hau washe haƙora ita a dole yarinyarta tazo, duk da ganinsu su biyu be sa ta ɓata ranta ba, sai ma rungumesu da tayi, tace a shigar dasu ciki suyi wanka sai suci abinci, driver yace "Hajiya har da kashi fa a mota, Talatu tace "to me tonon silili anji ai he ka wuce ko?"
Hajiya tayi dariya ta shiga ciki.
Sai da sukayi wanka suka sauya kaya, wata koɗaɗɗiyar atamfa Talatu tasa, ita kuma gudidi zani daban riga da ban ɗankwali daban haka ta saka, ga wata kwalliya da sukayi iri ɗaya, sun lafka janbaki ja a leɓensu anyi jagira da koren pencil,
Koda suka fito ƴan aikin gimtse dariyarsu sukayi, sbda suma dai a gidan aka wayar dasu, a parlo suka zauna yayinda Hajiya ta sanya a kawo musu farfesun naman kaza, da soyayyen dankalin turawa da kunun gyaɗa, sai ruwan gora a gefe,
Talatu ta kwaso kulolin duka gabanta, kafin tace "Gudidi bari kiga idan bamu raba shi ba, ƙur'ani zasu ce mana ƴan ƙauye,
Talatin ta yago cinyar kaza takai baki, tana cewa "ungo wuya da gurin ɗuwawu kinsan bana cin su"
Gudidi tace "kai Talatu me makon ki raba mana tare hine zaki nuna min waraki?"
Murguɗa mata baki tayi, yayin da take sake yago naman kana tace "tausaya miki fa nayi hi yasa nace kizo mu tafi, idan ba zaki ci ba to hikenan cinye wannan na kwanon dan ban san meye ba, ga dukkan alamu zai iya tsurar da mutum"
Gudidi ta karɓi wuyan kazar da kwankwaso ta koma gefe, dama a saman Capet suke zaune, ta buɗe kular dankalin turawar da aka soya da ƙwai, ashe har da dambun nama a gefe, ko gayawa talatu batayi ba ta dinga ci hannu baka hannu ƙwarya, bata cinye na bakinta take sa wani, sallamar da Ma'aruf yayi ne yasa Talatu da gudidi suka juya a tare....!
Idan ana comments in sauya taku idan ba'ayi muci gaba da tafiya a haka, idan na gaji in dena posting
Mom Islam ce 08141799224
*NA KASA JUREWA*
🪻🪻🪻
Mom Islam
Page 23-24
Sanye yake da blue jeans da t-shirt milk color, fuskarsa tana ɗauke da annuri, hannunsa na riƙe da wayarsa yayinda ya tsunsa suka kasance da tsadaddun zobuna masu kyau, ko da yaga babu kowa a parlo ya tsaya bai ƙarisa ciki ba, ƙare wa su Talatu kallo yakeyi, yayin da suma shi ɗin suke kallo, Talatu ta wani ƙwalalo masa idanunta, Gudidi na suɗe hannu tace "Talatu idanunki sun gano miki abinda na gani kuwa?"
A hankali tace "wa Gudidi, zo ki dangwali romo muyi kamar zamu wuce ta gabansa se mu hyafa mai"
Kamar inda Talatu ta tsara haka sukayi, kafin zuwan su yana ta, ƙare musu kallo sbda bai taɓa ganin irinsu a gidansu ba, yayi nisa da tunani ya ji sun ruga waje da gudu suna dariya, sai yanzu ma ya gani wa shi suke yiwa dariyar, ashe ɓata masa jiki sukayi,
Cikin zafin zuciya ya kalli kulolin da suka ci abincin kafin yace "su waye waɗannan kamar ba mutane ba?"
Kai tsaye ya wuce room ɗin Hajiya mama, ya sameta tana shafa mai, kasancewar ta fito daga wanka, "Hajiya su waye a parlo kamar mahaukata?"
Inda yai maganar ta gane Bama shawara yake bata ba, umarni yake bata, "Ma'aruf ka nutsu kasan me kake yi, yarinyar nan da ka ga tazo zama daram a gidannan babu inda zata je"
"Yara dai, Hajiya ki daina cewa yarinya ai su biyu na gani kuma wallahi da su da mahaukata duk tafiyar su ɗaya, Hajiya ki duba rigata ki ga wulaƙancin da sukai min"
Yai maganar yana zuba hannayensa cikin aljihu rai a ɓace.
Ɗayar ƙawarta ce tare suka zo ɗazu,
Beyi abin da ya kawo shi ba ya fice, sbda haushi da takaici, a rayuwarsa ya tsani ƴan ƙauye.
