x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 22 - NA KASA JUREWA book 1

  • 63001 words
  • 66000 words
  • Out of 86738 words

Category: Love Stories

Views 133

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
Sai kin zo ɗin kawai ina jiranki"
Hajiya Zaliha tai maganar tana share ƙwalla.
Suna cikin jajanta lamarin alhaji, anty Hadiza na shigowa parlor kai tsaye bedroom ɗin Hajiya Zaliha ta wuce, saboda basa parlor, tura ƙofar da zatayi ta samu sunata kuka dukkansu, da sauri ta ƙarisa tare da neman gurin zama, kafin tace "Hajiya kekuwa baki jira zuwan ba, kike sake tada hankalinki?"
Cikin muryar kuka Salma tace "anty Hadiza Dady ne ya cucemu, wannan wane irin tozarci ne, da ƴar cikinsa fa yake yawo" anty Hadiza tayi salati tare da cewa "oh ni Hadiza naga abinda ya isheni" sai kuma tace "amma dai ku kwantar da hankalinku, saboda wlhi nasa ayiwa Alhaji aikin mantau, ta inda bazai sake tuno da waccar karuwar ba, a tarihin rayuwarsa, inaso dukkanku ku cire damuwar Alhaji domin kuwa wasan yazo ƙarshe...
Salma na share hawaye tace "anty Hadiza nifa maganar mijina?" Anty Hadiza tayi murmishi tare da cewa "baki da matsala Salma, ke da kishiya har abada..
Salma tayi tafi cike da farin ciki, har tana zuwa ta rungume anty Hadiza.
K.D
Kwanci  tashi babu wuya a gurin ubangiji yau satin su Majeed da Najma ɗaya a gidansu Yaseen da Yusra kullum yana  fita aiki sai ta ɗora abinci cikin tukunya ta kaiwa dabbobin nan, suna mugun jin daɗi sosai,
Ranar ta kasance Monday tushen aiki, dama duk ranar Monday baya dawowa da wuri, tana zaune a parlor taji mararta na murɗawa, a hankali ta zube ƙasa daga saman kujerar tare da runtse idanuwanta, da alamu tana jin zafi sosai, da ƙyar ta janyo wayarta ta danna number Yaseen yana ganin kiranta ya ajiye aikin da yake yi ya ɗaga tare da cewa "my life yakike" saukar numfarfashi da yaji ne ya tabbatar masa da babu lafiya, bai sallami mutanen dake gabansa ba, bare ya kalli wanda suka zauna a harabar Company ɗin, suna roƙonsa, kai tsaye mota ya shiga hankalinsa a tashe, driving yakeyi kamar zai tashi sama saboda tsananin firgici da yake ciki,
Ikon Allah ne kawai ya kawo shi gida, lokacin ta galabaita sosai, tana durƙushe a gurin,
Cikin hanzari ya ɗagata cak kana ya kaita mota, sannan ya dawo bedroom ɗinta ya ɗauki jakar kayan baby, kana ya shiga mota suka fice, ko takan baba mai gadi bebi ba, ya dinga sharara gudu a titi, har suka iso PLATEAU hospital, kai tsaye aka wuce da ita emergency room, manya manyan likitoci ne suka taru a kanta suna bata taimakon gaggawa, yayinda Majeed yake waje yana ta zirga zirga, ko wacce likita ko doctor suka fito basa sauraren sa, hakan ba ƙaramin ɗaga masa hankali yayi ba, cikin sauri ya lalubi number mahaifiyar Yusra ya kirata, tana ɗagawa ya sanar mata da Yusra na hospital, mahaifiyar Tata, tace "gata nan zuwa"
Tun ƙarfe 12:pm suke hospital ɗin har ƙarfe 2pm bai ji wani cikakken bayani ba, sai yanzu da wani doctor ya gaiyyacesa zuwa office ɗinsa, bayan sun gaisa yace "matarka aihuwa zatayi, gashi har yanzu shiru, sannan bata da wani power a jikinta ina tunanin zamuyi mata Cs idan har ka amince, ga takarda kasa mana hannu, damuwarsa bai wuce ya ga Yursa cikin ƙoshin lafiya ba, da sauri yasa hannun tare da ɗaga hannu yana roƙon Ubangiji, kai tsaye aka wuce da ita ɗakin tiyata domin kuwa bata cikin haiyyacinta, bata san waye a kanta ba,
