zuciya, tabbas tayi barci, cike da kallon tausayi ya bita, a fili ya ce "ta gaji sosai"
Ya gyara mata kwanciya, tare da jan blanket ya lulluɓeta, ya ci gaba da kallonta cikin so da ƙauna, shikam har ga Allah ya sonta so mai tsanani,
A dole yaje yayi wankan shi kaɗai, kana ya fito yana sanye da Bathroom, tsayawa yayi yana kallon mirror, yana tsaye a gaban mirror ɗin, wayarsa da ya kunna kafin shigarsa wanka ta fara ringing, number Hajiya Zaliha ya gani tana yawo a kan screen ɗin wayar, sbda tanada numbers ta waje, amsa wa yayi tare da cewa "Aslmu alaikum"
"Ba sallama nace kayimin ba, so nakeyi ka gayamin a wane matsayi na ajiyeni? matar aure kokuma free wife?..!
Rashin comments yasa banayi yi muku posting mai yawa, idan kun cigaba da comments nima zan gyara...
Mom Islam ce 08141799224
[7/12, 2:34 PM] Mom Islam: *NA KASA JUREWA*
🪻🪻🪻
Mom Islam
Masu Arewabook ayi haƙuri anjima zanyi muku posting page 11&12
Please masu nema daga farko kuyi following channel ɗina ga link nan👇
https://whatsapp.com/channel/0029VbBCPdgEawdlPZsXnp3t
Domin samun more pages kuyi following ɗina a Arewabook danna blue link👇
https://arewabooks.com/u/momislam11
Ga wanda basa Arewabook ga link na Wattpad hilis ayi following ɗina 👇
https://www.wattpad.com/user/Momislam2021?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
Page 9-10
Cikin isa da jiji da kai ya furzar da isa mai huci kana yace "me kike nufi?, ba dan an takura min ba me zan ci dake?, kinga ni sauƙi ma kika nema min kije na sakeki saki uku"
Kafar a kunnen Hajiya mama dake ta kwaɗa sallama tun daga parlo bataji motsin kowa ba, a take a gurin ta faɗi sumammiya, cikin azama Saudart ta taho da gudu zata taimaka mata, yai saurin dakatar da ita gami da cewa "idan har kika taɓa ta wallahi sai na illata ki"
Ko da jin haka ta miƙe zuciyarta fess dan har ta fara jin tausayin Hajiya, tunda ya gaya mata magana tayi ta kanta, cikin farinciki da samun ƙwarin gwaiwa ta harhaɗa komai nata, kuɗin da Anam ta turo mata ta sake dubawa, a fili ta tace "hmm wallahi bazan sanarwa kowa maganar sakin nan ba, amma fa dole in nemo sheda kodan kar Dady yace min ƙarya nakeyi.
Biro da takarda ta ɗauka zuciyarta fess ta wuce ɗakinsa, a bakin ƙofa ta sameshi yana yayyafawa, Hajiya ruwan sanyi, tace "yaya nazo ka rubuta min shedar saki"
Babu musu ya karɓa saboda har ga Allah ta zame masa tamkar gobara, duk da tashin hankalin da yake ciki na suman Hajiya be hanashi rubuta mata saki ba, ya miƙa mata tare da cewa "kafin inje asibiti in dawo kar in sameki anan"
"Ai bazaka sameni ba, yanzu kam meye haɗinka dani, Allah yabi bayan me gaskiya" ta faɗa tana wucewa abin ta,
Ko saurar ta beyi ba ya kin kimi Hajiya zuwa parking space yana ƙwalawa Idi mai gadi kira, da gudu Idi ya taho yana cewa "lafiya kuwa alhjaji?"
"Dalla can buɗe min get, lafiya ne zan dinga yi maka wannan kiran?"
Jikin Idi na rawa yai azamar zuwa buɗe masa get sbda yasan halin uban gidan nasa.
