ƙamshi ne ya ziyarci hancinsa, ya jima yana sinsinarta kafin ya ci gaba da murza kan nipple ɗinta cikin salo na jiyar da ita daɗi, idanunsa a lumshe yake cewa "Baby kinsan me?" ƙara turo masa ƙirjinta tayi tana ce masa "a'a"
Murya a matuƙar sanyaye yace "walhi duk lokacin da muka kasance a tare koda ina cikin damuwa sai inji ta shuɗe babu wacce nake kallo a duniya sai ke, babu wacce nake mafarki sai ke, my baby kullum sabuwar soyayyarki tana ƙara shigata,
Tun ɗazu Talatu take gurin a tsaye, sbda ta zo kiran anty Tasneem ta ji Junaid yana ta dagargazo kalamai, mutuwar tsaye tayi lokaci guda ta sauke numfashi, ita dai bata san menene so ba, sannan bata san me akeji game da shi, janye ƙafafuwanta tayi, gudun kar anty Tasneem ɗin ta fito ko mijinta, suyi mata wata fassarar, kai tsaye bedroom ɗinta ta wuce, ta zauna tayi shiru.
After 1week
Alhmdllh Talatu ta fara nutsuwa sannan komai nata ya sauya, sbda ta rage guje guje da rawar kai, su kaɗai ne a gidan sai ƴan aiki, ko da yaushe idan anty Tasneem zata shiga kitchen tare suke shiga, sannan ko waya zatayi da mijinta a gaban Talatu takeyi, wani lokacin ma Talatun ce ma zata ji kunya itako anty Tasneem ko a jikinta,
9:am shine lokacin da mai koya mata lesson yake zuwa ya bar gidan ƙarfe ɗaya na rana,
Sosai karatu yake zama a ƙwaƙwalwarta kasancewarta mai basira,
Kuɗin da anty Jamila ta bawa anty Tasneem tass ta ƙarar dasu gurin yiwa Talatu siyayya, bayan wata ɗaya, Talatu tayi ƙiba tayi fresh ta murje harda kumatu, uwa uba harda mazaunai hips ɗinta ya fito ga shi mai ɗaukar hankali, gashin kanta kuwa koda yaushe cikin shan gyara yake, wata ranar sunday Talatu ta yi wanka ta sanya riga da skirt na atamfa, Masha Allah simple makeup tayi, sosai tayi kyau, idan ka kalli ƙirjinta ya fara fito da ƙirgen dangi sun tsa cak hakan yasa suka sake ƙara mata kyau sosai,
Ƙarfe 4:pm time ɗin sun kammala girki, sosai ta mayar da hankali a TV, tana kallo, remote ne a hannunta, ta fara ƙoƙarin sauya tasha, nocking taji daga bakin ƙafa, cikin nutsuwarta ta miƙe kafin taje ta buɗe, sai kuma ta juyo ba tare da ta kalli fuskar mai shigowar ba, dawowa tayi kana ta zauna tana ci gaba da sauya tasha, sallama yayi tare da zama kusa da ita, ciki-ciki ta amsa kamar wacce ta cusa wani abu a bakinta, "zama yayi a saman couch wacce take kallon wanda take zaune, ya ɗan danna wayarsa kafin ya ɗago kai ya kalleta, "bakya magana ne?" "Uhm" tace masa tana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, tasowa yayi daga inda yake zaune ya dawo kusa da ita kafin ya zauna tana cewa "idan babu damuwa ki zo muje shan ice cream, tasan ice cream saboda duk anty Tasneem tana wayar mata da kai, kuma ya zamo best ɗin ta sbda tana yinsa sosai, ɗago fararen idanuwanta tayi, kafin ta ɗora su a nasa cikin siririyar murya tace "sai na tambayi anty" murmishi ya sakar mata mai kyau, kafin ya miƙe yana cewa "hajiyarmu" anty Tasneem ta fito fuskarta ɗauke da murmishi tace "Arman kai ne a gidan namu?" Shima murmishin ya mayar mata kafin ya haɗe hannayensa cikin sigar roƙo yace "anty Please zamuje shan ice cream tare da wannan baƙuwar walhi yunwa nakeji" dariya ma ya bata, amma sai tayi murmishi kana tace "ba yunwa kakeji ba, kawai dai yawo zakaje"
Ya miƙe yana cewa "ƴar anty tashi muje ki rakani"
Talatu ta miƙe tana cewa "anty in bishi"
Inda tayi maganar a shagwaɓe sai abin ya birge Arman, anty Tasneem tace "jeki ɗauko mayafi"
