x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 18 - NA KASA JUREWA book 1

  • 51001 words
  • 54000 words
  • Out of 86738 words

Category: Love Stories

Views 130

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ta fita a wannan gida ina zata dosa,
Wata mata ta fito daga wani ɗaki, a ƙalla matar zatayi shekaru arba'in a duniya, tana sanye da atamfa mai ratsin green and light pink, anyi mata ɗinkin doguwar riga, sai da ta gama ƙare wa Gudidi kallo, kafin tace "yarinya daga ina kike" Gudidi kam tayi nisa a tunani bata san anayi mata magana ba, har sai da matar ta taɓa mata kafaɗa, firgit ta firgita tare da juyowa, zuciyarta cike da tsoro tace "Hajiya dan Allah kiyi hakuri Wallashi zanyi miki aikatau" Hajiyar ta kalli Gudidi kana tace "aiki kuma, keɗin daga ina kike?" Gudidi tayi shiru bata ce komai ba, matar ta fita ta barta a gurin ta zubawa TV ido.kamar zata shige ciki,
Kai tsaye ta wuce kitchen ta ɗibo mata jollof ɗin couscous wanda yaji kifi dasu carrot, a gaban Gudidi ta ajiye, kana ta buɗe fridge ta ɗauko mata zoɓo da ruwa ta ajiye mata, ba tare da ɓata lokaci ba, Gudidi ta ajiye cokalin a gefe tasa hannu kana ta fara ci, kamar wacce tayi sati bata ga abinci ba, Matar na zaune tana kallon Gudidi, sosai gudidin ta bata tausayi, sai girgiza kai takeyi, bayan ta gama cin abincin ta ture plate ɗin gefe, ta ɗauki gorar zoɓo ta shanye, ta ɗauki ruwan leda shima ta shanye, tare da yin gyatsa mai sautiii, "Hajiya dan Allah zan iya kwanciya?" Hajiyar ta gyaɗa mata kai, alamar eh ta kwanta, da gudu ta haye saman kujera 3sitter kana ta kwanta, lokaci ɗaya barci ya ɗauketa,
Hajiya dai ta kasa tashi daga gurin Gudidi, ta jima a zaune a saman kujera mai zaman mutum ɗaya, tana ƙare mata kallo tare da tarin tambayoyi da tunani iri-iri,kwance a zuciyarta.
Innalillahi wa inna ilahir raji'un, Ruqaiyya ta ambata kana ta fara ƙoƙarin janyo bedsheet tana rufe jikinta, Sabeer sai wani ƙwaƙumeta yakeyi, ita kuma ta ƙoƙarin suturta jikinta, cikin Muryar firgici tace "Sabeer ka rabu dani Sabeer ka ƙayaleni baka tunanin komai game da yarinyar nan da ta shigo ta fita?" tai maganar ƙirjinta na tsananta bugawa, "sai da nace miki bai kamata muzo gidanku ba, Gara mu haɗu a hotel kikace babu damuwa, kuma ai kince Mom ɗin naki ta fita ko?" Girgiza kai ta farayi tana kuka tana yarfe hannaye, cikin yanayi na damuwa tace "Mom ta dawo saboda na ji maganarta, nifa babbar damuwata yarinyar nan, duk da ban taɓa ganinta ba, amma na tsorata sosai, yanzu duk ba wannan ba, ka tashi kasa kaya ka fice gobe zamu haɗu a club" ta kai ƙarshen maganar tana haɗe hannayenta biyu alamar ban haƙuri, "shikenan, amman kinsan Wlhi kin ja min rai, Ruky bazan iya ƙarashe wunin yau ba tare da keba, dan haka zan tafi, i swear idan baki zo ba, ni zan sake dawowa"
Sabeer ya bata amsa yayinda yake sanya rigarsa,
"In...i...in...sha...inasha... Allah zan zo" ta faɗa tana miƙewa tsaye, saboda ta zumbula doguwar rigar da ta cire sbda zuwansa,
"Ruqaiyya... Ruqaiyya... Ruqaiyya..mom ta fara ƙwala mata kira, sai da ta tabbatar da Sabeer ya fice kana ta amsa tana mutsike idanunta alamun daga barci ta tashi, lokacin da ta shiga parlon Mom ta sami Gudidi tana kwance tana barci, acan gefe kuma Mom ce tana daddana waya, Ruqaiyya ta ƙaraso jiki a sanyaye, ta durƙusa a gaban Mom kana tace "Mom gani" tana maganar tana sake mutsika idanu,
Mom tace "dama inason zanje anguwa dan Allah ki kularmin da gida, karki fita ko ina" Ruqaiyya ta gyaɗa kai tana cewa "to" sai kuma ta sake kai kallonta ga Gudidi kafin tace "Mom wannan kuma wacece, a tsorace tayi maganar sbda gudun kar Gudidin ta tona mata asiri, Mom tace "barinje in dawo zanyi miki bayani, amma idan ta tashi ki bata ruwa tayi wanka" mom na gama maganar ta wuce bedroom ɗin ta, mayafi da waya ta ɗauka sai key car kana tayi musu sai ta dawo.
