x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 8 - NA KASA JUREWA book 1

  • 21001 words
  • 24000 words
  • Out of 86738 words

Category: Love Stories

Views 141

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
dogon hanci wacce alhji ya kumbura wa baki"

"Naji dai Dija ci gaba ina jinki, ya akayi?"

Dija ta taɓe baki kafin tace "wai ita Hajiya take so ta auri Alhji"

"Kai kai kai, "Dija kunnuwanki basu jiyo miki dai-dai ba, saboda babu inda za'ayi kamar Alhaji ya auri wannan yarinyar, da idan tayi kwalliya kamar ka gudu"

Hajjo tai maganar tana girgiza kai.

"To shikenan Hajjo dama ni idan na kawo miki magana baki cika amincewa da magana ta ba"

Dija ta faɗa tana ci gaba da tafiya.

"Haba Dija ai abin ne banbara kwai babu daɗin ji"

Daga nan suka kawar da maganar ta hanyar ci gaba da hira.

Bayan su Hajiya sun koma ɗaki, Gudidi ta kalli Talatu kafin tace "kinga basu kawo mana ruwa ba, ruwan nasu ma marar garɗi kizo kawai muje wannan ɗakin mu hya me sanyi"

"Riƙe min hannu in tahi wannan mai ƙirar samudawan sai mun ɗauki fansa a kansa, duk da dai gyatumansa sunyi masa faɗa amma ni naso a dalla masa mari yasin" suka wuce room ɗin su suna ɗingishi,

Yau ma kamar jiya, suka shiga toilet ɗin, wani sanyin ƙamshi ne ya ziyarci hancinsu, sbda a rana sau biyu ƴan aiki suke gyara ko ina,  "yasin Gudidi duk inda za'ayi yau anan zamu kwana ni ko a ƙasa ma zan kwana"

Gudidi na ɗingishi tace "uhm ni ƙafa ce ta dameni da zugi ɗiban ruwan dan Allah"

Talatu ta ɗauki cup ɗin ta ɗibo mata ruwan tasha tace "ahhh sanyi me sanyaya zuciya, ina tunanin komawa ƙauye ina tunanin barin wannan lagwadar daɗin"

Gudidi tace "hikenan da ina so in samo mana wata hyawara in kin amince?"

Talatu tace "ina jinki"

"Kizo mu je tsakar gidannan muga me akeyi muma fa ya kamata mu fara aiki ana biyan mu, mun zauna kara zube kamar wasu malalata"

Talatu ta waro idanu kafin tace "ke ai bazasu barmu muyi komai ba, sai dai muje wani gidan mu nemi aiki kinga hikenan asirinmu a rufe"

Gudidi ta kurɓi ruwan p-toilet tare da yin farrr da idanu tace "zan ɗura ruwannan a gora na rantse in samu na hya in zamu fita neman aiki"

Talatu tace"to bari dai mu samu lafiya se mu fara zuwa"

ƘAUYE
Bayan tafiyar su Talatu.

Ke ina Gudidi taci da ƙohi bata kwahe kayan wanke-wanken tayi ba, yarinyar dake zaune ta fara gyangyaɗi tsabar ƙoshi tace "Gudidi fa ta bi Talatu Binni tace in gaya miki "

Tabaiyye ta zaro idanu tare da riƙe baki, mayafin ta dake rataye jikin igiyar shanya ta ɗauka fuuu sai gidan Inna, tana tafe tana sababi har ta iso gidan Inna, tun daga can zaure take kwaɗa sallama, lokacin kaka na zaune a tsakar gida, suka amsa da "wa'alaikumussalam, hannu da zuwa Tabaiyye "

"Hmm kafin dai in amsa muku jama'a kuyi hakuri wai da gaske ne Gudidi ta bi Talatu binni?"

