x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 15 - NA KASA JUREWA book 1

  • 42001 words
  • 45000 words
  • Out of 86738 words

Category: Love Stories

Views 134

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
da tayi har wannan lamari ya faru, miƙewa tsaye tayi tana mutsike idanunta masifar kishi na cinta, tace "wayo Allah, ta dafe dai dai saitin da zuciyarta ke bugawa,
Itako Hadiza barci takeyi harda munshari, Hajiya Zaliha ta fara zagaye ɗakin tana neman mafita,
Bazata iya bari gari ya waye ba, bata ɗauki mataki ba, tayi tunani iri iri, daga ƙarshe dai ta buɗe ƙofa ta fito harabar gidan tana sake ƙare masa kallo, gingina kai takeyi tana taɓe baki gami da yin tsaki mtswww, takai kusan 30mints barci ya ƙauracewa idonta tsabar zafin kishi.
Har yanzu dai ta kasa haƙura gari ya waye ta sake zuwa gurin ƙofar ta bubbuga kamar zata ɓalle door ɗin, a firgice Saudart ta buɗe ido, ta fara ƙoƙarin tashi zaune, kallon hannun Alhjin da ya rungumeta sosai tayi, a hankali ta zame daga jikinta tare da saukowa daga saman bed ɗin ta tsaya cak a tsakiyar ɗaki, zuciyarta ta rabu gida biyu, shin taje ta buɗe ƙofar taga waye yake nocking kokuma ta tashi alhaji?, "Ina!!" Ta faɗa a fili a hankali ta juya key ɗin ƙofar dan batayi tunanin komai ba, kofar ta buɗe....
SINGAPORE
Buland island
Tun tafiyar Anam da sukayi da Dady, aka juyar mata da hankali, ta koma sai inda akayi da ita, duk da sanin Dady, wannan abin ya faru.
A estate ɗin su, A ranar da aka kawo Anam aka sauya mata suna zuwa Neria, ita kuma Hussaina sunanta Misha, ikon Allah kenan, lokaci ɗaya jininsu ya haɗu, sosai Misha ta ja Anam a jiki kasancewar ta shiga ranta, gata yarinya ƙarama a shekaru bata wuce 16yrs ba, duk da ƙarancin shekarunta sai da suka san inda suka sa ta fara tarbiyya da maza Christian ƴan uwanta, tunda yanzu ta fita a musulunci, tun tana jin kunya tana ɓoyewa har ya zamo ta zamo ƴar gari, amma sai dai duk wanda zasuyi taraiya dashi sai anyi taste an tabbatar da lafiyarsa kana kuma ya sauke maƙudan kuɗaɗe, yau ma kamar koda yaushe, suna zaune a ɗakinsu, kasancewar Misha tace Anan ɗin ta kwaso kayanta, ta dawo ɗakinta, bayan sun gama tsara kwalliya aka fara koyar da ita sanya kaya matsatstsu kuma iya cinya, da yawo babu ɗankwali, dole takeyi dan bata iya yin musu sai dai wani abun a ƙasa ranta tana jin zafinsa amma bazata iya furtawa ba,
A yau ne oga ya shirya babban taro wanda ya kasance jimami ga dukkan ƴan matan dake cikin estate ɗina, abinda ke faruwa shine, haka kawai aka ga uwar ɗakin nasu ta faɗi ta mutu babu wanda yasan abinda ya faru da ita, a ranar ansha giya kamar ba gobe, wasu alamomin sukanyi nuni da kamar ogan yanada masaniya akan mutuwarta.
Bayan sati ɗaya da mutuwarta ya shirya babban taro a hall ɗinsa dake nan Buland island, babban Hall ne, wanda ya amsa sunansa, ko wacce budurwa an jere mata drinks da snacks da giya da sauran kayan shaye-shaye, bayan ya buɗe taro da yaba musu da yayi kana ya fara gabatar da dalilinsa na haɗa wannan taro,
"Mun samu canji sosai, bazance mutuwar uwar ɗakinku alheri bace a gareni, haƙiƙa naji mutuwarta, kuyi hakuri zaku sameni mai baku duk abinda kukeso a faɗin duniya, Abu na farko da nakeson sanar daku shine, akwai wani cigaba da na hango mana, wanda kuma zaku sake samun canji duk da nasan a cikinku babu wacce zata ce ta buƙaci wani abu bata samu ba, na farko dai shine..
"Inason ko wacce budurwa a cikinku idan ƙarshen wata yayi kokuma in ce lokacin da ta fara period ta kawomin pad ɗinta na adadin kwanakin da takeyi, akwai wani magani da za'ayi na rigakafi" ya kai ƙarshen maganar yana tuntsurewa da dariya, ragowar abokan aikin nasa ma dariyar sukeyi, yayinda suma ƴan matan suke dariya gami da yin tafi,
Sosai taron yayi masa daɗi, hakan ya sake tabbatar masa da cewer, aikin bokansa yana tafiya inda ya kamata,
Bayan nan yace "yau a club ɗinsa akwai shagali na musamman"
Suka sake yin tafi raf...raff..,
Daga nan ya rufe taro da yi musu faɗa akan duk wani abu da suka rasa su gaya masa,
Duka suka cewa "toh"
Daga nan taro ya watse kowa ya nufi sashensa,
Bayan Oga ya dawo gida, ya tuntsure da dariya, babban dalilin da yasa ya kashe uwar ɗakin nasu shine, sam bata goya masa baya a wasu abubuwan nasa, to meye amfanin zamanta a duniya tunda har bazata bari su haɗa kai su yi kuɗi na ban mamaki ba.
Washe gari.
Akwai wani babban kamfani da yake dashi wanda suke safarar haramtattun magunguna wanda suke ƙirƙira sannan suyi rubutu da sunan wata ƙungiya, sau biyu ana yi masa worning amma yaƙi fahimta, cikin basaja mutanensa suke kai magunguna tare da nuna shaidar amincewar gwamnati, hakan yasa masu asibitin basu da tabbacin banbance marar kyau da mai kyau,
Safiyar yau Monday an tsananta bincike game da masu aikata laifin,
Oga Reed na zaune saman tsafaffiyar kujerarsa, ɗaya daga cikin securities ɗinsa yayi masa magana, da cewar yayi baƙo da alama akwai alƙairi game da zuwan bakon, Cikin amincewar Reed aka shigo da baƙon, fari ne tass Balarabe ɗan ƙasar Saudiyya, abinda ya bawa Reed mamaki bai wuce, ya akayi wannan Balaraben ya san da zamansa har ya kawo masa ziyara?" ba yanzu zai buƙaci wannan amsar ba,
Tabbas idan har mutumin bai zo da wata ƙullalliya ba, zai yi musu amfani, idan kuma ya kasance mai kishin musulunci ne yazo leƙen asiri ne,
Reed yayiwa baƙon nasa umarni yace "inayi maka maraba, da Yaren su, kasancewar Balaraben yana ji, ya amsa da yauwa tare da miƙawa Reed hannu cikin muryarsa mai daɗin amo yace "sunana Thabit ina fatan zamu zamo abokai"
Reed ma ya miƙa masa hannu kana ya kasa ɓoye mamakinsa yace "amma mai ya baka sha'awar siyarda ranka har kazo inda nake kai tsaye ba tare da kayiwa zuciyarka shawarar ka ci gaba da rayuwa a duniya ba?" Thabit yai ɗan gajeren murmishi, kafin yace "wato Reed idan har mutum yana neman hanyar da zai zamo wani abin kwatance a duniya ba sai ya tsaya jin tsoro ko makamancin haka ba, kawai kai tsaye zai miƙo buƙatunsa idan anyi na'am dasu to, idan kuma rai yayi halinsa duk ɗaya"
Sosai maganar Thabit ta shigi zuciyar Reed lokaci ɗaya yaji ya fara amincewa dashi, sai dai ya yi umarni da a kawo masa wata kujera Thabit ya zauna a kai, kujerar itama tsafaffiya ce sosai, wadda take auna abinda ke zuciyar mutum na alkairi ko na sharri, koda aka Thabit ya zauna a wannan kujera sam bata bada wata matsala ba, hasali ma tayi nuni da gyara tare da ci gaba zai kawowa Foundation ɗinsu" dama Reed ya daɗe yana jiran wannan rana, ranar da zai samu mutumin da zuciyarsu zatazo iri ɗaya, tabbas ranar yau ta zamo ranar shagali a gareshi, ranar yau ta zame masa haske, ya mikawa Thabit hannu suka tafa tare da rungume juna,
Tun a daren suka fara gabatar da aiki gadan gadan babu wasa...