Bayan fitar Mom Ruqaiyya ta fara roƙon Allah, yasa Gudidi ta tashi daga barci kafin Mom ta dawo, sabda idan har Mom ta dawo bazata samu damar yin magana da ita ba.
Kai tsaye bedroom ɗin Mom ta wuce ta fara gyara bed kana ta shiga toilet tayi wankan tsarki, kana ta wanke ta share ko ina, ta dawo parlor ta goge kujeru sannan ta haɗa kayan wanke-wanke tayi, bayan ta gama ta kunna A.C kana ta fesa room freshener, ko ina ya ɗauki ƙamshi mai daɗi,
A hankali sanyin A,C ke shigarta, ta fara tattare ƙafafuwa alamun sanyi takeji, sai kuma ta buɗe idanu tare da tashi zaune, tana sake ƙare wa parlorn kallo, Ruqaiyya ta shigo hannunta riƙe da tray na indomie sai ƙamshi ke fita, tunda sukayi ido biyu da Gudidi ta runtse idanunta tare da toshe baki, in one time jikin Ruqaiyya ya fara kyarma tasan asirinta zai tonu, amma sai ta wayance da yin murmishi tace "Baƙuwarmu kin tashi ne" Gudidi ta cire hannu a baki, sai ta fara ganin kamar ba ita ta gani da wani saurayi tsirara ba, gyaɗawa Ruqaiyya kai tayi,
Ruqayya ta taso daga inda take zaune tace "Baƙuwarmu dan Allah inason in tambayeki" Gudidi tace "to" Ruqaiyya tace "lokacin da kika shigo gidannan baki ga wata budurwa da wani saurayi a ɗaki ba?" cikin sauri kamar wacce aka zabura Gudidi tace "tabbas na gansu tsirara aihuwar uwarsu da ubansu" sai da Ruqaiyya ta zaro idanu kafin ta sake ce mata, "kinasan me nakeso dake?" Gudidi tace "a'a" Ruqaiyya tace "inason ki yi shiru da bakinki Wlhi tallahi idan har naji kin gayawa wani sai na kasheki, sosai tsoro da firgici ya shiga zuciyar Gudidi, da sauri ta yayibo ɗan siririn mayafinta, ta fara shirin guduwa, saboda dama ance ana yawan kashe mutane a binni, hamdala Ruqaiyya tayi, saboda tayi nasarar tsoratar da ita, sbda ko a yanayin ta ma tasan ta tsorata sosai, "ki tashi kije kiyi wanka, zan baki kayana kala goma sai ki dinga sawa, amma kafin nan daga ina kike?"
Gudidi ta riga ta firgita sosai tace "ni ƴar uwar Hajiyar gidannan ne, na dangin NoNo" Ruqaiyya kam bata gane wannan Hausar ba, ta ce "jekiyi wankan kawai"
Ta miƙe ko ina nata kyarma yake, saboda a duk tunaninta Tana shiga banɗaki Ruqaiyya zata kasheta, ko da Ruqaiyyan ta nuna mata toilet ta shiga sai da tasa saƙata, kana tayi wankan a gurguje, bayan ta fito, taci karo da tsadaddun kaya wanda Ruqaiyya ta ajiye mata, sai dai duk masu gidan sa nono ne, itakam da babu komai a ƙirjinta, wata doguwar riga ƴar kanti tasa, tayi mata yawa, saboda Ruqaiyya tanada tsayi kuma shekarunsu ba ɗaya ba, sabda Ruqaiyya zatayi 23yrs,
Ruqaiyya na fitowa tayi murmishi, kana ta ƙara so ta sanya maɗaurin rigar ta ɗaure mata, hakan ya taimaka mata gurin rage tsayin rigar, ta kawo mata man shafawa ta shafa, sannan tace "zan shiga bedroom ɗin Mom zanyi waya, duk wanda ya shigo kice bana nan, amma idan Mom ce kimin magana"
Gudidi ta amsa mata da cewa "to" bayan shigar Ruqaiyya, sai da Gudidi ta tabbatar da Ruqaiyya ta rufe ƙofar, sannan ta fara shirye-shiryen guduwa, saboda tana ganin Ruqaiyya zata iya kasheta.
Acan bedroom ɗin Mom, Sabeer ne ya dameta da kira, wai sai dai tazo Gidansa kokuma su haɗu a hotel shi bazan iya jure rashinta ba, haƙuri ta dinga bashi, yace sai dai suyi video call idan ta yarda, dole ta yarda tunda tana tsananin sonsa, ya sata ta cire komai na jikinta ta kafe wayar inda zai dinga kallon komai nata, sunata baɗalarsu, shima hakan yayi, yasata tayi wannan ya sata tayi wancan daga ƙarshe dai ta kwanta tana mayarda numfashi, dama da biyu yayi hakan yasan dole sai ta buƙaceshi, tana sauke wani fitinannen nishi tana cewa "Sabeer NA KASA JUREWA bazan iya jurewa ba, Please kazo da mota ka ɗaukeni Please my Sabeer" ransa fess dama abinda yake jira kenan, kasancewarsa mai wayo da dabara, ba wani jimawa sai gashi a ƙofar gidansu, ya kirata a waya, tace masa gata nan fitowa, sai da ta sake yin wanka kana ta sauya kaya, sannan ta fito, "ina kuma yarinyar nan ta shiga?" Ruqaiyya ta tambayi kanta tana ɗaura ɗankwali, ta fito ta zagaye ko ina bata ganta ba, ta tambayi mai gadi yace shima bai ganta ba, hankalinta a tashe ta dinga zagaye anguwarsu, tana dawowa ne ta hango motar Sabeer, ƙara sawa gurinsa tayi, ba tare da tunanin komai ba, yaja mota sukayi gaba...