Cike da mamaki suke kallonta wanda a iya saninsu Talatu ita kaɗai ce a cikin mota,

Inna tace"any kuwa? gaskiya bata bi ta ba"

"Tabaiyye tace ƙanwarta ce ta tabbatar min da haka hiyasa nazo kai tsaye"

Sosai maganar Tabaiyye  ta basu mamaki, kaka tace "abinda ya kamata ke Inna ki tahi ki je gurin mai hyago ki ari Salular sa ki kirawo Jamila ko Hajiyar ki tambsyesu "

Inna tace "to ai kuwa maganin kokwanto"

Tabaiyye ta zabga uban tagumi gami da cewa "na saro rogo har na ɗubu da ɗari biyar amma tsiyar da ƴar nan zatai min kenan Inna tace "kiyi hakuri  bari inje in duba"

Inna ta lulluɓa zani ta fice, kai tsaye gurin mai shago ta nufa, bayan sun gaisa tace "dan Allah idan salularka da kuɗi ka yiwa Hajiya flahin ta kira zan tambayeta ne"

Yana yin flashin sai ga kiran Hajiya, bayan sun gaisa, Inna ta tambayi Hajiya, Gudidi ta biyo Talatu ne?"

Hajiya tace "eh ta biyo ta"

Inna tace "gahi nan zata ɗaga mana hankali dan Allah idan da hali ta dawo tun kafin mahaifinta ya sani"

Hajiya tace "munyi shawarar hakan insha Allah gobe driver ze kawota yanzu kam dare yayi,

Kasancewar lokacin da Inna tayi kiran har sun fara barci, anty Jamila kam tuni tayi barci.

Inna ta mika masa wayar kana tayi masa godiya,

Tana komawa gida Tabaiyye ta miƙe tsaye kai kace ance gudidin ta mutu, tare da dafe ƙirji tace "ya akayi Inna?"

Inna tace "hamm walhi tare suka tafi, amma gobe insha Allah me mato zai kawota" Tabaiyye tace "alhmdulilah barin koma gida in san ƙaryar da zanyiwa babanta"

Babu wanda ya tanka mata ta fice.

WASHE GARI.
Lokacin da Ma'aruf yai musu wannan dukan ashe Hajiya na ayyyana inda zata tari Gudidi da maganar tafiya, gashi kuma ya take mata ƙafa, duk da dai bata ji ciwo ba,

Umarni ne na Hajiya duk wani baƙo da yazo za a kai masa ruwan wanka ƙarfe 12:am idan har baka son yi da safe,

Cikin bin umarnin Hajiya Dija ta shiga ɗakin su Talatu ta samesu suna ta wasa suna ihu, haushi ma suka bata cikin yatsina baki kai kace ƴar wani mai muƙamin ta wuce toilet, ko da ta shiga suka bita da sauri, Talatu tace "karki kuskura ki kwahe mana ruwan daɗi dan wallahi bazamu barki ba, sai kinyi kuka" she's 18yrs Dija, su kuma 12yrs ta wani yi musu kallon tara saura kafin ta watsar ta kutsa kai cikin toilet ɗin, suma shiga sukayi, "ahe ma ba nan ta nufo ba"

Cewar Gudidi,

Talatu taje da gudu ta zauna a saman p-toilet tana turo kumburarren bakinta, da yake Dija bata fahimci abinda suke nufi ba, tai ficewarta, har ta kai tsakiya sai kuma ta tsaya, tace "ga ruwan wanka nan kuyi"

Tana fita, Talatu tace "yasin bazamu yi ba, se kace wasu agwagi mtswww Hegiya kawai" ta tashi tsaye tana kwaikwayon tafiyar Dija tare da yanayin maganarta, suka sheƙe da dariya.

Saboda kar ace ba suyi wankan ba, suka ɗauraye jikinsu, sabulun kam yasha gurza a cewarsu ƙanshinsa yayi yawa, gara yayi ya ƙare.

Ko da suka fito daga wanka kayan da suka cire shi suka mayar,  suka lamɓaya mai suka fito.