A guje ya fice daga gidan kamar wanda zai tashi sama, cikin ransa ya dinga mai-maita innalillahi wa inna ilahir raji'un, har suka iso (Mai tama District Hospital)
Emergency room aka wuce da ita, inda aka bata taimakon gaggawa,
Duk wanda ya kalli fuskar Ma'aruf ko ba'a gaya masa ba yasan yana cikin matsanancin tashin hankali, adu'arsa bata wuce Allah yasa babu abinda ya sami hajiyarsa ba, idan kuma ta kamu da wani ciwon ta sanadinsa fa?"
Gaskiya bazai yafewa kansa ba.
Duk wani likita me shige da fice a ɗakin da aka kwantar da Hajiya, sai ya bishi yana cewa "likita dan Allah ya farfaɗo? likita tana magana?,
Inda kasan zautacce haka ya koma, wayarta dake hannunsa ya kalla, a sanadin faɗuwarta, duk ta farfashe, ya kawar da kallon wayar da yake sakamakon rurin da wayar ta farayi,
Sunan Anty Jamila ya gani yana yawo a fuskar wayar, sosai gabansa ya bada rass, lokaci ɗaya zufa ya fara karyo masa, be san amsar da ze bata ba, ƙarfin hali yayi ya ɗaga a ɗarare yace "As...asalamu a.."
"A'a Ma'aruf yakuke ina Hajiyar?"
Shiru yayi bai bata amsa ba, jin shirun yayi yawa, ta katse kiran ta sake kira, dolensa ya ɗaga, duk girman kansa da jan ajinsa baya yiwa mutum biyu, idan ka cire mahaifinsa da ya rasu, wato Hajiyarsa da Anty Jamila ƙanwarta kenan.
"Kayi magana mana, wai meke faruwa ne Ma'aruf?"
"Hajiya na hospital"
Kalmar da ya iya gaya mata kenan ya katse kiran.
Sosai hankalinta in yayi dubu ya tashi, ta fara harhaɗa kaya,
ƘAUYE
Ko da aka tashi daga islamiyya kowa ya watse amma Talatu bata matsa ko nan da can ba, sbda tun kafin a tashe su malamin ya fita, anyi masa kiran gaggawa, ɗaya daga cikin manyan ɗaliban ne ya yi musu addu'a kowa ya watse, har lungu Talatu taja wuyan hijabin Gudidi, mutane biyu ne a biye dasu, ɗaya sahura ce ƙawar Gudidi, ɗayar kuma Lantana sunanta ƙawar Talatu,
Rawa suke tiƙa sunayi musu waƙa suna cewa ...
"🎺A casu mata a casu, ku casu ba me rabaku araba ace anyi cuta, a zamanin nan na yanzu"
Sosai suke tiƙar rawa, kan kace me har Talatu tayiwa Gudidi lilis, babu mataimaki sai Allah, duk su biyun ƙawayen nasu basu isa suja da ƙarfin Talatu ba, sosai ta haɗawa Gudidi jini da majina, kafin faɗan ya ƙare, Gudidi na tafiya tana ɗingishi, tace "Hegiya maiyya jaka me ƙarfin Allatsine me kai kamar na duwatsun murhu"
Talatu ta biyota da gudu, itama gudun takeyi tana ɗingishi har ta ƙarisa gidansu,
Tana shiga ta samu Tabaiyye da malam sai uban musayar yawu suke yi, ita kuma ta shigo tana kuka babu wanda ya saurareta,
Wucewa tayi ɗakin Tabaiyyen ta kwanta a ƙasa ko zataji sassaucin mutsikar da tasha gurin Talatu.