LAYLA
Rai a ɓace ta ƙarasa shigowa gidan, da kuka ta shiga ɗakin mamanta, mama na zaune tana ninke kaya, Layla ta sameta, cikin Muryar kuka take cewa "mama zan ajiye aiki wallhi bazan iya ba, mama bazan iya JUREWA ba"
Maman bata fahimci komai ba, ta matsar da kayan da take ninkewa cikin yanayi na damuwa tace "Layla meke faruwa? Dan Allah kar in sake ji kince zaki bar aiki"
Hawaye na bin kumatun Layla tace "mama na kamu da soyayyar wanda bai san inayi ba, mama na furta masa yana ƙoƙarin hukuntani, Wlhi har wulaƙanci yayimin, mama bakiga korar karen da yayimin ba, ƙarshe cewa yayi ya tsaneni" Mama ta zaro ido, kana tace "kina nufin yace karki sake zuwa gurin aiki "Layla na kuka tace "eh" maman tace "inko haka ne ai bamu ga ta zama ba, Wlhi tallahi sai inda man mu ya ƙare, amma fa kinsan malam mai yanzu-yanzu aikinsa akwai tsada abinda nakeso dake yanzu, kiyi hakuri ki bar min komai a hannuna tunda yace "abinda zeyi kenan kawai ki ƙyaleshi, ni zan ji da komai" mama ta kai ƙarshen maganar tana kwashe kayan ba tare da ta ƙara sa ninkewa ba ta kaisu uwar ɗaka, ta ɗauko hijabi tana cewa "yanzu nawa ne a gurinki?" Layla tace "dubu biyar, amma ai yau za'ayi mana albashi, mu jira zuwa anjima mama"
Maman ta ajiye hijabin, ta shiga kitchen kana tace mata "idan kuɗin ya shigo kiyimin magana"
Kai tsaye ta wuce ɗakinta tare da tunanin idan har bata mallaki Ma'aruf, ba zuciyarta tana iya fashewa, tana tsaka da tunani ƙarar alert ya shigo wayarta, ihu ta kurma tare da duba alert ɗin, ware idanu tayi tana cewa "Allah na gode maka, zan mallaki wannan haɗaɗɗen gayen ko ta halin ya ya" da gudu ta nufi inda mama take, cikin farin ciki tace mama kuɗi sun shigo 100k yanzu ya za'ayi?"
Mama tace "jeki ciro dubu talatin, kinsan ance komai ayishi da zafi zafi yafi, ke ƴar nan idan har kika auri wannan mutumin ba ni kaɗai ba, har dangina sun warke da nera, mama ta janyo hijabi ta fice tana kiran Layla, a tare suka tafi, Layla na cire kuɗin a POS ta miƙawa mama 40k ta riƙe 10k dama 50k ta ciro ya zamo tanada 15k a hannunta, kai tsaye mama ta wuce bakin titi, nan ta wuce baban Layla a majalisa, mashin ta hau ta gaya masa anguwar da zai kaita, bayan sun iso ta sauka, kana ta sake hawa wani mashin ɗin da zai kaita ƙauyen da take son zuwa, daga gefen hanya mai mashin ɗin ya ajiyeta, ta bashi kudinsa kana ta ci gaba da tafiya, tayi tafiya mai nisan gaske har haɗa gumi takeyi, tana tafe tana ta saƙar inda bikin Layla zai kasance idan har tai nasarar samun Ma'aruf,
Tana isowa gurin wata tsangaya ta tsaya tare da ɗagawa malamin hannu, sbda yana tare da almajirai,
Malamin na ganinta ya washe haƙora, saboda yanayi mata aiki sosai tana kawo masa mutane, aikin mallakar baban Layla ma ita tayi masa,
Tashi yayi daga inda yake zaune, kana yace suci gaba da karatu, iso yayi mata zuwa ɗakin da yake karɓar baƙi, bayan mama ta zauna suka gaisa, ta ce masa "dan Allah ya taimaketa yarinyarta tana kwance babu lafiya ta kamu da soyayyar wanda take yiwa aiki a Company ɗinsa, sun rasa gane kanta" malam yayi murmishi kafin yace "Hajiya wannan duk mai sauƙi ne, wato matsalar shi wanda takeso shine...
Bayi da ra'ayin soyayya, sannan bai sanya mace a lissafinsa ba, amma idan har tace zata iya zama dashi a haka, zanyi mata aiki mai ƙarfi wanda zan janyo hankalinsa ya karkato gareta"
Mama tayi shiru, kafin tace "malam bari in kirata kar ayi abun da ka"
Malam yace "babu network anan, ki fita can waje zakiga wani ƙaton dutse anan muke samun network"
