x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 4 - NA KASA JUREWA book 1

  • 9001 words
  • 12000 words
  • Out of 86738 words

Category: Love Stories

Views 142

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ba'a basu damar shiga ba, dole suka nemi gurin zama suka zubawa sarautar Allah idanu,
Tunani Anty Jamila ta farayi, to me ya faru da Hajiya har abin ya kaita ga haka, duk da ansan cuta da mutuwa duk na Allah ne, amma jikinta yana bata akwai wani abu da ya faru,
Kallo ɗaya tayiwa Ma'aruf ta kawar da kai, kafin tace "wai meke faruwa ne ban gane ba?"
"Na me fa anty?"
Anty Jamila tace "my son kafin faruwar ciwon Hajiya babu abinda ya faru"
Shiru yayi kamar me tunanin wani abu, hakan ya bata damar gano zargin da takeyi akan faruwar ciwon hajiyar, "ina magana baka ce min komai ba?"
"Um..am..da...dama"
Katse shi tayi rai a ɓace tace "ka yimin bayani inda zan fahimta"
"Dama mun rabu..."
Ma'aruf ya fara magana yana sarƙewa, cikin tsoron magar da ya fara yi tace "kun rabu da wa?, Saudart?"
"Eh, Anty amma dan Allah ki fahimceni, wallahi har yanzu ba ta dena posting hotunan banza ba"
Sosai jikin Anty Jamila yayi sanyi ta tabbatar wannan maganar ce ta jawo  ciwon na hajiya, gashi abu yayi tsamari tunda ba'a bari a ganta, "can anjima likita ya fito daga room ɗin da aka shigar da Hajiya, "yauwa kune ƴan uwan matar da aka kawo jiya ko?"
"Eh mune"
Anty Jamila tai saurin amsawa,
"Ina son ganinki a office" daga faɗar haka likita ya wuce.

Kafin yakai ga shiga office ɗin nasa har ta ƙaraso, kusan a tare suka shiga.
Nuni yayi mata da gurin zama, bayan ta zauna ya zauna shima, kana ya ajiye fil ɗin dake hannunsa,  cire farin gilashin dake manne a idanunsa yayi kana yace "ƴar uwarku tana buƙatar kulawa sosai, a iya binciken da muka yi, mun gano tana daf da kamuwa da ciwon zuciya, ya kamata kuyi ƙoƙarin ganin kun bi matakan da zamu gaya muku",
Hankalin Anty Jamila a tashe tace "likita ina jinka"
"A rage yawan ɓata mata rai, sannan a yawaita sa ta farinciki dan Allah"
"Insha Allah" ta ce tana share ƙwallar da ta kwaranyo mata,
Daga nan ya basu wata takarda yace taje ta siyo magani a pharmacy, godiya tayi masa kana tace "yanzu zamu iya ganinta? "Eh" yace mata "amma banda hayaniya" kai tsaye ta wuce  zuwa siyo magani.
Tare da Ma'aruf suka je pharmacy ɗin, bayan sun dawo suka ɗunguma dukkansu zuwa room ɗin Hajiyar har da Inna,
Alhmdllh ta tashi, Norse suka samu a ciki tana ɓarewa Hajiya ayaba, gefe kuma ga ragowar kayan marmarin da Ma'aruf ya siyo,
Koda suka haɗa ido da Ma'aruf juyar da fuskarta tayi, sai kuma tace "Allah sarki Inna wallahi kuna rai na"
Inna ta gaishe ta, bayan ta amsa tayi mata ya jiki,
Anty Jamila ma tayi mata ya jiki, amsawa tayi, kana tace "Ma'aruf ne ya gaya miki bani da lafiya ko?"
Murmishin yaƙe tayi, tana gyaɗa kai da sauri"
Mayar da kanta tayi ta kwanta, har yanzu tana jin ɗaci a cikin zuciyarta.
          **************
Duk wani kaya da tasan nata ne, sai da ta kwashe shi, abinda tasan ba nata ba ko kallonsa batayi, takai ƙarfe 1:pm tana tattara kayan, daga bisani ta fito harabar gidan tana ƙwalawa driver kira, da sauri ya taho yana cewa "Hajiya Barka dai"
"Yauwa Barka, dama inaso ka ɗauko car key  kashigo ciki, zaka taimaka min in fito da kaya"