Ƙarfe 1:pm Hajiya ta fito da wata babbar jaka, wacce ke ɗauke da kayan abinci da kayan sawa sababbi masu tsada, Hajiya taje parlo gurin Gudidi da ke gaban TV kamar za ta shige ciki tace "ƴata kiyi hakuri mamarki ta kira jiya wai ki koma gida, ga wannan kayan ki tafi dasu"

Gudidi ta kalli Talatu suka zaro idanu, Gudidi ta tsandara ihu tana cewa "yasin ni bazan koma ƙauye ba, bazan iya zama a can ba yanzu na higa uku wayo Tabaiyye zata cuceni waye daɗin binni wayo ruwan sanyi mai garɗi"

Haƙuri Hajiya ke bata amma ina sai surutai takeyi sam bata ma ganewa, anty Jamila da ke fitowa yanzu hannunta rike da waya, ta ƙwalawa driver kira, yazo cikin ladabi ya durƙusa, tace masa ya sa kayan a mota, tunda Talatu taga da gaske ne, ta marairaice murya tace "gudidi kiyi hakuri zan dinga tara miki ruwan daɗin a jarka idan ya ɓubɓugo" koda suka iso harabar gidan da ƙyar ta shiga mota sai kuka takeyi, driver ya fice bayan an buɗe masa get suka nufi hanyar ƙauye...!

Masha Allah naga comments naji daɗi ina fata zan dinga samu any time,

Dan Allah kuyi haƙuri zan dinga hutawa Asabar da lahadi, saboda aiyukan gida, sannan inaso in ƙara muku yawan typing kamar read more shida inda zaku ji daɗin karatu, kunga komai sai da lokaci, yanzu dai insha Allah Monday zaku jini nayi muku alkawarin sa ku farinciki insha Allah.

Mom Islam ce 08141799224

*NA KASA JUREWA*
      🪻🪻🪻

    Mom Islam


Page27-28

Bayan tafiyar Gudidi, Talatu ta shige ɗakinta da gudu tare da rushewa da marayan kuka gami da kurma ihu tana shure-shuren ƙafafu, lokaci ɗaya zazzaɓi mai zafi ya kamata, bakinta ya fara karkarwa, ta haɗe guri ɗaya idanunta kuwa sunyi jajir kamar garwashi

Daƙyar take buɗe su.

Acan ɓangaren su Hajiya da anty Jamila, tun bayan tafiyar su Gudidi suka fita anguwa har misalin ƙarfe 5:pm basu dawo ba,

Gidan tsit ba kajin ƙarar komai sai na TV,  a tare suka fito parlo suna sheƙewa da dariya, Dija tace "Hajjo nifa kinsan bakina baya shiru, yau ina waɗannan yaran masu kama da sheɗanu"

Sai kuma ta rufe baki,

Hajjo ta zaro ido kafin tace "Dija ki rufa mana asiri, dan ma Allah ya taimakemu su Hajiya sun fice, zo muje muga ƙwaƙwaf kodai an tafi da su ne?"

Cikin sanɗa suke tafiya har suka iso part ɗin Talatu, a hankali suka murɗa handle na ƙofar, hangota sukayi ta kwanta saman Capet sai juyi takeyi, duk iya shegensu sai da ta basu tausayi, dukkansu sun tsorata, sbda a yanayin da suka ganta sai ka rantse idan ka matsa daga gurin zaka nemeta ka rasa.

A ƙa'idar gidan duk wani wanda bashi da lafiya, muddin babu kowa a gidan, Hajiya tace ayi gaggawar sanar da ita tun kafin ta dawo, gudun kar suyi leifi yasa Dija dawowa parlo ta ɗauki wayar tafi da gidanka ta kira Hajiya, bayan ta ɗaga kiran ta sanar mata da cewa, ɗaya daga cikin wadannan yaran babu lafiya farar me dogon baki,

Daga can ɓangaren Hajiya take sanarwa da Anty Jamila, kai tsaye anty Jamila tace "Hajiya me zai hana ki kira son ki gaya masa ya kai ta Hospital kafin mu dawo, amma fa sai kinyi masa gargaɗi.