Mama ta fita tare da hawa saman Dutse kana ta fara lalubar number Layla,
Layla na ganin kiran mama tai saurin ɗagawa, cikin farin ciki take cewa "mama an dace ko?"
Mama tace "Layla kina jina?" Layla ta amsa da "eh, "
Tayi mata dukan bayanan da malam yayi mata, kana tace "kin amince ayi aikin?"
Layla tace "eh na amince"
Mama ta katse kiran ta koma gurin malam, tace ayi aiki kawai, malam yace "yanzu ma kuwa, tambayar sunan wanda Layla takeso malam yayi, mama tace "Ma'aruf"
Malam ya zuba wani irin ruwa a ƙwarya kana ya fara ƙwalawa Ma'aruf kira da ƙarfi, sai ga Ma'aruf a cikin wannan ruwan ya baiyyana, gashi a zaune a office yana shan coffee, malamin ya fara wasu surkulle wanda ni kaina ba riƙe su nayi ba, daga ƙarshe ya ɗibi ruwan a gora ya miƙawa mama, kana yace a kaiwa Layla tayi wanka dashi babu sabulu, sannan ga wannan powder idan zataje Company ta shafa, ko wani saurayi ya ganta babu damuwa ai da sunan wanda takeso akayi aikin" mama tace "to malam mun gode sai dai baka faɗi abinda za'a baka ba?"
Malam yayi dariya, kana yace "kuɗin aikinku dubu talatin da biyar" mama ta ƙirgo ta miƙa masa, kana tayi masa sallama, ta fito.
Cike da fatan nasara ta ƙara so bakin titi inda zata samu abin hawa, mai mashin na zuwa ta hau suka wuce anguwarsu, kasancewar idan daga nan zaka tafi ana samun mashin direct zuwa unguwarsu,
Har ƙofar gida mai mashin ya sauketa, ta shige gida zuciyarta fal farinciki, lokacin anata kiraye-kirayen sallahar magriba, sai da tayi sallah kana ta zauna bawa Layla labari, har suna tafawa saboda farinciki, ta miƙawa Layla ruwan maganin da Powder tayi mata bayani, kana tace "bata son mahaifinta ya sani, cikin sirri sukayi abin, har baba ya shigo bayan an idar da Sallah, ya tambayi mama ina taje, tace masa gidan wata ƙawarta, bai sake cewa komai ba.
Washe gari Layla ta ɗau alwashin bazata je aiki ba, zata gwada ta gani maganin yana aiki, kwanan ta biyu babu wanda yai cigiyarta a gurin aikinsu, sosai ta fara damuwa saboda gani takeyi maganin ma baya aiki, ƙarfe 10:am ta kwanta barci mai cike da mafarki mai daɗin gaske, wayarta ta fara ruri, tsaki taja saboda mafarkin masoyinta takeyi gashi wanda yake kira ya katseta, da sauri ta ɗaga kiran cikin tausasa murya tace "Sir Barka da safiya da fatan kana cikin ƙoshin lafiya" ya Subhanallah ji yayi kaf duniya babu Muryar da takai ta Layla daɗi, bayan sun gaisa shine har da ce mata wai yayi missing ɗinta, sannan yana son tazo office idan bai ga kyakkyawar fuskarta ba bazai iya yin aikin komai ba, sosai ta dinga furta masa kalamai masu tsayawa a zuciya cikin sanyin murya wacce ta sake Ratsa zuciyarsa da zallar soyayyarta,
Bayan sun gama waya, shine har da ce mata I love you, da wasu hote things.
Tana ajiye waya ta shirya cikin sauri tare da baɗa powder har taso tayi mata yawa,
Koda taje gurin kayanta ta jima tana zabar kayan da zai dace da shigar da takeson yi, saboda yau ranace ta musamman a gareta, wata baƙar doguwar riga ta ciro wacce akayi mata tattara ta gaba, anyi mata ado sosai da pink and golden ɗin zare, kana an yalwata ta da stone masu walwali, ga wasu tutoci a zagayen jikin rigar, mayafin rigar tayi rolling dashi kana taje gaban mirror ta ƙare wa kanta kallo, ko ba'a gaya mata ba, ta sani tayi kyau sosai, tasa pink lipstick tare da fesa turaruka masu ƙamashi.
Hand bag ɗinta ta ɗauka kana ta rataya, sannan ta ɗauki farin mayafi ta ninkeshi a kafaɗarta, ta fito parlor sai zuba ƙamshi takeyi, Mama ta kalleta cike da ƙauna irin ta ɗa da uwa, tayi murmishi kafin tace "har na hangoki a gidan Ma'aruf, suka kwashe da dariya, Layla tace "mama inasha Allah, adu'arki ai karɓaɓɓiya ce a gurin Ubangiji".
Mama tayi mata Allah ya kiyaye ta fice zuwa company.
Afuwan kuyi hakuri baku samu update da wuri ba, Wlhi nayi baƙi ne, sannan ina jiran shar'hi, wanda suke son shiga group ɗin da nake posting suyimin magana WhatsApp 08141799224

