x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 5 - NA KASA JUREWA book 1

  • 12001 words
  • 15000 words
  • Out of 86738 words

Category: Love Stories

Views 118

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
"idan kin isa ki tsallake wannan layin"
Hansai ta riƙe baki, a fili tace "tunda nake a duniya ban taɓa cin karo da fitsararriyar yarinya irinki ba, amma yanzu nan zan koya miki hankali"
Hansai ta matsa zata cafko talatu, Talatu ta fizge bulalar dake hannun kaka da ta zama kamar gunki, kan kace me ta zafgawa Hansai a ɗuwawu, a zabure tai waje da gudu tana tsinewa Talatu, hamdala kaka tayi, da fitar Hansai  a gidan, tace "ƴar albarka Nagode miki"
"Kika godewa wa?"
Kaka tace "ke mana Talatu tawa.."
"Mtsw ki jira haɗuwata dake wallahi sai na rama dukan da kikai min"
Kaka ta zaro idanu tare da tafa hannu, cikin mamaki tace "yanzu idan aka ce ki dukeni zaki iya dukana?"
"Fess ma kuwa harda kwantar dake in ɗame miki fatarin sikel ɗinki in tsula miki"
Cikin sauri kaka ta koma ɗakinta, sbda ta tsorata da lamarin Talatu,
Dama ba tun yanzu ake kawo mata ƙorafin Talatu ba, wasu suce kodai bata da hankali ne, kowa da abinda yake cewa.
To my lovely fans, yanzu zamu tsunduma cikin labarin,
FARKON LABARI.
Keffi
Gidane ɗan madau-daici, wanda ya kasance mu haɗu a parlo, alhmdulilah Alhaji Aliyu ɗan kasuwa ne, duk da cewar be ɗaukaka sosai ba, amma yana da rufin asiri, matarsa ɗaya Zainab, suna zaman lafiya tun auren saurayi da budurwa, takai kusan shekaru 3yrs Allah be bata aihuwa ba, kwatsam Allah ya bata rabo, wanda ya kasance suna ta murna da, kaf danginsu sai da suka kira suka sanarwa, sosai Alhaji Aliyu yake bawa Zainab kulawa ta musamman, baya fatan a wayi gari Zainab ta nemi wani abu a duniya bata samu ba, ga shi ya ɗorawa kansa son Duniya, kwanci tashi cikin zainab yakai 3months, taje scanning akayi mata albishir da tagwaye duka mata, bakinta sam yaƙi rufuwa tsabar murna da farinciki, koda ta dawo gida ta nunawa Alhaji Aliyu takardar scanning ɗin, sai ma ya fi ta murna.
Dama yana tura takardar neman aiki a kafafen sada zumunta, Allah besa ya samu ba, koda yaushe burinsa ya siyi motoci sannan yayi gida na alfarma, hakan be samu ba saboda hidimar yau da kullum,
Yau ma kamar kullum yana tsaye a bakin titi yana ta re mota, wata danƙareriyar mota tai parking a gabansa, ƙirar Lexus, burinsa be wuce yaga waye mamallakin motar ba, a hankali ya rage tsayin gilashin motar, tare da washe haƙora yace "Alhaji Aliyu manya, ashe kana duniyar nan"
Alhaji Aliyu ya zaro ido tare da cewa "Innalillahi Muktar kai ne a wannan mahaukaciyar motar?"
Wanda Alhaji Aliyu ya kira da Muktar yace "haba mutumina dan wannan motar ai ba komai bace, saboda inada waɗanda suka fisu tsada a gida, insha Allah zanyi maka alkairi abokina"
Jikin Alhaji Aliyu yana rawa ya shiga mota, suka ci gaba da fira, firar duniya kawai suke yi.
Muktar yayiwa Alhaji Aliyu kwatancen gidansa,
A kasuwa ya ajiye shi, kasancewar yana siyarda takalma da handbag.