Number Ma'aruf Hajiya ta kira, sanin muhimmanci mai kiran ya sa shi ɗauka haɗe da sallama, bayan ya gaisheta ta amsa tace "kaje gida ka ɗauki A'isha babu lafiya yanzu yanzu fa, kuma idan har na samu labarin ka wulakanta ta sai ma saɓa maka"

"Toh"
Kawai yace, tunda ya tabbatar da umarni ta bashi.

Kwance yake a saman Royal bed wanda aka lulluɓe shi da farin bedsheet, ya rungume pillow idanunsa a lumshe yake, yayinda ƙa'idojin Hajiya suka sake dawo masa, "wai kar ya kuskura ya wulakanta ta,

Juyi ya dingayi a saman bed ɗin gami da tunanin shikam ya zai yi da rayuwarsa, ko dai ya kira drivern gidan ya ce masa ya kai ta ne?,
Yana tsaka da tunani wayarsa ta sake ringing a karo na biyu, kafin ya ɗaga sai da kiran ya katse kafin ya ɗaga, kafin yai wata magana Hajiya tace "na kira su Dija sunce babu wanda ya shigo, me kake nufi ne Ma'aruf?"
"Babu abinda nake nufi Hajiya wanka na shiga"
Tabbas kalaman kare kanta da ya gaya mata, sunyi tasiri a zuciyarta, dole badan ya so ba, ya sanya ƙananun kaya wanda suka zamo a koda yaushe su yake da muradin sa wa,

Kai tsaye Lokar da yake ajiye key ɗin motocinsa ya nufa, key ɗin MBW BJ 2020Silver ya ɗauko, kafin yaje gaban mirror ya ƙarewa fuskarsa kallo, lokaci ɗaya ya haɗe rai, bayan ya kammala shiryawa ya fito cikin takun isa da ƙasaita, kai tsaye gidan su Hajiya ya nufa, bayan yayi horn mai gadi ya buɗe masa ya kutsa kai ciki, parking yayi a harabar gidan ya danna horn, mai gadi ya taho da gudu ya durƙusa a gaban Ma'aruf yana cewa "Allah ya taimakeka ubangidana, babu wasa ko alamun zai yi murmishi, "ka shiga ciki ka ce ƴar ƙauyen nan ta fito ina jiranta"

Cikin bin umarnin Ma'aruf yai sallama, Dija da Hajjo ne a parlo suna zaune saman Capet suna kallo, "wai yarinyar da tazo daga ƙauye ta fito inji Alhaji"

Mai gadi yai maganar ya juyawa ba tare da ya jira amsar su ba.
"Mtswww walhi Hajjo ina jin haushin yarinyar nan, ki ga wani har fita zai yi da ita"

Hajjo ta kama baki, kafin tace "wato kin mance bata da lafiya ko ko ba ke kika kira waya ba?, Kuma Hajiya ta kira ɗazu kin ce be shigo ba"
"Mtsw"
Dija ta sake jan tsaki a karo na biyu,
"Hmm in tayi wari ma ji, nidai na fara hasashen kina son Alhji ne, wanda idan mafarki kikeyi sai kin farka, saboda bazai taɓa sonki ba,  tunda kaf ƴan matan duniyar nan ya kasa ware ko da ɗaya ce ya ce yana so har yanzu, kinsan kuwa duk wacce aka sake aka haɗata dashi sai ta sha baƙar wuya, miskili ga jinkai da iko uwa uba sarauta kamar wani sarki bayan haka ga tarin dukiya, ke ni kaf anguwannin nan ban taɓa jin mai kuɗi irin nasu ba"
"Ke Hajjo ki tsaya a matsayinki, idan ma nace ina sonsa ai halak ne, kuma naga zan iya ne ehe "