"Toh"
Yace mata, tana komawa ciki Idi mai gadi ya kalli driver kafin yace "idan an baka naka kason dan Allah ka tuna dani"
Suka kwashe da dariya.
Bakinsa ɗauke da sallama driver ya shiga ciki, koda Saudart taji muryarsa ta ce masa ya shigo, bayan ya shiga ya taimaka mata suka fito da kayayyakin, shi kansa yawan kayan ya bashi mamaki "anya ko lafiya?"
Ya tambayi kansa.
Kai tsaye mota suka kai kayan, kasancewa akwai Toyota Coaster, ta kwashe har kayan gadon nata.
Abin mamaki da ya ishi su driver da mai gadi, amma basu da bakin magana sbda gargaɗin me gidan ne,
Kai tsaye Keffi suka nufa, suna cikin tafiya wayarta tayi ruri, sunan Anty Jamila ta gani yana yawo a kan screen ɗin wayarta, zaro ido tayi a fili tace "ai na tambayeki aka ce min kinje anguwa, gaskiya bazan amsa wayarki ba, kokuma ai yanzu an free barin ɗauka"
Ta danna kore tare da karawa a kunnenta, "Assalamu alaikum anty ina yini kinje lafiya"
Saudart ta gaishe ta cike da ladabi,
"Naje lafiya Saudart, yanzu kina ina ne?"
Kai tsaye ta bata amsa "Ina Keffi anty"
"Keffi kuma?"
Saudart ta bata amsa da "eh"
Wani ƙululun baƙinciki ne ya tokarewa anty Jamila a  maƙoshi,
"Amma me yasa zaki yanke hukunci ba tare da kin shawarce mu ba?"
Dariya ma abin ya ba Saudart, tai ƙoƙarin dai daita nutsuwarta kafin tace "anty ai saki uku yai min"

Dumm...dumm..dumm, Ƙirjin anty Jamila ya bada, zufa ya fara keto mata, lokaci ɗaya numfashinta ya fara barazanar ɗauke wa, Inna dake la'akare da yanayin da ta shiga tace "Jamila wani abun ne ya faru?"
"Hmm Inna, wai Ma'aruf ne ya saki Saudart, abin haushi ma har saki uku"
Waro idanu Inna tayi kafin tace "wannan ai ganganci ne, shi beyi shawara da kowa ba kenan?"
Duk wannan maganar da suke yi a harabar asibitin suke yi, gudun kar hankalin Hajiya ya sake tashi.
Sai yanzu Antu Jamila ta daɗa gano sanadiyyar rashin lafiyar Hajiya.