ƘAUYE
A ranar da gudidi ta koma ta dinga ihu tana birgima a ƙasa, sam bata ƙaunar sake rayuwa a cikin ƙauyen, koda mahaifiyarta Ramma tayi mata tsawa, itama tsawar ta daga mata tare da cewa "yasin wannan baƙinciki ne, ina cikin ni'imar Ubangiji kin wani dawo dani nan, a aljanna ta ɗaya muke, ramma tace "kiyi hakuri Gudidi gonar rogo na siya nasa aka haƙomin kaɗan daga ciki nakeson in fara siyarwa ko Allah zai taimake mu, Gudidi ta kwaɓe fuska kafin tace "yasin hedai ki nemi wanda zeyi miki talla naje binni nahya ruwan garɗi kuma yanzu kice wani talla yasin bazanyi ba, bari ma kiga in samu kuɗi Wlhi binni zan koma zaman ƙauye ai sai wanda yayi niyya, tunda ba anan aka binne cibiyar mutum ba, tai maganar tana taɓe baki.
Ramma ta zaro idanu tana dafe ƙirji kafin tace "Wlhi idan hakane zaman binni bai tsinana miki komai ba, kwata-kwata kwanan ki ɗaya kika dawo, amma duk kinbi kin fetsare, to Wlhi tallar rogo babu fahi sai kinyi kinji na gaya miji" Ramma tai maganar tana nunata da yatsanta, kuka sosai takeyi tana ta shure-shure,

