x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 28 - NA KASA JUREWA book 1

  • 81001 words
  • 84000 words
  • Out of 86738 words

Category: Love Stories

Views 136

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
fassara.
Acan fada, Akwai wasu dattijai waɗanda suka zamo masu bawa mai martaba shawara, sosai suka zamo Amintattunsa
Cike da izza da kamala mai martaba ya fara magana yana daga zaune a kyakkyawar kujerarsa wanda gabaki ɗaya gidan an zaneshi da tambarin sarauta,
"Ina son asa ranar auren Murad da Ruma, nan bada jimawa ba"
Wani dattijo yace "ran Sarki ya daɗe Allah ya ƙara girma Ubangiji ya tsare ka daga dukkan sharri, abinda kace shi za'ayi"
Kan kace me, labarai sun isa ɓangarori biyu, ɓangaren Fulani da kuma ɓangaren Gimbiya, cike da ɓacin rai Gimbiya ta miƙe tare da cewa "tabbas anzo gurin, gaskiya bana fatan haɗa zuri'a da Fulani, mai yasa mai martaba zai yi haka?"
Shigowar Prince Murad kenan ya tsinkayo maganganun Gimbiya cikin fushi,
Cikin ƙanƙanin lokaci ya birkice, saboda ya ji maganganun da Umman tasa take yi, Hadimanta suka tashi suka bata guri, domin ta gana da ɗanta ɗaya tilo,
Zagaye ɗakin Gimbiya ta fara yi, tare da ɗaga kai sama cikin fushi tace "Murad tabbas wannan hukuncin beyi min daɗi ba, mai yasa mai martaba ba zai yi shawara dani ba?"
Murad ya zauna a saman couch domin kuwa ƙafafuwansa sun gaza ɗaukarsa, yace "Umma shin da gaske ne mai martaba zai haɗani da Ruma?"
Yai maganar cikin yanayi na damuwa, "tabbas Murad kasani idan har mai martaba ya yanke hukunci babu wanda ya isa ya sashi saɓawa, dan haka kawai kayi masa biyayya, saboda yana girmama duk abinda ɗan uwansa ya bari, nima kaina banji daɗi ba, babu inda zamuyi kayi haƙuri karka nuna ɓacin ranka bare har akai ga labari yaje wa mai martaba"
Kansa a sunkuye yake saurararta, shiɗin mai biyayya ne, amma baya jin zai iya karɓar Ruma a matsayin matar da zasuyi zama na har abada,
Wunin ranar Prince ya rasa abinda yake yi masa daɗi, acan part na Fulani abin ya birgesu, saboda babban burinta ƴarta ta auri Murad ko babu soyayyarsa a cikin zuciyarta, gashi buƙatarsu ta biya tun ba aje ko ina ba, tabbas wannan rana ta zame musu abin alfahari abin kwatance domin kuwa har sun fara tsara yanda shagalin bikin zai kasance..,