Dija tai maganar cike da ƙufula,
Allah ya baki haƙuri,
Hajjo ta faɗa tana miƙewa zuwa kiran Talatu, a bakin ƙofa ta sameta sai juyi takeyi, tabbas abin a tausaya mata ne, duba da irin galabaitar da tayi sosai, har ya kai ga magana ma ta gagareta ga kuma rashin ƙarfin jiki ta kasa tsayuwa, rungumeta Hajjo tayi suka fito parlo, Dija ta sake jan dogon tsaki mtswww, a karo na uku, Ita dai Hajjo ko saurararta ba tayi ba, suka wuce inda motar Ma'aruf take, sai lokacin ta ɗan buɗe ƙwayar idanunta ta ɗora su a nashi, kallon tara saura kwata yayi mata, kafin yace "in zauna jiranku ne?"
Hajjo tace "a'a alhji ayi haƙuri" ta buɗe motar ta sanyata kana ta rufe murfin motar, a ɗari ya figi motar, already yace wa driver ya buɗe masa get tun kafin isowarsu, tuƙi yake kamar zai tashi sama inda ita kuma Talatu, bata ma san yanayi ba, sbda barci da ya ɗauketa,
Kai tsaye Hospital ɗin da Hajiya mama ta kwanta nan ya kaita, ko da suka shigo Hospital ɗin ko ta kanta beyi ba, ya fito dama fuskarsa na sanye da Black I glass wanda baka ganin ƙwayar idonsa, nurses na ganinsa suka taresa kasancewar sunsan waye shi, tunda tun mahaifinsa na raye suke zuwa Hospital ɗin, "akwai marar lafiya a backside" abinda ya faɗa kenan.

Kai tsaye ya wuce office na doctor wanda aka sauya bayan rashin lafiyar Hajiya, doctorn ya kasance babban abokinsa ne,
Sau ɗaya yayi nocking, daga cikin room ɗin doctor Habib yace masa "Yes come in"
Bakinsa ɗauke da sallama ya shigo,
Doctor Habib yai murmishi kafin yace "mutumina yau kai ne?"
Sai da Ma'aruf ya zauna kafin yace "ka wani hakimce a kujera kamar mutumin kirki"
Habib ya bigi ƙafarsa ta ƙasan table yace "da mutumin meye?"
Suka sheƙe da dariya,
Oh ashe dai Ma'aruf yana dariya?, sosai fa dariyar tayi masa kyau har point na kumatunsa na loɓawa, niko nace "wow, gaskiya har yanzu mun kasa ƙarasa kwatancen kyau da izza irin ta Ma'aruf,
Bayan su gaisa doctor Habib yake tambayarsa ya Fadwa?" Doctor Habib yace "tana lpy baka san tayi nauyi ba ko?"
Sai kuma ya jefo masa tambaya,
"Ina amarya fa?"
Lokaci ɗaya Ma'aruf ya nemi walwalarsa ya rasa, sbda kiran Saudart da doctor Habib yayi, "wani abin ne ya faru?"
Doctor Habib ya sake jefo masa tambaya"
Kaga abokina mubar wannan maganar marar lafiya na kawo.."
Doctor yace suje ya ganta,
Babu musu suka fito a office ɗin, "wane room aka shigar da ita?"
"Room5"
Ma'aruf ya faɗa a takaice,
"To muje"
"Sai dai kai kaje, zan leƙo ta window"
Ma'aruf yai maganar ko a jikinsa.
A tare suka nufo ƙofar ɗakin da aka shigar da Talatu, sai dai shi gogan fur ya ƙi shiga, kamar inda ya faɗa ta window ya leƙa ta, shi tun da suka zo gidansu be taɓa ƙare mata kallo irin na yau ba, ita ɗin fara ce amma ba can ba, zamu iya kiranta da wankan tarwaɗa, color na skin ɗin ta mai kyau, ni mom Islam nice nace muku me kyau fa😂 ba Ma'aruf ba.
Ta da dogon hanci bakinta yana da ɗan girma ba irin mai sa muni ba, gashin girarta yayi luff baƙi wuluk, tanada faɗin fuska, tana da manyan idanu, uhm in taƙaice muku dai, Talatu kyakkyawa ce,
Tsaki yaja mtswww, wanda yasa Doctor Habib waigowa yana kallonsa, sai kuma ya ci gaba da ƴan gwaje-gwajen da yake yi mata,
Kafin ya sake juyowa ya ga babu Ma'aruf babu alamarsa,