Ta sake kwaɓe fuska, kafin tace "anty nifa ban san wanne zan sa ba" anty Tasneem ta bi ta har bedroom ɗinta, bayan sun shiga anty Tasneem ta kamo hannunta kafin tace "A'isha ki kama kanki dan Allah ki riƙe mutuncin ki, Arman ɗan uwana ne, kinga bazan shede shi ba, sannan ki san maganar da zaki dingayi, inason ki kasance mai aji da iya magana tare da sarrafa harshe,
Cikin girmamawa tace "Nagode anty"
Anty Tasneem ta fito mata da mayafi, da hand bag irin takalmin suka fito a tare, tana cewa "Arman ka kular min da Aysha fa"
"Insha Allah" ya ce mata yana karkaɗa key car ɗinsa,
Suka fice, kai tsaye motarsa suka nufa, mai kyau da tsada, kasancewar Arman ɗan uwan Tasneem ne uwa ɗaya uba ɗaya, infact ma shine autansu, suna ji dashi sosai,
Har ya buɗe backside ya ce ta dawo gidan gaba, bayan ta dawo ya rufe murfin motar suka wuce, kai tsaye gurin shan ice cream ɗin suka wuce kamar inda ya faɗa mata, sunyi nisa babu mai cewa kowa komai, a hankali yace "dama sunanki Aysha ne?" gyaɗa masa kai tayi tare da sunkuyar da kanta, me kikeson ci idan munje?"
Lumshe idanunta tayi kafin ta jingina da jikin bangon kujerar da take zaune, har suka iso bata ce dashi komai ba,
Koda yai parking ya fito, yaje ya buɗe mata, tana fitowa, ta gyara zaman mayafinta, ashe ɗaya wayar da yayi kamar yana danne-danne yana yi mata photo ne, sosai tayi kyau, idanu sai suka dawo kanta, sbda dama gurin ya haɗa da samari da ƴan mata, Arman yana tsaye can gefe yana waya, da alamu wayar da yakeyi mai muhimmanci ce, wani saurayi matashi wanda bazai girme masa ba ya tako zuwa inda Talatu take a tsaye, cikin faɗaɗa fara'arsa yace "amincin Allah ya tabbata ga kyakkyawa mai kyan hali tare da kyan zuciya, da fatan banyi laifi ba da nayi miki magana?"
Sai da ta sake gyara tsayuwar ta, kafin tace "babu damuwa, amma mai ya kawo ka gurina?" dama tun ina zaune na hango tsayuwar motarku, walhi tunda nayi tozali da kyakkyawar fuskarki lokaci ɗaya na ji na rasa nutsuwata, dan Allah kiyi min wata alfarma, yai maganar yana kallon Arman dake tahowa, kasancewar tsakaninsu akwai nisa, cikin sauri ya miƙa mata wata takarda kana yace "ki yimin koda flashin zan kira mu dinga gaisawa, yana kai ƙarshen maganar Arman na isowa, cikin takunsa mai ɗaukar hankali, shi kuma saurayin yana barin gurin, "waye wancan?" Arman yai maganar cikin yanayi na ɓaci rai, cikin siririyar muryarta tace "oho nima ban sanshi ba" ta ɓoye takardar da ya bata, koda ta kalli yanayin fuskarsa sai da gabanta ya bada rass, amma sai ta basar tare da kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta, shi haushi ma ta bashi, ko shan ice cream ɗin ma basuje ba yace ta shiga mota, babu inda ta iya, dole ta shiga motar suka wuce, again dai wani gurin shaƙatawar suka nufa, wanda ya doke wannan a kyau da tsari, dakaga gurin kasan na zuwan ƴa ƴan manya ne, koda suka fito a mota, ba samari ba, har ƴan mata hankalinsu na gurin Talatu, wata anan sukayi faɗa da saurayinta ta tashi ta barshi, kujeru ne iri iri masu kyau gunin ban sha'awa, yayi mata nuni da ta zauna a wata wacce babu kowa, kuma tana can nesa da mutane, kamar inda ya umarceta hakan ko tayi, ta zauna anan tana ta ƙarewa ko ina kallo, wasu harufan ta haɗa ta karanta wasu kuma sun gagareta ta ƙyalesu, yana can shi dai yaje sama musu abin sha, ita kuma tana zaune tayi shiru kamar mai nazarin wani abu, "Aslmu alaikum Beautiful girl dafatan na sameki lafiya?" tuno nasihar da anty Tasneem tayi mata tayi, na cewar karta yarda ta wulakanta mutane, sbda ɗan Adam daraja ce dashi, sai tayi amfani hakan, ta amsa masa sallama, hakan ya bashi damar zama ya fara gabatar masa da kansa, "da farko dai sunana Ibrahim keda?" yai maganar yana jifanta da ƙayataccen murmishi, "Aysha" ta faɗa ba tare da ta kalli inda yake zaune ba,