Bayan an shigar da ita, doctor's suka fara hada hadar fara aiki, lokaci ɗaya ta wani daƙarƙare ta zafga ƙara tare da riƙe ƙarfen gadon da take kwance, sai ga baby ya faɗo, likitocin sai hamdala sukeyi, sakamakon tausaya mata da sukeyi,
Da sauri wata likita ta fita ta samu Yaseen dake zaune a saman benci fuskarta ɗauke da murmishi tace "sir matarka ta aihu" kafin ya buɗe baki tayi gaba, Yaseen kam wani daɗi ne ya lulluɓeshi sakamakon wannan albishir da wannan likita tayi masa, da sauri ya wuce masallaci ya kabbara sallah tare da sake miƙa godiyar sa ga Allah, lokacin da ya fito daga masallaci, Momcy tana parking mota ita da kakar Yusra ta gurin mahaifiyarta, ko gaisawa basuyi ba, suka hau tambayar jikin Yusra, yayi musu albishir da aihuwarta, suma su Momcy ba'a barsu sun shiga ba, sai bayan wasu lokuta kana aka basu damar shiga, dukkansu suka shiga ko wannensu fuskarsa ɗauke da fara'a, yaro ne Kyakkyawa mai kama da mahaifinsa, ga shi jajir dashi, an nannaɗeshi cikin kayan sanyi masu kyau sosai, Yusra kam tana da barci saboda drip ne ma a hannunta shiyasa akace kar suyi hayaniya, kaka sai cewa take yi "Masha Allah yaro kamar babansa" shikuma Yaseen yanata sunkuyar da kai, ko da Momcy ta karɓi yaron ta ji wani soyayyar jaririn na shigar mata rai, a hankali ta dinga tofa masa adu'oi daga ƙarshe ta miƙawa Yaseen, shima yayi masa adu'a, tabbas bai gaji da ganin ɗansa ba, haka dai ya danne ya sake miƙawa kaka, tare da kallon Momcy yace "Momcy ki faɗa min abubuwan da ake da buƙata, Momcy ta lissafa masa ya fice, suna yi masa Allah ya kiyaye hanya,
Acan gidan Yaseen dabbobi sunyi kuka har sunji ba daɗi, tsabar yunwa Barin ma su Majeed da Najma abin sai wanda ya ganni, saboda durƙushewa sukayi gefe guda sunata kuka,
Shinan Yaseen yama mance da maganar abincin dabbobi, har aka kwana aka wuni, da yamma da ya tuna ya sa aka kai musu, yana daga Hospital ɗin yayi waya da wani tsoho akan ya zo ya kwashe dabbobin yakai su kasuwa, abar masa saniya guda biyu su za'a yanka, hakan ko akayi, su Najma sunyi kuka sosai, koba komai sun fara sabawa da nan ɗin, yanzu basu san inda za'a kaisu ba, gaskiya suna cikin wani hali,
Kai tsaye aka wuce dasu kasuwar dabbobi, inda tsohon ya zauna yake karantar yanayin ko wacce dabba, tsohon ya kasance mafarauci ne, sannan yana da sani akan wasu abubuwan, tunda idanunsa a buɗe suke, ji a jikinsa da yayi ne ma, yasa yake ta kallon dabbobin, ko da idanunsa suka sauka akan su Najma da sauri ya sake ƙura musu idanu, ya girgiza kai tare da ɗauko wani kaskon wuta kana ya zuba wani abu hayaƙi ya tashi, sannan ya matso kusa da su ya ɗibi wani ruwa mai warin gaskiya ya watsa musu, kafin ya sake ɗibo wani garin magani ya kaɗa a ruwa ya basu suka sha, sannan yayi kabbara Allahu Akbar... Allahu Akbar.... Allahu Akbar, sau uku, abin mamaki sai ga Majeed da Najma sun baiyyana cikin kayan da suka fito dashi daga gidan tun watanni takwas da suka wuce, dukkansu a durƙushe suke, sai da tsohon ya sake ɗibo wani man shafawa ya shafa musu a guwaiwar hannu da ƙafa da wuyansu, kafin ya umarcesu da su miƙe tsaye, suka miƙe tare da fara rarraba idanu, dukkansu sai suka fashe da kuka a tare, tsohon ya ɗaga musu hannu kana yace "godewa Allah ya kamata kuyi, bai kamata kuna kuka ba, ya ƙwalawa yarinyarsa kira wacce bata wuce sa'ar Najma ba, sannan ya ƙwalawa yaronsa wanda Majeed ma zai girme masa kamar da shekara ɗaya, yace "a basu ruwan wanka da abinci, shi namjin ya bawa Majeed kaya, ita kuma macen ta bawa Najma kaya, suka amsa da cewa "to"...