Rai a ɓace ya fito daga side na Hajiya yana ƙwalawa anty Jamila kira Hajiya tace ta fita har yanzu bata dawoba"
Yanke shawarar ya fice a gidan yayi, ya fito parlo kafin ya buɗe, ƙofa yaji an cakumeshi tana cewa "yasin na kamaki kuma mintsini sittin zanyi miki"
Idanunta a ɗaure take maganar.
Ƙare mata kallo yayi up and down, kafin ya fara kiciniyar fincike hannunta a jikinsa, cikin ƙyanƙyami yake ƙwace hannun nata, har ga Allah bata san ba gudidi ta kama ba, ita kuma gudidi tana can corridor tana jiran Talatu ta kira ta, abin ya matukar bashi mamaki wai namiji kamar shi ya kasa cire hannun talatu a jikinsa? meye hakan yake nufi?"
wani gigitaccen mari ya zabga mata kafin yace "ba kisan wa kika riƙe ba ko?"
Ya ƙara da cewa "wawuya ƙazama me warin awaki"
Jin shigar marin tayi har cikin ƙwaƙwalwar ta, lokaci ɗaya taji zafin na shigarta sosai, tai saurin cire ɗankwalin da ta ɗaure idanun nata, buɗe idonta ke da wuya ta ɗora su a na Ma'aruf, hannunta a saman kumatunta tana sosa gurin tace "me nayi maga mugu kawai, na ɗauka ma Gudidi ce ashe Garba ne"
Tai maganar tana murguɗa baki, hannunsa yakai bakinta ya ɗanne sai da taji zafi sosai ta ruga da gudu idanunta sun cika da hawaye tace "mugu basamude"
Babu hali ya bita sbda sai ta rai nashi haka dai ya fice a gidan zuciyarsa babu daɗi.
Kai tsaye gidansa ya wuce, bayan an buɗe masa ya shiga, kai tsaye bedroom ɗinsa ya wuce, kallon kansa yayi a mirror kafin ya ja dogon tsaki mtswww, sai kuma ya hau ɓaɓɓalle bottoms ɗin rigar, lokaci ɗaya faffaɗan ƙirjinsa ya baiyyana, wanda ke ɗauke da kwantaccen gashi baƙi gunin birgewa, gashin yayi lufff kai kace an tace shi,
Har yanzu yana cikin ɓacin rai, ya zauna saman bed ko me yake tunani oho, ya ciro wayarsa ya fara gwada number anty Jamila, ringing ɗaya zuwa uku ta ɗaga, cikin katseta a maganar da takeyi yace " Anty kina da labarin mahaukatan da suka zo gidan Hajiya kuwa?"
Anty Jamila ta zaro idanu kafin tace "shine babu wanda ya kirani, Ma'aruf yace "dan girman Allah ko sun zo yin kwana biyu ne ki fitar dasu anty naje rai na a ɓace na dawo gida.
Sallama sukayi ya ajiye wayar, sai yanzu hankalinsa ya kwanta a tunaninsa Anty Jamila bata da masaniyar zuwan su Talatu.
A gurguje ta koma gida hankali a tashe, tun daga harabar gidan take ƙwalawa drivers da mai gadi da ƴan aiki kira, da gudu suka taho dukkansu suka durƙusa a gabanta, cikin zafin rai da ɗaga murya tace "waye ya bari mahaukata suka shigo gidannan?"
A ƙalla ƴan aikin gidan zasu kai goma, kuma ko wanne a wata ana biyansa albashi mai tsoka.
Ƴan matan da suke aiki da mai bawa flowers ruwa da mai gadi da ɗan aikan gidan da sauran ma'aikatan suka rantse da Allah basu ma ga mahaukata ba"
Anty Jamila ta ɗibi sauri sai cikin gida, tana shiga tun daga parlo take cewa "Hajiya wai gidannan lafiya kuwa?"
Lokacin ma sallahar magriba tayi, ta fito parlo ta samu anty Jamila na ta haɗa gumi tace "lafiya Jamila?"
"Au Hajiya lafiya fa kike tambaya ta, ni da aka kirani musamman wai mahaukata sun shigo gidannan"
Hajiya ta riƙe haɓɓa kafin tace "injiwa?"
"Son mana"
Anty Jamila tai maganar tana kallon su talatu da suka fito sunata tsotse ƙashi,
Hajiya ta nemi guri ta zauna kana tace"Jamila ki fita harkar Ma'aruf wallahi, ƙanwarsa ya gani ita da ƙawarta shine yake kiransu mahaukata,
Hajiya tace "ai su biyu suka zo?"
