da tace komai ba.
Da sallama doctor ya shigo hannunsa riƙe da takardar sallama, ya miƙa wa umma, cikin girmamawa, ta karɓa tare da cewa "Masha Allah, jakadiya sai a harhaɗa kayan ku taho tare"
Umma ta faɗa tana buɗe kofar ɗakin ta fice, tunda ta fita daga ɗakin dogarai su duƙa kwasar gaisuwa,
Bayan jakadiya ta kammala tattara kayan, ta bawa Umar ya fita dasu zuwa motarsa, ta riƙe hannun Gudidi da lokacin da ta miƙe take shirin faɗuwa, doctor ya bamu magunguna, kai tsaye suka wuce masarautar MANDU..
SINGAPORE
Bayan kwana uku da yin taro, wani allo da oga Reed ya rataye tsafaffe wanda zai dinga yi masa nuni da adadin matan dake period,
A yau ya sami mata sama da hamsin, wanda suka kai masa pad ɗinsu, a take a lokacin aka turawa da bokansa, shi kuma ya jira sakamako, acan ɓangaren Thabit ya matsa lamba dan ganin anyi nasara jiragen ruwa sun tsira daga hannun hukuma, cikin sa'a prime minister ya amince da tayin da Thabit yayi masa, cike da farin ciki ya samu Oga Reed ya sanar masa, wani irin hugging yayi masa cike da tsantsar farinciki, a take a lokacin oga Reed ya yiwa Thabit kyautar wani danƙareren gidansa dake kusa da anguwar tasu, Sosai Thabit yaji daɗi tare da ce masa, ai wannan kaɗan ka gani daga aikin Thabit, nidai fatana in ga ance Jirgi ya iso"
Wayoyinsa guda uku duka suka hau ringing, duk ya birkice yama rasa wacce zai ɗaga, wayar dake gabansa ya ɗauka kafin yace "Oga an saki jirginmu gamu a hanya" ɗayar wayar ma haka aka gaya masa, yayi farinciki sosai, ya sake ƙara yiwa Thabit wata kyautar, kafin yace "a cikin ƴan mata nan ya zaɓi guda ɗaya wacce zata dinga ɗebe masa kewa" dama wannan ranar yake jira, aiko yace "toh tare da sake yiwa ita Reed godiya"
Tunda Misha ta koma ɗakinta hankalinta sam ya gaza kwanciya, "da gaske yake yi kokuma yaudararta zai yi? itaɗin wacece meye alaƙarta da musulmai, bayan ko hausarsu ma bataji, ta dafe kanta tare da miƙewa tsaye ta fara zagaye ɗakin, Neria dake barci ta jiyo surutan Misha sai kace a mafarki, duk da dai bazata iya maimaitasu ba, saboda sama sama take jiyo maganganun nata, murya irin ta mai barci tace "anty Misha lafiya kuwa, naga sai zirga-zirga kikeyi, kuma ga dukkan alamu bakya cikin kwanciyar hankali, tunda nazo ban taɓa ganinki cikin irin wannan yanayin ba sai yau Please mi ke damunki?"
Misha ta furzar da iska mai zafi, tare da sauke ajiyar zuciya, kafin tace "Neria, bansan meye yake damuna ba, bansan meye yake tunkaroni ba, i don't know what to do"
Ta tura hannunta da yasha farcen Bature cikin sukar kanta, tare da zubewa saman bed tana tsaki,
"Amma ya kamata ki kwanta kiyi barci"
Neria ta gaya mata itama tana mayar da kai ta kwanta.
Zaune yake a gidan da Oga Reed ya bashi, dalilin zuwansa gidan shine..
A ranar da oga Reed yayi masa kyautar gidan yace ya kamata ya koma, saboda babu wanda yasan ko gidan waye, ta haka ne zasu dinga gano masu yi musu zagon ƙasa, saboda babu wanda yasan Thabit yana yiwa Ita Reed aiki,
Washe gari.
Tun da asbha yasa aka ɗauko masa Misha, yaso haɗawa da Neria, hakan ba zai yiwu ba, saboda CCTV camera yana nunawa iya Reed komai, dole Misha ya ɗauka, zaune suke a parlor tayi shigarta na arna kamar yadda ta saba, riga iya cinya sai takalmi mai tsini sosai a ƙafarta, wayarsa ta fara ringing, ganin number Umminsa yasa shi ɗauka tare da cewa "Assalamu alaikum ya Ummi.., afuwan wlhi Ummi ina son zuwa anjima zan tura da kuɗin ayiwa Marwa aikin na samu alhmdulilah" Ummin tayi murmishi daga can ɓangaren kafin tace "nidai matar da zaka aura nakeson ka kawomin, yace...!
