x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 23 - NA KASA JUREWA book 1

  • 66001 words
  • 69000 words
  • Out of 86738 words

Category: Love Stories

Views 144

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ta gani a saman kujera sunkai kala tara, duk na Rukaiyyan ne, ta nemi guri kana ta zauna tare da tunani iri-iri kwance a zuciyarta.

Hotel
Tun ƙarfe 10:am Rukaiyya ta bi Sabeer ga shi yanzu har ƙarfe 4:pm bata dawo ba, hankalin Hajiya Lubabatu ya tashi sosai, saboda bata san Rukaiyya tana yawace-yawace ba,

Astagfirullah innalillahi wa inna ilahir raji'un, dan girman Allah iyayena mata mu kula, tabbas duk wanda Ubangiji ya azurta da aihuwar ƴa mace, tofa bata da kwanciyar hankali har sai ta ganta a ɗakin mijinta, bawai dan kinada budurwar ƴa ki sake mata komai ba, wlhi tallahi mu kula, ranar lahira sai Ubangiji ya tambayemu, akan tarbiyya,

Suna kwance a saman bed ya rungumeta, ga dukkan alamu babu kaya a jikinsu, hankali kwance suke barcin, Ruqaiyya ce ta fara farkawa, da sauri ta sauko daga gadon tare da wucewa toilet tayi wanka ta tsarkake jikinta, kafin tazo ta fara tashin Sabeer, a hankali ya buɗe idanu tare da cewa "Ruky karki damu fa.."
"Wane irin kar in damu har ƙarfe biyar da rabi tayi, ka kalli agogon dake jikin bango ka gani mana, idan momy tazo ai na shiga uku wlhi sai ta kusa kasheni"
Ruqaiyya ta faɗa tana yayibo ƙaton hijabinta da hand bag ɗinta, da sauri ya tashi, cikin sauri shima ya shiga toilet ɗin, tare da yin wanka kana ya fito, ko mai bai shafa ba, ya sanya kaya yayi mata rakiya suka fito har harabar hotel ɗin, "ban gane ba mai kake nufi?"
Ruky tayi masa magana saboda ta fahimce bazai mayar da ita gida ba, "kinga kiyi hakuri Wlhi barci nakeji sosai, kinga a irin wannan condition ɗin bai kamata inyi driving ba, sai mu samu matsala"
Ya ƙarashe maganar yana ɗaga mata gira,
"Uhm Sabeer ni zaka wulaƙanta, a lokacin da ka buƙaci jikina ɗaukoni kayi har nan, bayan ka biya buƙatarka sai ka watsar dani ko?, kana nufin sai gobe kuma idan ka sake jin wani jarabar sai ka nemeni?"
Tayi maganar tana zubar da hawaye, kafin ya buɗe baki yace mata wani abu, har ta buɗe get ta fice da gudu, tana kuka, tafiya take tana cewa "tabbas Allah ba azzalumin kowa bane, na cutar da kaina wayo Allah, bansan mai yasa Sabeer ya lalatamin rayuwa irin haka ba, innalillahi wa inna ilahir raji'un, ta dinga mai-maitawa tana kuka, sai da ta gaji da tafiya, kafin ta tsari mai adai-daita ya kawo ta har ƙofar gida, koda ta fara buga get ɗin kamar zata cireshi tsabar bugu, saboda gabaki ɗaya bata cikin nutsuwarta, mai gadi ya taso zai yi masifa ya ga itace ai yayi gum da bakinsa, da gudu ta shiga gidan tana ci gaba da kuka, har ta shigo parlon momynta tana cigaba da gunjin kuka,
