x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - NA KASA JUREWA book 1

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 86738 words

Category: Love Stories

Views 139

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ƙarshe ta jingina kanta a jikin bango sbda barci ya ƙauracewa idanunta,
Tana sanye da hijab har ƙasa ta fito parlo ta zauna, remote ta ɗauka sannan ta kunna TV ta nemi guri ta zauna a 3sitter ji tayi kallon ma babu wani daɗi ta kashe TV tare da ɗaukar ɗan ƙaramin pillow ta rungume a ƙirjinta, tayi nisa a tunani batayi aune ba taji an watsa mata ruwan sanyi, da sauri ta mike tsaye jikinta na karkarwa bakinta na ɓari tace "yah..ma..ma" ragowar maganar ta sarƙe mata a maƙoshi, kallon ƙasa kan tayis tayi taga gudajin ƙanƙara, sosai jikinta ke rawa ga wani azababben sanyi da takeji, sbda ruwan da ya zuba mata ba ɗan kadan bane,
"Ƙin ɗauka zaki dawo kici gaba da rayuwa kamar da ne? tambayarki nakeyi?"
"Jikinta na cigaba da karkarwa tace "ka...ka...ka...."
Cikin daka tsawa yace,
"Shot up your mouth idiot"
Waro dara daran idanunta tayi, tare da janye jikinta daga gurin tunda ko tayi masa magana ba saurararta zeyi ba, "dawo nace..!!"
Da baya da baya ta, dinga takowa har zuwa inda yake, batace masa ƙala ba itadai tana tsaye.
"Ungo cire wannan munafukin hijabin naki ki sanya waɗannan kayan yanzu a gabana"
"Yah Ma'aruf bazan iya ba, sunyi nuna tsaraici da yawa"
Ta faɗa tana dafe hannayenta a ƙirji sbda har yanzu sanyi takeji,
"Munafuka ni zaki gayawa sunyi tsaraici, ba cikin dare kike ficewa a gidan nan kike zuwa yawon nuna tsaraici ba?!!,
Waro dara daran idanunta tayi kafin tace "wallahi tallahi bayan mahaifiyata da ta raineni tun ina ƙarama babu wanda ya taɓa ganin tsaraici na, sai..."
"Sai kuma me? wallahi tallahi idan kika bari na sake magana sai na zaneki munafuka kawai"
Yai maganar yana zaro belt ɗin wandonsa.
"Sai kai"
"Kutumar uba"
Ya faɗa yayin da ya fara lafta mata belt ɗin wandonsa,
Ihu take na neman agaji, anyi rashin sa'a babu wanda yaji bare yasan tanayi, sai da ya tabbatar da ta daku, ta kusa fita a haiyyacinta kafin ya ƙyaleta, ya shiga toilet na bedroom ɗinsa yai wanka bayan ya fito ya gyara jikinsa ya ciro ƙananan kaya blue jeans da t-shirt light blue mai gajeren hannu wace ta daɗa fito da ainihin kyawunsa, sai da ya gyare sumar kansa kafin ya feshe jikinsa da turaruka masu sanyin ƙamshi kana ya fito parlo.
Inda ya barta anan ya sameta tanata rusa kuka, tsaki yaja "mtsw" kafin ya fice.
Da rarrafe ta ƙarisa ɗaki sbda sam komai ya sauya mata, tashi ɗaya jikinta yayi tsami sosai,
Babbar damuwarta idan har tace zata gayawa momy sai sun sami matsala da Dady inba sa'a ba ma yai sanadiyar igiyar aurenta, ta girgiza kai tana faɗin "Noo, zan yanke shawara da kaina"
A take ta yanke shawarar inasha Allah idan gari ya waye zata gudu Kano gurin dangin Dady, dan bazataje dangin momy ba.
A ranar dai tasha bakar azaba, gashi tanaji tana gani akayi ta nocking ƙofar parlon takasa miƙewa taje ta buɗe haka ta mayar da kanta ta kwanta.
Babu abinda ta sa a bakinta, dan ko yunwar ma bataji, sai ma barcin wahala da ya ɗauketa, kamar koda yaushe yauma mafarkin matarnan tayi, a firgice ta tashi, dudu du ma barcin ba wani mai yawa tayi ba,
Ta duba agogo ƙarfe 12:pm 10 miss call ta gani a wayar tata tai saurin duba wanda yayi mata, innalillahi ta ambata tare da waro idanu, Hajiya mama Anty Jamila ta faɗa a fili, gashi wayarta babu ko sisi, kuma batada ko biyar a account,
"To shikenan sai inta kai musu ƙorafi?, ai gara nima wannan karon in nemawa kaina ƴanci"
Ta faɗa tana rarrafawa ta buɗe drowa gurin kayan ta, sai yanzu ma ta tuna ai akwatin kayanta yana mota, wasu ta ɗiba kamar kala goma kana ta sanya cikin jaka ta zuge jakar, cije lip ɗin tayi tare da sake fashewa da kuka, "shikenan bani da gata babu me sona na *KASA JUREWA* wayo Allah na, tawa ƙaddarar kenan" ta faɗa yayinda ta sake fashewa da marayan kuka.