Kano
A ƴan kwanakinnan barci yayiwa idanunsa ƙaura, babu wacce yake muradin gadi da ya wuce Aysha, sosai yake jin zuciyarsa tayi masa ƙunci, hatta iyayensa ma sun kasa gane masa, har wata ƴar rama yayi, fuskarsa tayi fayau,
Babbar damuwarsa ya za'ayi yaji koda muryarta ne, ko zai samu sassauci daga ciwon soyayyarta da ya addabi zuciyarsa, badan ya shirya zuwa gidan anty Tasneem ba, ya fice a motarsa, saboda baya zuwa idan har Junaid ya dawo, koda ya shigo cikin gidan, nocking ya dingayi, ya jima yana tsaye, badan uzirinsa ne ya kawosa ba, da tuni ya cikawa rigarsa iska, Junaid ne ya buɗe ƙofar tare da fitowa, cike da fara'a ya miƙawa Junaid hannu, suka gaisa, Junaid ɗin yace ka shiga tana ciki, dama yayi shirin fita ne, zai mayar da Umaimah gida, yau kwanansa ɗaya da dawowa, Allah ya kiyaye hanya yayi masa kana ya wuce ciki, ya samu Umaimah na fitowa, hannunta riƙe da jakar kayanta anty Tasneem tana ce mata ta gaida su Hajiya, sai sunyi waya.
Bayan ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun mai zaman mutum ɗaya, ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya kafin yace "anty Please kizo ki sallameni"
Anty Tasneem ta nemi guri ta zauna kafin tace "Arman ina saurarenka?"
"Anty dan Allah ki taimakawa rayuwata zuciyata tana daf da fashewa na rantse miki da Allah anty ina son Aysha, tun daga ranar da na fara sanyata a idanunsa, har kawo yanzu wlhi bazan iya daina sonta ba, gashi yana neman yimin illah" sosai ta hango tsagwaron gaskiyarsa a ƙwayar idanunsa, tabbas yana sonta, saboda ko itama ta zargi hakan, sai dai bata furta ba, itafa abin ya ɗaure mata kai, tace masa "Arman yanzu mai kakeso?"
Murya kamar zai yi kuka yace "anty dan Allah kije ki nema min izinin yin hira da ita, kokuma kisan inda za'ayi in dinga jin muryarta wlhi zan iya shiga wani hali idan har ban samu Aysha ba"
Ajiyar zuciya ta sauke tare da riƙe baki kana tace "taɓɓ hmm Arman ka manta ko wacece Hajiya mama?, in tashi daga nan in tafi Abuja in dawo raina a ɓace?, sai dai zanyi maka abu ɗaya, zan kira anty Jamila idan har wayar ta shiga zance a bawa Aysha mu gaisa idan na gaisa da ita zan baka sai ku gaisa, amma wannan maganar kam a WhatsApp zanyi da anty Jamila" sai yanzu yaji zuciyarsa ta fara sanyi,
Neman guri tayi ta zauna, kafin ta kira anty Jamila tace "Arman wai ma tukunna kasan me kake faɗa kuwa?" Aysha kwata-kwata shekarunta 14yrs ne fa?" Ya katseta da cewa "anty wlhi ko goma ne zan iya aurenta"
Anty Tasneem tace "tabbas ka samu taɓin hankali wlhi ba za'ayi wannan haukar dani ba, ƙaramar yarinya? ai ni su Hajiya zasu bawa rashin gaskiya gaskiya Arman bazan iya ba, ka sauya shawara, kokuma ka bari idan ta sake girma tunda girman ɗan mutum babu wuya"
Tai maganar tare da sauya yanayin fuskarta zuwa ɓacin rai, "Allah sarki anty wato bakisan abinda nake ji bane da har zaki yanke min wannan hukuncin"
"Hmm Arman ga ƴan mata nan da yawa, ka tsaya bata lokacinka akan wata Aysha da ko two weeks batayi da fara period ba?"
"Nidai ita nakeso kuma zanje Abuja a satinnan wlhi"
Ya faɗa yana miƙewa tsaye da sauri ya fice a parlorn ransa a ɓace...

Bikin bidiri Zyd a Abuja Arman a Abuja hhhh yanzu wasan ya fara

Mom Islam 08141799224

*NA KASA JUREWA*
💋💋💋
💋💋
💋

_Mom Islam🍹_

Kuyi following ɗina Arewabook zaku samu more pages ga link nan 👇
https://arewabooks.com/u/momislam11


Page 77-78
KEFFI
Dady ne zaune a gaban boka, yana labarta masa nasarorin da ya fara samu, tunda yayi wanka da ruwan jini,
Cikin Muryar mai ɗauke da ƙaraji boka yace "nasara yanzu ka fara ganinta, sannan komai zai ci gaba da tafiya yanda ya kamata"
Cike da samun ƙwarin gwaiwa Dady yace "godiya nake" ya ajiye wa bokan wata ƙatuwar jaka mai ɗauke da maƙudan kuɗaɗe kana ya miƙe yana yi masa sai anjima, boka yace "duk halin da ake ciki su dinga yin waya.."

Zaɓe ya rage saura wata biyu, daga Dady har momy babu zama, shi yana neman inda zai cigaba da samun ƙarɓuwa a gurin mutane, ita kuma tana son ta mallakeshi, ta kowace hanya, na duk abinda tace sai yayi mata shi.

Haka dai rayuwa taci gaba da tafiya anyi primary Election anci nasara, duk wani Election Dady ne a first, saboda ya samu magoya baya sosai da sosai, domin kuwa ya ɓarar da Naira tare da jinin al'umma, shikam ba a gurin ubangiji yake neman dacewaba, a gurin boka yake nema.

Gidan Dady ya kasance cikin tsaro koda wane lokaci, tun kafin ya zamo shugaban ƙasar ma mutane suka daina sashi a idanunsu, domin kuwa ya tafi ƙasar waje, hatta ita momyn uzuri takeyi masa saboda su samu abinda suke so.