Momyn ta fito da sauri kana ta kalli Rukaiyya tare da cewa "Rukaiyya ina kikaje me kuma ya faru?"
Bakinta ta toshe da tafin hannunta tana kuka,
Cikin daka tsawa tace "ina kikaje?"
Muryarta na sarƙewa tace "mo..mo...momy, na...na...naje, islamiyya ne, shine malaminmu ya ce ya koremu"
Momy ta nemi guri ta zauna, kafin tace "amma ai baki gayamin zakije ba"
Tana shesheƙar kuka tace "momy Ummu ce tazo bayan fitarki tace wai yau akwai islamiyya, kai tsaye momy tace "toh shikenan"
"Mai ya haɗaki da Yarinyar nan, na ganta a can kusa da bakin titi, ko da na tambayeta, na nemeta na rasa ta gudu?"
Zaro idanu Rukaiyya tayi, kafin tayi yunkurin bata momy amsa, cikin rashin tsammani amai ya taho mata wanda ita kanta bata san da zuwan aman ba, "innalillahi Rukaiyya dama baki da lafiya ne"?
Ta jefo mata tambaya, tana miƙewa da sauri ta kawo ruwa a cup kana ta shafa mata a fuska, sannan ta riƙe hannunta suka shiga toilet, ta wanke baki, acan toilet ɗin ma tayi amai sosai, lokaci ɗaya jikinta ya fara karkarwa, cikin sauri momy ta ɗauko mata rigar sanyi, tare da cewa "Rukaiyya mai yake damunki?"
"Uhm momy wlhi zazzaɓi ne"
Momyn ta fice da sauri tana ƙwalawa mai gadi kira akan ya kira mai mashin,
Bai daɗe da fita ba, sai ga shi nan ya shigo tare da mai mashin ɗin, ta riƙe hannun Rukaiyya suka fito harabar gidan, momy ta miƙa mata hijab ta saka, kana ta hau mashin ɗin momy ta hau bayanta suka wuce Hospital,
Sai da suka fara ganin likita, akayi wa momy tambaya "tun yaushe ta fara rashin lafiyar?" Momy tace "yau ne ta dinga amai"
Doctor yace za'ayi mata test, momy tace babu komai,
Bayan an ɗibi jininta aka bata wata roba tayi fitsari a ciki, kana aka ce suje su zauna kafin su jira result sai asan taimakon da ya dace a bata, sun ɗan jima a saman benci a zaune, doctor ya ƙwalawa momy kira, bayan ta zauna yace "tanada aure ne?" Momy tace "bata da aure yarinyar da ko samari bata da su" doctor ya jinjina kai kafin ya fara sosa kansa, saboda ya kasa yi mata bayanin abinda ke faruwa, cikin tuhuma momy tace "doctor lafiya naga bakinka yana ta motsi kamar kana son cewa wani abu?"
Doctor ya ajiye pen ɗin dake hannunsa kafin yace "Hajiya idan yarinyar ki ce, tanada cikin wata biyu, idan baki yarda ba zaki iya zuwa wani Hospital ɗin.
Tun da ya fara magana momy ta daskare a gurin, lokaci ɗaya jikinta ya fara karkarwa, da sauri ta ce "Doctor ciki fa kace?"