Tunani ta farayi, "bata da kuɗi ta ya za'ayi ma tafiyar tayiwu?"
Number Anam ta yiwa mtn beep, kana ta mayar da wayar ta ajiye.
Har aka kira sallahar azhar bataji jikinta ya sake ba, daƙyar ta miƙe tana tafe tana dafa bango ta shiga toilet ta haɗa ruwa mai zafi ta shiga ciki a bathroom kana tayi wanka daga ƙarshe, sosai taji daɗin jikinta, ta fito ɗaure da towel, tofa, yanzu ne ta fara dawowa haiyyacinta sbda yunwar dake ƙwaƙularta, cikin ƙwarin gwaiwa ta wuce kitchen, murɗa handle ɗin ƙofar da zatayi taji a kulle da key, jingina tayi da jikin bango tare da sauke ajiyar zuciya mai nauyi,
Sosai da takejin yunwa, i zuwa lokacin sallahar la'asar yunwa ta fara galabaitar da ita, dan a zaune tayi sallah, tunaninta shine da yaushe Ma'aruf ya shigo gidan bataji alamunsa ba, ko lokacin da tayi barci?",
Ta tambayi kanta.
har aka kira sallahar magriba tayi tana zaune aka kira isha'i, ta rasa me keyi mata daɗi gashi har yanzu Anam bata kira ba,
Data ta kunna kasancewar tana da, ta duba Anam ɗin ko tana online, cikin sa'a ta samu Anam ɗin a online, tai saurin yin mata sallama, Anam ta amsa tare da cewa "Anty Saudart kin koma gida lafiya?" Rubuta mata, "lpy Lou har Kun tafi ne? na nayita yi miki mtn beep baki biyo kiran ba"
Eh wallahi ai na sauya simcard, ya dai mutumin naki?"
"Hm Anam nidai wata alfarma nake nema a gurinki, banaso kowa ya sani Please ya zamo sirri daga ni se ke, Saudart ta faɗa tana sheshekar kuka, a voice.
"Ina jinki Anty Saudart duk maganar da muke yi dake ta sirri ai ban taɓa faɗawa kowa ba"
"Shikenan"
Saudart ta faɗa, yayinda take sauke ajiyar zuciya.
"Please Anam ki turomin da 50k yanzu gobe zanyi tafiya zanbar gidannan saboda wallahi ina cikin matsanancin hali"
"Ba sai kin haɗani da Allah ba Anty Saudart barin turo miki, a wane bank?"
"First bank ai kinada"
"Eh barin tura miki"
Ko 30mints ba'ayi ba sai ga alert na 70k Kasancewar any months Dady yana tura mata da kuɗi, ada yana turawa Saudart, daga baya yace mijinta ai shima mai hali ne, yana iya yi mata abinda yafi haka"
Hamdala tayi sai ma taji yunwar da takeji ya ragu, tunani ta farayi to wa zata aika ya siyo mata abinci?"
Yanzu ba kamar ɗazu ba ta ɗanji daɗin jikinta, ta fito parlo sanye da ƙaton hijabi, ta murɗa handle na ƙofar taji a kulle, a fili ta furta "kodai Ma'aruf yana son kasheni ne?"
Tun jiya da yabar gidansu bai koma ba, sannan ya juya sim ɗinsa dan karsu kirashi, yana zaune a office sanye shadda mai ruwan ƙasa, tayi masa kyau sosai, idanunsa na nanne cikin baƙin gilashi, sai juyi yake a kan kujera,
Idanunsa a lumshe suke, duk da tulin file ɗin dake gabansa bai hanashi jin fargaba ko wani abu ba, nocking akayi yanaji yayi burus becewa me ƙwanƙwasawar ya shigo ba, sai da akayi sau uku kafin yace "Yes come in"
Tunda ya buɗe ƙofa ya hango mutumin nasa yasan yau yanajin rashin mutunci, sbda ba lallai su kwashe ta daɗi ba...!