Sosai furta kalmar Aysha ya birgesa, domin kuwa ji yayi muryarta tayi kamar ana busa sarewa tsabar daɗi, kai tsaye yace "ko zan iya samun lambar wayarki?" Karaf a kunnen Arman dake dawowa hannunsa riƙe da wata takarda, wani mutumi ma'sikacin gurin yana biye dashi da wani kyakkyawan faranti an jere kayan ƙwalama a ciki, sam bata ma nunar da tasan da zaman Ibrahim a kusa da ita ba, sai ta wani sha ƙamshi tana sake gyara ɗaurin ɗankwalinta, ajiyar zuciya ya sauke, wace na kusa dashi yana iya tabbatar da hakan, rai a ɓace yace "malam kasan dai haramunne, yin magana da matar da ba muharramarka ba ko?" jiki babu power Ibrahim ya miƙa tare da kama bakinsa da hannu, kafin yace "dan Allah a gafarceni abokina, ya bar gurin, itako shi take kallo, saboda a inda yai maganar sai ka rantse ita ɗin matarsa ce,
Tunda yaga kallo ya koma kanta, ya tattara kayan yaje ya karɓo leda, yace ta tashi su wuce, haka dai ta tashi ba tare da tayi masa musu ba,
Koda ya fara driving, sai satar kallonta yakeyi, magana ya farayi a cikin zuciyarsa, "bai kamata in sanarwa da yarinyar nan ina sonta ba, saboda wallahi zata yimin wata fahimta da ban, zan bari idan ta ƙara girma sai in sanar mata, Yes hakan ma shine dai-dai" Ya ƙare maganar yana murmishi yana shafa sajensa, har suka iso gida bai ce mata ba, itama bata ce masa ba, koda suka iso parking space, ta fara shirin buɗe murfin mota Arman ya hanata, yana son ya yaudarar da ita suyi hira, yace "Aysha dan Allah ki tsaya kiyi karatu ki mori lokacinki karki fara soyayya yanzu Please and please na roƙeki, idan kika duba shekarunki kwata-kwata bazasu wuce 14yrs ba, kinga kinada sauran lokaci....!
Kaina bisa wuyana, insha Allah daga yanzu da izinin Ubangiji zaku dinga samun update koda yaushe.
Mom Islam 08141799224
*NA KASA JUREWA*
🪻🪻🪻
Mom Islam
Page 35-36
Sunkuyar da kanta tayi, kana ta janyo zaren mayafinta tana wasa dashi, gaskiyarsa ne, sai dai bata ma kai shekaru goma sha huɗun da ya ambata ma,
Har ya gama yi mata nasiha ƙala bata ce masa ba, sai dai jinjina kai da takeyi,
Daga ƙarshe dai suka fito a motar suka wuce ciki, gurin anty Tasneem, a parlor suka sameta tana zaune tana waya, sai dariya takeyi, "Aysha kinji ana ta kiraye-kirayen sallahar magriba Please kafin in dawo ki ajiye min abinci"
To kawai ta ce masa ta miƙe, ko da ta shiga kitchen ɗin tunani iri-iri ta farayi, sosai ta san da cewar ta shigo sabuwar rayuwa, sannan ta ga sauyi sosai a tare da ita, bayan ta gama zuba masa abincin ta kawo parlor ta ajiye a saman table ɗin dake a tsakiyar ɗakin, kafin ta wuce domin ta kabbara sallah, sbda anty Tasneem ma lokacin da ta dawo daga kitchen bata parlor,
Sai da akayi sallahar isha'i sannan Arman ya dawo, time ɗin dukkansu suna zaune a parlor, Tasneem ta kalli Talatu kafin tace "Aysha ina tsarabar mu?" murmishi kawai tayi, kana kuma tace "yana can mota"
Anty Tasneem ta sake jefo mata tambaya, "to wa kuka barwa?" Shiru tayi bata ƙara cewa komai ba, sai ga sallamar Arman, fuskarsa ɗauke da murmishi yake cewa "anty wai yarinyar nan taki bata magana ne?"