Malam ya gyara zaman babbar rigarsa kana yace "Wallahi wannan hine gargaɗi na ƙarhe idan kika sake ragemin hatsi kowa ze kama gabansa"
Cikin masifa Tabaiyye tace "yo in kama gaban nawa mana, ka gayamin me na tsinana tunda na aureka, kaf kiwon da iyayena suka haɗoni dashi sun ƙare, me kake dashi da zan ɗin ga ɗiba? ta gyara ɗaurin zaninta taci gaba da cewa "ko yanzu na fita a gidanka zan samu saurayi sabo fil gada gau me jini a jika"
Tun da ya ji ta faɗi haka, ya wuce ƙofar ɗakinsa kana ya ɗauki buta ya kuskure bakinsa, har ya nufi hanyar zaure ya juyo yace "Tabaiyye kiji ta tsoron Allah karki ragemin masara"
"Da tsoronka nakeji mtsw"
Tai maganar tana yatsina masa fuska.
Hankali kwance Talatu ke tafiya har ta iso gida, tunowa da babbar baƙuwar da Inna ta gaya mata zasuyi ne yasa ta washe haƙora, a fili tace "na rantse da Allah ina son ganin ƴan binne" da gudu ta shige tana cewa "Inna dan Allah ki biyoni ban ɗaki da buta tsuuuuu (Gudawa) nakeyi"
Sam bata ma ga Anty Jamila dake zaune saman tabarma ba, cikin ɗaga murya Inna tace "Talatu zanci mutuncin ki", tana ƙare maganar ta miƙe takai mata buta,
"Yauwa Innata idan nai aure zanyi kewarki"
Ko ƙala Inna batace mata ba ta dawo gurin Anty Jamila.
Murmishi Anty Jamila tayi kafin tace "wallahi A'isha tana birgini"
Inna tace "taɓɓ bakisan waye A'isha bane"
"Haba Inna ai Kowane yaro da ƙuruciyarsa"
"Hakane kam"
Inna ta faɗa tana dariya.
Bayan ta fito daga banɗaki ta ware idanunta, fess ta ɗora su kan Anty Jamila, washe jajayen haƙoranta tayi kafin ta taho da sauri tace "ahe kin ƙaraso Inna Jumai?"
"Na ƙaraso A'isha, amma sau nawa zan ce miki bana son ki dinga ce min jummai?"
"To kiyi hakuri yasin mancewa nakeyi, amma dai kinzo kiyi mana wata da watanni ne ko?"
Anty Jamila tai dariya kana tace "a'a yanzu ma daga Madobi nake gobe insha Allah zan koma Abuja"
Zaro idanu Talatu tayi sai kuma ta matso kusa da Anty Jamila tace "dan Allah ina Hajiyar nan da take zuwa tana raba mana hinkafa?"
Anty Jamila tace "Hajiya tana gida, sbda rashin lafiyarta ne ma zan koma gobe"
"Ahe bata da lafiya?"
Talatu ta faɗa tana ƙara tattaro nutsuwarta, kai kace dagaske,
Ita ko Anty Jamila duk tambayar Talatu tayi mata sai ta bata amsa.
Koda Inna tazo ta samesu sunata hira, abin yai mata daɗi,
Tace "Jamila kuna zantawa ne da ƴar taki?"
Anty Jamila tai murmishi.
Jollof ɗin dawa da wake Inna ta kawo wa Anty Jamila, ayko taci sosai ba laifi dan kaɗan ta rage tasha ruwa,
Wayar Anty Jamila ta fara ringing,
Ganin sunan Ma'aruf yana yawo a kan screen ɗin wayar yasa tai saurin ɗagawa, tare da cewa "my Son ya akayi?"
"Anty Jamila Hajiya fa bata magana kwata-kwata"
Cikin firgici Anty Jamila ta fara mai-maita "innalillahi wa inna ilahir raji'un"
Kana tace "son kayi haƙuri yanzu dare ya fara tunda ana shirin kiran sallahar magriba, insha Allah gobe ƙarfe huɗu zan taho, Allah ya bata lafiya"
Sosai hankalin Anty Jamila ya tashi, sanda a iya saninta Hajiya ba ta taɓa irin wannan ciwon ba.
