x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - NA KASA JUREWA book 1

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 86738 words

Category: Love Stories

Views 120

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
yarana"
"Lafiya lau" tace ma sa, a takaice,
Ya lura ta sauya sosai, amma dole ya sanar mata sbda lokaci yana ƙurewa.
Janyota jikinsa yayi, ya cire mata hijab kana ya zuge mata zip ɗin rigar jikinta, lokaci ɗaya halittun ta suka baiyyana, ɗan turo cikin tayi sai kuma ta cuno baki"
"Mene ne?"
Ya tambaye ta in cold voice, "babu komai uhm Habiby duk ka sauya bana jin daɗin hakan, ko kana son yaran mu suma su fuskanci ɓacin raina? kuma kasan illa ne a gare su"
Tana gama rufe baki ya zura harshensa a bakinta, ya fara yi mata wani salo me wuyar fassara, hannunsa ya zagayo dashi ta ƙugunta cikin cold voice yace "komai ya canja ciki har da abinda na fi ƙauna"
Ɗan turo masa ƙirjinta tayi kafin tace "uhm dole ka bar wa yara tunda ka girma"
"Kafin su zo ai zan ɗan sha koda na one week ne"
Zainab ta waro idanu kafin tace "ka mance har ruwa yana fitowa?"
Suka sakarwa junansu murmishi me kyau,
"AM kinsan me?"
"A'a habiby"
Zainab ta faɗa tana rangwaɗar masa da kai.
Yace "baki tambayeni ya mukayi akan maganar neman aiki ba?"
Cikin nutsuwarta tace "Habiby ai kai ne ya kama ta ka bani labari"
Sai da yaja dogon numfashi kafin yace "Zainab bazan ɓoye miki komai ba"
Ya kwashe kaf inda sukayi ya gaya mata, da sauri ta matsa kusa dashi, tana ja da baya tana daga zaune,
"Haba Zainab, a tunani na zakiyi min maganin damuwata? me yasa zaki gujeni?"
Abin sai kace wani sihiri, ko da yake ya riga yasa an juyar mata da hankali, lokaci ɗaya ta share hawayen dake kwaranyo mata tace "shi kenan Habiby na amince"
Tattaro ƙarfinsa yayi kana ya ɗaga ta sama yana juyi da ita, suna yiwa junansu murmishi...!