9:pm Alhaji Aliyu ya dawo daga kasuwa, ya fara bawa Zainab labarin haɗuwarsu da Muktar sbda abokinsa ne tun suna primary, harda kyautar da yace zeyi masa, sosai tayi farinciki, take ce masa kasan wasu abokan alkairi ne, "wasu kuma akasin haka"
Already sunyi musayar lamba.
Washe gari tun ƙarfe 7:am time ɗin ma yana barci, saboda tun sallahar asbha da ya dawo ya koma ya kwanta, janyo wayarsa yayi dan yaga me kiran nasa, yana ganin number Muktar ya miƙe zaune har yana mutsike idanu, kafin ya amsa kiran, "Hello abokina barka da safiya"
Muktar yace "Barka dai, dama nace ya kamata kazo zuwa gobe zan wuce SINGAPORE"
"To..to..to gani nan zuwa yanzu ma kuwa insha Allah"
Alhaji Aliyu ya ba Muktar amsa, ko wanka beyi ba bare brush haka ya sauya kaya, yayiwa Zainab sallama ya wuce.
Be wani sha wahala gurin gano gidan nasa ba, kasancewar ya bashi adreshi da komai, sai da ya gama ƙarewa anguwar kallo kafin hankalinsa ya dawo gurin get ɗin da yake tsaye, ya Subhanallah 🥳 gidan fa abin a kalla ne, dole Alhaji Aliyu ya koma kamar ya fito daga garin su Gudidi, kamar wani me jin tsoro, ya miƙa hannu a hankali kana ya danna ƙararrawa, sai ga me gadi nan ya buɗe masa, "daga ina?"
Me gadin ya jefo masa tambaya,
"Ni dama abokin me gidan ne, kuma yasan da zuwana"
Me gadi yayi murmishi kai da ka gansa ma kasan ba musulmi bane, "mu ai bamu san da zuwanka ba"
Alhaji Aliyu ya zaro ido tare da cewa "yanzu dai ba wannan ba, ka taimaka ka buɗemin"
Me gadi yace "sai ka bani abin shan sigari"
Sosai Alhaji Aliyu ya fara tsoron me gadi kasancewarsa zabgege ga damtse na ƙarfi, jiki na rawa ya tura hannunsa cikin aljihu ya ciro ɗari biyar,
"Haba me zanyi da wannan, nasan idan ka shiga gurin me gida sai ka samu abinda ya ninninka shi, dan haka nayi maka sauƙi kawo 5k, Alhaji Aliyu ya waro ido kana yace "da wannan ɓata min lokacin da kake yi ai gara in kirashi"
Ya danna number Muktar, ringing ɗaya ya ɗaga kana yace "ka iso ne?"
"Eh wallahi, gani a get anƙi barina in shigo"
"To idan kuka gama ina jiran ka ni zan fita ta ƙofar baya"
Muktar ya faɗa yana katse kiran,
"Tofa ga ƙoshi ga kwanan yunwa, ya Allah ka ɗorani a kansa, jiya har ina mafarkin mota wallahi, ace dai yau in koma da galleliyar mota wallahi da na haye wow"
Duk wannan zancen a zuci yakeyi,
Daga ƙarshe dai yace "kayi haƙuri ga dubu ɗaya dan Allah"
"Abinda na gaya maka shi zaka bada ai zaka samu idan ka shiga"
Me gadi ya faɗa yana sake tare bakin get, dama kuɗin nasa dubu goma ne, idan ya bada dubu biyar ai ya zaftare kudin, amma haka zeyi shahada ya bayar tunda babu inda ya iya.
Daga ƙarshe dai dole ya ƙirgo dubu biyar ya mika masa sannan ya barshi ya shiga.
"Aljannar duniya"
Alhaji Aliyu ya faɗa yana tafe yana ɗaga kai sama,
Ze iya cewa a iya saninsa da kalle-kallensa be taɓa ganin gida irin na Muktar ba,
Yama rasa inda ze dosa tunda ko ina ƙofofi ne na gilashi kai kace ƙofofin zinare,
Ƙara kiran waya yayi, Muktar ɗin yace ze turo yanzu a ɗauke shi, yayi masa godiya ya tsaya yaci gaba da kalle kalle-kallensa....!