Nan ta labartawa Inna abin da ke faruwa, Inna tace "itama zata bi Anty Jamila su tafi tare"
Talatu tace "taɓɓ wallahi he anje dani kawai ki tafi har binni ki barni hu'um"
"Ba fa wani abin daɗi ne ze kaini can ba, rashin lafiya ne, kuma befi in ɗauki kaya kala ɗaya ba"
Da ƙyar da lallashi dan sai da Anty Jamila tayi mata alkawarin zata turo me mota ya kawo ta Abuja sannan ta amince,
A daren Inna ta haɗa mata kayanta a bako sbda kafin su wuce zata kai ta gidan mahaifiyar babanta.
Bayan sallahar isha'i, suka wuce gidan Kaka, da sallama Inna ta shiga kafin tace "zauna mana ai dai kya gaihe ta"
"Ina wuni"
Talatu ta faɗa tana turo baki, "lafiya lau ƙawata na ganki da jakar kaya?"
Inna tace "wallahi na kawo ta ne zamu wuce Habuja gobe saboda Hajiya Habiba babu lafiya"
"Ash sha, Allah ya bata lafiya, zaki daɗe ne?"
"A'a kwana ɗaya zanyi"
Inna taba kaka amsa, kaka tace "to ki ja mata kunne banda rahin kunya, dan ba kowa bane ze ɗauka"
Sosai Inna tayiwa Talatu faɗa kana tayi musu sallama, bayan ta miƙa wa Talatu ɗari biyu taba wa kaka ɗari uku,
Kaka ta washe haƙora tana cewa "Allah ya tsare, "maiyyar kuɗi" Talatu ta faɗa tana hararar kaka"
"Nayi ɗin naga uwarki ce ta bani ko?"
Koda taji barci kaka ta hanata hawa gado wai kar tayi mata fitsarin kwance, sai da Talatu ta bari kaka tayi barci kana ta lallaɓa ta kwanta can gefenta,
Kaka dai tasan ta hana Talatu hawa gado, gashi fitila ta mutu, tunda su basa ganin wutar lantarki, cikin ihu da kururuwa take cewa "ke Talatu tahi ki gani kwarto"
Tunda Talatu taji kaka ta faɗi haka, ayko ta kunce zanin kaka ta cukuai kuyeshi, ta janyo hannun kaka kiiiii ta janyo ta ƙasa, ta haye gadon daga can inda take ta sauya murya tace "ke ƴar tsohuwa jiya naji kina adu'ar Allah ya baki miji hine nazo mu shirya"
Haba kaka ta sake rikicewa, bakinta na rawa tace "nifa tsohuwa ce haba kai kuwa baka ga jikina duk a tamushe ba, na roƙeka nidai ban ce haka ba"
"Zo nan"
Talatu ta faɗa cikin daka tsawa, ganin kaka ta rikice sosai yasa ta koma kan gadon ta kwanta tunda tasan bazata taba komawa ta kwanta acan ba.
Ƙarfe huɗu na asbha Anty Jamila ta farka, dan ba wani barci me nauyi tayi ba, ko wanka batai ba, ta shirya cikin leshi Black anyi masa ado da zare golden color me adon duwatsu farare, mai kawai ta mutsika, tayi tunanin Inna tana barci sai taga itama har ta gama shiri, kasancewar basu da wani kaya me nauyi suka fita neman me mashin, sbda masu mashina ba kasafai suke yawo ba, kasancewar ƙauye ne sosai, idan kaga mashin sai na masu zuwa gona, can maƙotansu Inna taje ta roki alfarma, tai sa'a yaron gidan na nan, ya fito da mashin ɗinsa suka hau zuwa tasha,
Sai da suka kai ƙarfe shida kafin motar ta cika, sannan suka fara tafiya...!