Idan naga comments gobe nayi muku alkawarin read more 6 insha Allah

Mom Islam 08141799224

*NA KASA JUREWA*
      🪻🪻🪻

      Mom Islm

Page 19-20

Sai da ya tabbatar da ya kwantar mata da hankali, kafin yabar bedroom ɗinta, time ɗin ya barta har ta fara barci,
Kai tsaye bedroom ɗinsa ya wuce, ya baje a ƙasa tare da zuba wa kwalayen da suke ɗauke da kuɗaɗen idanu tunanin wace irin sana'a ya kamata ya fara, tun kafin a fara yi masa tambayar ƙaƙa uwarka ta haifeka, lokaci ɗaya ya yanke shawarar buɗe katafaren shagon siyarda atamfofi lases da su abaya da duk wasu kaya na mata da maza,
Tunda waɗannan kuɗaɗe suka zo masa ya ƙaurace wa kasuwar da yake zuwa,
Kwanci tashi asarar mai rai, ranar Litinin ranar da ta kasance musu rana mafi ɗumbin tarihi.
Tun dare ta fara naƙuda aka wuce da ita Hospital, cikin hukuncin Allah ta haifo yaranta guda biyu duka mata, kamar su ɗaya sak komai nasu iri ɗaya, badan alama da Norse sukayi musu ba, ƙarya ne ka tantance su, koda aka kai ta ɗakin juyawa cewa takeyi "ina yarana ina yarana?"
Dole aka kawo mata su ta rungume su, wasu zafafan hawaye suka kwaranyo mata, nadama mai cike da dana sani ta fara yi, duk da ita ta amsa masa, kama daga danginta har da gin alhji Aliyu, duk wanda yazo ganinta ba'a bari ya shiga, sannan babu wanda ya san me ta haifa,
An so sallamo su da yamma, alhji Aliyu yace a bari zuwa gobe da asbha, lokacin ta sake hutawa, amma yanzu idan aka sallameta mutane zasuyits hayaniya, haka ko akayi, ƙarfe 11pm na dare, Muktar yazo ya tafi da ɗaya daga cikin ƴan biyun wato Usaina, idan kuka ga inda ake fita da jariran sai abin ya bawa mai karatu mamaki, ba wai na alhji Aliyu kawai aka ɗauka ba, jarirai da yara wanda aka ɗiba a Nigeria sunkai dubu, koma duk wata hakan yake kasancewa,
Bayan hakan ta faru, suka tattara kayan su zuwa gida, dangi kuwa kowa ya kama gabansa tunda sun san faɗan sa  dole suka barsu.
Kamar inda ya faɗa da asbha suka wuce gida,  nan fa ya fara kiran ƴan uwansa da ƴan uwanta, tashi ɗaya aka cika gida, Zainab tayi iya bakin ƙoƙarinta gurin ganin ta mance da ɗiyar tata, sai dai wani lokacin zaka same ta tayi shiru, abin da ya bawa ƴan uwa mamaki bai wuce, saniya da suka gani an shigo da ita ba, kowa sai mamaki yakeyi, wasu na cewa "ashe dama alhji Aliyu yana da kuɗi sosai haka?"
Hhh ƴan uwa daga masu kwaso kaya bayan suna zasu tafi, haka dai sukayi ta facaka tunda komai a kwai shi enough,
Ranar suna raguna biyu ya yanka irin manya manyan nan, ga ragowar naman saniya da aka yanka, sai da yayi wa Zainab da jaririyar ta, kaya na gani na faɗa, ga gift da aka rarraba Masha Allah.
Washe garin suna dangi sun gama komai, suka fara hidimar komawa gida,
Ko wanne sai da aka bashi kudin mota,
Haka rayuwa taci gaba da tafiya musu cikin daula da kwanciyar hankali, tunda dai ko sun nuna damuwa ƴarsu baza ta sake dawowa ba,
A halin yanzu Zainab ta kasance mafi soyuwa a cikin dangi sbda tana da kyau ta sosai ga fara'a da sakin fuska,
Watan ta bakwai da aihuwa ya siyar da gidan da suke ciki ya siyi wani anan keffi, danƙareren gida mai kyau da tsari, wanda daga bakin get ma kaɗai zaka bawa wasu labari, masu zuwa ziyara ko basa yanke wa sam,
Hassana wace suke kira da Saudart lokacin ta fara wayo, ga dariya ga ta kyakkyawa kamar mahaifiyarta zainab.
              ************
Girman ɗan mutum babu wuya,