Acan fanin anty Hadiza, sun tafi Dubai ita da ƴarta da mijin Salma zai aure wato Junaid,
Siyayya suka dinga yi kamar na hauka, saboda Junaid ya tabbatar ma da hindu yana dawowa daga Kano, zai turo iyayensa, yafi son ayi komai a gaban idanunsa, 2weeks suka kwashe kafin suka dawo Nigeria, washe gari Iyayen Junaid suka zo gidansu Hindu nema masa aurenta, cikin mutuntawa sukayi komai da tsari tare da girmama juna, sha tara ta arziki anty Hadiza tayi musu, manya manyan kaji anty Hadiza tasa hindu ta soya musu, akayi musu cake da kunun gyaɗa mai daɗi, tare da shinkafa da miya, bayan sun ci sunsha anyita yin raha da wasa da dariya, aka yanke wa iyayen Junaid dukiyar aure, dubu ɗari bakwai aka yanke musu, sai suka bada, 1million kasancewar su ɗin masu hali ne, sosai, haka ma mijin anty Hadiza shima yana da nasa halin dai-dai gwargwado saboda baza'a kirasa da talaka ba, a take a gurin aka saka rana wata ɗaya,
Bayan tafiyarsu, baban Hindu ya mayar wa da Anty Hadiza inda sukayi, har rawa sai da tayi tsabar farin ciki, tana cewa "ashe zanga aurenki hindu?, idan kana da ƴa mace muddin baka aurar da ita ba, kana cikin fargaba, yau dai Allah ya yanke miki wahala Hindu, yarinya kamarki shekaru 34yrs talatin da huɗu wasa ne?"
Baban Hindu yace "dama komai da lokacinsa, idan ka miƙawa Ubangiji lamuranka, sai kaga komai ya zo maka da sauƙi cikin sassauci, dama shi muke roƙo kuma gashi ya amsa mana" baban Hindu yace "ku samu paper da pen ku rubutomin duk wani abu da za'a buƙata ni zan fita"
Anty Hadiza tace "to baka da matsala" yau dai sun kasance cikin farin ciki, idan ka cire hindu da ta rasa inda zata tsoma kanta tsabar farinciki.
Hajiya Zaliha ce zaune a parlor ita da Salma, Dan tunda Junaid yayi tafiya ta dawo gidan suna ta jajantawa juna,
Wayar Salma ce ta fara ringing, suna cikin magana da mahaifiyarta, ta janyo wayar kasancewar tana ajiye a gabanta saman table, a kunne ta kara bayan ta danna kore, lokaci ɗaya walwalar fuskarta ta ɓace ta fara haɗa gumi, cikin sauri ta janyo mayafinta tana fifita, sai kuma ta miƙe tsaye a zabure cike da masifa tace "wlhi tallahi yau akwai kutumar bura uba, ni anty Hadiza zata cutar?" tai maganar tana ajiye wayar,
Cikin sauri Hajiya Zaliha ta miƙe tsaye tare da yi mata alama da hannu "mai ya faru?"
Salma na sauke numfarfashi tace "momy anty Hadiza wlhi tallahi ta cuceni ta gama da rayuwata, Junaid har ya kaiwa ƴarta sadaki bani da labari, yanzu ƙanwarsa ya kirani take gayamin, ta janyo mayafi zata fice da sauri, Hajiya Zaliha ta riƙo mata hannu kafin tace "wato Salma ita duniya dama haka take, wlhi ni dama hankalina gabaki ɗaya bai gama kwantawa da wannan muguwar matar ba, wato tanan ta ɓullo, wallahi idan har zan ƙarar da duk abinda na mallaka akanta billahillazi sai na sa ta shiga taitayinta, kokuma ni ban cika ƴar halak ba, Salma ki kwantar da hankalinki, abinda nake so dake... Ki aiyyanawa ranki cewar, labari aka baki bai tabbata ba, idan har ina numfashi bazaki haɗa miji da wata ƴa mace ba, sannan Junaid naki ne har abada"
Cikin faɗa da tashin hankali gami da tsananin ɓacin rai mahaifiyar tata take maganar, Salma ta durƙushe a gurin tana kuka, cikin muryar kuka take cewa "momy Meye bana yi masa, ga shegiyar jaraba koda yaushe a cikin yin wankan tsarki nake, haka nake daurewa amma yace zai..." Ta sake fashewa da kuka, sosai mahaifiyar Tata, ta lallasheta kana tayi shiru.
SAUDIYYA
