x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 14 - NA KASA JUREWA book 1

  • 39001 words
  • 42000 words
  • Out of 86738 words

Category: Love Stories

Views 145

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
titi kana suka tari napep ya wuce dasu kasuwa, acan suka je suka siyi wayar, koda suka siya sun sami har ragin 5k saboda mai siyar da wayar saurayin Umaimah ne, kuma ɗan uwansu ne.
Chanjin da suka samu yakai dubu talatin da biyar 35.000, suka wuce gurin da ake siyarda su chocolate da su shawarma, daga ƙarshe dai sun siyi simcard canjin hannunsu ya rage saura 5000, daga nan suka wuce gidan wata ƙawar Umaimah da tayi aure sati biyu da suka wuce, sosai ta ji daɗin kawo mata ziyarar da sukayi, har ta tashi zatayi musu girki sukace zasu tafi, Umaimah ta jona wayar a chaji kafin su tafi,
Can anjima sukayi mata sallama suka wuce, ta basu cincin da dublan sukayi mata godiya, kai tsaye suka hau napep zuwa gidansu, lokacin da suka dawo ƙarfe 12:pm, dalilin da yasa basu wani damu ba, anty Tasneem ta ce musu sai 4:pm zata dawo wai ana yiwa ƙawarta kishiya shine taje gidan bikin,
Koda suka shiga gidan basu wani kula breakfast ba, ana ta zumuɗin sabuwar waya, Talatu ta sakawa ƙofar key kana ta dawo ta zauna, Umaimah ta sake jona chaji, can anjima ta ciro ta saka mata numberta tunda anyiwa simcard ɗin register da NIN ɗin Umaimah, itama ta ɗauki nata number, kana ta buɗe mata WhatsApp ta nuna mata inda ake amfani dashi, sannan tasa mata number saurayin nata tayi masa serving, kana aka sake mayar da wayar chaji,
Suna zaune suna hira, sukaji ana nocking ƙofar ɗakin Talatu tace "nasan ba zai wuce Yah Arman ba" aiko cikin sa'a tana buɗe wa ta hangoshi, parlor ya koma yana jiran isowarta, "Barka da zuwa yah Arman" tai maganar cikin dadaɗar muryarta, lumshe idanu yayi kafin yace "ina kikaje ɗazu na shigo bakya nan?" "Uhm dama Umaimah ce tace in rakata siyo kati zata kira dadynta"
Arman ya wani haɗe rai gami da cewa "duk yawan ma'aikatan dake gidannan sai kun fita da kanku, idan haka ne meye amfaninsu?"
Talatu tayi shiru, "ki kawomin abinci Please idan kuma babu ko indomie ne ki dafamin yunwa nakeji" yai maganar yana shafa cikinsa,
Kai tsaye ta wuce dinning ta ɗauko masa abincinsu, saboda Allah-Allah takeyi ya wuce, bayan ta zuba masa plate ta ɗauko fork ta ajiye masa da Black tea ɗin da anty Tasneem tayi, har zata wuce yace "ban baki izinin tafiya ba" ta wani rausayer da kanta, dole ta zauna a kujera mai kallon tasa,"acan bedroom ɗin su, Umaimah tayiwa saurayin Talatu flashing har ya kira, ta rasa inda zatayi wayar tayi ringing har sau uku bata ɗaga ba, cikin ɗaya murya tace "Aysha kizo ki karɓi waya anty Tasneem ta kira, tace in baki" Talatu tasan duk low ne ta tashi da gudu tana cewa gani nan, ƙila abinci za'a ɗora mata, da haka ta zame ta barshi a gurin,
Koda ya gama cin abinci ya mayar da hankalinsa ga kallon TV har aka kira sallahar azhar, ƙarfe1:pm ya miƙe ya fice.
Talatu na shiga ɗakin Umaimah ta miƙa mata waya, kana tace "ya kira fa, amma ni nayi masa flashing" Talatu ta dafe goshi,
Bayan ya sake kira yace,
"Kyakykyawar Zuciya tana rayuwa ne a karkashin inuwar Aminci da Amincewa,