Muje zuwa 💥
Kunsan me na fara ji ga me daku fans?
Naga kamar labarin beyi muku ba, jikina ya fara sanyi, bana ganin comments sam wallahi bana jin daɗi.
Wanda suke son shiga group ɗina ko channel wanda nake posting kumin magana ta WhatsApp kawai Please 08141799224

Mom Islam ce..
*NA KASA JUREWA*
       🪻🪻🪻

       Mom Islam





Page 15-16

"Alhaji Aliyu.."
juyawa yayi dan yaga me kiransa, security ya hango yana sanye da bakaken kaya kai kace police, kafin yai magana, ya ji ance masa, "Alhaji yace ka shigo ciki"
Jiki na rawa ya bi bayansa suka wuce,
Tofa anan ne Alhaji Aliyu yayi suman tsaye, "shin wannan gurin anya ba wata duniyar bane?"
Tambayar kansa yake yi a cikin zuciyarsa,
"Barka da shigowa abokina"
Muktar ya katse masa tunani,
"Yauwa Barka nayi sa'a"
Alhaji Aliyu ya faɗa yana murmishi,
Bayan sun gaisa Muktar yace "kamar inda nayi maka alkawarin mota gashi, irin wacce ka ganni a ciki jiya Lexus"
Tsabar farinciki be san lokacin da ya zame ƙasa ya riƙe ƙafafun Muktar yana yi masa godiya ba,
Muktar yace "babu komai abokina ai ka wuce nan"
Daga nan suka ɗan taɓa fira, Muktar yace ze fita gobe yana son barin ƙasar, sallama sukayi yana ta yi masa godiya har parking space Muktar ya rako Alhaji Aliyu, securities suna biye dasu, Boot aka buɗe masa, yaga kayan abinci iri iri, nan ma ya sake kwasar godiya, aka miƙa masa key ya shiga, kai tsaye ya wuce yana ɗaga musu hannu, har yanzu ya kasa tabbatarwa da kansa shine yayi wannan haɗaɗɗiyar motar?" can kuma yace "na yarda da maganar da bahaushe yake cewa idan rabonka ya rantse..."

Allah ya temakeshi ya iya driving,
Cike da shauki ya ƙarasa gidansa, Zainab da taji horn ɗin mota ta fito da gudu, ganin mijinta ne a ciki yasa ta yin farin ciki marar misaltawa, bayan ya fito a motar taje da sauri ta rungume shi.
Daga nan rayuwa ta fara sauya musu, lokaci ɗaya Alhaji Aliyu ya zamo attajiri, kasancewar any months se Muktar ya tura masa kuɗi,
After 1 month Friday, bayan an sakko sallahar juma'a, lokacin cikin Zainab yakai 6momths suna zaune a parlo tana zaune saman cinyarsa, cikin shagoɓa tace "Habiby sana'ar da abokin ka yakeyi ta birgeni, sbda kyautata wa mutane da yakeyi"
Alhaji Aliyu yace "Kamar kin shiga rai na  kuwa, amma kinsan me?"
"A'a" tace tana girgiza masa kai,
"Nifa har yanzu ban tambayeshi wace sana'a yakeyi ba"
Alhaji Aliyu yai maganar yana shafa mararta da cikin ke kwance se motsi yake.
Zainab tace "Gara ka tambayeshi kaga kai ma sai ka dinga taimakawa na ƙasa da kai, Allah se ya daɗa buɗa maka"
"Toh bari zan tambayeshi, idan da hali sai in roƙe shi arziki"
Yanzu kam ba koda wane lokaci suke haduwa ba, yawanci ma sai a WhatsApp tunda baya zama a Nigeria sosai.