Ayi haƙuri babu yawa please
Mom Islam ce..08141799224
*NA KASA JUREWA*
💋💋💋
💋💋
Book
Page 65-66
_Mom Islam🍹_
"Ummi zamuyi magana zuwa anjima"
Ya katse kiran yana kallon Misha, da itama shi ɗin take kallo,
"Naga kamar kinason yin magana?"
Thabit ya tambayeta ba tare da ya kalli fuskarta ba,
"Waye kai, me kake nema a gurina..?"
Ta jefo masa tambayoyi tana mayarda numfashi kamar wacce tayi gudu,
Thabit yayi murmishi, kafin yace "ni ba kowa bane face bawan Allah, ban gaya miki wannan maganar dan in cutar dake ba, ki fahimceni taimakonku nazo yi"
Da sauri ta miƙe tsaye, tare da cewa "babu wani taimakonmu da ka zo yi, in banda ka wulaƙantamu, ko da yake na fara tunanin kazo ka dulmiyar damu a cikin addininku ne, wanda babu komai a cikinsa in banda takura, shi yasa kake wani cewa wai asalinmu musulmai ne"
Sosai ta bashi mamaki, saboda yin maganar kawai takeyi, sai ka ce ba a cikin haiyyacinta take ba, sai da ya bari ta gama surutunta kafin yace "duk abinda zaki faɗa sai dai ki faɗa, saboda taimakonku da nake sonyi ba zan fasa ba, dole in cika alƙawarin da na ɗauka"
Ya ƙarashe maganar yana buga table ɗin dake gabansa,
"Ka nemo min wine"
Kai tsaye yace "musulunci ya haramta mana shan ta" ta wani juya idanu tare da yin bakin ƙofa, tace "ka janye duk alwashin da ka ɗauka a kanmu idan ba haka ba, tabbas zakayi nadama wacce baka taɓa yi ba" tana gama faɗar haka ta buɗe ƙofar ta fice da sauri...
Iska mai zafi ya furzar tare da miƙewa tsaye ya fara zagaye ɗakin yana tunani iri-iri,
Acan gidan oga Reed, yana zaune a ɗakin da yake ajiyar gwala-gwalai, fuskarsa fal farinciki da annashuwa, sakamakon isowar da jirgin ruwan yayi, har kayan sun shiga kasuwa, CCTV camera yake kallo, sboda tsarinsa ne, sanya ido akan komai da komai, hatta gidan da Thabit yake ciki yayi connecting da CCTV camera, yau ne ma ya fara ganin musayar yawun da Misha tayi da Thabit, Oga Reed yayi murmishi tare da cewa "impossible, wannan mutumin da biyu ya shigo rayuwata, akwai abinda yake nema...
Acan ɓangaren Thabit, shikam bai ma san da akwai CCTV camera ba, sai yanzu da ya ɗaga kansa sama, a ɗan firgice ya sake kallon gurin, kafin ya sauke numfashi, shawara ɗaya ya yanke wa zuciyarsa, lokaci ɗaya yasa gidan a kasuwa, ko zai yi waya baya taɓa sakewa yayi a gidan, har ya zamo ma ya siyar da gidan, saboda oga Reed ya damƙa masa takardar gidan a hannunsa, ko da suka gama cikini ya samu abu ya lulluɓe Camera ɗin, a ranar da zai bar gidan kenan, A fili yace "Misha nayi niyyar taimakonku, hakan bai samu ba, amma nasan insha Allah watarana zamu haɗu, ya fice da school back ɗinsa, Kai tsaye ya wuce airport..
Oga Reed yabi ƙididigin camera na gidan Thabit amma ina, duhu kawai yake nuno masa, abin mamaki, ga shi rabonsa da Thabit ɗin yau kwana biyu kenan, tabbas idan beyiwa tufkar hanci ba, zai kaisa ya baro sa,
1:am na dare, yanada ikon shiga ko ina inhar ya kasance mallakinsa ne, dan haka kai tsaye ya fito daga gidansa ba tare da securities ba, cikin zafin rai ya nufi gidan Thabit ɗin, sai dai kash, ko da ya iso bakin get na gidan, ya samu an garƙame gidan da ƙaton kwaɗo, a gigice ya sake kallon babban kwaɗon, kana ya kai kallonsa ga wata takarda da aka manna a jikin get ɗin,
"Gidannan ya zamo mallakin gwamnati, Nagode da karamcin da kayimin, dama na fito neman kuɗi ne, ƙanwata ce take Hospital babu lafiya, za'ayi mata tiyata bamu da komai a hannunmu, shiyasa nazo na taimaka maka"
Oga Reed ya dunƙule hannu tare da kaiwa get ɗin naushi, cikin takaici yace "har yanzu ban gama yarda da kai ba Thabit, i swear akwai wata a ƙasa..."