Zuciyar da aka cudanyata da tsarkakakkiyar soyayya tana samar da ingantacciyar lafiya a gangar jikin mamallakin ta shaukinta yakan bi sassan jini dana ruwa domin cigaba da ginin gangar jiki mai'inganci so kalmar datafi komai dadin fade da saurare
shike haifar da zaman lafiya a kowane karni. Keba zinariya ba, keba luuluu ba, ke ba a zurfa ba, amma dukkanin su kinfi su kyau "
Koda ya gama rera mata nau'i'kan kalamnsa, tayi murmushi mai sauti kana tace "uhm zan kiraka da number ta, mun siyo wayar ammafa Umaimah ce ta matsa min"
Yana dariya yace, "wacece kuma Umaimah?" Ƴar uwata ce" Talatu tai maganar tana murmishi,
"Bata"
Talatu ta mikawa Umaimah, Umaimah ta karɓi wayar, tare da cewa "Barka da wannan lokacin haƙiƙa kayi sa'ar tsinto zinare daga cikin wani gu wanda mai samunsa sai mai tsananin rabo" daga can ɓangaren yace "gaskiya ina godiya bisa gudunmawar da kika bayar dan ganin soyayyarmu tayi zurfi Nagode sosai"
B"abu komai Allah ya inganta soyayyarku"
Ya amsa da amin, ta mikawa Talatu, sun daɗe suna waya har yake ce mata bata tambayi sunansa ba, ta zaro ido cike da mamaki itakam ta mance, sai da ta bashi haƙuri kafin ya gaya mata sunansa Zayden, ta maimaita sunan cikin harafi mai daɗi, wanda shi kansa sai yaji kamar tafi kowa iya ambaton sunanta, "Aysha inason kiyimin alkawarin bayan ni bazaki sake kula wani namiji ba a faɗin duniya da niyyar soyayya?" tabbas bata san menene so ba sannan ita farin shiga ce a fanin soyayya, bata san meye ƙalubalen soyayya ba, lokacin Umaimah taje ɗauko musu breakfast tace "nayi maka alkawarin, amma nima sai kayimin, yace na me "kayimin alkawarin bazaka sake kula ko wacce mace ba bayanni sannan kayi haƙuri, bazaka dinga samu a any time ba, saboda idan har aka san na riƙe waya zan iya fuskantar ɓacin rai" ta ƙarashe maganar tana marairaice murya, "calm down my beauty karki damu na shirya gwagwarmaya akan soyayyarki insha Allah sai burinmu ya cika" zan jure duk wani ƙalubale da izinin Ubangiji, sukayi sallama tare da furta mata i love You, tace love You too"
Dai dai lokacin da Umaimah ta shigo taji ana zancen love ta tuntsure da dariya, tana dukan Talatu tace "Aysha tashi Sooo"
KEFFI,
A yau ne dubban al'umma suka shaida ɗaurin auren Saudart da mijinta Alhaji Salisu Alherin Allah, lakadan ba ajalan ba, ɗaurin auren da ya samu halartar mantar shuwagabanni da governor's da ƴan siyasa harda shugaban kasa sai da yazo, kai har da turawa ƴan ƙasar waje duk sun samu halartar taron,
Acan gidansu momy kuwa ba'ayi girki ba, odar ɗinsa akayi, tunda momy ta ji Dady ya kusa zama president ta kasa zaune ta kasa tsaye, saboda bata son a sami matsala a auren, ta kwantarwa da Saudart hankali, cike da tausasa kalamai har tana cewa idan ta musguna wa mijinta Dady itama zai saketa, idan sun zauna lafiya shine farincikinta, da haka dai Saudart take daurewa, badan tana jin zata iya samun rayuwar farincikin a gurin wannan dattijon ba,
Tun gyaran jikin da akayi mata bayan fitowar ta daga gidan Ma'aruf shine, kuma har yanzu da haskenta, a jiya ƙawayen momy suka zo, har danginta sai jiya ta sanar musu, ada ta yanke shawarar babu wanda zata gayawa, kasancewar sunada hannu da shuni (dukiya) yasa ba ayi mata wani faɗa ba, da asubha wasu suka hallara, aiko an ɗurawa Saudart magungunan mata sosai, sannan a daren aka dinga turarata da turaruka masu zama jiki, Masha Allah tayi kyau, ranar bikin tasa kaya sunkai kala goma sha biyar, kuma ko wanne haura dubu ɗari uku, wasu suna cece kauce wasu kuma sunata farincikin,
A ranar da yamma aka wuce da ita gidanta dake Badiko gidane na gani na faɗa amma yana tsakiyar gidan talakawa, gidan ya mamaye anguwar, sannan ita kaɗai ce a ciki, a cewarsa ta ɗan zauna na wani lokaci kafin subar ƙasar, ko meye dalili oho,
Duk wanda ya zo kawo amarya sai ya tafi da maganar gidannan a baki, saboda kyawun gidan da yanayin tsarin gidan da ya mamaye anguwa guda, gidan sama ne mai hawa ɗaya, ƙofar shiga ma kana danna lamba zata buɗe ta gilashi ce mai ɗaukar ido, zallar parlorn ya ishi mai surutu ya je yayita zabgawa, bare a kai ga shiga asalin cikin gidan, get biyu ne a gidan, dana baya dana gaba, har da gurin shakatawa, gashi komai akwai a gidan furniture's duk Alhjin ya hana Dady ya siya komai, ya zamo nashi kawai idanu da fatan Alheri,
Zuwa dare kowa ya watse daga ita sai ƙawayenta guda biyu, wanda suka zo da amincewar momy ragowar duk ta hanasu zuwa, "daga can parlor ake ta ƙwala musu kira, suka miƙe ɗayar tace "Saudart kekam kin samu aljannar duniya saura ta lahira, nasan babu abinda zaki nema ki rasa wallahi, dan Allah kiyiwa mijinki biyayya kina gani dai gamu daga masu mashin sai masu Aron mota suzo zance gurinmu, ɗayar tace "hm Saudart Wlhi tallahi kin gama hutawa irin wannan aljannar duniya haka, ni Wlhi ko gidan da bai kai wannan ba na samu nasan zan huta bare ke kalli TV a ko ina har toilet, taɓɓ gaskiya kin zo duniya da hannun dama, daga nan suka wuce bayan sunyi mata sallama, tabbas bata taɓa mafarkin shiga irin wannan gidan ba, dadynta yanada mahaukatan kuɗaɗe duk iya yawonsu basu taɓa zuwa irin wannan gidan ba, sosai take mamakin wai yau itace a wannan duniyar?, dan wannan gidan ya wuce a kirashi da gida sai dai duniya, tunanin inda zata koyawa zuciyarta son Alhjin takeyi, saboda ta faranta wa iyayenta rai, duk da yin hakan a gurinta abu ne mai matukar wahala amma zata daure ta danne zuciyarta ta kwatanta hakan, sallamarsa taji sai da gabanta ya bada rass, lokaci ɗaya hankalinta ya tashi...!
Idan har naga comments zaku samu fiye da haka.
Mom Islam ce taku ta gargajiya ga numberta ga duk wani mai son magana dani 08141799234