wata kyakkyawar budurwa na hango, tana sanye da doguwar riga ta atamfa, mai adon koren ganye da shuɗi, yanayin ɗinkin da zanen dake jikin atamfar ya amshi jikinta doguwar riga ce buba ɗinkin riga da zani, ita kaɗai take zaune gefe kuma takardu ne wanda zaka tabbatar da bitar karatunta takeyi, Saudart Aliyu kenan, kyakkyawar yarinya mai tashe, duk wani ɗalibi da malami yasan waye Alhji Aliyu, hakan yasa ake kaf kaf da Saudart, har tazo matakin ƙarshe na kammala karatu, bata kula samari a cewar Zainab wacce a yanzu Saudart take kira da momy, su zasu zaɓa mata mijin aure, sai mai nera dan ba zasu siyar da akuya ba,  ta dawo tana ci musu danga.
Kasancewarta yarinya mai hankali da jin maganar iyaye, yasa bata tsallake maganarsu ba.
Koda ta kammala karatu zata tafi bautar ƙasa, ta sha jan kunne sosai.
Koda aiki ya fito mata bata wani yi na'am ba haka ta ci gaba da zaman gida, tunda babu abin da ta nema ta rasa,
A sanadin kasuwanci Alhji Aliyu ya haɗu da mahaifin Ma'aruf, lokacin ya zo da su Hajiya mama siyan kayan sallah, daga nan suka ƙalla abota mai ƙarfi, har sukayi musayar numbobi, a zahirin gaskiya mahaifin Ma'aruf ya fi Alhji Aliyu kuɗi, nasan zakuyi mamaki...
Mahaifin Ma'aruf. Asalinsu noma da kiwo shi ya karɓesu, ta haka suka tara ɗumbin dukiya tun iyaye da kakanni, tun duniya na kwance suke siyan filaye, iyayensa shi kaɗai suka haifa, asalinsu Fulanin jihar Yola ne, duk shekara suna shirya gagarumin taro nasu na Fulani, wanda ilahirin mutanen ƙauyen suke halarta, a wannan shekarar ma mutanen da suka halarci taron bazasu ƙirgu ba, saboda gabaki ɗaya yankin suka tafi, sai dai Allah mai iko babu wanda ya dawo a raye duk sun mutu, sai mahaifin Ma'aruf shine kawai a raye, shima duk ya ji rauni ta ko ina,
Bayan ya warke ya ci gaba da tafiyar da kayan iyayensa, kasancewarsa mutum me gaskiya da amana yasa ya samu al'umma masu ƙaunarsa, alhmdulilah yayi boko dai-dai gwargwado kowa na alfahari dashi, ga taimakon talakawa, ko bayan rashin iyayensa be hana shi ci gaba da noma da kiwo ba,
Kasancewar lokacin Ma'aruf yana ƙaramin, shi kaɗai suka haifa, mutum ɗaya ne ya rage a danginsu wato Inna, wacce take ƙauyen Kano, aure ne ya kai ta can, Allah yayiwa mijin nata rasuwa amma ya jima sosai tun bayan da ta haifi Talatu, wannan kenan.
After 3days
Hajiya ta ji sauƙi sosai, se dai har yanzu ta kasa kiran  momyn Saudart saboda takaici,
A ranar Inna ta shirya komawa ƙauye, Hajiya mama da Anty Jamila suka ce mata ta turo musu Talatu suna son ganinta, sai da tayi musu alƙawarin idan ta koma zata sata a mota drivern su ya kawota, kaya da yawa Hajiya mama ta haɗa mata, anty Jamila ma ba'a barta a baya ba gurin zaɓo mata hijabai da sikel ɗin ciki.
Ƙarfe 9:am Inna ta bar Abuja, suka kama hanya sai Kano..
Sun sha tafiya sosai saboda sunyi awanni kana cikin hukuncin Ubangiji sai gasu a cikin garin Kano, sun sake yin tafiya mai nisa kafin suka Iso ƙauye.
Shugowar motarsu ke da wuya, yara da ƴan mata suka cika gurin, kai kace biki akeyi,  can na hango Talatu sai tuture mutane takeyi, tana cewa hegu ƴan ƙauye, tana rattaba motar, Inna ce ta fito tana murmishi, Talatu ta je da gudu ta rungume ta tana cewa " kun higa uku kudai, to Inna aka kawo a mato se kowa ya watse ƴan cusa kai..
Parking ɗin motar yayi a gindin bishiyar dake ƙofar gidan su Talatu kana ya jingina kansa a jikin kujerar motar ya ciro waya yana dannawa,
Suna shiga gida, kafin su kai ga shiga ɗaki kaka tayi sallama, suka amsa, a tsakar gida ta zauna tana yiwa Inna Barka da dawowa, ganin anata fitowa da jakar kaya ya sanya ta cewa "ina kuma ja a kai su?" wallahi su Hajiya ne suka ce Talatu taje tayi musu kwana biyu shine na haɗo mata kaya"
"Alhmdllh na gode musu, wallahi dama ta isheni taɓɓ duk wanda ya kwashi wannan yarinyar to ya kwasar wa kansa"
Kaka ta ƙare maganar tana riƙe haɓa,
"Ni ki dena yimin baki, wataran na ga me tare miki faɗa wallahi"
Kaka ta raɓe baki, gami da cewa "kafin ki taremin faɗa kin bani wuya"
Inna ko ta kansu bata bi ba, sbda idan sun haɗu sana'arsu kenan da kaka da talatu, Talatu ta ruga gidansu Gudidi, a tskar gida ta sameta tana cin rogo da ƙuli, Gudidi na ganinta ta ɗora ƙafafu a saman kwanon tana wulli wulli da idanu, "keee"
Talatu ta faɗa a hankali,
Yi mata alama da ta taso tayi, ta taso tazo gurinta, lokacin Ramma tana ɗauki tana sallah,
"Ki faɗa min menene ko kinzo sake dukana ne?"
"Ke dalla can binni zani hine nace bari inzo in gaya miki, al'kur'an idan zaki ki ɗibo kayanki ki watso min ta katanga sai in kwahe mu wuce kinga mun zamo ƴan binni"
Cikin sanɗa taje ta miƙa mata kwanon abincin nata, tace ɓoye maci a mato, Talatu ta juye a ɗankwalinta ta cukuikuye guri guda, ɗan zirine mayafie da taci ɗammara dashi ta ɗaura, har gudidi ta gama tattaro kayanta ta watsa su ta baya Ramma bata sani ba, ashe barci ma takeyi,
Gudidi ta kalli ƙaramar ƙanwarta wacce bata wuce shekaru biyar ba, tace "ke Atika ki ce wa Ramma na tafi binni ni da Talatu"
Yarinyar sam bata ma gane me Gudidin take nufi ba, ta amsa da "toh" suka wuce,
Tunda driver ya san tare da Talatu zai koma ko me ta kawo baya yi mata musu, har kayan Gudidi sai da ta saka a boot,
Daga ƙarshe suka raba rogon tare, Talatu ta tura gudidi a boot kana ta rufe, dama kafin Gudidin ta shiga,  Talatu tace mata ta daure, idan suka je can kilihi zasu dinga ci"
Talatu ta koma gida tana tsalle, Inna tace "dan Allah talatin ki nutsu ban da yawan magana, Kaka tace "ban da mugunta, hannan ban da  idan ayi maka ka rama"
"Wallahi duk wanda ya nuna min yatsa he na karyehi kohi waye"
Talatu tai maganar tana tsalle.
Horn ɗin da driver yayi ne, yasa su fitowa, Inna ta miƙawa talatu wani babban buhu mai ɗauke da daddawa da kuka da su barkono,
Har za a saka a boot, Talatu tace "za'a sace a hanya a bata a hannunta, sbda asirinta zai tonu.
Koda driver ya tada mota su Inna suna ta ɗaga masa hannu da yaran dake gurin har suka ɓace wa ganinsu,
Sunyi nisa sosai dan sun bar garin Kano, zamu iya cewa sunyi ra bi a tafiyar tasu, Talatu tace "me mato dan Allah ka tsaya zanyi fitsari"
Gefen hanya ya samu yayi parking ta fito ya miƙa mata gorar faro "yace gashi" karɓa tayi, bayan tayi fitsarin tana dawowa ya fito shima, cewa take "Gudidi zan buɗe ki yanzu ki dawo cikin mato idan kuma kin mutu hikenan maci naman kaza babu ke" driver yace "Kee! Waye Gudidi? kinada hankali kuwa, a jeji muke da zaki dinga kirawo mana wasu mutane wanda sunan ma babu daɗin ji, daga cikin Boot ya ji ance "me mato ka buɗe ni in fito yasin na gaji da zaman kurkuku"
Driver ya zaro idanu tare da matsawa a jikin motar, ya tsorata sosai, tunda a iya saninsa mutum ɗaya ya ɗauko, Talatu tace "kiyi hakuri idan mukayi mihi rabine kunya ze zubemu a nan bari in lallaɓa hi"
Ta durƙusa har ƙasa tace "kayiwa darajar gyatumarka ka fito min da ƙawata"
A tsorace ya buɗe Boot ɗin sai ga Gudidi tasha kuka ta gaji har da majina,
Driver yace "ke ai ke kadai aka ce in ɗauko wannan kuma wacece?...!