"Alhmdllh" Saudart ta ambata lokacin da drivernta yai horn a bakin get na gidansu, sai da me gadi ya buɗe ƙaramar ƙofa ya leƙo kafin ya buɗe get ɗin yana ɗagawa Saudart hannu,
Itama hannun ta ɗaga masa har suka wuce parking space.
A hankali ta buɗe murfin mota ta fito zuciyarta fess kamar anyi mata bushara da gidan aljanna, drivern ya fara firfito da kaya yana ajiye wa, sai da ya kammala kafin ta ce "ka zauna gurin me gadi barin sa a kawo maka abinci"
"To yace mata yana washe haƙora"
Sallama yayiwa me gadi bayan ya amsa, suka fara hira kai kace tun dama can sun san juna,
Can anjima sai ga ƙatuwar foodflaks, da sauri me gadi ya karɓa yana cewa ƴar aikin "Nagode sosai" ta wuce tana amsa masa.
Me gadi ya shimfiɗa musu tabarma suka baje abincin a plate suka fara ci, jollof ɗin taliya da wake, yaji kifi sosai,
Nan suka fara ci hannu baka hannu ƙwarya, bayan sun kammala ci sukayi hamdala aka ci gaba da fira,
Saudart ta aiko ƴar aiki da kuɗi, koda tazo cewa tayi "sannunku driver anty ce ta aiko ni"
"To to gani"
Ya miƙe tare da sanya takalminsa ya bita,
"Gashi wai kasha mai"
Jiki na rawa ya karɓa yanata yi mata godiya, daga nan yayiwa driver sallama ya wuce,
Yana tafe hanya yace "taɓɓ motar da take shaƙe da fetur shine zata wani ce insa mai, wallahi nabar sawa.
Yai maganar yana ci gaba da driving.
Bayan shigarta gida, ta samu momy na kitchen ita da ƴar aiki, lokacin sun kammala abincin rana kenan, tunda momy ta ganta jikinta ya bata babu lafiya, sbda ganin yanayin jikinta da fuskarta duk tabon duka wani gurin yayi ja wani gurin fari, da kallon tausayi tabi ɗiyar tata, cikin sanyin murya tace "Saudart jeki huta ina zuwa.
Kai tsaye ɗakinta ta wuce, komai yana nan fess kamar tana gidan, tunda dama su biyu suke zama a ɗakin ita da Anam, koda yaushe a tsaftace yake, kasancewar da suna nan da basa nan ƴan aiki suna gyara ko ina,
Bayan su momy sun kammala hidimar abinci, ta wuce ɗakin Saudart, a zaune ta sameta tana shan yoghurt, wanda ta ɗauko yanzu a fridge, "Saudart ya sake yin tsiyar tasa kenan?"
Momy ta jefawa Saudart tambaya,
"Hmm momy kenan, ni wallahi azaba ta isheni, wai har yanzu zargina yakeyi bayan ni ban ma san wacce yake zargi ba, yace kullum sai tayi posting hotunan banza, ɗazu ma ya nuna min, kamar mu ɗaya momy"
Bubbuga bayanta momy tayi kana tace "Saudart ki kwantar da hankalinki, inaga zamanki da wannan mara mutuncin yaron yazo ƙarshe"
Saudart tai murmishi takaici, kafin tace "momy yau na nemi saki a gurin Ma'aruf kuma Allah ya taimakeni"