Sallamar su anty Jamila da hajiya ne ya sanya doctor Habib ɗagowa daga ƴan rubuce-rubucen da yakeyi, da sauri Hajiya mama ta ƙaraso tana cewa "sannu A'isha ya jikin dai?"

Yanzu ne ma take ta ƙoƙarin buɗe idanuwanta, cikin murya irin ta marasa lafiya tace "da sauƙi"
Anty Jamila ta kamo hannunta tana ɗan mammatsawa a hankali,
Bayan sun gaisa da doctor Habib ya miƙe tare da cewa "insha Allah zata warware zazzaɓin cizon sauro ne yayi mata chronic insha Allah zata samu lafiya"

Suka amsa da cewa "Allah ya yarda"
A hankali anty Jamila ta tallafo kanta da pillow kafin ta ɗauko ɗaya daga cikin ledoji biyu da suka ciko da kayan ciye-ciye, ayaba ta ɓare cikin sigarallashi tace "A'isha ki daure ki ci ko kaɗan ne"
Ba dan tana jin daɗin ba kinta ba, ta karɓa daƙyar ta haɗiye gami da runtse idanunta,
Hajiya tace "a barta haka  tunda bata so, A'isha ki fadi duk abinda kikaso a dafa miki zan kira ƴan aiki sai suyi miki" in cold voice tace "ruwan daɗi zan hya"
Hajiya ta buɗe leda ta fito da faro water ta buɗe murfin kafin tace "ga shi" a shagwaɓe tace "ai ba hi bane wannan"
Anty Jamila tace "wane iri ne?"
"Na cikin rijiyar banɗaki"
Tai maganar irin ko a jikintan nan dan a iya tunaninta rijiya ne.
Hajiya ta zaro idanu kafin tace "innalillahi wa inna ilahir raji'un" A'isha ruwan banɗaki kike sha?"
Talatu ta juyar da kai tare da turo dogon bakinta,
Dole Hajiya ta tilasta mata tasha ruwan kaɗan.
Wayarta ta ciro a bag ɗinta kana ta fara lalubar number Ma'aruf, Yana picking tace "wa ka bari da marar lafiyar?"
"Barci takeyi shi yasa na fito waje"
Ma'aruf yai maganar sbda yana son ya kare kansa,
"To mun zo gamu a hospital ɗin"
Hamdala yayi a cikin ransa, a fili yace "toh barin je sallah dan har an shiga ma"

Har akayi sallar isha'i Ma'aruf bai dawo ba, Hajjo ce ta kawo musu abinci, Dija kam tace ta tsani Talatu,
A takaice dai Hajiya ta koma gida anty Jamila ce ta kwana da Talatu a hospital,...

Please my lovely fans ayi haƙuri ba haka naso ba, walhi zazzaɓi nake tun ranar Saturday da safe, har yanzu jikina babu ƙarfi, ban samu na cika muku alkawari ba, am so sorry please I need your prayers.

meson shiga group ɗin da nake posting littafin NA KASA JUREWA kuyi saving numberta kuyimin magana da done zanyi adding ɗinku. 08141799224

Mom Islam

*NA KASA JUREWA*
      🪻🪻🪻

    Mom Islam

Inayiwa ɗaukacin al'auma barkanmu da Sallah Allah ya sa muga ta haɗu, ya Ubangiji ka yafe mana zunuban mu, ya Allah ka kyautata farkonmu da ƙarshe =

Page 29-30

Ko
End Ads