Sharhin ku shi zai bani damar yi muku typing da yawa.

Wanda suke karantawa basa magana karku damu zan tafi hutu kunji?.

Mom Islam 08141799224

*NA KASA JUREWA*
       🪻🪻🪻

Page 21-22

Talatu na matsar ƙwalla tace "ƙawata ce"

Kai tsaye ya zagaya ya shiga mota bai sake bi ta kansu ba, koda suka shiga mota basu kulle murfin motar ba, driver ya ce "ke rufe murfin motar mana"

Talatu tace "da ƙarfi ko a hankali?"
Driver yace "idan kika rufe a hankali kika faɗo mutuwa zakiyi"

Ai da sauri Talatu ta buga murfin motar gaaaam!!! ,

A tsorace ya ambaci sunan Allah, suka ci gaba da tafiya,

Suna gaf da shiga Abuja dan har sun wuce Keffi, Gudidi tace "me mato ka dakata yasin rogo ya sa ni gudawa"

Wani dogon tsaki yaja mtswww, kafin yace "ni fa na gaji da ɓatamin lokacin da kukeyi, mun kusa isa gida sai kuyi acan.

Gudidi sai cije baki take alamun kashi ya matseta, suna hawa gargada ta sake kashin tsuuuuu, wanda ya fara cika gurin da ɗoyi, ba driver ba, hatta Talatu toshe hanci tayi, sai kuma ta dinga sake tusa tana cewa "na higa uku ni gudalle Allah ka sa ban ɓata musu mato ba"

Talatu tace "Hegiya ance miki ki bari aje can gidan amma kin ƙi, saboda taurin kai irin naki"

"Talatu kinsan idan naci rogo cikina yana lalacewa, yanzun ma wani kahin nakeji"

Driver yace "wallahi idan kika sake yin kashi zan sauke ku duka"
Tsit sukayi babu wanda yayi magana, sbda sunga babu wasa a tattare dashi.