Tafi momy tayi, wanda yai nuni da tana cikin tsantsar farinciki, ta rungume ɗiyar tata kana tace "na gode miki, kinga yanzu ko dadynki ya dawo kinada sheda, tunda dama goyon baya ya samu shiyasa ya dinga ci miki mutunci, in banda shinɗin me kuɗin gaske bane wallahi da tuni na shiga na fita, amma babu wani abu da kika yayibo mana?"
Saudart ta yamutsa fuska kana tace "momy iya kaya na ne sai furniture ɗin da driver ya ɗauko suna can ɗakin baƙi"
"Mtsw, kedai anyi wa wuya wallahi, ki rasa abinda zaki kwaso duk girman gidannan?" Momy ya sawa ko ina key fa"
"In ya sawa ko ina key bazaki ɗauko ko wani abun ba, wanda zaki tunguna masa haushi?"
Momy tai maganar tana yin tagumi,
Su ma gidan nasu tubarkalla sbda gidane na gani na faɗa, amma ta sawa kanta done abin duniya.
Kwanan momy uku a asibiti sannan aka sallameta, Inna kam batayi tunanin haka jikin yayi tsamari ba, shiyasa ta zauna, dan kaya kala ɗaya ta taho dashi, daga ƙarshe dai ta koma sa kayan Hajiya mama,
A ranar da aka sallamesu, suka wuce gida, bayan sun karɓo magunguna da sauran abubuwan buƙata.
Jiki yayi sauƙi alhmdulilah sai dai ƙarfin jiki, koda suka iso gida an gyareshi tsaf, kasancewar sunada ƴan aiki sunkai su uku duka mata, biyu ƴan mata ɗaya dattijuwa.
A falo suka zauna, aka kawowa Hajiya pillow ta sanya a saman 3sitter ta kwanta.
"Inna muyi wanka se muci abinci ko?"
Antu Jamila ta yiwa Inna magana.
"Toh" Inna tace tana tashi ta wuce ɗakin Antu Jamila, tunda dama gidan ba baƙonta bane,
Kai tsaye ta wuce toilet tai wanka, kasancewar duk wasu na'ura da ake amfani dasu tun zuwanta na farko aka nuna mata yanzu kam bata wani tambaya, tunda a ƙalla tayi zuwa biyar har da wannan.
Bayan ta fito a wanka ta samu Anty Jamila ta ajiye mata kaya riga da zani na atamfa, da sabon skirt.
Bayan ta shafa mai ta sanya kayan, kana ta fito parlo, "sannu ta yiwa Hajiya kana ta nemi guri ta zauna"
"Yauwa Hajiya ta amsa tana ce mata, kin baro mutuniya ta acan kenan?"
Inna tayi murmishi kafin tace "ai kam tana can gurin kaka"
Hajiya tace "ina son ki dinga tafiya da ita fur kinƙi"
Ai bata taɓa zuwa Habuja ba ko wani gari ban taɓa zuwa da ita ba, kinsan ta akwai rawar kai"
Inna tai maganar tana kallon ƙaton TV wanda ya kusan ɗauke bango guda,
Har gabanta aka ajiye mata abinci a kuloli biyu, ta farkon ta buɗe, faten dankalin turawa ne a ciki, sai soyayyen naman kaza a sama, hannu tasa kafin taci tai bismillah, ba wani me yawa taci ba ta mayar da murfin ta rufe,
Hajiya mama ta ƙwalawa yarinyar da ta kawo abincin kira, da sauri tazo, Hajiya mata tace "ki damawa Inna kunun tamba idan akwai"