Anty Tasneem ta kalli Talatu kafin tace "Arman me ka gani?",
Sai da ya sake kallon Talatu kafin ya sake cewa "walhi anty shiru-shiru kamar ma yin magana yana wahalar da ita" a yanayin inda yake maganar sai ya bawa anty Tasneem dariya, itako Talatu tashi tayi a gurin sbda da gasken ita kanta tana jin kamar an sauya mata ƙwaƙwalwa da ma komai na jikinta, babu wata magana da anty Tasneem zata gaya mata ko faɗa bata riƙe shi a ƙwaƙwalwarta ba, a duniya tana mugun girmama anty Tasneem ko mai yasa oho, ta sauya ɗin kamar inda Arman ya faɗa, domin kuwa ada idan ka ji wacce ba'a ɗagawa ɗan yatsa sai ta karyeshi to ita ce, a yanzu kuma ko hannu ka sa mata a baki bazata ciza ba, ko meye dalili oho,
Bayan tafiyar Talatu bedroom ɗinta, Arman ya matso kusa da anty Tasneem kasancewar tana saman couch mai zaman mutum biyu, "Anty gaskiya inada shawarar da zan baki, inhar wannan yarinyar zata daɗe a gurinki, kinsan me?" Anty Tasneem tace "a'a, ƙanina sai ka faɗa ina sauraronka" Arman yace "anty dan Allah karki bari yarinyar nan ta san menene so, sannan tasan abubuwan da suka shafi soyayya, dalilina na sanar dake, shine, ya kamata ta mori ƙuruciyarta da lokacinta da tunaninta, tayi karatu mai kyau, kinga da farko dai babu wani namijin da zai kalli Aysha ya ji bata shiga ransa ba sai dai in ƙarya yakeyi, saboda Ubangiji yayi mata baiwa ta ɓangarori da dama".
Ya kai ƙarshen maganar yana cewa "anty Please ki fahimceni"
Anty Tasneem tace "wallahi Arman duk wannan maganar da ka faɗa gaskiya ce, sannan insha Allah zanyi ƙoƙarin ganin na inganta mata komai nata wanda zata yi alfahari dashi a nan gaba, bana son rabuwa da Aysha, kasancewarta yarinya mai shiga rai, ga jin magana, tunda tafiyar da zamuyi next week mai zuwa Junaid yace sai end of the year zamuyi, kaga zan sake nusar da ita abubuwan da suka dace, wlhi Arman Aysha nima ta shiga raina ba sai an kai ga maza ba, yanzu dai abinda nake so, a nemo min makaranta mai kyau sannan mai tsada wacce ake karatu sosai,
Sallama yayi mata kana ya wuce, da niyar zai bincika makarantar da za'a sakata,
Washe gari, tunda Aysha tayi sallah bata koma barci ba, tunda ta fara azkar har sai da gari yayi haske sosai, ta fito taje bedroom ta gaishe da anty Tasneem da masu aikin gidan kana taje kitchen ta ɗora ruwa, can anjima ta shiga wanka.
Ƙarfe 12:pm lokacin suna lesson a parlo, sbda har da Islamic duk yana koyarda ita, Arman ne yai sallama, suka amsa a tare, sam beji daɗin ganin wannan mai koyar da ita karatun ba, sabda sai wani kallonta yakeyi kallon ma mai ɗauke da fassara iri, iri, bayan sun gaisa da malamin kai tsaye ya wuce ciki gurin anty Tasneem, daga corridor yake ƙwala mata kira, ta fito da sauri tana cewa "Arman wannan kira haka walhi ka tsoratani, murmishi yayi kafin yace "anty an samu makarantar,
St Thomas, kuntau science Academy.
Anty Tasneem tace "wow kenan yau zaku tafi ko sai gobe, amma kuɗina yayi ƙasa abinda ke account ɗina bai wuce 100k ba, nasan ba zai isa ba"
Arman yace "karki damu ba sai kin bada kuɗi ba, amma ta shirya mu wuce, ina sauri zan wuce office daga nan"
Har anty Tasneem ta fara tafiya, sai ta dawo da baya, kana tace "dama inason in ce maka, a aji nawa za'a saka ta, kaga tayi girma fa?"