Washe gari yana zaune saman two sitter Zainab na kusa dashi tana ɗaura masa agogon hannu, wayarsa ta fara rurin neman agaji, kasancewar wayar tana saman table wanda ya kasance a tsakiyar ɗakin, Zainab ta mike zata ɗauko, ya riƙe mata hannu kafin yace "na hutar dake maman ƴan biyu,
Ko da yaga Muktar ne me kiran yai murmishi yana ce mata "abokina ne"
Ya ɗaga tare da sallama, daga can ɓangaren Muktar yace "wallahi jiya na dawo idan da hali yau ka zo mu tattauna wata magana"
Cikin rawar jiki yace "to abokina insha Allah zan zo da yardar Allah ga mom twins ma tana gaishe ka"
Muktar yace "ina amsawa, ka ce mun samu ƴan biyu?"
"A'a zadai ku samu"
Muktar yace "to Allah ya sauketa lafiya, Alhaji Aliyu ya amsa da amin"
Zuwa yamma da misalin ƙarfe 5:pm ya kai masa ziyara, wannan karon be sha wahala gurin ganinsa ba, koda suka zauna sun tattauna akan matsalolin rayuwa, sannan ya yi masa godiyar alkairan da yake yi musu, kana yace masa yaga ana ta ginin masallaci, a takaice dai yana ta yabonsa, daga ƙarshe Alhaji Aliyu yace "nima in da hali a taimaka min da sana'a amma nafi sha'awar irin taka"
Muktar yai murmishi kafin yace "abokina samun damar shiga sana'ata ba abu bane me wahala, idan ka amince da ƙa'idoji"
Cikin rawa jiki yace "haba wane ƙa,idoji?, Nifa nan da kake gani na, na shirya wallahi"
Muktar ya katse shi da cewa "ka shirya ranar sunday, kaga dama saura kwana biyar, zan koma SINGAPORE se muje tare in kai ka gurin me gidana"
Koda ranar sunday ta zagayo an gama visa da komai da komai, yayiwa Zainab alƙawarurruka da dama, kafin tafiyarsa.
A ranar da zasu wuce tasha kuka kamar me,
SINGAPORE
A wani danƙareren gida aka yi musu masauki, inda Alhaji Aliyu yai ta cewa "ashe mu muna ƙauye ne, ashe duk ƙyale ƙyalen da yake gidan Muktar bagu ne, wannan masaukin da suke ciki ya mugun tafiya da tunaninsa, sai na natawa yake a zuciyarsa yana cewa "kuɗi sunyi a rayuwa"
Kasancewar Muktar ɗin ya fita ganawa da oga yasa Alhaji Aliyu tashi tsaye tare da ɗaga hannayensa biyu yace "ya Ubangiji ka yalwaceni da dukiya me yawa wacce za'a kirani a faɗin duniya da ƙasar waje"
Daga ƙarshe ya nemi guri kana ya zauna cike da tarin damuwa.
Abin mamaki, idan ka shiga bazaka fita ba har se lokacin da aka sallameka, duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa yayi, kana yace "ƙarfe biyar, babu azhar babu la'asar?, Wannan asara tayi yawa"
Gama maganar tasa yayi daidai da shigowar Muktar, cikin fara'a yace "abokina ka shigo ciki, tofa, sai yanzu ya fara tunanin yayi babban ganganci fiye da inda beyi zato ba, "to dama kai nake ta jira ka tafi ka barni shiru" Muktar yace ai munata shawarin inda za'a ɗauke ka ne, yanzu dai mu shiga ciki"
Kafin ya miƙe tsaye se da ƙirjinsa yace "rass" ya dafe ƙirjin nasa yana maimaita innalillahi wa inna ilahir raji'un, a zuciyarsa,
Kai tsaye suka wuce part nan oga, wani abu Muktar ya danna kawai suka yi ƙasa suuu, sai gasu a wani kyakkyawan ɗaki me kyau, ya hakimce akan wata haɗaɗɗiyar kujera wace zamu iya cewa ta zinare ce, mutumin zeyi shekaru 50yrs a duniya, yayi musu nuni da su zauna, da yaren su, tunda oga ya fara magana Alhaji Aliyu kallonsa yakeyi kawai badan ya san me yake cewa ba, sai da ya gama magana Muktar yace "Abokina nasan baka fahimci abinda oga yace ba, dama cewa yayi duk wani bawa ba haka kawai yake samun kuɗi ba, wasu sana'arsu siyar da kayayyakin masarufi wasu kidnaping wasu siyar da kayan shaye-shaye wasu neman mata da sauran su, mu sana'ar mu itace siyan mutane mu shigo dasu addinin mu, saboda musulunci yayi yawa a duniya, gaskiya anata ƙoƙari gurin ganin anyi yaƙi da hakan, daga trillions har abinda ya ninninka shi zai baka idan ka amince..!