Doctor ya sake gyaɗa kai, "Nagode nawa ne kuɗin?"
Ya gaya mata ta bashi sannan ta fice da sauri, "Rukaiyya tashi mu je gida"
Momy ta faɗa tana kallon Rukaiyyan, kafin ta miƙe, momy ta rigata yin gaba, sboda jikinta babu ƙarfi sosai, momy na fita a hospital ɗin ta iso bakin titi, hankali a tashe, Ruqaiyya na zuwa suka hau mashin suka dawo gida, bayan sun shigo parlorn Ruqaiyya ta nemi guri a 3sitter kana ta kwanta, sboda kasalar da takeji, sai da momy ta wuce ɗakinta tasha kuka mai isarta kafin ta fito parlor, "Ruqaiyya tashi zaune"
Momy ta faɗa a taƙaice,
Ruqaiyya ta tashi zaune kamar inda momy ta buƙata, "waye yayi miki ciki, ashe dama yawon banza kike zuwa?"
Momy ta jefo mata waɗannan tambayoyin, ƙirjinta ne ya bada rass, ta dafe ƙirji kafin tace "haba momy kinfi kowa sanin wacece ƴarki, wlhi bana bin kowa hasali ma ko saurayi bana..."
Momy ta gwaɓe mata baki tare da cewa "wlhi tallahi idan har baki gayamin wanda yayi miki ciki ba, sai na kasheki"
Da sauri ta zabura, kafin momy tayi wani yunƙuri ta ɗauki wayarta ta gudu, kasancewar get ɗin abuɗe yake, ta fice.
Momy ta ɗora hannu a kai tare da kurma ihu, tsananin baƙinciki da takaici yasa ta kasa furta komai, a gurin ta durƙushe tana kuka, a halin yanzu bata san wa zata ta ra da wannan maganar ba, waye zai fahimceta?"...
      *****
Har yanzu tana emergency room bata san inda kanta yake ba, shiko yana zaune a office ɗin doctor, kasancewar doctorn abokinsa ne, yayi tagumi cikin wani irin yanayi, sai mai-maita Innalillahi wa inna ilahir raji'un, gabaki ɗaya ya gama rikicewa saboda tunaninsa yarinyar da ya bige bazata rayu ba, mutuwa zatayi, duba da jinin da ya zuba daga jikinta mai yawa sosai, Doctor yace "Prince Murad ka kwantar da hankalinka da izinin Ubangiji komai zai zamo normal"
Prince Murad ya miƙe tsaye, sanye da Kayan sarauta, tsantsar cikar kamala da izza gami da ruwan sarauta duk sun yalwatu a jikin Prince Murad, "Allah ya bata lafiya" ya faɗa yana ficewa a office ɗin, doctor ya amsa da amen"
Dama dogarensa na daga bakin ƙofa, suna ganin ya fito, suka zube a gurin suna miƙa jinjina,
Ransa a ɓace yake, saboda ko kaɗan baya fatan ya ga ya wulaƙanta wani ɗan adam a doron duniya, burinsa kyautatawa al'umma,
Kai tsaye haɗaɗɗiyar motarsa ya shiga,  drivernsa  ya rufe murfin motar, ganin haka yasa dogarai suma suka shiga tasu motar, Prince Murad yace kaini "gurin Umma"
