x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 19 - NA KASA JUREWA book 1

  • 54001 words
  • 57000 words
  • Out of 86738 words

Category: Love Stories

Views 128

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ya fice daga cikin makarantar.
Da sallama ta shiga class ɗin, wasu ƴan mata guda biyu suka amsa mata fuska cike da fara'a, suna ce mata Aysha Barka da zuwa" duk da bata wani daɗe da shiga makarantar ba, ta fara sabo da ƴan matan ajinsu, sosai ta sake wayewa idanunta suka sake buɗewa, sabda ƴan matan ajin nasu duk wasu sun girme mata wasu kuma ta girmesu, alhmdulilah karatunta yana tafiya inda ya kamata, tunda wasu ma gurinta suke zuwa su tambayeta abinda basu ganeba,
Ko da aka fita break ƴan ajin nasu basu fita ba, kasancewar suna meeting akan inda zasu yi birthday ɗin ɗaya daga cikin ɗaliban mai suna Laurat, ko wacce tana faɗar abinda zata kawo, dai-dai ƙarfinta,
Aysha tayi murmishi kafin tace "nikam zan zo ayi aiki tare dani, idan har na samu abin kawowa zan kawo"
Nan fa suka kaure da ihun murna, suna class har aka dawo break, a ranar malamai huɗu ne, suka shigar musu aji, kuma alhmdulilah duk wani malami da ya shiga ajinsu yana alfahari da basirarsu saboda suna ƙoƙari sosai, bayan sunyi sallahar azhar suka koma aji, yau kam da wuri aka tashesu dan basukai 6:pm ba, saboda ankai wata Malama Hospital,
Ta rasa inda za'ayi ta koma gida, ga shi tsakanin makarantar da anguwarsu akwai nisa sosai, shawarar taje office ko akwai mafita ne ya faɗo mata, bayan tayi sallama shugaban makarantar ya amsa kafin yace "yarinya lafiya?"
Aysha tayi rau-rau da idanu kafin tace "Dama number wayar dreban gidanmu ko ta yayana nake nema.."
Shugaban makarantar ya buɗe wani babban littafi wanda suke ajiye number saboda irin haka, kasancewar ita bata jima a makarantar ba, yasa ya gane sunan yah Arman, ya ɗau number tare da kiransa, ringing ɗaya wayar yah Arman tayi kana ya ɗaga, bayan sun gaisa shugaban makarantar yace "dama mun tashi ɗalibai ne, sakamakon wata Malama babu lafiya an wuce da ita asibiti, Yah Arman yace "okay ta jirani gani nan zuwa"
Kallon tulin file's ɗin dake gabansa yayi, saboda ya fara cikewa kenan aka kirashi, shi kuma bayajin zai iya haƙura ta hau mashin ɗin wani ko adaidaita, yana tsaka da tunanin tafiya makaranta, PA ɗinsa ta sake shigowa a karo na biyu, "Sir dama nazo in gaya maka ne, ya kamata a cike takardunnan a yau saboda yin hakan yanada muhimmanci sosai"
"Naji..."
Shine amsa da ya bata, koda tayi masa godiya ta fita, tsaki yaja mtswww, tare da tashi tsaye, ya ɗauki key car ɗinsa, cikin sauri dan baya buƙatar wani dakatar dashi, ya shiga mota kana ya fice da a guje, yayi gudu sosai kafin ya iso makarantar, a waje yayi parking motarsa kana ya fito ya shiga cikin makarantar, tana zaune ita da ƙawarta, Laurat kasancewar itama bata da number kowa na gidansu sannan bata je office ta tambaya ba, sukan ɗanyi fira jefi-jefi kafin Yah Arman ɗin ya iso, yana isowa inda suke Laurat ta gaishe sa, kafin Aysha ta gaishe sa itama, amsa musu yayi a lokaci ɗaya, tare da cewa "Aysha wacece wannan?"