Mom Islam ce...🤙

*NA KASA JUREWA*
💋💋💋
💋💋
💋
_Mom Islam_


_SANARWA_
Aslamu alaikum masoya makaranta littafin NA KASA JUREWA, kuyi haƙuri da tsaikon da ake samu gurin posting, jiya na samu matsala da WhatsApp, yau kuma yarinyata ta tashi babu lafiya, alhmdulilah jiki yayi sauƙi, akwai wata sanarwa da naga ya dace in yiwa masu bibiyar labarin, idan har na kai page 50 zan dinga posting ƙarfe 12:pm insha Allah, sannan inayi muku albishir da cewar, daga yanzu zaku dinga samunsa akan lokaci da izinin Ubangiji, masu Arewabook posting ɗinku special ne.


Page 55-56

Washe gari sunada makaranta dan haka ta shirya da wuri, anty Tasneem da Umaimah ne suka ƙara sa aikin gidan, tana fitowa harabar gidan ta hango motar yah Arman, mamaki ne ya kamata sai ta ci gaba da tafiya, har ta iso inda motar tasa take, "yah Arman ina kwana" ta gaishe shi tana ɗan sunkuyawa, "lafiya lau ƙanwata da fatan kin tashi lafiya" ta gyaɗa masa kai, tare da buɗe gidan gaba ta shige, bayan ta rufe murfin motar, yayiwa mai gadi horn suka fice, tunda suka fara tafiya take ta kalle-kalle, shi ko idanunsa suna kanta, duk wani motsi nata akan idanunsa takeyi, ikon Allah ne kaɗai ya kaisu makarantar, domin kuwa bai mayar da hankali ga tuƙinsa ba, mai gadin makarantar nasu na ganin mota ta taho, ya miƙe da sauri yana buɗe get, har cikin makarantar yah Arman ya shigar da ita, bayan ta fito yace "Aysha.." ta amsa da cewa "na'am.."
Kamar ba zai yi magana ba, sai kuma yace "kinzo da kuɗi ne?"
"Eh yaya" ta faɗa tana kama hanyar tafiya zuwa ajinsu, tunda ta fara tafiya ya zuba mata idanu, har ta ɓacewa ganinsa, sannan ya ja motar kana
End Ads