da maganar zuwa gurin malamin da tace zatace "
Salma ta dauki wayar Hajiya Zaliha ta kira lambar anty Hadiza, sai da tayi ringing sau uku ana uku Kafin ta ɗaga "Hajiya ina hanyar zuwa gidanki, yanzu"
Hajiya Zaliha tace "Allah ya kawo ki ina jiranki akwai wata, bura ubar sabuwa"
Hajiya Hadiza tace "shafamin ya akayi?" Sai kin zo ɗin kawai ina jiranki"
Hajiya Zaliha tai maganar tana share ƙwalla.
Suna cikin jajanta lamarin alhaji, anty Hadiza na shigowa parlor kai tsaye bedroom ɗin Hajiya Zaliha ta wuce, saboda basa parlor, tura ƙofar da zatayi ta samu sunata kuka dukkansu, da sauri ta ƙarisa tare da neman gurin zama, kafin tace "Hajiya kekuwa baki jira zuwan ba, kike sake tada hankalinki?"
Cikin muryar kuka Salma tace "anty Hadiza Dady ne ya cucemu, wannan wane irin tozarci ne, da ƴar cikinsa fa yake yawo" anty Hadiza tayi salati tare da cewa "oh ni Hadiza naga abinda ya isheni" sai kuma tace "amma dai ku kwantar da hankalinku, saboda wlhi nasa ayiwa Alhaji aikin mantau, ta inda bazai sake tuno da waccar karuwar ba, a tarihin rayuwarsa, inaso dukkanku ku cire damuwar Alhaji domin kuwa wasan yazo ƙarshe...
Salma na share hawaye tace "anty Hadiza nifa maganar mijina?" Anty Hadiza tayi murmishi tare da cewa "baki da matsala Salma, ke da kishiya har abada..
Salma tayi tafi cike da farin ciki, har tana zuwa ta rungume anty Hadiza.
K.D
Kwanci tashi babu wuya a gurin ubangiji yau satin su Majeed da Najma ɗaya a gidansu Yaseen da Yusra kullum yana fita aiki sai ta ɗora abinci cikin tukunya ta kaiwa dabbobin nan, suna mugun jin daɗi sosai,
Ranar ta kasance Monday tushen aiki, dama duk ranar Monday baya dawowa da wuri, tana zaune a parlor taji mararta na murɗawa, a hankali ta zube ƙasa daga saman kujerar tare da runtse idanuwanta, da alamu tana jin zafi sosai, da ƙyar ta janyo wayarta ta danna number Yaseen yana ganin kiranta ya ajiye aikin da yake yi ya ɗaga tare da cewa "my life yakike" saukar numfarfashi da yaji ne ya tabbatar masa da babu lafiya, bai sallami mutanen dake gabansa ba, bare ya kalli wanda suka zauna a harabar Company ɗin, suna roƙonsa, kai tsaye mota ya shiga hankalinsa a tashe, driving yakeyi kamar zai tashi sama saboda tsananin firgici da yake ciki,
Ikon Allah ne kawai ya kawo shi gida, lokacin ta galabaita sosai, tana durƙushe a gurin,
Cikin hanzari ya ɗagata cak kana ya kaita mota, sannan ya dawo bedroom ɗinta ya ɗauki jakar kayan baby, kana ya shiga mota suka fice, ko takan baba mai gadi bebi ba, ya dinga sharara gudu a titi, har suka iso PLATEAU hospital, kai tsaye aka wuce da ita emergency room, manya manyan likitoci ne suka taru a kanta suna bata taimakon gaggawa, yayinda Majeed yake waje yana ta zirga zirga, ko wacce likita ko doctor suka fito basa sauraren sa, hakan ba ƙaramin ɗaga masa hankali yayi ba, cikin sauri ya lalubi number mahaifiyar Yusra ya kirata, tana ɗagawa ya sanar mata da Yusra na hospital, mahaifiyar Tata, tace "gata nan zuwa"
Tun ƙarfe 12:pm suke hospital ɗin har ƙarfe 2pm bai ji wani cikakken bayani ba, sai yanzu da wani doctor ya gaiyyacesa zuwa office ɗinsa, bayan sun gaisa yace "matarka aihuwa zatayi, gashi har yanzu shiru, sannan bata da wani power a jikinta ina tunanin zamuyi mata Cs idan har ka amince, ga takarda kasa mana hannu, damuwarsa bai wuce ya ga Yursa cikin ƙoshin lafiya ba, da sauri yasa hannun tare da ɗaga hannu yana roƙon Ubangiji, kai tsaye aka wuce da ita ɗakin tiyata domin kuwa bata cikin haiyyacinta, bata san waye a kanta ba,