"Akwai Hajiya ai jiya muka je kasuwa tare da Alhaji"
Kawar da kai Hajiya tayi, kafin ta ƙirƙiro murmishi tayiwa Inna,
Wow Masha Allah, anty Jamila tayi kyau sosai, doguwar riga ta sanya A baya coffee brown ta gaban rigar anyi mata adon light pink tasha stone, tayi rolling ɗankwalin a kanta,
Cike da nuna kulawa tace "Hajiya ya ƙarfin jikin?"
"Yayi sauƙi jamila, ina Ma'aruf?"
"Ai tunda aka sallameki bai biyomu ba"
"To babu damuwa"
Hajiya ta faɗa a takaice.
Tea anty Jamila ta haɗa tazo ta zauna tana kallon TV tana sha, can anjima aka zubowa Inna kunun tamba wanda ya ji kayan ƙamshi ga fanke a gefe, Hajiya ma tace "idan da ragowa a kawo mata"
Koda aka kawo mata harda fanken tasha kunun sosai kuma taci fanken, daga nan kuma hira ta ɓarke a tsakaninsu, har aka kira sallahar azhar ba'a sake ɗora wani abinci ba, na safen suka ci.
Kasancewar ba a motar Ma'aruf ɗin suka dawo ba, shi kam ya wuce nasa gu,
Zaune yake a restaurant yayi uban tagumi, sam ya rasa abinda yake damunsa, sannan ya rasa abinda ma yake tunani, daga ƙarshe yace " yanzu da wane ido zan kalli Hajiya?" Sai kuma yace "to me na aikata da nake jin shayin haɗa ido da ita?" Koda aka kawo masa list na abinci ya zaɓa ɗaga musu hannu yayi, cikin nemawa kansa ƙakwarin gwaiwa yabar gurin, kai tsaye motarsa ya shiga ya wuce gidansa, sai da yai wanka kana ya fito cikin shiga ta alfarma, yau kam sarautar ce ta motsa, sbda kayan sarakai ne a jikinsa, sumar kansa tasha gyara Masha Allah gaskiya Ma'aruf kyakkyawa ne, ya fito sai ƙamshi yakeyi.
Kafin yai nocking na a get ɗin gidan Hajiya sai da ya ɗau tsawon mintoci daga ƙarshe yai nocking me gadi ya buɗe masa, in kaga yadda yake taku kai kace basaraken ne, sai dai fadawa ne babu a tare dashi, kai tsaye ya wuce sashen Hajiya, da sallama ya ƙarisa badan yaji Muryar Hajiyar ta amsa masa ba, muryoyin mutum biyu yaji, na anty Jamila da na Inna,
Bayan ya gaishe su, ya durƙusa ya gaishe da Hajiya mama, cikin fushi ta amsa, ya koma ya zauna, wayarsa ya ciro ya ɗan fara danne danne, yana jiran sakamako,
"Ma'aruf..!"
Hajiya ta kira sunansa murya a dakile,
"Na'am Hajiya?"
Ya amsa yana kallon ta, ka kyauta basan me zance maka ba, amma bazan ci gaba da sa maka ido baka da mata ba, tunda har ka zaɓi ɓata min rai akan abinda hasashen sa kakeyi, ko yanka ka za'ayi bazaka tan tantance gaskiya ba, ka nemo mata nan da sati biyu, "Hajiya mat..."
Ta katse shi da cewa "wannan umarni ne bawai shawararka nake nema ba"
Daga Inna har anty Jamila babu wanda yace ƙala, sbda dama tun kafin zuwansa, Hajiya ta yi musu magana akan idan tana magana dashi karsu sa mata baki...!