Washe gari, samarin ƙauyen suka dinga shigo da rogo a buhu, bayan sun gama kawowa, Ramma ta haɗa wutar kara ta dafa rogo ta saka a farar ledar buhun suga, ta zuba ƙuliƙuli dakakke wanda aka zabga masa farin maggi da gishiri,
"Gudidi kizo ki higa wanka ni na kammala nawa aikin ke nake jira, abin mamaki ko musu batayi ba, ta tashi ta shiga wanka, tana fitowa ta tsantsara kwalliyar hauka, janbaki har a saman gira, harda wani wai hawayen masoyi, ta zabga farin janbaki abin dai sai wanda ya gani.

Wasu daga cikin kayan da Hajiya mama ta bata, ta ɗauki atamfa ɗinkin buba ta saka, Wow Masha Allah tayi kyau sosai, Masha Allah,
Bayan ta gama sanya kayan ta ɗauko wani baƙin mayafi duk ya tattare ta ɗaureshi a ƙugu, kana ta ɗauki tiren tana cewa "na tafi" Ramma dake ɗakin girki ta fito da gudu tana cewa "Gudidi bakici komai ba" Gudidi tace "na nawa zanci?" Ramma tace "na Ahirin" babu musu Gudidi ta wuce, mamanta nayi mata Allah ya tsare...!

Idan kinason shiga group wanda nake posting kimin magana ta WhatsApp 08141799224
*NA KASA JUREWA*
💋💋💋
💋💋
💋
Mom Islam


Page 47-48
Tun a hanya ta fara ciniki, kafin takai ga gurin da take zama har rogon ya ƙare, sai dai anyi ba ayi ba, wai matar bakanike ta haifi sifana,