Kai tsaye suka wuce garin MANDU, har cikin gidan sarki suka shigar da motar, inda sukayi parking a inda aka tanadarwa motoci, bayan an buɗewa Prince Murad murfin mota ya sauko da ƙafarsa ɗaga, kafin ya sake sauko da ɗayar ƙafar, yanayin takunsa kaɗai ya isa ya tabbatar maka da ko shi waye, yana tafe dogarai na biye dashi, ko da yazo shiga babban parlon Sarauniya, tsayawa sukayi daga bakin ƙofa, tafiya yakeyi ko gabansa baya kallo, saboda tsananin ɓacin ran da yake ciki, bai yi tunanin kiranta a waya ba, har ya wuce parlon bai san da cewar Sarauniyar na zaune a parlon ba, hadiman ta suna ganin Prince Murad suka duƙar da kansu ƙasa, "Murad lafiya na ganka cikin wannan yanayin?"
Sarauniya ta tambayesa, tana daga kishingiɗe a saman wata kujera mai kama da katifa tsabar taushi, da sauri hadiman suka fice, suna cewa "Allah ya taimakeki Allah ya ƙara Miki lafiya, mun barki lafiya" a hankali ya juyo cike da sarauta, kafin ya zo gabanta ya nemi guri ya zauna a saman Capet, kana yace "Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana Umma na kusa kisan kai, a halin da ake ciki ma, wlhi bansan zata rayu ko bazata rayu ba oho" a ɗan firgice ta tashi zaune tare da gyara zaman alkyabbar dake jikinta, kafin tace "Murad mai kake nufi ban gane ba?"
Idanunsa sun kaɗa sunyi jajir yace "Umma muna cikin tafiya a mota, Umar driver ya kaɗe wata yarinya tana can rai a hannun Allah, Umma yanzu idan har yarinyar nan ta mutu ya zamuyi?"
Sarauniya tace "Murad ka kwantar da hankalinka, komai fa ikon Allah ne, shi yake raya wanda yaso sannan ya kashe wanda yaso, yanzu dai waye a gurinta?"
Kan Murad a duƙe yace "Allah ya taimakeki, Falmata ce a gurinta"
Sarauniya ta jinjina kai, sannan tace "ya kamata kaje kayi wanka kaci abinci, saboda kar ulcer ɗinka ya tashi, idan baka manta ba, doctor ya ɗoraka akan magani sannan yace "ba'a son ka ji yunwa komai ƙanƙantar ta?" ya miƙe tare da fita daga sashen mahaifiyar tasa kafin ya wuce sashen sa, wani haɗaɗen ɗaki ya shiga ko ina walwali yakeyi Masha Allah, a kujera one sitter ya zauna, ya fara tuno irin hatsarin da sukayi, yana tsaka da tunani, Ruma ta shigo fuskarta ɗauke da murmishi, ko sallama babu ta yiwa kanta mazauni, kafin tace "yaya Murad lokaci yayi da zamu fito mu faɗawa mai martaba da Umma cewar mun shirya a ɗaura mana aure.." da sauri ya kalleta, kallo yakeyi mata mai cike da zallar tsana, ransa a ɓace yace "tashi ki fita.. ta wani matso kusa dashi tare da cewa "ko kanaso ko bakaso aurena ya zame maka tilas ragowar jiji da kai da taƙama duk zanji dasu, nidai burina..."
Kafin takai ƙarshen maganar ya wanka mata mari lafiyayyu masu zafin gaske, wanda yasa ta riƙe kumatunta, tare da ficewa da gudu, tayi sashen Fulani...!
Comments and share fisabilillah
Mom Islam ce 08141799224