Kafin tai wata magana Talatu tace "ai dama kema anan gidan kike?"
Anty Jamila ta gyaɗa mata kai.
Bayan anyi sallahar isha'i, Hajiya ta nuna musu ɗakin da zasu dinga kwana, babban ɗaki ne, haɗaɗe kai kace ɗakin amarya, ga gado makeke ga katifa mai laushi, wani tangamemen tv ne a manne jikin bango, yayinda remote ya kasance a cikin drowa dake gefe, acan, tsakiyar ɗakin yana malale da grass Capet, yayinda can saman pop ya kasance akwai wasu ado kusa da ƙwanlantarki a taƙaice dai ɗakin yayi kyau over,
Koda suka rufe ƙofa, talatu ta fara jin kashi, ta tashi gudidi da ta fara barci tace "ke tahi ki rakani banɗaki alƙur'an kahi nakeji" cikin barci gudidi tace "unn ke komai kahi Allah hi ƙara ai romon da kika hya ne"
"Nidai ba wannan ba ki tahi muje in yaso idan muka dawo sai ki ci gaba"
Tana maganar tana tsalle, dole gudidi ta tashi suka murɗa handle na ƙofar toilet ɗin suka shiga, "lalala na higa uku wannan aljannar duniyar haka?"
Talatu ta faɗa tana ƙarewa toilet ɗin kallo, "kinsan meye gudidi?"
Gudidi tace "a'a amma dai yasin sun cucemu ga guri me sanyi da ni'ima sun wani sa mu cikin ɗumi, "
"Ke har na ji kahin ya koma, yanzu dai zo mu kinkimo katifa mu kawota nan"
Talatu ta nunawa Gudidi toilet,
Yasin bazamu iya ba, kafin mu kinkimo ina jin ƙihi, yauwa ka kofi, ta ɗauko wani cup wanda yake ajiye a can sama dan har da abin ajiye shi, kai idan ka ga cup ɗin kamar ka cinye amma wanka akeyi dashi, babu wani datti a jikinsa sai sheƙi yake, Gudidi ta fara dube duben inda zata samu ruwa, "lahh ga rijiya kuma ga dukkan alamu ruwanta ze yi sanyi sosai"
Gudidi ta faɗa tana buɗe p-toilet, dumbulo ruwan tayi kafin ta kurɓa cikin jin daɗin sanyi da ya ratsa ta tace "ahhhh"
Talatu ta karɓe cup ɗin tare da ɗibowa itama tasha, har tana wani lumshe idanu, sai kuma ta sake ɗibowa, kowaccensu ta sha ya kai cup biyar biyar, daga nan suka fito bedroom sukayi ta kiciniyar ɗauko katifa tafi ƙarfin su, dole suka hakura suka kwanta, "wayo daɗi Talatu ƴan binni suna morewa wannan katifar kamar lallausan burodin hyagon Lado" Gudidi tai maganar tana bubbuga ƙafafunta, da haka har barci ya ɗauke su.
Acan ɓangaren Hajiya suna zaune da Anty Jamila, Hajiya tace "Jamila ina son zumuncin mu yaci gaba da ɗorawa da yaɗuwa ta hanyar haɗa auren Ma'aruf da A'isha"
Anty Jamila ta ja gauron numfashi kafin tace "Hajiya wato Hajiya wani hanzari ba gudu ba"
Hajiya mama tace "ina jinki"
Anty Jamila tace "da farko dai a mayar da ƙawar A'isha daga nan sai mu fara tunanin abubuwan da ya dace muyi mata"
"Hakane gaskiya banyi tunanin hakan ba sai yanzu, kinga idan ta ga ita kaɗai ce zata fi kintsuwa, akwai wasu kuɗaɗe da zasu shigo end of this month za'a cire wasu daga ciki ayi mata siyayya, Jamila kinsan abu na gaba wanda nake tunani?"