Washe gari, musamman yasa aka kirawo masa Misha, sosai ta firgita, saboda sai suyi 3monthts basu sanyashi a idanunsu ba, idan ba meeting zasuyi ba, bayan tazo ya dinga yi mata tambaya game da Thabit, babu abinda ta ɓoye masa, ya jinjina kai tare da yi mata godiya kafin yace "Misha, kinada sha'awar komawa wani addini ne?" da sauri ta girgiza kai tare da cewa "bana da"
"Okay jeki, duk a tunaninsa maganganun da Thabit yayi mata sunyi tasiri a zuciyarta,
Bayan tafiyarta, ya fara tunani iri iri, tare da ɗaukar alwashin sai ya sa an nemo masa Thabit duk inda ya shiga, mutanensa ya tura da motoci, akan subi duk wata hanya da suke ganin zasu sameshi, sai dai kash ya tsere musu, a halin yanzu ma ya sauka a ƙasarsa Egypt.
KD ƙauyen ƴan kifi,
Bayan sunyi wanka, Inna ta kawo musu ɗumamen tuwo sukaci,
Haka suka ci gaba da rayuwa a wannan ƙauyen..
Wata ranar Talata, kwanansu biyar a gidan malam, sai dai babban abinda zai bawa mai karatu mamaki, bai wuce mancewar da su Majeed sukayi akan ko su suwaye ba, bazasu iya tuno asalinsu ba, sai dai ilimin da suke dashi yana nan zaune a brain ɗinsu da kuma sunayensu..
Yau ne malam ya fara tafiya da Majeed gona, sam Majeed bai iya komai ba, Haladu ne ya dinga nuna masa inda zai yi,
Acan gida gurin Inna, kasancewar tana yawan fita kasuwa kai kaya kamar su, masara da sauran su hatsi dai, Karima ta kalli Najma ta taɓe baki, kafin tace "ke tashi kiyi wanke-wanke dan wlhi yau tsinke bazan kawar a gidannan ba, kamar inda Karima ta bata Umarni, ta miƙe ta tattara kwanukan kana ta kaisu mawanki ta wankesu tsaf, ta share gidan, Karima ta watso mata kayan wanki tace "ga sunan ki wanke idan ba haka ba in naɗa Miki na jaki"
Najma ta waro idanu, dubada wankin yanada yawa sosai, tace "gaskiya sunyi yawa ba zan iya ba, ta miƙe tare da wanka mata mari, cikin zafin rai Najma ta rama, tare da cewa "a girma nasan na girmeki kawai dan kin ganni a gidanku, karki manta duniya da faɗi a duk inda muke ni da yayana Ubangiji zai karemu, tunda bamu san danginmu ba.."
Karima ta kwashe da shewa tana ce mata, "wa ya sani ma ko a titi aka haifeku,"
Sosai maganar ta daki Najma ta runtse idanu, cike da ɓacin rai tace "wlhi ƙarya kikeyi"
"Ubanki ne yake ƙarya?"