NA KASA JUREWA*
💋💋💋
💋💋
   Book
Page 63-64

Kuyi following ɗina Arewabook
https://arewabooks.com/u/momislam11

                 _Mom Islam_

A hankali ta fara motsa hannayenta, tare da yunkurin tashi zaune, tsananin zafi da raɗaɗi ne sukai mata sallama, saboda duka jikin nata ciwo yakeyi mata, in ka cire goshinta da ya sha ɗauri, "yi haƙuri insha Allah zaki samu lafiya"
Wata likita tayi mata magana cikin tausasa harshe,
Tabbas tasan lokacin da ta zata tsallaka titi, bayan nan babu abinda zata iya tunawa sai ganinta da tayi a asibiti, meke faruwa da ita?,
Kuka ta farayi tare da mutsu mutsu, wanda yasa ta kusa tsige drip ɗin dake hannunta, likitoci biyu ne a ɗakin hakan yasa suka riƙeta sosai, tana ta kuka, tana cewa "nikam na haƙura da rayuwar binni wlhi gara in koma gurin mahaifiyata wayo Allah na zan mutu waiyyo Allah..."
Duk waɗannan maganganun da takeyi, a kunnen Prince Murad ta yisu, ba kayan ɗazu bane a jikinsa ya sauya wasu, sai dai a sama akwai wata ƴar riga mai tambarin gidan sarauta a jiki, ga dukkan alamu bayan yayi wanka ne ya dawo Hospital ɗin, cikin takunsa mai ɗaukar hankali ya shigo room ɗin tare da amsa gaisuwar likitocin da sukayi masa, "ya jikin?"
Ya tambayeta cikin dakakkiyar muryarsa,
Waro idanu tayi, kafin tace "da sauƙi, kana ta mayar da kai ta kwanta, ammafa abin ya bata mamaki, gani takeyi kamar wani ɗan gidan sarauta ne, sboda sunsha zuwa kallon al'adun sarakuna da akeyi a ta wajajen ƙauyukan su, "mai kike da buƙata" Prince Murad ya tambayeta"
Duk da raunin dake a goshinta bai hanata yin murmishi ba, a zuciyarta tace "wannan fa wata dama na samu da zanci abinda zuciyata takeso"
"Kaza nake son ci wlhi idan da hali kace asa yaji sosai, amma kayi haƙuri idan baka da kuɗi ko kifi ka siyomin"
Tayi maganar tana runtse idanu, sabida lokaci zuwa lokaci jikin nata kan ɗan yi mata zafi,
"Shi kenan" ya faɗa yana miƙewa kana ya fice, dogarai suka ci gaba da binsa tare da securities, acan harabar asibitin ya hango Falmata tana tsaye tana waya, ga dukkan alamu wayar da takeyi tanada muhimmanci, tabbas yin hakan da tayi ya sosa masa zuciya, an bar mai jinya ita kaɗai, hakan bai dace ba,
Bayan komawarsa gida, a harabar gidan, ya tarar da Umma wato mahaifiyarsa matar sarki  tana shirin shiga mota, sai da ta jira ya fito, tayi masa ya mai jiki, kafin tace masa Hospital ɗin zataje sboda ta dubo jikin yarinyar" Prince Murad yace "Allah ya ƙara miki lafiya, godiya nake Ubangiji ya kaiki lafiya ya dawo dake lafiya, Allah ya tsare gabanki da bayanki ummana, sosai take ƙara jin son ɗan nata guda ɗaya tilo wato Murad a cikin ranta, saboda nutsuwarsa da hankalinsa,  yayi mata Allah ya tsare ta shiga mota suka wuce.
Har motarsu ta ɓacewa ganinsa yana tsaye a gurin, ya sanya hannu a aljihun rigarsa ya ciro wayarsa, number drivernsa umar ya kira, bayan ya ɗaga yace masa, inason ka koma Hospital yanzu, amma kafin kace, ka siya mata kaji guda uku masu kyau sai ka kai mata, ka haɗa mata da lemun kwalba kokuma dasu fruit"
Cike da girmamawa driver Umar yace "an gama ranka ya daɗe, abinda kace shi za'ayi Allah ya ƙara maka lafiya"
Ya amsa da Amin.
Acan Hospital, tun da Gudidi ta farka bata sa wata Falmata a idanunta ba, tunda bata san ma itace mai jinyarta ba, ko da ta ga, Prince ya fita, ta cuno baki, tare da cewa "mtswww a sawa mutum rai da abu sai ya gama ammanna sannan a yaudarehi"