Bayan an shigar da ita, doctor's suka fara hada hadar fara aiki, lokaci ɗaya ta wani daƙarƙare ta zafga ƙara tare da riƙe ƙarfen gadon da take kwance, sai ga baby ya faɗo, likitocin sai hamdala sukeyi, sakamakon tausaya mata da sukeyi,
Da sauri wata likita ta fita ta samu Yaseen dake zaune a saman benci fuskarta ɗauke da murmishi tace "sir matarka ta aihu" kafin ya buɗe baki tayi gaba, Yaseen kam wani daɗi ne ya lulluɓeshi sakamakon wannan albishir da wannan likita tayi masa, da sauri ya wuce masallaci ya kabbara sallah tare da sake miƙa godiyar sa ga Allah, lokacin da ya fito daga masallaci, Momcy tana parking mota ita da kakar Yusra ta gurin mahaifiyarta, ko gaisawa basuyi ba, suka hau tambayar jikin Yusra, yayi musu albishir da aihuwarta, suma su Momcy ba'a barsu sun shiga ba, sai bayan wasu lokuta kana aka basu damar shiga, dukkansu suka shiga ko wannensu fuskarsa ɗauke da fara'a, yaro ne Kyakkyawa mai kama da mahaifinsa, ga shi jajir dashi, an nannaɗeshi cikin kayan sanyi masu kyau sosai, Yusra kam tana da barci saboda drip ne ma a hannunta shiyasa akace kar suyi hayaniya, kaka sai cewa take yi "Masha Allah yaro kamar babansa" shikuma Yaseen yanata sunkuyar da kai, ko da Momcy ta karɓi yaron ta ji wani soyayyar jaririn na shigar mata rai, a hankali ta dinga tofa masa adu'oi daga ƙarshe ta miƙawa Yaseen, shima yayi masa adu'a, tabbas bai gaji da ganin ɗansa ba, haka dai ya danne ya sake miƙawa kaka, tare da kallon Momcy yace "Momcy ki faɗa min abubuwan da ake da buƙata, Momcy ta lissafa masa ya fice, suna yi masa Allah ya kiyaye hanya,
Acan gidan Yaseen dabbobi sunyi kuka har sunji ba daɗi, tsabar yunwa Barin ma su Majeed da Najma abin sai wanda ya ganni, saboda durƙushewa sukayi gefe guda sunata kuka,
Shinan Yaseen yama mance da maganar abincin dabbobi, har aka kwana aka wuni, da yamma da ya tuna ya sa aka kai musu, yana daga Hospital ɗin yayi waya da wani tsoho akan ya zo ya kwashe dabbobin yakai su kasuwa, abar masa saniya guda biyu su za'a yanka, hakan ko akayi, su Najma sunyi kuka sosai, koba komai sun fara sabawa da nan ɗin, yanzu basu san inda za'a kaisu ba, gaskiya suna cikin wani hali,
Kai tsaye aka wuce dasu kasuwar dabbobi, inda tsohon ya zauna yake karantar yanayin ko wacce dabba, tsohon ya kasance mafarauci ne, sannan yana da sani akan wasu abubuwan, tunda idanunsa a buɗe suke, ji a jikinsa da yayi ne ma, yasa yake ta kallon dabbobin, ko da idanunsa suka sauka akan su Najma da sauri ya sake ƙura musu idanu, ya girgiza kai tare da ɗauko wani kaskon wuta kana ya zuba wani abu hayaƙi ya tashi, sannan ya matso kusa da su ya ɗibi wani ruwa mai warin gaskiya ya watsa musu, kafin ya sake ɗibo wani garin magani ya kaɗa a ruwa ya basu suka sha, sannan yayi kabbara Allahu Akbar... Allahu Akbar.... Allahu Akbar, sau uku, abin mamaki sai ga Majeed da Najma sun baiyyana cikin kayan da suka fito dashi daga gidan tun watanni takwas da suka wuce, dukkansu a durƙushe suke, sai da tsohon ya sake ɗibo wani man shafawa ya shafa musu a guwaiwar hannu da ƙafa da wuyansu, kafin ya umarcesu da su miƙe tsaye, suka miƙe tare da fara rarraba idanu, dukkansu sai suka fashe