Anty Jamila ta bata amsa da cewa"a'a ,ya za'ayi soyayya ta shiga tsakaninsa da Aisha? kinsan dai halin Ma'aruf miskilanci da jinkai, babbar damuwar ma ya ce yana ƙyanƙyamin ƴan ƙauye"
Momy na gama maganar tai tagumi,
Cikin kwantar mata da hankali anty Jamila tace "karki damu A'isha ƴa mace cefa, sannan wallahi tallahi sai Ma'aruf ya so A'isha fiye da ko wacce mace, amma kafin hakan ya yiwu sai an sha wuya, Hajiya in ba'a haɗasu aure ba, to bamusan wacce zai jajiɓo mana ba, tunda duk ƴan matan ba zama da shi tsakani da Allah zasuyi ba, saboda dukiyarsa zasu so shi, duk da cewar shi ɗin ba mai kule kulen ƴan mata bane"
"Hakane, Jamila amma A'isha zata sha wuya sosai"
Hajiya ta faɗa tana gyara pillow ta kwanta,
"Hajiya na ɗan lokaci ne, bari Allah ya kai mu gobe insha Allah a kuɗin business ɗin a zan ware mata 50k kafin ragowar su zo"
Anty Jamila tai maganar sbda tana son kwantar wa da Hajiya hankali.
Fans nasan kuna son ku ji waye anty Jamila ko?
Anty Jamila ƙanwa ce ga Hajiya mama, uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, bayan rasuwar mahaifin Ma'aruf ta dawo gidan Hajiya, tana business ɗin kayan kitchen sbda har babban shago ne da ita, shekarunta 37yrs kafin zuwanta tayi aure a Niger, mijin ya gudu Mali ya barta, yakai shekaru 7 bai dawo ba, daga ƙarshe ya aiko mata da takardar saki, shine ta dawo gurin Hajiya mama.
Asalinsu ƴan Bauchi ne, dalilin haɗuwar Hajiya da mahaifin Ma'aruf, ta fita anguw a yayi tozali da ita, daga nan magana tayi ƙarfi har akayi aure ga Ma'aruf ɗin mu nan na A'isha komai dozin🤣, wannan kenan.
Ko da Dady ya dawo daga masallaci ya samu saudart tana zaune saman kujera tana danna waya, "sannu da dawowa Dady"
Saudart tayiwa dadyn yayinda take sauke kanta ƙasa,
"Yauwa amma lafiya dai na ganki a gida ko?"
"Kanta a sunkuye tace "Dady Ma'aruf ya sake..."
"What!!! kinsan me kike cewa kuwa?"
Kuka ne ya kufce mata ba tare da ta shirya Ba, sbda ita a gurinta abin farin ciki ne, yanzu kam ba ta san kukan me takeyi ba,
Dady ya katse ta da cewa "kimin magana, sannan kuma ki tashi driver ya mayar dake gida"
"Da gaske takeyi Habiby ba wasa bane, har saki uku yayi mata, wallahi nima nayi yunƙurin ta koma, amma abin ba zai yiwu ba, tunda har da shai da ya bata kaga kuwa magana ta ƙare, nidai ina roƙonka alfarma karka sake ka je ko ka kira iyayensa wannan tashin hankalin ya isa haka, Saudart fa ba wai ta rasa mijin aure bane, Dady yai gyaran murya kafin yace......!
Uhm jiya na samu comments na mutum ɗaya idan har kinci karo da godiyar da nayi miki much love, comments da sharhi shine farinciki na.
Mom Islam ce 08141799224
*NA KASA JUREWA*
🪻🪻🪻
Mom Islam
Page 25-26
"Kinsan komai Zainab ba sai nayi miki dogon bayani ba, duk da muna da tarin arziƙi, ba shine zai hana mu aurar da yarinyar mu ga wanda ya fi mu tarin dukiya ba, wannan shine dalili na"
Dady yai maganar rai a ɓace.
Rurin da wayarsa tayi ne ya sanya shi miƙewa yana cewa "ba zan zauna in zuba miki idanu ba, kina gama idda zan aurar dake insha Allah "
Dady yai maganar yana bi ta gaban Saudart ɗin ya wuce,
Cike da tsantsar tausayi momy ta rungume ɗiyar tata tana bubbuga bayanta, kafin tace "daughter ki yi hakuri komai yai tsanani maganinsa Allah, har yanzu dadynku bai fahimceni ba, amma a ganinsa mune ba mu fahimce sa ba, duk soyayyarsa da dukiya ai ya kamata ya kankaro miki mutunci"
Dukkansu kuka suke mai cike da tausayi.