More comment more typing..

Mom Islam 08141799224
*NA KASA JUREWA*
       🪻🪻🪻

       Mom Islam






Page 13-14

Ta inda Hajiya ta shiga ba tanan take fita ba, sai da tayi masa tass kafin tace "ka tashi kabani guri"
  Jiki babu ƙwari ya miƙe, sam bega lefin faɗan da Hajiyar tayi masa ba, tunda ya rabu da Saudart, dama ita ce ta zame masa ƙarfen ƙafa..,
ƘAUYE
Inna kam barci ra bi da ra bi tayi, kasancewar tashin hankalin da ta shiga a daren jiya, abin da bata so shine ya faru, wato makara ta makara har gari yayi haske sosai, da sauri ta tashi ta waiga inda Talatu take kwance, sbda a iya tunaninta talatu ta kwana a inda ta barta jiya.
Cikin sauri ta fito tsakar gida tana ƙarewa ko ina kallo, "lahaula wala ƙuwwata illa billah" Inna ta ambata tana tafa hannu, sbda ganin ɓarnar da Talatu tayi mata, cikin ɗaga murya ta ƙwala mata kira "Talatu..."
Ta amsa da ƙarfi kana ta rugo a guje tana cewa "kaka meye?"
"Mele dan gidanku, ina ƙulin ƙosai na?"
"Yana waje har na gama suya jiran masu siya kawai nakeyi"
Talatu ta bata amsa tana washe haƙora,
"Talatu kin cuceni"
Inna ta faɗa tana zabga uban tagumi,
Talatu tace "kaka kike zaure ki duba idan banyi dai-dai ba seki sake toyawa"
Kaka ta ma rasa me zatace mata, kai tsaye ta wuce zauren ta barta a gurin, kafin takai ga duba ƙosan da talatu soya talatu tai wuf ta cika hannu ta jefa a baki, da sauri ta furzar tana kakarin amai,
Kaka ta durƙusa a gaban ƙosai tana ƙare masa kallo, kafin takai hannunta ta ɗauki guda ɗaya ta ɗan gutsira, da sauri ta furzar tare da salati,
Kaka na ji kamar ansa kubewa, "uwarki ce tasa ko ni ce na saka?"
Kaka ta mulmula mata zagi, Talatu tai tsuru da idanu kafin kaka ta yanke hukunci talatu ta ƙwalawa al'majiran da suke kusa dasu kira, tace "suzo ana sadaka"
Kafin kaka tayi wata magana ƙosai ya ƙare, suma masu karɓar sadakar Basu san meye ba, suna dai kallonsa kamar ƙosai, jiki babu ƙwari kaka ta tattara kasko suya ta koma ciki, sai zuwa ake ana cewa a bada ƙosai, kaka tana cewa "babu"
Talatu ta shigo tana rawa tace "albihirinki kaka"
Kaka tai banza da ita, Talatu tace "yo tunda bazaki amsa ba, dama zan ce miki kowa ya samu,
Kaka ta tashi kamar me zuwa ɗakin girki ta ɗauko bulala, ta dinga shinfifaɗawa Talatu, ihu take iya ƙarfinta amma kaka taƙi dena dukanta, tun talatu na ganin abin kamar wasa har takai ga, ta riƙe bulalar hannun kaka, tana kuka ta riƙe kwankwaso kana tace "alƙur'an sai ayi kare jini biri jini, ki sake dukana ki gani idan ban karya ƙashinki naba karnuka ba" kaka ta zaro ido tare da ƙoƙarin fincikar bulalar, ta ga ina bazata iya ba, ranta a ɓace tace "Talatu ki saki wannan tsumagiyar kokuma in ɗauko wace zata sa jikinki lauhi, banda rahin  kunya da tarbiyya ki dubeni ki dinga gayamin wannan maganar bayan kin yimin asara kuɗi ba nawa ba kuɗin bahi ne fa"
Talatu tace "daga abin arziƙi ya koma na tsiya, wallahi kaka ki rabu dani kar in sake yamushe miki fatar jikinki"
Tunda kaka ta ji haka, ta sakar mata tare da cewa "shegiya addababbiya me ƙarshen Giwa"
"Eh naji ko me ƙashin meye ai ni jikarki ce kuma in haka ne ma ƙashin mu iri ɗaya ne"
Talatu na gama rufe baki, Hansai me siyarda wake da mangyaɗa tayi sallama, kallon ta Talatu ta tsaya yi, a iya zamanta a ƙauyen bata san ta ba, doguwa ce sosai ga ƙiba da ɗuwaiwaka bugu da ƙari kana ganinta sai kace irin samudawan nanne,
"Kaka tace "maraba da Hansai, yau kece a gidan namu?"
"Eh nice, ba zama ne ya kawoni ba, dama nazo karbar kuɗin wake ne wallahi kaka kin saɓa alƙawari, yau mako ɗaya da kenan"
Hansai tai maganar cike da masifa,
Kaka tace "dan Allah kiyi hakuri asara nayi yau"
Hansai tace "na rantse da Allah bazan matsa ko nan da can ba he an bani kuɗin wake da mai"
Talatu ta matso kusa da Hansai kafin tace "kina ta wani yiwa mutane rantsuwa ba se akwai bane za'a baki? kokuma za'a baki babu ne?"
"Kan uba, kaka wannan wacece ?"
Hansai ta jefawa kaka tambaya,
"Jikata ce"
Kaka ta bata amsa.
Hansai ta nuna Talatu da yatsa tace "wallahi ki kiyayeni in ba haka ba, zan takaki"
Kaka tace "a gaba na?"
"To bakya ganin rahin kunyar da take yimini?"
Idan ku ka ga Talatu a gaban Hansai, abin sai ya bawa me karatu dariya, ƴar ɗugul amma bakinta yaƙi mutuwa,
"Kiyi abinda zakiyi ke kin daɗe bakiyi ba, ga fili ga me doki, da kaka zakiyi faɗan ko dani ki zaɓa a ciki?, tai saurin ɗauko gawayi ta zana a ƙasa tana cewa
End Ads