Da sallama ta shiga gidan murya a sanyaye tace "Ramma na dawo, jin Muryar Gudidi yasa Ramma fitowa da sauri daga ɗakinta, fuskarta ɗauke da murmushi tace "hannu da dawowa Gudidi mai kasuwa da sunan Allah, ajiye tiran ki higa ɗaki ki ɗauko fura da nono ɗazu yaro ya kawo talla na siya miki.."
Duk da tsananin fargabar da take ciki bai hanata zuwa ɗakin Ramma ba, taje ta iske fura da nono mai sanyi, sai da ta cika cikinta kana ta fito tana goge baki,
Bayan ta dawo gurin Ramma ta kunce ɗamarar da tayi, kana ta durƙusa har ƙasa, idanunta cike da hawaye tace "dan Allah dan Annabi Ramma ki dubi sallahar iyayenki ki yafemin"
Ramma ta tsorata sosai dan ita bata san dalilin neman yafiyar ba, "tashi ki zauna kiyimin bayani inda zan fahimta"
Ramma tayi maganar tana kallon Gudidi, da har yanzu kuka takeyi,
Sosai sautin kukan gudidin ya cika mata kunne, ta daka mata tsawa saboda haushin da ta bata, kafin tace "wallashi ko kiyi magana ko in zaneki da tsumagiya, jin haka yasa Gudidi share hawaye tare da zuƙo majina ta shanye🤣 kafin tace "Ramma Wlhi na yi ciniki sosai, na kamo hanyar dawowa gida, na nemi kuɗin na rasa"
Da sauri Ramma ta tashi tsaye tana dafe ƙirji kana tace "Na higa uku Gudidi kin cuceni, Wlhi da ki yimin wannan ɓarnar ai gara ki gaura min mari"
Ramma ta wani rarumo ƙatuwar sanda tare da cewa "gara in karyaki Hegiya kawai, kuma wallashi kije duk inda kuɗi yake ki nemo min kuɗina dan wallhi bazan ɗauki asara ba, saboda suma masu rogon ba yafemin zasuyi ba" ta ƙare maganar tana bin gudidi da gudu ko mayafi babu a jikinta, cikin ɗaga murya Gudidi take cewa "dan Allah Ramma kiyi hakuri Wlhi tallahi ban gansu ba, ni ban ci miki kuɗi ba"
Har yanzu dai surfa mata masifa takeyi, na,,, taje duk inda kuɗi yake ta kawo mata idan ko bata samu ba, sai ta kusa sumar da ita,
Tana tafe tana share hawaye, ta hango ƙulin baƙar leda irin wanda ta ƙulle kuɗin rogon a ciki, tana ci gaba da kukan ta sunkuya ta ɗauki ledar kana ta kunce, "alhmdulilah ta ambata tana kuka tana dariya" ta waiga taga babu kowa, ta ruga da gudu, tayi nisa sosai da gidansu, sai da ta isa gindin bishiyar mangoro kana ta nemi guri ta zauna, ta ciro kuɗin a leda kana fara ƙirgawa, dubu biyar ne cif, ta washe haƙora, kome ta tuna oho sai kuma ta turɓune fuska kamar zatayi kuka, kalmomi biyu da mahaifiyarta tayi mata ne yasa ta sauya yanayi, na farko, Taje duk inda zataje ta nemo mata kuɗinta, na biyu, kar ta sake ta dawo mata gida babu kuɗi"
"Ko bin maza zanyi kenan?" Tai maganar tana tura kuɗaɗen cikin ɗankwalinta.
Da sauri ta miƙe tsaye kana ta fara tunanin meye mafita a gareta,
Tafiya tayi mai nisa wanda ita kanta bata san inda zataje ba, tabbas akwai wani abu da yake birgeta da rayuwar ƴar binni, tana bala'in son ilimi a rayuwarta bugu da ƙari tana son itama ta zamo kamar ƴan gayun da ta gani lokacin da suka je binni, tuno, rayuwar da Talatu zata ci gaba da yi tayi, hakan ya ƙara mata ƙwarin gwaiwar son taga ta fita a ƙauyensu, tana tafiya tana tafiya sai gata a tashar mota, gabaki ɗaya ta riƙiɗe sosai, bata ma san inda zata nufa ba, duk a tunaninta idan ta shiga mota, kai tsaye gidansu Anty Jamila za'a kaita, hakan yasa ta kwantar da hankalinta tare da zama daram a mota, har ta fara hango idan har ta je suka haɗu da Talatu zasu zuba yanga, tana tsaka da tunani karen mota yace "ta kawo kuɗi, ta tambayeshi nawa ne yace mata dubu "uku" ta ƙirgo ta miƙa masa ya rage saura dubu biyu kenan, ta ƙullesu da kyau, kana ta zubawa masu zirga-zirgar wucewa idanu,
Ta ɗan ɗauki lokaci a tasha motar bata tashi ba, dan har adu'ar kar Allah ya haɗata da wanda ya santa ta dingayi har motar ta tashi, ...