A tunanin Hajiya su Talatu sun tashi sunyi sallah, shiyasa bata leƙa su ba, a cewarta su huta sosai,
Ƙarfe 9:am time ɗin sun kammala breakfast an jera a dining table, kalolin abinci ne sunkai uku, Dafaffiyar doya da miyar ƙwai sai Potatoes Salad sai Dambun couscous da sai kuma drinks na Abarba da kwakwa, gabaki ɗaya sun hallara a dining, Hajiya da Anty Jamila da Ma'aruf, Dafaffiyar doya da miyar ƙwai aka sa masa sai su anty Jamila da suke cin Dambun couscous, Hajiya ta yiwa ƴar aikin magana mai suna Dija tace ta kira mata yaran da suka zo jiya, da sauri Ma'aruf ya miƙe tsaye yana jan t-shirt ɗinsa, kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa yayi, kafin ya bar gurin, ko tsakiyar parlo bai kai ba, sukayi kiciɓis da Talatu ita da Gudidi, be yi aune ba suka wani tafi dashi kiiiii sai ya faɗi saman kujera daɓas, waro ido yayi yana kallonsu, ga mamakinsa sai ya ga suna ta dariya har da nuna sa da hannu kamar sun ga sabon mahaukaci, cike da bala'i ya miƙe sbda ba suyi tsammanin hakan ba, tunda suna ta wasa ne wanda suka saba yi a can garinsu, ya zare belt ɗin wandonsa kana ya shaƙo wuyan Talatu gudidi zata gudu ya sa mata ƙafa ta faɗi, ya shure ta da ƙafa, "ke wace irin daƙiƙiya ce, kinsan waye ni kuwa?"
Ya zabga mata lafiyayyen mari wanda yai sanadin ɗaukewar jin ta na ƴan wasu lokuta, sai kuma ta tsala ihu, sbda take mata ƙafa da yayi da cover shoe ɗinsa, ƙarar muryarta da su anty Jamila suka ji ne ya sanya su tasowa a tare ita da Hajiya, har ma da ƴan aikin gidan, sukayo kanta, turus sukayi sbda aika aikan da ma'aruf yayi wa yaran, bakin Talatu sai jini yake, ita kuma gudidi tana riƙe da kai itama tasha mari dan zai kai biyar,
Rai a ɓace Hajiya mama ta nemi guri ta zauna kafin tace "last warning Ma'aruf wallahi idan ka sake kuskuren taɓa yarannan Allah sai ranka ya ɓaci, "shikenan daga zuwansu ka sasu a gaba sam baka tunanin zumuncin dake tsakaninku?"
"Allah ya kyauta wallahi gara in ƙare rayuwa bani da dangi da dai ace wannan mahaukaciyar itace dangina"
Anty Jamila tace "har matarka ma, to ya zakayi idan hakan ya kasance?"
Ma'aruf ya tofa mata miyau a fuska kafin yace "tur har abada wallahi da na haƙura da aure dama bani da niyya"
Cikin yanayin ɓaci rai Hajiya mama tace "Jamila ki daina yi masa misali ki rabu dani kawai zan yanke hukunci nan ba da jimawa ba, ko yayi masa dadi ko kar yayi masa babu ruwana"
Tunda ya ji Hajiya ta tsomo baki yai tsit sbda ya san a inda yake magana, babu wasa, bai sake magana ba ya fice, Hajiya kam tana rungume da Talatu baki yayi sungumeme, fans a memakon kuyi mata sannu sai kunyi dariya irin sosai ɗinnan 🤣,
Rarrashinsu Hajiya da Anty Jamila suke yi su ko sun ware baki suna ci gaba da cewa "mun higa uku me mato yazo ya mayar damu ƙauye rayuwar binni babu riba" ba Hajiya ba, har anty Jamila sai da tayi dariya.
Har inda suke zaune ƴan aiki suka kawo musu abinci, aka bubuɗe musu kuloli, a tare suka matsa Talatu tana cewa "idan kinga me nama a ciki gudidi karkici"
"Sabo da me, ke da kika sauya kamanni kamar goggon biri, gudidi tayi maganar tana riƙe da ƙafarta kana ta sheƙe da dariya,
"Ka ji hegiya ba dan na taimaka miki ba ubanwa ya isa ya sa ki zo wannan tafkeken gidan?"
Gudidi tace "a hakan dai gahi kin fini hyan wuya koba komai baki yayi sungumeme"
Ta miƙe da faɗa zata daki gudidi, Hajiya ta riƙeta tana bata haƙuri.
Suna breakfast ɗin suna faɗa, da gori da haka sai da suka cinye ragowar abincin tass kafin suka ture kulolin, ma'aikatan dai suna ganin ikon Allah, cike da gulma suka bar gurin suka koma part ɗin su.
"Dija dame muka fi waɗancan ƙauyawan, mu fa ba dan talauci ba wallahi da baza a ganmu a nan ba, kinsan meye Hajjo?"