*NA KASA JUREWA*
💋💋💋
💋💋
💋
_Mom Islam_


45-46

Cikin sauri ta fara ƙoƙarin gyara zaman mayafin da aka lulluɓe mata fuska dashi, kafin ta ji sautin muryarsa ɗazu tayi wa zuciyarta alƙawarin zama dashi, lokaci ɗaya zuciyarta ta raunata, cikin sanyin murya ta amsa da "wa'alaikumussalam"
Kallo ɗaya tayi masa ta cikin mayafin, kasancewar ba mai duhu bane, ta kawar da kai, tare da ƙoƙarin danne zuciyarta, "Masha Allah" ya ambata lokacin da yake kutsowa cikin ɗakin hannunsa riƙe da ledoji guda biyu manya, "sannu da zuwa" Saudart ce masa tana goge hawayen da ya fara zarya a kumatunta, tabbas shikam fuskarsa wasai take, kai kace wanda aka yiwa bushara da gidan aljanna, sai wani washe haƙora yakeyi, bayan ya ajiye ledojin a saman wani haɗaɗɗen table na glass mai ruwan golden color anyi masa ado da flowers masu kyau da ban sha'awa, ya tako a hankali zuwa inda take bayan ya amsa mata, "amarya bakya lefi, Barka da shigowa gidana, yarinya ki kwantar da hankalinki zan baki farinciki fiye da yadda kike tsammani, ina fatan zaki farantamin?" Yai maganar yana ƙoƙarin yaye mata mayafi, bata da zaɓin da ya wuce ta amsa masa, murya a hankali tace "insha Allah" sannu a hankali yake matsawa kusa da ita, har ya zo daf da ita, yana murmishi yace "tashi ki ɗauko plate a kitchen kinji, kokuma muje in rakaki tunda baki san ko ina na cikin gidan ba" ya ƙare maganar yana miƙewa tsaye, a hankali ta zuro ƙafafuwan ta da suka sha zanen lalle baƙi, kana ta gyara zaman mayafinta a kafaɗa, ya lura da kuka tayi, sbda idanunta sun ɗan kumbura, a maimakon yayi gaba ita ta dinga bin sa, kawai sai ya wani tsaya a baya yana yi mata kwatancen inda kitchen ɗin yake, dalilinsa ko na tsayawa a baya, ya kasa haƙura da maitar son ya kalleta, sai bin ta yakeyi da wani irin fitinannen kallo yana lashe baki, koda suka iso kitchen ta buɗe ta shiga, kanta kusan juyewa yayi, lokaci ɗaya ta fara tunanin shima kitchen ɗin yana cikin wata duniyar kenan, "wai wannan mutumin wane irin dukiya yake dashi, irin wannan kitchen ɗin ai ya ninka parlon gidan Ma'aruf a kyau, ya lura da tunanin da takeyi, "ɗauko mana Habibty" yai maganar cikin Muryar lallashi, "wow wannan sunan yayi mata daɗi, inama ace wanda takeso ne matashi ya aureta ba wannan tsohon ba, da ta ji daɗi wlhi,
Wani haɗadden plate ta ɗauko, wanda samun irinsu a Nigeria yana iya yin wuya, tunda kaf kayan ko cokali ma daga ƙasar waje aka kawo su, koda ta ɗauko plate ɗin zata juyo ya rungumeta, tare da cewa "muje kici abinci"
Tofa🤣
Lokaci ɗaya ta mance da wa take tare, domin idan baku mance ba, bazawara ce...