Aysha tayi murmishi kafin tace "yah Arman ƴar ajinmu ce"
"Me yasa bata tafi gida ba"
Laurat ta karɓe da cewa "drivern mu ne bai zo ba"
Yah Arman yace "okay muje sai in saukeki a hanya"
Laurat tace "ai sai na rigaku sauka ma"
Suka wuce zuwa mota,
Yah Arman da Aysha suna gaba, Laurat tana baya, sunyi tafiya ba mai nisa sosai ba, suka iso ƙofar get ɗin gidansu Laurat, kasancewar gidan yana bakin hanya, tayi musu godiya kana ta fita tare da ɗagawa Aysha hannu tana murmishi,
Sunyi tafiya mai nisa kana ya waigo ya kalleta sannan yace "Aysha ana karatun kuwa?" Ta gyaɗa masa kai,
Cikin yanayi na bada umarni yace "karki kuskura wani namiji ya fara wata magana dake, a school ko a hanya ke ko a ina ne, wlhi idan har kika fara soyayya Aysha kin cuci kanki, sbda inaso kiyi karatu sosai ki zamo wa iyayenki abin alfahari"
Aysha tace "insha Allah yah Arman, Nagode sosai"
Koda suka iso ƙofar gidan anty Tasneem, bai shiga ba, ya ajiyeta a bakin get, tayi masa Allah ya kiyaye hanya, kana ya wuce.
Kafin ta kai ga shiga gidan, sai da ta daɗe a tsaye tana tuno faɗan da Yah Arman yayi mata, lokaci ɗaya zuciyarta ta kasu gida biyu, ɗaya tana ce mata, tabbas Aysha kinyi ganganci, ɗayar kuma tana ce mata "inda kika fara samun farinciki bai kamata kiyi wasa da damarki ba, ga shi Zayden yana mugun sonki kawai ki mance da batunsa,
Ko wacce shawara ta yanke oho, kai tsaye ta wuce cikin gidan tare da yin sallama, sai da ta gaishe da mai gadi kana ta shige ciki.
A parlor ta samesu da Anty Tasneem da Umaimah suna zaune a saman kujera suna hira, sannu tayi musu kana itama tayiwa kanta mazauni tana cewa "wash na gaji"
Umaimah tasa dariya tare da cewa "haka muma muka sha fama da wannan zirga-zirgar" Aysha ta turo baki gami da cewa "anty bakiga na dawo da wuri ba?" Anty Tasneem tace "wlhi kinga tambayar tana bakina, amman dai lafiya ko?"
Aysha tace "ai wata Malama ce babu lafiya"
Sukayi mata adu'ar samun lafiya, Umaimah tace "barin taimaka in kawo miki abinci, Aysha ta washe haƙora tana dariya.
SINGAPORE
Buland island
Wani haɗaɗɗan ɗaki Reed ya shigar da Thabit, cikin kakkausar murya yake gaya masa ɗakin sirrinsa ne, saboda kaf duniya bashi da kamarsa, ɗaki ne wanda aka gina shi da zinare, ko ina walwali yakeyi, sai dai shima ɗakin a tsafe yake sosai, a saman wata kujera mai zaman mutum biyu suka zauna, abin mamaki, a hankali kujerar ta fara tafiya har ta kaisu ga wani rami mai kyau, ramin an sarrafashi da gwala-gwalai, sannan komai na cikinsa gold ne, Oga Reed ya kalli Thabit kafin yace "wannan guri da kake ganinsa, idan har mutum ya shiga ba tare da amincewata ba, gawarsa za'a gani, sannan waɗannan gwala-gwalai da ka gansu mallakina ne, yau ma za'a sake kawomin wasu a cikin dare" Thabit ya jinjina kai, kafin yace "baka da matsala dani shugabana ni mai biyayya ne ga duk wasu abubuwan da ka sakani zanyi maka" Oga Reed yai murmishi kafin yace "yayi dai-dai, yanzu ya kamata mu koma ɗakin da buka baro, sbda inason mu tattauna wasu muhimman abubuwa" Thabit ya jinjina wa Oga Reed kai tare da binsa suka koma ɗakin da suka baro a da,
Thabit ya ɗauki school bag ɗin da ya shiga gurin Oga Reed da ita, zuge zip ɗin baya yayi kana ya ciro wani ƙaton mangwaro jajir dashi, sai dai jan da yayi bai hanashi yin tauri ba, Thabit ya miƙawa Oga Reed, Oga Reed ya miƙa hannu tare da cewa "Me ya kawo mangwaro cikin shirin da muke son aiwatarwa?" Thabit yai murmishi kafin ya juya bayan mangwaron kana ya sanya hannu ya tura ɗan yatsansa sai ga shi ya ciro sabon memory card, ya miƙawa Oga Reed,
Kana yace "wannan memory card ɗin da kake ganinsa akwai abubuwan da zasu amfani tafiyar da zamuyi kawai ka tsaya ka kalleshi daga farko har ƙarshe,