Ayi haƙuri jiya baku ga posting ba, wallahi kuna raina kunsan weekend mutum ba shi da wani hutu sosai.
Share fisabilillah 👏
Mom Islam ce 08141799224
[7/16, 8:21 PM] Mom Islam: *NA KASA JUREWA*
💋💋💋
💋💋
💋
_Mom Islam🍹_
Kiyi following ɗina Arewabook zaki samu more pages ga link nan 👇
https://arewabooks.com/u/momislam11
Page 71-72
Ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyar Yaseen, duk cika bakin da ya dinga yi akan bazai barta taje wankan gida ba, yasha ruwa, saboda daga Hospital gidan Momcy aka wuce da ita, dole ya ƙulla ƙawance da zirga-zirgar zuwa gidan Momcy kullum, kaka ce take yi mata wankan jego,
Sati biyu Yusra ta samu a gidan Momcy, tayi kyau tayi ƙiba sosai, ita da yarinyarta da suke kira da Mirah, sosai mimrah take kama da Yusra har ɗan ƙaramin bakin,
Yauma kamar kullum, koda ya je can gidansu sai ya ga gidan yayi masa girma sosai, acan gidan Momcy yake cin abincin dare kullum,
Ƙarfe 7:pm ya kama hanyar zuwa gidan Momcy, ga wani uban hadari dake haɗawa, hakan bai sa ya fasa ci gaba da driving ba, horn yayi a bakin get ɗin mai gadi ya buɗe masa, ya shigar da motarsa, a lokacin har an fara yayyafi, da sauri ya shige gidan tare da kutsa kai cikin parlorn, babu kowa a parlor dukansu suna ɗarin Momcy hakan yasa shikam kai tsaye ya wuce ɗakin Yursa, wayarsa ya ciro tare da danna numberta ya kirata, kasancewar wayar a vibrat take, ta ɗago kai a hankali kafin ta kalli kaka, sai kuma ta kalli Momcy da ita take kallo, cikin ɗan duburburcewa tace "am..dama...um.." Momcy tace "Yaseen ne yazo ko?"
Ta ɗanyi murmishin yaƙe tare da cewa "uhm Momcy ya akayi kika gane?"
"Kinga tashi kije, wlhi idan har kika biye masa yayi miki daɗin baki ke kika sani, dan ɓatan watanki ya ɗauke ba shi ke nufin ki koma ga mijinki ba, ah to, wallhi ina nan babu ruwana,"
Kaka ta faɗa tana bin ta da kallo, sake ɗago idanu tayi ta kalli Momcy,
Momcy tace "tashi kije amma fa ki kula"
Har ta fito bakin ƙofa, Momcy ta ƙwala mata kira ta dawo, "zo ki ɗauki ƴarki"
Momcy ta miƙa mata mimrah,
Bayan ta karɓeta ta fice a ɗakin kai tsaye ta wuce ɗakin ta,
A saman sallahya ta samesa yana ta kwararo adu'oi, bayan ya shafa, ya miƙe yana ninke sallahyar yana yiwa mimrah murmishi, kafin ya matsa inda Yusra take tsaye, ya buɗe hannayensa, ta matso ya rungumesu, tare da cusa kansa cikin jikin Yusra, a wani irin yanayi ya tsinci kansa, wanda yasan idan har bai samu abinda yake so ba, komai yana iya faruwa, sauke wani irin numfashi yayi, tare da zame jiki sa a na Yusra, in Cold voice yace "my life wlhi NA KASA JUREWA, yanzu shikenan an shiga tsakanina dake har sai nan da sati biyu?"