Nazari yayi kafin yace "gaskiya zan ce a sata a pr 3 yayi ko?" Badan ranta ya so ba tace yayi sai ɗan babu inda zata iya, a hakan ma adu'arta ɗaya idan aka zo yi mata intabiyu ta basu haɗin kai,
Kai tsaye parlorn ya wuce ta samu Malamin tace masa, zasu je makaranta tunda dama shi ya bada shawara sannan yace idan ta dawo gida sai ya dinga zuwa yana sake tuna mata karatun, sosai ya ji daɗi yace "inada tabbacin insha Allah zatayi ƙoƙari sosai a makaranta, anty Tasneem ta faɗaɗa fara'arta kafin tace "Allah yasa" Talatu dake zaune gaban malamin tana rubutu, itama farinciki takeyi, dan ko a yanayin mood na fuskarta zaka tabbatar da haka,
Cikin bin umarnin anty Tasneem ta miƙe ta sauya kaya zuwa riga da skirt English wear ta zura hijabi kana ta ɗauko wata ƙaramar jaka, wacce ma babu komai a cikinta sai lipstick, man baki.
Ta fito, time ɗin Arman yana can kitchen dan ya kasa zaman parlor, sosai yake kishin duk wani wanda yake da burin yin taraiyya da Talatu, malamin yayi musu sallama ya fice, duk wannan abin da Arman yakeyi anty Tasneem bata sani ba.
Sai da sukayi breakfast sannan suka wuce, ada Talatu farkon zuwanta bata jure yunwa, amma yanzu sai ta kai ƙarfe 1:pm bata ci komai ba, sabda haka rayuwar anty Tasneem take, bawai babu bane kawai ra'ayin ci ne bata da shi, amma bata hana wanda zai ci ya ci ba.
KEFFI
Kwanci tashi asarar mai rai, Saudart har ta gama idda, tunda Dady yaga ta gama idda ya fara yi mata siyayya,kamar su kayan makeup har gurin gyaran jiki yake kaita, cikin ƙanƙakin lokaci Saudart tayi ƙiba ta murje gunin ban sha'awa,
Wata ranar Asabar tana zaune a parlor tana danne-danne a wayarta, gefe kuma tirai ne na apple cikin shauƙin bin waƙar da ke tashi a wayar ta kai hannu zata ɗauki apple ɗin wayarta tayi ringing ga shi babu suna, sai da tayi ringing ta ƙatse ta sake yin ringing kafin ta ɗaga, "Aslmu alaikum da wa nake magana?"
Saudert tai maganar sabda tana neman sani,
"Dariya yayi, kai da kaji Muryar ma kasan ba ta saurayi bane, muryarsa ko daɗi babu, yace "yarinya nine Alhaji Alherin Allah, ina fatan dai kin sanni kuma zaki amshi soyayyata, saboda idan har kin amince bana son bikinmu ya wuce wata ɗaya dan nikam a shirye nake"
Abinda ya bata mamaki bai wuce, tunanin da ta farayi ba, kamar tana yawan jin labarin Alhaji Alherin Allah a gurin dadynta,
Daga can ɓangaren nasa yace "yarinya naji kinyi shiru? Ko in baki lokaci ne?"
"Eh" tace masa, sabda ko sautin muryarsa bata buƙatar ji, yana katse kiran ta miƙe zuciyarta na yi mata zafi wani dummm takeji a kwanyarta, cikin sauri ta wuce ɗakin momy, tana shiga ko sallama bata ma yi ba, dan ko lura da Dady dake kusa da momyn batayi ba, ta rushe da kuka mai tsuma zuciya, cikin muryar kuka take cewa "momy tsabar wulaƙanci da rainin wayo ko wane tarkace sai ya zo yace yana sona, walhi nidai na gaji momy zan bar garinnan Allah kuwa" Dady ya ɗan matsa a jikin momy kafin yai gyaran murya, kana yace "Saudart ki tsayar da hankalinki guri ɗaya, ba wani bane kike kira da tarkece face aminina Alhji alherin Allah, kuma nine na zaɓa miki shi a matsayin miji, Saudart ya kamata ki gane waɗannan samarin da suke ruɗarki,