Da sauri Oga Reed ya janyo system ɗinsa kana ya jona memory card ɗin, ya buɗe, videos ya gani sunkai kala uku, ya kunna na farko, sosai videon ya ja hankalinsa, sakamakon tare wasu jiragen ruwa da akeyi, abin takaicin ma, nasa ne, jiragen ruwan sunkai su biyar, amma duk an riƙesu, wasu a cike da ƴan mata, wasu kuma an cika shi da miyagun kwayoyi, wani an cika shi da magunguna masu cutarwa, wasu kuma an cikosu da ma'adanai na ƙarshen shine wanda aka cika shi da wasu manyan kwalaye ko meye a ciki oho..,
Kafin Oga Reed ya kai ga kallon video na biyu, hankalinsa in yayi dubu ya tashi, rai a ɓace ya miƙe tare da kashe kallon, kana ya juya ga Thabit sannan ya marairaice idanu, ya sani idan har waɗannan jiragen ruwan suka salwanta, tabbas kashinsa ya bushe har gida za'azo a ƙamashi, sboda bashi da tarin ƴan matan da zai biyasu dashi, a yau yau ɗin nan ya ƙuduri aniyar ɗaukar ƙwaƙwaran mataki akan wannan ɓarna da ake shirin yi masa, Yace "ɗan uwa Thabit Please I need your help, kaima zaka more duniya idan har ka taimakamin wannan lamari bai faru ba, Thabit yace " Oga baka da matsala dani, dama kuɗi na fito nema saboda talauci ya isheni tabbas idan na zauna baƙinciki zai kasheni" sosai hankalin Oga Reed ya kwanta, ya matso kusa da Thabit kana yace "yanzu me kake ganin ya kamata muyi?" Thabit yai shiru da alamu yana nazari ne, ya daɗe bai cewa oh Reed komai ba, daga ƙarshe dai yai gyaran murya kafin yace "Oga kuɗi zaka fitar masu yawa, saboda mu siye manya manyan masu ruwa da tsaki a ƙasarnan, ta inda ko me zaka shigo dashi babu mai yi maka magana, ya kasance duk wata kana biyansu lafiya lau fa" Oga Reed yace "tabbas na daɗe ina tunanin hakan amma kasan me?, ya za'ayi su fahimceni?" Thabit yace "karka damu zasu fahimta"
Cikin ƙoƙari irin na Thabit ya fara ƙoƙarin gwada number Prime minister, abin mamaki shine oga Reed yace "Thabit ya akayi ka samu numbersa kai tsaye?" Thabit yayi murmishi gami da cewa, idan har kanason dukiya dole ka yi faɗi tashi gurin ganin ka cimma manufarka" Oga Reed ya jinjina kai tare da cewa, amma kana ganin Prime minister zai iya gyara komai?" Thabit yace "eh amma fa sai ka saki kuɗaɗe"
Iya Reed ya gyara zama kafin yace "indai kudi ne babu matsala nidai fatana komai ya tafi dai-dai kar a samu matsala".
Daga nan suka fara shirya yanda komai zai tafiyar musu dai-dai,
Agogon sanarwa ne ya buga daga ɓangaren hagu, Reed ya kai dubansa ga agogon kafin yai tsaki, tare da cewa "shagali za'ayi bana jin zan iya aiwatar da komai saboda wlhi ina cikin wani hali, bana jin daɗin yanayin da nake ciki a yau"
Ya kai ƙarshen maganar yana miƙewa tsaye kana ya fara zagaye ɗakin,
Thabit ya miƙe tsaye shima, kana ya tako har kusa dashi sannan ya dafa kafaɗarsa, cikin ƙarfafa masa guwaiwa yace "Oga Reed ka kwantar da hankalinka, waɗannan ƴan mata da ka tara, kamar inda kace idan an tashi siyar dasu akwai kuɗi sosai, bai kamata mu saka musu fargaba, ni Thabit zan jagiranci shagalin ina fatan zaka goyamin baya" oga Reed yayi murmishi kafin yace "gaskiya Thabit bani da kamarka, ina alfahari da kasancewar mu tare, fatan alheri abokina"
Thabit ya koma ya zauna tare da fara latsa wayarsa,
Acan ɓangaren su Misha, ita da Neria suna zaune a parlor ko waccensu da glass cup a hannunta table ɗin dake gabansu an jereshi da faifan wainar ƙwai da chips na dankali da Biryani, hankali kwance suke cin abincin, kasancewar lokacin bai wuce 7:pm ba, cikin yanayi na jin daɗi da annashuwa Misha tace "Neria ya kamata ki tashi mu shiga boutique mu zaɓi kayan da zamu sa, kinsan time yana tafiya fa"
Wacce Misha ta kira da Neria, wato ƙanwarta uwa ɗaya uba ɗaya da bata sani ba, tace "anty Misha Please muje ki zaba min" suka tashi kai tsaye suka wuce gurin zaɓar kaya, akwai wani tsari da gidan nasu yake da, duk wanda zai karɓi kaya sai an bashi wani kati, sai ya wuce gurin karbar kayan, kasancewar gurin akwai kasuwanni kuma duka domin waɗannan ƴan matan, sannan duk wani motsi na kowa yana tafin hannun OGA Reed, hakan yasa babu wanda yake yunkurin cutar dashi, CCTV tsaf zai nuno kowa.