Kunsan me yasa? kun kashe min jiki babu comments babu shar'hi ko kunfi so ya koma paid book ne?
Mom Islam ce 08141799224

*NA KASA JUREWA*
       🪻🪻🪻

       Mom Islam

Page 17-18

Yana matuƙar ƙaunar musulunci a rayuwarsa, lokaci ɗaya kansa ya fara juyawa ya rasa wane irin tunani yakeyi, gaskiya akan son Duniya baze iya ja da addinin musulunci ba,
Duk wannan shawarin a zuciyarsa yake yi, yayi nisa da tunani ya tsinkayo maganar Muktar yana ce masa, "abokina duk wata shawara da zakayi ai bakin alƙalami ya bushe, kana tunanin zasu ƙyale ka ne?, ka riga da ka gama sanin sirrin su, hamm kayi haƙuri kawai ka mori duniya son ranka sannan ka mori lokacinka da tarin dukiyar da zaka samu, wanda kaf danginku idan an bibiya babu wanda ya taɓa riƙe dukiya irin ta.
Cikin ƙanƙanin lokaci shaiɗan yayi galaba a kansa, sukayi yarjejeniya,  akan ze kawo musu ƴan mata ko jarirai guda uku, Muktar yace "abokina ai baka da matsala tunda bawai zaka kawo su duka lokaci ɗaya bane, shawarar da zan baka, tunda likitoci sun tabbatar muku da ƴan biyu matarka zata haifa, ka bada ɗaya se ku riƙe ɗaya"
Sosai tsoro da firgici gami da munmunar nadama mai ɗauke da dana sani suka ɗarsu a zuciyar Alhaji Aliyu, babban tashin hankalin ma "wai wanda ya shiga baya fita"
Se yaji kamar zai amince sai wata zuciyar ta dinga nusar dashi, daga ƙarshe dai ya amince da bayar da ɗaya daga cikin ƴan biyun da Zainab zata haifa, kafin nan ya roƙesu alfarma akan a juyar mata da tunani kar ta taɓa jin wata damuwa game da bayar da ƴar Tata, wace bata san  a ina zata rayu ba.
Hakan ko akayi, tun kafin yaje mata da labarin bokan su ya gama aiki,
Wasu mahaukatan kuɗaɗe aka bashi wanda suka zarce tunanin mai tunani, tashi ɗaya Alhaji Aliyu ya fara birkicewa, tunda a iya tsawon rayuwarsa bai taɓa ganin irin wannan tarin dukiyar ba,
Akwai wani tsafi da suke yiwa masu ƙaramar ƙwaƙwalwa, sai da akayi masa kafin ya dawo daidai,
Kwanansa biyar suka dawo gida Nigeria, kai tsaye ya wuce gidansa, dan ya kasa riƙo kuɗaɗen suna gidan Muktar wasu ko suna bank,
Duk wanda ya kalli fuskar Zainab ze gane tana cikin farinciki saboda dawowar mijinta, sannan ga dukkan alamu anyi nasara duk da ƴar ramar da yayi.
Kallon tausayi ya bita dashi, sbda zuciyarsa ta karye sosai, kamar wanda aka cirewa lakka a jiki ya rungume ta suka wuce ciki,
"Habiby ya naga kamar baka so dawowa ba, naga mood ɗin ka duk ya sauya"