More comment more typing
08141799224 WhatsApp only

Share fisabilillah inci arziƙin Manzon 👏


Mom Islam ce....
[7/12, 2:33 PM] Mom Islam: *NAKASA JUREWA*
🪻🪻🪻


Mom Islam


Domin samun more pages kuyi following ɗina a Arewabook danna blue link👇
https://arewabooks.com/u/momislam11


Ga wanda basa Arewabook ga link na Wattpad hilis ayi following ɗina 👇
https://www.wattpad.com/user/Momislam2021?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends





Page 5-6

"Kai abokina kana cin duniya fa, kaga inda ka sake yin fresh kayi kyau, gaskiya amaryarmu ta iya kula da miji Masha Allah, ai da naso ma in..."
Muhammad ya faɗa yana dafa kafar Ma'aruf.
"Kai dalla kauce ka bani guri, uban me ya kawo ka office ɗina?"
"Nazo inji ya aka kashe boss ne a daren jiya"
"Mtsw tashi ka fitar min wallahi zan ci ubanka"
Dariya Muhammad yakeyi son ransa, dan ya lura abokin nasa yau a up yake,
Ganin baya son wasan ya nemi guri ya zauna har yanzu fuskar Ma'aruf ɗin a murtuke take, yace "abokina Hajiya ce ta aikoni wai idan ka tashi a office tana nemanka",
"Naji"
Ma'aruf ya faɗa a taƙaice.
Koda Muhammad ya gama zamansa ya miƙe tare da yi masa sallama, bai samu albarkacin amsa wa ba ya fice, tunda ya isar da saƙon da mahaifiyarsa ta bashi.
Wani ƙululun bakin ciki yaji ya turnuƙe shi, kasancewar shiɗin ɗan duniya ne ya basar tare da duba time 5:20pm ya rufe takardun da ya buɗe dan yau be taɓuka komai ba, ya rasa nutsuwarsa, kai tsaye hanyar gidansu ya nufa, sai da ya biya gurin mai siyarda banƙararriyar kaza ya siyo guda huɗu, na Hajiya ɗaya na Anty Jamila ɗaya, sai nashi ɗaya ɗayar kuma 🤔ina tunanin na Saudart ne uhm.
Horn yayi aka buɗe masa get, ya kutsa hancin motarsa ciki a parking space ya ajiye motar tare da fito da ledojin, kana ya shiga ciki,
Da sallama ya shiga babban parlon nasu tare da ƙwalawa Hajiya kira saboda bata parlo, babu kowa sai ƙarar TV,
Daga bedroom ɗinta ta jiyo muryarsa, da sauri ta fito tana washe haƙora, tana cewa "ɗan albarka, inata cigiyarka, naso in shigo gidan naku sai nayi baƙi"
"Hajiya ai dama inada niyar shigowa, sai ga Muhammad ya biyoni har office"
Ma'aruf ya faɗa yana ajiye wa Hajiya mama leda biyu,
Cikin farinciki ta ɗauko ledar tana cewa "amma dai Saudart na nan lafiya ko?"
"Eh Hajiya, tace ma a gaishe ki, da zamu shigo tare, sai kuma na shigo kafin in shiga gida"
A wannan karon hankalin Hajiya mama ya kwanta sosai, dan a iya tunaninta Ma'aruf ya sauka kama inda zuciyarta ta labarta mata,
Nan sukaci gaba da fira kamar babu wata damuwar da ta gifta a tsakaninsu,