Idan kaga gidan nasu sai ka rantse ba hannu ne ya gina shi ba, saboda kyau da tsari, kasancewar ginin irin na turawa ne, babban parlor ne mai ɗauke da ɗakuna sunyi bakwai, ko wanne da abinda ake sawa a cikinsa wani mutane ne a ciki, zaune suke a parlor shi da Mahaifiyarsa da ƙanwarsa da akayi mata tiyata ta warke, Umminsa tace "Thabit ya maganar ƴan matan da muka yi magana dakai kwanakin baya kace zaka cetosu?" Thabit ya dafe goshinsa kana yace "ummi tunkarar Oga Reed ba abu bane mai sauƙi, nidai yanzu abinda nake buƙata adu'arki tare da fatan nasara" Ummi ta kai lallausan tafin hannunta ta shafi kwantaccen baƙin sumar da yayi luf a kansa, kana tace "insha Allahu bazaka taɓa shiga musifa ba" ya haɗe hannunsa da nata yace "amin ya rabbi Ummina"
Ummin tace "Thabit Ubangiji yayi maka baiwar da ba kowane ɗan Adam yayiwa ba, Kanada damar da zaka taimaki waɗannan bayin Allahn bansan mai kake jira ba?" Ummi tunda har kinyi min adu'a insha Allah zan sake sabon shiri in koma, ammafa Ummi idan na samu wanda sukayi min gardama tabbas bazan taho dasu ba"
Ummin tace ta amince,
Yace "nan da kwana bakwai zan je Singapore, dalilin da yasa zan bari sai zuwa one week, zan dai daici lokacin da aiki yasha masa kai, Ummi ƙazantar rayuwar da sukeyi acan wlhi babu kyan gani, ni kaina badan dole ba, wlhi ba zan raɓesu ba...
Tofa, gadai Thabit ya fara shirye shiryen zuwa taho da ƴan gidan oga Reed.
ƘAUYE
Tun bayan tafiyar Gudidi Ramma ta gamu da wani irin ciwo, wanda ta rasa inda kanta yake, saboda Allah ya ɗora Mata son Gudidi kasancewar su biyu kawai ta haifa, da Gudidi da ƙaninta, a halin yanzu kullum suna cikin yawon zuwa karɓo magani, ita da mahaifin Gudidi, basa nan basa can, koda yaushe bata da maganar da ta wuce "a nemo mata Gudidi ina Gudidi take?"
Shi kansa mahaifin gudidin tafiyarta yana damunsa, babu inda zai yi ne kawai, har Hajiya mama aka kira a waya ko da ta ɗauka tace musu gudidi bata zo gidansu ba, dole suka haƙura suka ci gaba da adu'a,
Can fannin Inna kuwa, tunda Aysha ta dawo gidansu Hajiya suke yin waya akan lokaci, hakan yasa hankalinta ya daɗa kwanciya, sannan duk ƙarshen wata sai Hajiya ta aika mata da kayan abinci, ko ya ƙare ko bai ƙare ba, a halin yanzu ma da ake ta shirye-shiryen watan azumi Hajiya ta aika mata da buhun dawa da Gero dana shinkafa da kayan haɗi, akan kullum Inna ta dinga yin abincin sadaka,
ABUJA
Bayan kwana biyu da zuwan Ma'aruf da Layla, Aysha tace "anty wlhi budurwar yah Ma'aruf ta fiye ƙaton baki ga dogon gashi🤣. Hajiya taso yin dariya, amma sai tayi murmishi kana tace "itace zaɓinsa" anty Jamila ta taɓe baki, kafin tace Wlhi ni haushi ma take bani, nifa lamarin mamaki ya bani, son da baya kula ƴan mata, ko auren da akayi masa da Saudart zaɓin Alhji ne, amma wai shine har da kawo mana wata yarinya mai buɗaɗɗen idanu, wannan yarinyar da gani bata da kunya kuma ni ina ganin a girme na ta girme masa"
Hajiya dai ko uffan bata ce musu ba, saboda tsananin ɓacin rai da zuciyarta take ciki, su biyu suke ta surutansu,
Wayar anty Jamila ce ta fara ringing, bayan ta amsa wacce ta kirata tace "Please ki hau WhatsApp yanzu zan tura miki da wasu abubuwa, dan Allah ki fahimceni" cikin sauri anty Jamila ta katse kiran tare da kunna data kana ta online, wasu hotuna masu yawa ne suka dinga shigowa, sunkai guda goma, sai da ta bari sun gama buɗewa kafin ta mayar da hankali ga hotunan da aka turo, Hajiya dai na kallonta ita da Aysha, Hajjo ce tayi nocking a bakin ƙofar ɗakin Hajiya, bayan an bata izinin shiga tace "wasu ƴan mata ne suka shigo sai matar aure guda ɗaya, Hajiya tace "ayi musu iso zuwa parlor gani nan zuwa"