ANGUWAR ME GISHIRI
Dake cikin Ƙauyen Saminaka.
Wani gida na hango wanda aka gina shi da jar ƙasa, ko da yake yawancin gine ginen haka suke, gidan zagaye yake da katangar buhu, kasancewar katangar gidan ta fadi, malam Habu na Lami tsoho ne amma ba irin tukuf ɗin nan ba,, yanada matarsa ɗaya, Baaba Lalai, Baaba Lalai itama ta tsufa, saboda ko girki bata iya yi, sai dai surukarta wato matar ɗanta idan tayi take zubo mata, yawancin cimar tasu ma daga kunu sai fate, sai tuwo, duk da arziƙin dabbobi da Allah yayiwa malam Habu bai sa ya azurta iyalansa ba, a lissafin mutanen ƙauyen idan aka tashin lissafa masu tarin dukiya har dashi a ciki, saboda ko wacce shekara idan ka ka tayi lokacin da ake kwashe amfanin gona, Allah ya albarkaci nomansa, hakan yasa koda yaushe a cikin siyo dabbobi yake, wato ya siya ya siyar,
Yauma kamar kowane sati, kasancewar duk ranar Laraba ake cin kasuwar Saminaka, acan yake siyo dabbobin, kama daga Akuyoyi da raguna harda kaji na gida, sannan kuma ya siyar a kasuwar idan har aka ɗora masa riba,
Tun bayan da ya dawo daga sallahar asbha yake ta gyaran igiyoyi wanda zai ɗaure dabbobin nasa, bayan ya gama gyaran igiyar ya ƙwalawa magidancin ɗansa kira, kasancewar a gida ɗaya suke, "wanda ya kira da halliru ya fito yana cewa "hannu baba ka gama gyaran igiyar?"
"Eh halliru na gama, ungo ɗauresu sai mu tafi"
Cikin umarnin mahaifinsa ya ɗaure dabbobin kusan su ashirin, suka wuce kasuwa a ƙafa, koda suka isa babu wasu mutane sai dai shi malam Habu ƙa'idarsa ne zuwa da wuri, dan sai dai aje a sameshi badai ya sami wasu ba, bayan ya gama gyaran rumfarsa, ya ɗaure ko wacce dabba a tirke kana ya nemi gurin zama ya zauna.
8:am, lokacin ne mutane suka fara halartar kasuwar, kasancewar anata hidimar babbar sallah dabbobi sunyi tsada sosai, dabbobin malam Habu Masha Allah sunada kyau ga ƙiba shiyasa duk wanda yazo siya ya gaya masa gaskiya kuɗin inhar da gaske yake yi, bazai yi masa musu ba, alhmdulilah kafin ƙarfe sha ɗaya 11:am har dabbobi sun ƙare, saura guda biyu, wani abokinsa dake yawan zama a gurinsa ya ƙare musu kallo kana yace "malam Habu waɗancan dabbobin akwai shiga rai, Wlhi daga ganinsu naji sun higa raina, badan bani da kudi ba ai da siya, sai dai tausayin da nakeyi musu ba zai bari in yarda a yanka su ba" malam Habu ya jinjina kai, kafin yace "Muzammilu kana bani mamaki, wani lokacin idan kayi magana sai kace ƙaramin yaro, to ai naga dai Ubangiji ne ya halasta mana cinsu amma kana wasu maganganu"
Sallamar wani mutum wanda yai parking motarsa acan nesa dasu ne ya katse musu maganar da sukeyi, kallo ɗaya zaka yiwa mutumin ka gane nera da hutu sun samu mazauni, musamman ma idan ka kalli matarsa dake gefensa jajir da ita sai kace baturiya, tanada pink lips mai kyau, cikin shagwaɓe murya tace "Hayati Please kar mu wuce dabbobinnan gaskiya sunyi min" wanda ta kira da Hayati ya ƙare wa dabbobin kallo kana yace "My life ke har kinsan wasu dabbobi ne, ta ɗan ɗora kanta a saman kafaɗarsa tana dariya marar sauti, tunda har my life tayi magana sai shima ya sake ji sun shigar masa rai,
Bayan su Malam Habu sun amsa sallamar suka ƙarasa, matar ta fara shafa macen ragon, macen ragon ta lumshe idanu alamun tana jin daɗin hakan, ko da Matar ta matsa gefe, macen ragon sai ta fara kuka sosai, matar ta sake dawowa kana ta ci gaba da shafa ta, bayan sunyi ciniki mutumin ya siyi dabbobin aka sanyasu a mota suka kamo hanyar dawowa gida,
Yaseen da Yusra, masoyan juna kenan, nickname ɗinsu (Yasra) ko ni soyayyar su tana birgeni bare ku masu karatu da zaku so jin cikakken tarihin masoyan, Yaseen da Yusra a makarantar Jami'a suka haɗu, tun suna yiwa junansu ikirarin abokai, kwatsam sai abota ta juye soyayya mai ƙarfi wacce duk wanda yaga inda suke gudanar da tsaftsracciyar soyayyarsu sai sun birgeshi, kafin yiwuwar auransu sai da aka dinga kai ruwa rana, kafin iyayensu suka amince, Yaseen babban ɗan kasuwa ne, saboda yayi gadon mahaifinsa, mahaifin Yusra kuwa mataimakin gwamna ne, ko wanne iyayensa na damawa da nera sosai da sosai,
Anyi shagali sosai a bikinsu dan sai da aka shafe sati biyu ana shagali, a ranar bikin kuwa ɓangarorin iyayen biyu sun nuna bajintarsu, duk inda ka shiga a kafafen sada zumunta posting ɗin hidimar bikinsu kawai zaka gani.
Bayan anyi aure, burin masoyan biyu ya cika, nan fa rayuwarsu ta sauya cike da farin ciki da ƙaunar juna,
End Ads