Anan gidan hajiyar yai magriba yai isha'i, a takaice ma anan yaci abincin dare.
Ƙarfe 9:pm ya miƙe yana danna wayarsa, "Hajiya banga Anty Jamila ba ina ta shiga ne?"
"Ai ba kwanan gidannan ba yau kam, taje ƙauye"
"Ƙauye??"
Ya maimaita, "eh mana, nasan kai baka son zumunci shiyasa kake ƙyamatarsu, duk ɗan halak baya ƙin asalinsa, komai daren daɗewa dole kaje ka dubosu"
Kawar da kai yayi, tare da cewa "Hajiya sai da safe"
"Allah ya bamu alheri"
Hajiya ta faɗa, ta yago jinyar kaza, tare da binsa da murmishi.
"Allah ya tsallakar dani wannan case ɗin"
Ma'aruf ya faɗa time ɗin da yake ƙoƙarin shiga mota.
Kai tsaye ya wuce gidansa,
Bayan an buɗe masa get yayi parking motarsa,
Ya fito da ledojin tare da jakar aikinsa kana ya wuce ciki,
A parlo ya sameta tana zaune saman Capet hannunta rike da gorar hollandia yoghurt, gefe kuma tsire ne ta baje tana ci,
Sosai yayi mamakin, ya akayi ta samu arzikin cin waɗannan kayayyakin, koda yake bai kamata yayiwa kansa wannan tambayar ba,
"Amma waye ya siyo mata?"
Shine tambayar da yake yiwa kansa,
Niko nace horo da yunwa?
A zahiri taji shigowarsa, sbda ko sallama beyi ba, a matsayinsa na cikakken musulmi, ƙin ɗago kanta tayi bare ta nuna masa tasan da shigowarsa, dogon tsaki yaja "mtswww" tare da take mata ƙafa, har sai da ta ƙwalara ƴar ƙara, cikin jin tsananin azaba tace "sai Allah ya sakamin"
Har ya wuce ya dawo da baya, kana ya bige mata baki ya wuce.
Hannu ta ɗora a saman lips ɗinta cikin jin zafi ta runtse idanunta.
*****
ƘAUYEN ƊAN ƁAURE
Tuntsurewa tayi da dariya lokacin da take gwaguyar goruba, kafin ta kalli ƙawarta Gudidi tace "yasin raken Iliya kamar an zambaɗa madara da suga, wai kinhya kinji kuwa?"
"A'a Talatu ɗan hammin mana"
"Alƙur'an se kinyi min alƙawari"
Talatu ta faɗa tana ƙwalalo idanu.
Talatu ta sake cewa "kasuwa yau bana son Inna ta sani, idan na hammiki rakena kina faɗa wa Inna ga inda naje, wallahi tallahi sai nayi ƙulikulin kubura dake"
Talatu ta ƙarashe maganar tana murguɗa baki,
"Zaro ido waje Gudidi tayi, kafin ta haɗiyi wani miyau maƙwat, kana tace "yo ni hauka nakeyi Talatu? wallahi ko haurawa ta katanga kikayi bakina ƙanin ƙafata, amma dai hammin raken sbda miyau ɗina ya tsinke"
Talatu ta washe haƙora gami da cewa "ahe dai kina sona"
Gudidi tace "sosai ma"
Kafin ta gutsiro mata raken sai da ta gama wanke shi da miyau kafin ta miƙa mata, Gudidi na ƙarɓa ta ruga da gudu tana cewa "wallahi sena faɗa me warin baki kawai, da hakori kamar na kaza"
Sosai Talatu ta tunzura domin tabi Gudidi da uban gudu, cewa takeyi "tsohuwar munafuka zoki biyani raken da na baki, yau ko zaki hige cikin Ramma sai na ƙwaƙuloki"