Sallamar da taji anyi tare da turo ƙofar ne yasa ta sake ware idanunta tana ƙare wa Sarauniya kallo, tana cikin shiga ta alfarma wacce duk wanda ya ganta sai yayi sha'awar sake ganinta, sanye take da farin leshi mai adon duwatsu masu sheƙi, ta sanya alkyabba daga sama, ƙarasa shigowa sukayi itada jakadiya, hannun jakadiyar riƙe da wani babban basket mai kyau, ta ƙaraso tare da ajiye wa a can nesa da gadon da Gudidi take kwance, "ina wuninku"
Gudidi ta faɗa tana rarraba idanu,
Umma ta amsa da "lafiya lau ya ƙarfin jikin?"
Gudidi tace "yai sauƙi, amma yunwa nakeji"
Umma tayi murmishi tare da cewa "Masha Allah, jakadiya a tambayeta mai takeson ci"
Umma ta miƙe tare da fita waje, kira ne ya shigo wayarta, da alamu kiran yanada muhimmanci, "ranka shi daɗe, Barka da wannan lokaci"  Sarki ya amsa da cewa "yauwa ya mai jikin, da sauƙi dai ko?"
"Eh da sauƙi ina tunanin zuwa anjima a sallameta, sboda naga jikin nata alhmdulilah"
Umma ta tabbatarwa da mai martaba,
"Cikin bada umarni yace "idan an sallameta a taho da ita nan, ta huta kafin.."
Ya katse kiran.
Kai tsaye ta kira Prince, ta sanar masa da umarnin da mai martaba ya bata, shima yayi na'am, sukayi sallama ta katse kiran.
Cikin umarnin Umma jakadiya ya bubbuɗewa Gudidi foodflaks, kafin tace "wanne kike son ci?"
Waro idanu tayi, cike da nuna ƙauyanci tace "duka ma zanci, amma dai ki fara zubomin farfesu" jakadiya ta ɗauki plate kana ta zubo mata farfesun sannan ta miƙa mata,
Ci ta farayi hannu baka hannu ƙwarya, abin har yaso bawa jakadiya tsoro, da sauri ta matsa kusa da gudidi tace "akwai  abin da kike da buƙata ne bayan wannan?"
"Eh ai komai ma zanci kedai miƙomin waccan tuwon hinkafar, malmala biyu"
Jakadiya ta zaro idanu, dole ta saka mata, tunda umarni aka bata,
Kamar inda ta ɗauki alwashin cin duk abinda ke cikin basket ɗin, aiko sai da taci, kaɗan ta rage, sallamar Umar driver ne yasa tai saurin goge bakinta, sbda tayi dumu dumu da manja, bayan ya gaishe da jakadiya ya wuce gurin Gudidi, yayi mata ya jiki, ta amsa kana ya ajiye ledar a saman loka, yace "kaji ne, inji Prince yace a kawo miki" Allah ya taimakeni an cire ruwan baturen da ake ɗura min" ta faɗa tana saukowa ƙasa, sai dai babu takalmi a ƙafarta, hakan bai saka ta damu ba, ta zauna a saman tabarmar dake shimfiɗe a gurin, kafin tace "kai wlhi kunada kirki Nagode sosai, tai maganar tana buɗe ledar jikinta har yana rawa, wasu manya manyan gasassun kaji ta hango, sai ƙamshi sukeyi, a hankali ta haɗiyi miyau, tare da cewa "uhm yasin zagina sukeyi, hikenan sabuwar duniya" ta faɗa tana yagar naman kazar, tunda ta tauna taji ya cika mata baki, ga daɗi ga garɗi, ta wani lumshe idanu, tare da kallon Umar tace "kai wlhi ka yimin hajji da Umrah, dan Allah kace masa na gode"
Umar yayi murmishi tare da cewa "karki damu"
Jakadiya kam, taga ikon Allah, sboda Gudidi ta fara bata tsoro, duba da yanda take ta zura abinci sai kace ba mutum ba, daga can  harabar asibitin Ummar ta wuce office ɗin doctor, ta lura da Falmata ba zama gurin mai jinya bane ya kawota, saboda ta samu labarin ta koma gida,
Ya tabbatar mata da anjima za'a sallameta, already akwai wani ɗaki empty, Umma ta saka a gyara shi, duk da koda yaushe basa wasa da gyara ma'aikatan gidan, daga nan ta dawo ɗakin da aka kwantar da Gudidi, sallama tayi, suka amsa kana ta ƙarasa shigowa, "alhmdulilah ta ambata tare da cewa ,jiki yayi kyau, Masha Allah"
Jakadiya tace "ai kuwa, nikam Allah ya taimakeki har gabana yana lugude" Umma tace "name fa?"
"Hmm kaf abincin da aka kawo duk ta cinyesu har da kaza Umar ya kawo inji yarima ta kusa cinye guda ɗaya"
Umma tayi murmishi, ba tare
End Ads