Yai maganar murya a sanyaye,
Ɗan murmishi tayi, kafin tace "sati Uku dai" ya runtse idanunsa, tabbas tasan abinda yake damunsa, saboda har Hospital sunje watannin baya da suka wuce, hakan yasa take ƙoƙari gurin ganin ta kiyaye dokokin da aka gindaya musu, domin ya zauna cikin ƙoshin lafiya,
Cike da kallon tausayi ta bishi, tare da ajiye mimrah da tayi barci tun bayan da ya rungumesu a saman bed, kafin ta matso kusa dashi tace "Qalbi"
Lumshe idanunsa yayi yayinda ta ƙaraso garesa, sannan ya ji faɗar sunan da tayi ya sake saukar masa da kasala, saboda cikin sanyin muryarta da take hargitsa tunaninsa tayi maganar, janyota yayi jikinsa, kana ya rungumeta ya sake sauke numfashi, kafin ya zame ɗankwalin dake kanta, "Qalbi bamu da time wlhi su Momcy zasu gane" muryarsa tayi wani irin lokacin da yake ce mata, "yanzu ni da matata ta sunnah sai anyi min iyaka, gaskiya zanzo in ɗaukeki mu gudu"
Tai saurin toshe masa baki, tare da taimaka masa ya samu nutsuwa sosai..
A hankali ya ke sauke numfashi mai cike da nishaɗi, hatta mood na fuskarsa ya sauya, kana ganinsa kasan ya samu nutsuwa sosai,
Ya rungumeta yana saka mata albarka, da sauri ta miƙe taje tayi wanka, kana ta tsane jikinta sannan ta dawo gurinsa tace "Qalbi.." ya amsa mata da idanu kamar na mai jin barci, yace "wannan sunan yana yimin daɗi"
Ta yi masa murmishi tare da cewa "yanzu dai duk ba wannan ba, ka tashi ka sa kaya ka wuce wlhi zaka janyo min faɗa a gurin Momcy"
Dole hakan yayi, bayan ya kintsa, ya sa hula ya miƙe tsaye, ta wangale baki tace "wlhi kayanka sun yamutse ya zamuyi?"
Ya ɗage ƙafaɗa kana yace "karki damu, da ace ban samu honey milk ba, da ni kaina sai na zarce kayan gurin yamutsewa amma yanzu normal babu abinda ya dameni"
Tsayawa kallonsa kawai tayi, a fili tace "wato ma babu abinda ya dameka ko? baka san idan an aihu ba'a zuwa gurin miji sai anyi arba'in ba?, shikenan Qalbi ka sake yimin wani cikin" ta faɗa tana rushewa da kuka, "calm down haba wane ciki kuma, saboda shigar cikin babu wahala? Kinga ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru, ni bari in wuce, me kuke buƙata sai inyi miki transfer?"
"Zamuyi waya" ta bashi amsa tana share hawayen dake Zarya a kumatunta..
KD
Sosai take gudu har ta fita daga anguwarsu, kafin hankalinta ya kwanta, wayarta dake hannunta, ta kunna da tuni ta kasheta, hankalinta ya gushe tunaninta ya ƙare, ta rasa wa zata kirawo, kai tsaye ta saka number Sabeer, saboda ɗazu ta gogeta kuma ta haddace number a kanta, yana kwance inda ta barshi, yana kwasar barcinsa, gefensa wani glass cup ne mai ɗauke da wine a ciki, da alamu yasha ya bugu saboda wannan barcin nasa kamar ba na lafiya ba, ringing ɗin wayarsa ce ta tashesa, idanu a lumshe da ƙyar yake buɗesu ya ɗaga kiran tare da cewa yaaaa..akaaaayiiii...neeee.., murya dai sak ta mashayi, tana kuka game da toshe bakinta tace "Sabeer kaga abinda ka janyo min ko? Ga shi nan momy ta ce, sai ta kasheni "
Da sauri ya tashi zaune tare da ware idanunsa kana yace "akan me zata kasheki, tasan hukuncin wanda yayi kisa kuwa?"
Cikin daka tsawa tace "ni dallah rufemin baki, ba duk kai ka jawo ba, na biyewa daɗin baki da kuɗinka, ga shi yanzu ina ɗauke