Karaf sai a kunnen Ramma, mahaifiyar Gudidi, "ke Talatu uwa naji kamar zagina kikeyi?"
Ramma tai maganar tana yiwa Talatu daƙuwa,
Murguɗa mata baki Talatu tayi kafin tace "ki gayawa Gudidi ta biyani rakena"
"Dalla can tafi kiba mutane guri, lokacin da kika bata raken kin nuna min?"
Talatu ta wani murtuke fuska tare da riƙe ƙugu tace "kunci bahi, daga ke har ƴar taki"
Ta faɗa tana ficewa daga gidan.
Tunda Gudidi ta tabbatar da Talatu ta shigo gidansu take ta leƙe ta windo ga wata uwar zufa dake ta tsatsa tsafo mata,
"Ramma wallahi kibi Talatu a hankali ko kin mance wacece ita?"
Ramma ta wani mulmulo uwar ashar ta yiwa Gudidi gami da cewa "idan na sake ganinki tare da wannan yarinyar wallahi sai na lahira ya fiki jin daɗi"
"Toh" kawai Gudidi tace tana cino baki.
Tunda Talatu ta fice daga gidansu ta wuce can gonar baban Gudidi, mijin Ramma kenan,
Daga nesa ta hango shi, ya haɗa zufa sosai yasha aiki, sai da tayi nazarin kalaman da zata gaya masa, kafin ta ƙarasa gurinsa, har ƙasa ta durƙusa tace "ina kwana baba" lafiya lau ƴar albarka ya Innar taki?"
"Tana lafiya lau baba"
Gudidi ta faɗa tana sunkuyar da kai.
"Baba dama nazo in sanar dakai wani abu, amma kayi haƙuri baba"
Talatu ta faɗa tana wasa da sanda wace ta tsinta a inda take tsugune,
"Ina jinki ƴata gayamin koma menene, domin na yaba da hankalinki"
Talatu tace "baba dama kullum idan zamuje kai niƙan tuwo injin me Kano, kullum sai Gudidi ta tafi da leda ta rage gari, da na tambayeta sai tace wai Ramma ce tace mata ta dinga yin haka, tunda wai kana barinsu da yunwa sai kaje can waje kaci abincinka me rai da lafiya"
Koda takai ƙarshen maganar ta miƙe tsaye tare da cewa "amma dan Allah karka ce nice na faɗa maka, saboda gudidi ma taso gaya maka Ramma ta kamata tayi mata duka"
Jikin baba na rawa yace "yarinya Nagode, badan kinzo kin gayamin ba wlhi babu inda za'ayi in sani, ungo wannan kyasha alewa"
Ta durƙusa ta karɓi kuɗin tanayi masa godiya.
Har tayi nisa da hanyar gonar, bata duba ko nawa ya bata ba, sai da ta kusa da ƙofar zuwa gidansu kafin ta duba kuɗin, nera Hamsin ce,
Sosai tayi murna, tana ta taka rawa, tana cewa "idan rabonka ya rantse, kai kai kai idan rabonka ya rantse, ɗin ɗirin ɗin"
Ta ƙulle hamsin ɗin a hannun zani kana ta shige gidansu da gudu.
A tsakar gida ta samu Inna ta raba dambu, kasancewar shi suka girka, "wayo daɗi kaheni wuya barni" Talatu ta faɗa tana cigaba da taka rawa,
Kasancewar tsakar gidan nasu yanada tsaki, ita kuma Talatu tana can nesa, Inna tace "Talatu ina kikaje nasa a dubomin ke kizo ki ɗauki allo ki wuce islamiyya ba'a ganki ba"