Aysha ta miƙe tare da cewa "anty inzo mu kalla ne?" Anty Jamila ta girgiza mata kai fuskarta a murtuke kamar zata fasa ihu, lokaci ɗaya yanayin fuskarta ya sauya,
Aysha ta miƙe ta fice tana cewa "anty Allah dai yasa lafiya,
Kai tsaye ɗakinta ta wuce kana ta kunna wayar ta, massage ne ya dinga shigowa yakai kamar guda biyar duka na saƙon soyayya, daga masoyinta, wani irin murmishi tayi mai kyau, kafin ta fara karantawa..
"Kullum da nake numfashi, ka lmar da zuciyata ke furtawa ita ce: ‘Ke ce masoyiyata ta har abada"
"Sonki ya shige ni kamar jini cikin jiki, ba zan iya janyewa ba har sai zuciyata ta daina bugawa."
Haka ta dinga karantawa tana sake faɗaɗa fara'arta, idan har taga saƙon Zyd ko taji muryarsa sai ta rasa sukuni, sbda ta mugun kamuwa da soyayyarsa,
Kamar yasan ta kunna wayar, aiko taga kiransa, maganar jan aji babu tunda yau kwana ɗaya kenan bataji muryarsa ba, cike da shagoɓa tace....
Wallahi, idan soyayya ce mafarki, to ni bana so in tashi... in dai kai ne a cikin mafarkin.”
Ita kanta bata san ya akayi ta iya jera masa zance haka ba, yayi murmishi tare da cewa "
"Tabbas Ubangijina ya cancanci yabo ta kowacce fuska, bayan ni'imar rayuwa da ta lafiya da yayi mana, sai kuma ya kara mana da baiwar kasantuwar sanyin idanun mu a cikinmu, wadda muke kalla muji nutsuwa ta sauka a jikinmu, muji tabbas muma wasu mutane ne masu daraja, saboda kasantuwar me daraja a cikin mu."
Ya faɗa yana sake sanyaya muryarsa, murmishi tayi mai sauti kafin tace "kasan me?"
Yace "a'a"
"Mijina na shirya shiga ko wace gwagwarmaya idan har zan sameka"
"Wani irin shauƙin so yakeji wanda shi kaɗai yasan da hakan, a ganinsa ko ita idan yayi mata bayani ba ganewa zatayi ba, kai tsaye yace "gobe ina hanya.." tabbas tayi ganganci soyayya ta sanyata suɓutar baki yanzu ya zatayi..?
Oho ho, labari ya ɗau wuta 🔥, sai dai ina mai baku haƙuri tare da sanar muku da cewar, book 2 da book3 na littafin NA KASA JUREWA zai zo muku a na kuɗi, akan Naira 500 special group 1k nasan masoyana bazasu bani kunya ba, ta hanyar yin payments.
Insha Allah na kusa gama book1 saboda yana iya ƙarewa a koda yaushe,
Ga wanda zasu tura da kuɗinsu ga account number na 3175689751 Zainab Habibu first Bank, shaidar biya ta wannan number 08141799224, idan zakiyi vtu kimin magana idan kuma kati ne mtn


Idan na kammala book1 zan cigaba da posting a Arewabook idan kuma an gama payments zan fara posting a WhatsApp da wuri.

Mom Islam 08141799224

Mom Islam

*NA KASA JUREWA*
💋💋💋
💋💋
💋



_Mom Islam🍹_


Page 79-80

Singapore

Tunda Hajiya Zaliha ta fara magana bai ce mata komai ba, har ta gaji tayi shiru, cike da jin haushi gami da takaici tace "Alhaji na rantse da Allah bazan bari abinda kayimin ya tafi a banza ba"
Ta ƙarashe maganar tana katse kiran,

Har takai ƙarshen maganarta bai tanka mata ba, saboda yasan idan ya biye mata sai su wuni aje ma a samu matsala, lokacin da suke zuwa ƙasar waje Tare, duk ƙasar da ta zaɓa nan zasuje, "mai yasa tasa Saudart a gaba, yarinyar da babu ruwanta?"
Bayan ya ajiye wayar ya juya ya kalleta, barcinta takeyi cikin kwanciyar hankali, Allah ya jarabceshi da son Saudart, so mai tsanani, hayewa gadon yayi tare da jan blanket ɗin kana ya matsa kusa da ita, hugging
End Ads