Cike da kewarsa take maganar tana zaune a gefensa, janyota jikinsa yayi kana yace "ba haka bane maman ƴan biyu, sai kuma ya ji lokaci ɗaya ƙunci ya sake mamaye zuciyarsa, sbda ko ɗa guda ɗaya ta haifa dole ya bar musu"
"Habiby muje kayi wanka sai kaci abinci"
Ta katse masa tunani.
Dole ya miƙe sbda kar ta gane halin da yake ciki, bayan yayi wanka yaci abinci, ya fara tunanin ta ya ya ze tare ta da wannan maganar? ya jima yana tattauna maganar da zuciyarsa, har washe gari ya kasa ce mata komai 3:an motar Muktar ta shigo gidan Alhaji Aliyu, already ya san da zuwansa, lokacin kowa na barci ban da Zainab da hankalinta ya fara tashi,
Ta window take leƙensu,
Wani ƙatoton kwali babba sosai suka kamo Alhaji Aliyu ya shigo dashi parlonsa, bayan sun fito Muktar yace "abokina Zaka ji dadin wannan harkar fa, saboda ka zama sabon shiga shiyasa kake jin babu daɗi, ni nan da kake gani ƙanwata na bayar tun tana da shekaru 9yrs anata cewa ba'asan inda take ba, nayi ƙus da bakina..."
Alhji Aliyu ya katse shi da cewa "amma ka zuwa ganinta ko jin labarin ta?"
Muktar ya waro idanu kafin yace "abokina abinda nake so ka sani shine, idan har ka riga ka basu abinda suka nema har abada kai da tambayar su wannan abin, za ka sawa zuciyarka baka taɓa sanin wannan abin a duniya ba, sannan kaja bakinka kayi shiru, sannan ka nemi wata muhimmiyar sana'a wacce zata lulluɓe tarin dukiyar da kake da ita"
Babu inda ya iya dole ya ɗauki shawarar Muktar tunda ya fishi gogewa akan harkar, duk wani abu da Muktar ya san ze kawo wa alhji Aliyu matsala se da yayi maganinsa.
Bayan sun rabu da Muktar sam beyi barci ba a ranar, kasancewar gyare gyare da ya dinga yi, sannan ya shiga jiji app yana ta searching na gidan da ze siya da motoci da duk wasu kayan alatu, gaba ki ɗaya hankalin Zainab ya kasa kwanciya, duba da tunda sukayi aure baya taɓa ɓoye mata komai, abin mamaki yau ya ƙaurace wa ɗakinta, nasa ɗakin kuma yayi masa key, kiran sallahar asbha da akayi ne ya sa shi saurin  ƙarasa gyare-gyaren daga ƙarshe yai alwalah ya wuce masallaci, fitowa tayi kai kace munafuka ta murɗa handle na ƙofar taji a kulle, da sauri ta koma bedroom ɗinta ta jingina da bango tana ta saƙe-saƙe a ranta.
Bayan ya dawo sallahar asbha kai tsaye ɗakinta ya wuce, ya sameta ta idar da Sallah tana kan sallahya tana gyangyadi dan bata ji shigowarsa ba, zama yayi a gabanta tare da shafa cikin ta buɗe ido a hankali, bata nuna masa ɓaci ran ta ba tace "ina kwana Habiby"
"Lafiya mom ƴan biyu da fatan kin tashi lpy ya
End Ads