Da sauri ta dawo haiyyacinta ta turo baki tare da cewa za "meye haka?"
Alhaji yace "kam yayi da uwar ƙaton ciki yace "shauƙin ƙaunarki"
A hankali ta zame tare da wucewa ta gefensa tunda taga hanya, a saman table ɗin ta ajiye plate ɗin, kana ta koma saman gado ta zauna,
Mamaki ta bashi, sai ya nemi guri saman couch ya zauna mai zaman mutum biyu, kafin ya ɗauko ɗaya daga cikin ledojin ya buɗe guda ɗaya, soyayyen naman ɗawisu ne, a cikin wani bowl mai masifar kyau ɗan ƙarami, sai wasu kayan ciye-ciyen wanda nima ban sansu ba, "Habibty taso kici"
"Naƙoshi "
Saudart ta faɗa tana gyara kwanciyart, ita dama ba ci zatayi ba, kawai ta bishi ta ɗauko ne gudun kar ya ga kamar ta fara yi masa wulaƙanci tun yanzu,
Yoghurt ya ɗauko tare da glass cup wanda ya ɗauko acan kitchen, ya tsiyaya a cup ɗin, wanda ya ke haɗe da kwakwa da dabino da madara kai nama rasa sunan ragowar🤔, sai da ya cire babbar rigarsa kafin ya ɗauki yoghurt ɗin kana ya isa gareta, cikin sigar lallashi yace "haba Habibty ya kamata ko wani abun kisa a bakinki" itakam ta riga da tayi barci bata ma san yanayi ba, badan yaso faruwar hakan ba, ya dawo ya ajiye cup ɗin tare da zama gefen bed ya fara ƙoƙarin cire agogon hannunsa, kana ya cire rigar ciki, innalillahi lilahi wa inna ilahir raji'un, ba mutuwa akayi ba, shirgegen ƙaton cikin Alhaji na hango.
Har yakai hannu zai buɗe toilet, yaji ana nocking da ƙarfi kamar za'a ɓalle door ɗin, ɗaga kansa yayi sama, kana ya kalli makeken agogon dake manne jikin bango lokacin ƙarfe 11:pm na dare, kawar da tunanin zuwa buɗe kofar yayi ta hanyar murɗa handle na ƙofar ya shiga toilet ɗin, wow ya Subhanallah, banɗaki har TV ni mom Islam, uhm wasu na'urori ne suke sarrafa kowane kayan amfani na banɗakin, ruwan zafi ruwan sanyi da sauran abubuwa, kai harda jaridu wato drowarsu a banɗakin, nidai a tunanina idan kashi zakayi sai ka ɗauka ko?🤣hhh,
Sai da ya cire kayan jikinsa, kana ya tara ruwan wanka ya shiga ciki, lumshe idanu yayi tare da hango inama ace shi da Saudart ne a cikin wannan ruwan suke yin wanka, sai kuma ya sake jin nocking ɗin kamar ba na mai hankali ba, a gurguje ya yi wanka ya ɗauki ɗaya daga cikin towel ɗin da aka rataye su, ya goge jikinsa kafin ya fito, tare da ɗaura wani towel ɗin a ƙuginsa, fitowa yayi zuwa ɗakinsa har yanzu ana nocking, ya ɗauki jallabiya ya zura, har ya iso parlo wata zuciyar ta bashi Shawara akan ya kira mai gadi ya ji ko su waye,
Hakan ko yayi, koda ya kira mai gadi yace "masa wasu mata ne guda biyu Wlhi bai gane fuskarsu ba, thinking ya fara yi shin waɗanne mata ne zasu zo masa gida a dai-dai wannan lokacin?" Bashi da amsar tambayarsa hakan yasa shi, jingina da jikin bango tabbas ya fara tunanin anya ba Hajiya Zaliha bace?" Itama wannan tambayar da yayiwa kansa bashi da amsarta, ya yanke shawarar ya koma ciki, sam bazai bari kowa ya shigo masa gida ba, kai tsaye ya koma bedroom ɗin Saudart ya bi lafiyar gado, tare da matsawa kusa da ita, kana yayi hugging ɗinta yana sa wayarsa airplane mode.