Ƙarfe 8:pm ilahirin ƴan matan dake cikin wannan gida suka fito, ko wacce da kalar adon da tayi, amman duk cikinsu babu wacce ta sanya rigar da ta kawo mata gwaiwa, daga iya cinya ne, sai wacce da kaɗan ta wuce mazaunanta, cikin taku na isa da sarauta kai kace wani Sarki yake takowa, tun da ya fara idanun ƴan matan dake estate ɗin ya dawo kana Thabit dake takowa cikin hall ɗin, yana sanye da kaya irin na sarakai, tabbas duk wani mai fahimta ya fansa yasan shi ɗin musulmi ne, domin kuwa bai yi kama da kalar kafirai ba,
Yana tafe securities na biye dashi har ya ƙaraso cikin hall ɗin, aka fara yi masa tafi,
Kai tsaye ya wuce kyakkyawar kujerar da aka tanadar masa, bayan ya gama jawabai akan ko wacce budurwa tayi shagalinta iya son ranta babu mai takura musu, daga ƙarshe aka sake kida ko wacce ta tafi gurin shaye-shaye, wasu kuma suna can tare da samari ana holewa, Misha ce kwance saman ƙirjin wani saurayi, wanda shima yana ɗaya daga cikin mutanen gidan, ba wai iya mata suke ɗaukowa ba, harda maza, saboda su dinga taraiyya da matan, sosai.
Nocking aka farayi da ƙarfi, saurayin ya miƙe tare da cewa "Sir Thabit yana magana da Misha" da sauri ta miƙe a zabure tare da yayibar kayanta ta sanya, tana cewa "bansan laifin da na aikata ba, i know babban abokin OGA ne, ta mike tsaye tare da ɗaukar handbag ɗinta kana ta fice.
Sauri-sauri gudu-gudu takeyi har ta iso sashen da Thabit yake, nocking tayi jiki na karkarwa, "Yes come in" ya faɗa kana ya mayar da hankali kan wayarsa, jiki a sanyaye ta murɗa handle na ƙofar kana ta buɗe, tare da shigowa ta tsaya a bakin ƙofa, "Barka da dare" ta faɗa cikin harshensu, amsawa yayi da yauwa Barka, tare da ce mata ta ƙarasa, har yanzu jikinta bai daina ɓari ba, ta ƙaraso tare da tsugunawa, cikin girmamawa tace "gani" tashi ki zauna" ya mayar mata da maganar da turanci, ta tashi zaune har yanzu zuciyarta na ci gaba da tsinkewa, in Cold voice yace "kece Misha?"
Ta gyaɗa masa kai, ƙwarai ya lura da da yanayin rashin nutsuwar da take ciki, a hankali ya matso inda take kafin yace "yaushe rabonki da iyayenki?"
Sosai maganar ta juyar mata da ƙwaƙwalwa, saboda a iya tsawon zamanta a nan babu wanda ya taɓa yi mata wannan tambayar sai shi, bata da wannan amsar, sannan ko tayi yunkurin aikata wani abun sai taji rayuwar gurin yana sake shiga ranta, a hankali ya furta, "Rabonki da iyayenki tun ranar da mahaifiyarki ta haifeki, ke ba ƴar Nigeria bace, kana ke ba Christian bace, amman inason wannan maganar ta zamo sirri tsakanina dake, ni nan da kike gani hhhh, yayi dariya mai sauti...