Tofa.
Daga can inda take ta buga tsalle ta faɗi tik a ƙasa, ko gezau tunda dama ta riga ta saba, kurma ihu tayi tana cewa "wayyo na mutu na lalace wayyo na balaga ayimin aure wayyo Inna bata sona"
Inna na zuba yaji bata san lokacin da taketa zubawa a ƙasa ba, dan a iya tunaninta a abinci take zubawa,
Mamaki suruntun Talatu ya bata ko da yake ma, ai ba yau ne farau ba, inda sabo ma ai yaci ace ta saba,
Da gudu ta bita tana cewa "wallahi sai kinje makaranta, idan kika zauna a gida me zaki tsinana banda yawo a gari?"
A zauren gidan ta laɓe tanajin maganar da Inna takeyi, tana murguɗa baki.
Tana ganin Inna ta gama rabon damu ta wuce ɗauki, ta siɗaɗo a hankali taje ta ɗauki nata, ta nemi guri ta raɓe ta fara ci, duk wanda ya shigo ya ganta ze ce marai niya ce.
Ashe har tafiyar da takeyi a hankali da zuwanta ɗaukar abinci duk Inna ta gani, sai da ta bari tayi nisa sosai kafin ta leƙo, hannunta rike da bulalar inji ta riƙeta gam, tare da haɗe mata hannaye, cikin kururuwa take cewa "Inna kiwa Allah da ma'aikinsa ki yi hakuri Inna ki duba darajar Musa me jaki da tantabaru, Inna ki duba darajar Hama me tuyar ƙosai, kasaƙe Inna tayi tana jinta, abin ya matuƙar bata mamaki, sai haɗata da sana'ar iyayenta da basa raye take yi,
"Na duba darajarsu, amma ki tahi ki wuce makarantar Allo"
"Inna nifa malamin ne sai ya dinga ɗagamin gira, ɗan iska ne yasin"
Talatu ta faɗa tana buga ƙafa.
"La hula wala ƙuwwata illa billah ni Zainabu naga abinda ya isheni"
Inna ta faɗa tana riƙe haɓa,
"To tashi in rakaki yanzu"
Babu inda ya iya dole ta tashi ta ɗauko hijabinta, sbda basa wani rayuwa da hijabi, idan aika yayi nisa haka suke tafiya, koda yaushe rayuwarsu ta sanya riga da ban zani da ban ne.
Suna isowa makarantar, Talatu ta zame hannunta a na Inna, a hankali tace "Inna duk maganar da na gaya miki akan malaminnan ƙarya ne wallahi, dan Allah ki koma tun daga nan karki kaini gurin hi, gardawa zesa su ɗagani ya zaneni.
"To naji, amma tsan tsaya anan har sai naga higarki"
Inna ta faɗa tana yi mata nuni da yatsa,
"Wace ni Inna zan higa fa dan Allah ki koma kar malam yace "nayi taurin kai ne kikai min raki ya"
Sam bata son a daki Talatu, hakan yasa ta juya tana murmishi.
A gindin bishiyar mangoro suke yin karatu, inda suke shimfiɗa tampol a gurin, maza na can gefe mata ma suna gefe,
Kusa da gudidi taje ta zauna, cikin ƙasa da murya tace "idan kere na yawo zabo na yawo wata rana za'a gamu, wa na kama?"
Gudidi tayi wulli wulli da idanu, cikin marairaice murya gudidi tace "dan
End Ads