Najma tace "nasan darajar iyayena"
"Wato sai dai nawa uban ko"
Karima ta faɗa tana cakumo Najma suka kaure da dambe, sosai suke damben, har Inna ta shigo, da gudu ta ƙara so kana ta yarda itacen dake kanta, Karima ta kurma ihu tana cewa "wayo ta watsamin barkono a idanu" Inna ta juya gurin Najma ta wanka mata mari, tare da cukume mata wuyan riga cikin faɗa take cewa "daga alfarma sai ki zaƙe zaki kashe ƴar masu gida, walhi tallahi baki isa ba, shegiya kawai"
Najma ta fashe da kuka tana riƙe da kumatunta, zatayi magana Inna ta gwaɓe mata baki,
Karima ta cigaba da gurje idanu, taci gaba da cewa "Inna wai dan nace ta yimin wanki shine ta wani cukumeni da faɗa"
Inna ta riƙe baki, kafin tace "yo bata isa ta baki wankin bane? ko kina ganin zaki dinga cin abincin gidan ubanta a banza ne?" Najma ta rushe da kuka tana share hawaye,
Sai da aka kira sallahar magriba kafin su Malam da Majeed da Haladu suka dawo gida, bayan anyi sallahar isha'i suka zauna cin abinci, daga nan kowanne Ya tafi makwancinsa,
Washe gari, bayan su Najma sunyi sallahar asbha, har zata koma ta kwanta, Inna ta tasheta tace taje ta ɗibo ruwa a rijiya basu da ruwa a gida, ta miƙe jikinta yanayi mata ciwo, haka ta ɗauki bokiti Allah yasa ma rijiyar a gidansu take, bayan ta ɗibo ruwan ta ajiye, tare da komawa ɗakinsu ta kwanta a wani fallen zani, gashi inda take kwancen duk tudu da kwari, dayake babu siminti a ƙasa, itako Karima sai kwasar barcinta takeyi cikin kwanciyar hankali,
Ƙarfe 7:am Inna ta gama dama koko suka karya, daga nan tace "Najma ta kwashe kofuna ta wanke, babu musu ta wanke, malam ya ƙwala musu kira su biyu, Karima na turo baki ta tafi, tare da harar Najma, bayan sunje yace zai aikesu kasuwa su siyo masa masara saboda yau ba zai samu zuwa ko ina ba, yace su je su sanyo hijabi, kamar inda ya umarcesu hakan sukayi, ɗan babu hali ta hana Najma aron hijabi saboda zata iya fuskantar faɗa daga gurin malam.
Bayan sun zo gurinsa sun karɓi kuɗin, dama Karima ce ta karɓi kuɗin, suka fito ƙofar gida,
Karima tayi tsaki mtswww... tare da cewa "ni Wlhi na tsani tafiya da baƙauyen mutum, idan munje guri yayita kalle-kalle"
Najma dai bata ce komai ba, sun kusa isowa kasuwa, wata galleliyar mota tayi parking a gefensu, sukaci gaba da tafiya Karima nata zaginta, wani yaro ne ya taho da sauri yana cewa "wai wancan mutumin yana magana daku"
Karima tace "ki tsaya anan bari inje inji dan nasan kekam sai dai baƙinjini"
Harda ƴar rangwaɗa ta ƙarasa gurinsa tare da cewa "sannu da zuwa gani" tana washe haƙora,
"Yi haƙuri ƴan mata ba ke nake kira ba, waccar wace kuke tare"
Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokareta, ko tsayawa saurarar Najma batayi ba, ta wuce ta da sauri, ita da ta tsaya jiranta, cikin ɗaga murya yace "ƴan mata dan Allah ina magana" Najma ta tafi a hankali, cikin nutsuwarta kafin tace "ina kwana, lafiya lau, da fatan banyi laifi ba"
Murmishi tayi masa wanda ya sake ƙawata kyakkwar fuskarta, yace mata tayi masa kwatancen gidansu, zai ga iyayenta, babu musu tayi masa yayi mata godiya,
Karima na isa kasuwa ta auni masara ta kamo hanya bata ɗauko masarar ba, tace Najma ta wuce ta ɗauko, duk yana la'akare da abinda Karima take yiwa Najma, hakan yasa ya fara shan jinin jikinsa suɗin ƴan uwa ne kuwa?
har suka ɓacewa ganinsa kafin ya fara bin su sannu a hankali...
KEFFI
Kamar inda boka ya bashi umarni na wanka cikin dare hakan ko akayi, yace momy ta rufe ƙofa shikam a ɗakinsa zai kwana saboda yanada wasu takardu da zai cike, bayan sunyi sallama ya dawo ɗakinsa, yana zaune har dare yayi sosai kafin ya fara hasaso inda zai je yayi wankan, saboda ance masa a tsakar gida, wani keɓaɓen guri ya samu a gidan nasa ya yi zigidir kana ya buɗe murfin jarkar ya fara tsiyayawa a kansa, tare da sha sau uku kamar yanda abokin nasa ya jaddada masa, daga nan ya dawo ɗakinsa yana sauke numfashi,
Washe gari, da asbha dama babu maganar sallah, tunda umarnin boka ne, ƙarfe 10:am ya shigo ɗakin momy yana sanye da lallausan yadi, kana yace "shifa jiya ya kasa barci da tunaninta ya kwana, yanayi yana gyara hanky ɗin dake cikin aljihunsa, dama momyn a buƙace take, ta bada kai lokacin da ta gama lulawa duniyar Dady, cikin hikima ya shinfiɗa ƙyallen, ya kwanta akai kana ya ɗora momy a samansa, sosai suka gamsar da junansu, momy ce ta fara miƙewa ta nufi toilet, shi kuma ya fice zuwa ɗakinsa da sauri, leda ya samu ya ƙulle ƙyallen da niyar zai kaiwa boka..