KEFFI
Ikon Allah ne kawai ya kai Hajiya zaliha gidanta, saboda tsananin ɓacin ran da take ciki ko kaucewa gargada batayi, ko da ta iso bakin get na gidanta, wani mahaukacin horn ta yi, wanda yasa mai gadi buɗe get ɗin a tsorace, yana ganin Hajiyar ce ya ɗaga mata hannu, idanunta sun rufe ko ganinsa ma batayi ba.., ba a inda ake ajiye mota ta ajiye motar ta ba, tsabar zafin zuciya, tace "Hadiza yau kam naga tashin hankali, Hadiza ta hau tafa hannu gami da cewa "wlhi idan har baki tashi a tsaye ba, narantse miki da Allah indai miji ne kinaji kina gani zai fi ƙarfinki, yo ke a zamanin yanzu waye yake zama haka?" Hajiya Zaliha tace "hmm ke a tunaninki ban je gurin malamai bane? Wlhi cemin sukayi wai wannan auren baza a fasa shi ba, idan na dage zan iya mutuwa" Hadiza tayi tsaki kafin tace "kedai Hajiya Zaliha wlhi kin bani kunya, wato da ban shigo gidanki ba, bazaki gayamin an miki kishiya ba, Hajiya Zaliha tayi tagumi, gami da cewa "hmm abunne ya isheni shiyasa babu wanda na gaiyyata, "ga shi nan ai tana neman hallakaki, wlhi idan baki tashi tsaye ba, wannan tsinanniyar yarinyar sai ta ƙwace miki Alhaji, Hadiza tayi maganar cike da masifa,
Hajiya Zaliha tace "to yanzu meye abin yi?" Hadiza tace "abinyi karki damu na ɗauki nauyin komai da komai, kedai kawai ki amince dani" Hajiya Zaliha tace "ƙawata ai maganar amincewa ma ba sai kin tambayeni ba, saboda na daɗe da amincewa dake" nan dai suka fara tattauna ta ina zasu fara, Hadiza tace "tasha kuruminta ba sai ta biyota ba, insha Allah zata san inda zata yi akan Alhaji ya saki Saudart, suna tsaka da magana sai ga sallamar ƴarta auta wato Salma, tun daga corridor suke jiyo gunjin kuka, har ta ƙara so parlorn kuka take yi, cikin sarƙewar murya take cewa "Momy wato Dady ya ƙi ji sai da yayi aure nan?, Nan fa suka fitae koke-koke kai kace gidan mutuwa, Salma tace "wallahi momy nima ina cikin wata masifar, wai Imran na neman aure, har waya yakeyi da budurwarsa a gabansa, ke duniya maza basu da tabbas wallahi momy zan kashe aurena Gara in mutu ko in dawo gida da dai inga Imran ya ƙara aure wlhi, tai maganar tana sake fashewa da matsanancin kuka,
Hadiza tace "ƴata ki kwantar da hankalinki akwai mafita da izinin Ubangiji indai maganar aure ne, kamar an fasa shi, yanzu dai ki gayamin rabasu kikeso ayi kokuma kar ya sake marmarin ƙara kula ƴa mace a duniya?" Salma tace "anty Hadiza ko a lahira ma bana son ya kula ko wacce mace"
Anty Hadiza ta miƙe tsaye, tare da yiwa Hajiya Zaliha alkawarin raba auren Alhaji da Saudart, bayan tafiyar ta, Salma ta matso kusa da Hajiya Zaliha, ta sata a gaba tana rusa kuka, cikin jin haushin ƙara mata wata damuwar da tayi tace "Salma ki gode wa Allah ma bai yi auren ba, ni da dadynku yai auren fa, karki manta ƴar cikinsa ya aure, wacce bata wuce sa'arki ba"
Hajiya Zaliha tasa kuka itama.
Ko gida Anty Hadiza bata wuce ba, kai tsaye ta wuce gurin bokanta, bayan sun gaisa tace masa, akwai wani ana ce masa Alhaji Salisu Alherin Allah yayi sabon aure, sunan amaryar Saudart, tanason a raba auren har abada, sannan akwai wata ita kuma sunanta Salma mijinta yana neman auren ƴarta Hindu, tana son duk gurin malaman duniyar da zasuje kar suyi galaba akan hana auren, saboda Hindu tana son Imran sosai, boka ya ake ciki?" boka ya yi wasu surutai kana ya kwashe da dariya, kafin yace "akan maganar shi wannan Alhjin zanyi iya bakin ƙoƙarina gurin ganin an ruguza musu farinciki, sannan ita kuma Hindu ai wannan auren babu fashi, sai dai zata fuskanci ƙalu bale daga gurin Salma" anty Hadiza tace
End Ads