Acan bakin ƙofa kuwa, Hajiya Zaliha ce ita da babbar ƙawarta, cike da masifa suke tsaye a gurin zuciyarta sai turiri takeyi, rai a ɓace tace "wato wannan ɗan rainin hankalin ni zai nunawa yayi aure ko?" Ƙawar Tata tace "Zaliha kawai kizo mu koma gida in ya so gobe da sassafe sai mu yi sammako mu zo" "Hadiza Wlhi tallahi bakisan irin tuƙuƙin da zuciyata takeyi yi ba, abin kunya abin takaici kamar Alhaji ya auri ƴar cikinsa, haba, sannan tunda nake dashi bai taɓa raɓar wata mace ba bayan ni, inafa zan iya barci ai kwanan zaune zanyi, ina nan anan billahillazi"
Hajiya Zaliha takai ƙarshen maganar cike da ɓaci rai da takaicin abinda Alhjin yayi, dole Hadiza ta biye mata, nan fa suka fara tunanin inda ya kamata su kwana, Hadiza tace "ai baza'a rasa ɗakin baƙi ba, barin tambayi mai gadi, Hajiya Zaliha ta dakatar da ita, tare da cewa "ni zanje dawo" fuu ta tafi gurin mai gadi tana zuwa ta riƙe ƙugu kana tace "akwai wani emtin ɗakin kwanan baƙi ne anan?" tunda ya ga yanayinsu yasha jinin jikinsa da cewar akwai wata a ƙasa, tabbas waɗannan matan akwai abinda ya kawosu, cikin daka tsawa ta sake cewa "magana nakeyi baka ce min komai ba?" "Bab...bab...bu.." yai bata amsa muryarsa na rawa, Hajiya Zaliha ta yaye mayafin dake yafe a kafaɗarta tare da yafashi a gefe ta turo ɗaurin ɗankwali gaba, kafin tace "kai sa idonka a nawa, na rantse da Allah idan baka bamu gurin kwana ba sai nayi maka tijarar da har ka koma ga Allah baka mance ba, kasan ko Ni wacece?" Ya girgiza kai alamar "a'a"
Ta kwashe da dariya, kana tace "ni matar mai gidan ce, dama nayi tafiya ne yau na dawo, nayi kiran duniya yaƙi buɗemin kuma kayana suna ciki, tunda na jima da tarewa a gidan, da yaji tsoro yanzu kam ya washe haƙora kana yace "ahh Hajiya ai kin firgitani, ai bai kamata a baki ɗakin baƙi ba, barin buɗe miki ɗakin manyan baƙi, amma ko kin kira Alhjin a waya?" Hajiya Zaliha tace "eh amma inaga yayi barci ne"
Tai maganar cikin siyasa, saboda taga yin masifar ba zai kai ta ga nasara ba.
Kai tsaye ya wuce dasu ɗakin da Alhjin yake sauƙar manyan baƙinsa, haɗaɗɗen ɗaki ne, wanda ya amsa sunansa ɗaki, ga shi an yalwatashi da kayan alatu na zamani da ƙyale ƙyalen turawa, kasancewar sun gaji gado suka haye, Hajiya Zaliha ta buɗe hand bag ɗinta ta sa car key ɗinta kana ta kwanta, koda barcin ya ɗauke su ita a wani hali ta kasance, saboda mugayen mafarkai da ta dingayi akan Alhajin da matar da ya aura, bata ƙaunar ta ji wannan lamari ya faru ko kaɗan, sam bata so, bata son Alhaji yayi taraiyya da Saudart, saboda Alhaji nata ne ita kaɗai, ƙarfe 2:am na dare ta farka cike da tarin baƙinciki da takaici mai cike da tsantsar nadamar saken
End Ads