Ina mai bada hakuri babu yawa, amma insha Allah zanyi ƙoƙari inyi muku mai yawa,
Mom Islam ce 08141799224
*NA KASA JUREWA*
💋💋💋
💋💋
Free Book
Page 67-68
_Mom Islam🍹_
Bayan dawowar su Umaimah gida..,
Zaune suke a parlor, anty Tasneem tana ɗakinta, Umaimah tace "Aysha wace shawara kika yanke a game da auren baban Laurat?"
Aysha tace "uhm ke nifa kaina ya ɗauki wuta, kina nufin in aureshi kokuma me?"
"A'a Aysha kawai dai na tambayeki ne"
Aysha tai shiru, tare da yin tagumi, a karkashin zuciyarta kam tunani ne fal, "anya zata iya amincewa da tayin da laurat tayi mata kuwa?"
Wata zuciyar tace mata, ba fa shine yace yana sonki ba, dan haka kawai ki watsar da wannan maganar,
Hakan ko tayi, tun daga ranar ta share maganar,
Ranar Monday da ta koma school, suka haɗu da Laurat, canja mata fuska tayi, saboda kar ta sake yi mata maganar mahaifinta, amma Laurat ɗin bata damu ba, sai ta mance da alfarmar da ta nema a gurin Aysha ta dinga janta da hira, daga ƙarshe dai Aysha ta saki jiki, har aka tashi, Arman yazo ya ɗauke ta suka dawo gida.
Kwanci tashi asarar mai rai yau watan Aysha uku, a Kano, ta samu sauyin rayuwa, gogewa da sauransu, saura sati ɗaya uncle Junaid ya dawo, dan haka anty Tasneem ta cewa Aysha ta shirya kayanta zata mayar da ita Kano, tunda dama sunyi da anty Jamila akan zatayi wata biyu ne, gashi har ta shiga na uku, a ranar da Arman ya ji maganar tafiyar Ayasha, sam bai ji daɗi ba, ganinta kawai da yake yi duk da bai furta mata wata kalmar soyayya ba, yana jin daɗi a cikin zuciyarsa, rana tsaka wai zasu rabu, anya bazai je ya gaya mata abinda ke cikin ransa ba kuwa?, wata zuciyar tace masa "No karkayi haka, har yanzu bata gama mallakar hankalin kanta ba, tukuna, ana gobe zata koma Abuja, sai da tabi gidan ƙawayenta tayi musu sallama, ko da taje gidansu Laurat, jiki a sanyaye suka fito harabar gidan, cikin tausasa harshe "Aysha idan har maganar da nayi miki akan ki auri mahaifina ne yasa kika ja baya da zumuncin mu, ina mai baki haƙuri, amma karki manta in daɗa tunasar dake lada zaki samu"
Tai maganar hawaye na kwaranyowa daga idanunta, cikin Muryar kuka tace "Aysha ina yi miki fatan alheri"
Itama Ayshar jikinta yayi sanyi sosai, saboda Laurat tanada kirki ga hankali, tunani takeyi, "mai yasa zuciyarta ta kasa amincewa da tayin da laurat ɗin tayi mata?"
Aysha ta bata number wayarta, kana tace "zamuyi waya, insha Allah idan nayi shawara zan nemeki"
A ranar ne tayi sallama da school sboda an nema mata transfer,
Washe gari, ta gama shirya komai driver ita yake jira, Umaimah kam sai kuka takeyi, haka ma Ayshar sunsha kuka kamar ba zasu sake haɗuwa, tun jiya ta kira Zayd ta gaya masa, ransa sam beyi masa daɗi ba, babu inda ya iya dole sukayi sallama da niyar zasuyi waya.
Ƙarfe 9:am aka shigar da kayanta Booth, sosai ta rungume anty Tasneem tana ce mata, bansan da me zan saka miki ba, anty Tasneem Allah ya faranta miki, Umaimah ma rungumeta tayi, tana kuka ta shiga mota, har driver ya fice a gidan suna ɗaga mata hannu, tun kafin a kai ga wuni, sunji gidan shiru