   Zaman ta a gidansu ya fi mata kwanciyar hankali a bisa zamanta a gidan Ma'aruf, satin ta ɗaya amma ta fara murmurewa, abin mamaki har yanzu momy ba ta sanarwa da Dady Saudert ta dawo ba,
Sai da suka kwashe one month a can kafin Dady ya biyo jirgi ya dawo, ya bar Anam acan kasancewar tana karatu ne,
Wacece Anam?,
Anam ƙanwar Saudart ce, shakarunta 18yrs a duniya, Dady ya ɗora buri a kanta, sbda ita ce alkawarin su na ƙarshe da oga akan itama ze kai ta can wato ya bar musu,kamar inda ya bada ƴar uwar Saudart.
Girke-girke momy ta shirya masa masu rai da lafiya, ita da ƴan aikinta biyu da Saudart suke ta ƙoƙarin girkin, 5:pm driver ya ɗauko Dady daga airport zuwa gidansu,
Momy Saudart, duk sun ci kwalliya sunyi kyau sosai suna jiran shigowarsa, sallamar Dady ne ya karaɗe parlon, Saudart ta miƙe da gudu tana oyoyo dady, bubbuga bayanta ya ɗan yi kai kace wata baby kafin ta koma ta zauna tana murna, ya buɗe hannayensa ma me momy ta taho ya rungumeta, suna sakarwa junansu murmishi,
Bayan ya zauna aka kawo masa abinci saman table, sbda a ranar da ya dawo baya zuwa dinning cin abinci, farfesun naman rago ne da tuwon shinkafa miyar egusi sai lemon abarba da kankana wanda aka zuba masa peakmilk, sai da Dady ya cika cikinsa kafin ya wuce bedroom ɗinsa, acan ya samu momy tana ƙoƙarin fito masa da kayan da zai sa, ta baya ya rungumeta tare da cewa "Hajiya Zee meye sirrin komai nawa yana sake haɓɓaka" cike da so da ƙauna ta juyo tare da kwantar da kanta a faffaɗan ƙirjinsa, gami da shafo gashin gemunsa wanda ya fara zama fari da baƙi sbda ya fara manyanta, Habiby any time kana sake zamowa kamar saurayi"
Cikin shauƙin so ya wani zagaya da hannayensa zuwa wuyanta kafin yakai bakinsa kumatunta ya sakar mata hot kiss, kafin Dady ya shiga wanka an sha love fa.
A tare da momy suka shiga wankan sbda wannan umarninsa ne, idan har yana gari tare suke wanka, bayan ya fito yana tsane jiki, momy ma ta fito ɗaure da towel milk color, Habiby yau  zanje anguwa wata ƙawata ta aihu walhi yau 4days ko zuwa banyi ba"
Momy na gama rufe baki Dady ya sanya hannunsa a saman lips ɗinta kana yace "shiiii" wannan ranar tawa ce dan haka a bata haƙuri a tura mata da 100k, babu inda momy ta iya dole ta haƙura.
Duk wannan maganganun da suke yi a kunnen Saudart, tazo wucewa taji suna magana ita kuma ta tsaya, nikam nace Saudart ki rufawa kanki asiri, jin shiru yasa ta bar gurin ta wuce bedroom ɗinta, fashewa da kuka tayi yayinda ta tuno soyayyar da suka kwasa ita da Ma'aruf, daga ƙarshe ta juye ta koma ƙiyayya mai muni.
Lokacin da aka fara kiraye-kirayen sallahar magriba, Dady ya fito sanye da jallabiya, zai wuce ya kalli Saudart kafin yace "daughter yaushe kikazo?" fashewa da kuka tayi kana ta miƙe ta bar gurin da gudu, wucewa yayi masallaci sbda idan ya koma ciki yana iya rasa sallah.
Lokacin da su Talatu suka iso Abuja ana kiran sallahar isha'i, saboda tsayuwar da suka dinga sa driver yayi,

Tunda suka doso bakin get Gudidi take ƙwalalo idanu ita da talatu, koda aka buɗe get ɗin bayan yayi horn sakin baki sukayi, a parking space ya ajiye motar kana ya zare key ya fito suna gaisawa da mai gadi, Boot ya buɗe kana ya firfito musu da kaya ya wuce dashi side na su Hajiya mama, suma bayansa suka bi .
Hajiya mama na ganin driver ta
End Ads