KANO
ana gobe birthday party ɗin Laurat, Aysha ta gayawa anty Tasneem da Umaimah, bata hanata zuwa ba, hasali ma har tambayarta tayi mai zata kai wa ƙawar Tata a matsayin gift, Aysha tayi shiruuu, sboda bata sam mai ya dace ta kai mata ba, anty Tasneem tace "gobe idan Allah ya kaimu sai in baki abinda zaki kai mata, "Umaimah zakije koh?" Aysha ta tambayeta,
"Eh man zuwa sosai ma"
Umaimah ta bata amsa, wunin ranar dai sunata tsara irin shigar da zasuyi, kai kace sune masu yin birthday ɗin,  yau kusan kwananta uku bata kunna wayarta ba, Umaimah tayi tayi akan ta kunna saboda kar Zayden yayita tunanin ko bata cikin ƙoshin lafiya amma fur taƙi sai yau, kamar jira yake yi, ta kunna wayar, aiko sai ga kiransa tare da text message, kiran nasa ta ɗaga, cikin sanyaya murya, "amincin Allah ya tabbata ga masoyiyata abin alfaharina, ina fatan dai kwana biyu lafiya?"
"Uhm lafiya lau"
"Mai yasa wayarki bata shiga,"
"Haka kawai"
"Kinason ki azabtar dani ne?"
Ta fashe masa da kuka mai sauti, da sauri ya kalli wayar dake hannunsa kana ya kara a kunnensa kafin yace "Please beauty ki gayamin meke faruwa?"
"Zayd ina sonka, bani da damar da zan iya furta maka hakan"
Ta katse kiran tare da ajiye wayar, dariya ta farayi ga hawaye na, zuba, ta share hawayen, tare da kallon gefenta taga babu kowa, hamdala tayi kana ta tashi ta shiga toilet ta ɗauro alwalah kana ta shimfiɗa sallahya sannan ta kabbara sallahar magriba, tana cikin yin Sallah sai ga Umaimah ta shigo, da alamu daga can parlorn ta ɗauro alwalah, itama ta kabbara sallah, bayan sun idar sunyi addu'oinsu, Aysha ta kalli Umaimah, kafin tace "kinsan me?" Umaimah ta girgiza kai, Aysha tace "wlhi har tunanin ranar da zan koma gidan Hajiya nakeyi, babbar damuwata yah Ma'aruf, bashi da mutunci ko kaɗan"
Umaimah tace "uhm na taɓa ganinsa sau ɗaya a wata hira da akayi dashi a TV, wlhi bana fata in ganshi a zahiri, saboda Guy ɗin akwai kwarjini sosai, ga shi Ubangiji ya haɗa masa komai duka, ance ɗan adam tara yake bai cika goma ba, nikam a ganina wannan bawan Allahan ya cika ɗari ma, ga kyau ga kuɗi ga izza wow amma fa tsoronsa nakeji" Aysha tayi murmishi kana tace "wato Umaimah, babbar damuwata komawa gidan, kamar dai yadda na gaya miki, dalilin da yasa na fara tunani, hamm uncle Junaid ya kusa dawowa kinga anty Tasneem bazata barmu a gidannan ba, i swear" Umaimah tace "faɗi ki ƙara barinma kekam da zaki sace zuciyar duk wani lafiyayyen namijin da yayi tozali dake" Aysha ta zaro idanu tare da cewa "wlhi sharri dai babu kyau"
Umaimah tace "wlhi gaskiya nake gaya miki lokaci ɗaya kika wani cika, ƙila baki ga hips ɗinki bane ko?  One Month nazo gidannan lokacin ma ƙirgen dangin da kika farayi ƙanana ne, ga shi yanzu har ana saka bra, uwa uba 3 weeks ago kika fara period, hmm ai dole ki fara tunanin makomarki, amma ya maganar makarantar ki fa?" Uhm Umaimah, alhmdulilah insha Allah na koma Abuja zan ci gaba, amma nafison mai haɗe da islamiyya" Umaimah tace "ai karatun addini yanada kyau sosai, haɗuwarmu zatayi wuya sai dai a waya, wlhi zan gargaɗeki karki kuskura ki nunawa wani wayarnan, idan ba haka ba, wlh sai kin shiga tashin hankali" Aysha tace "hauka nakeyi Umaimah?"
Aysha ta faɗa tana riƙe baki,
Sunsha hira a daren, bayan an kira sallahar isha'i sunyi suka kwanta, wayar Umaimah ta fara ringing, tana dubawa taga Zayden, ta zaro idanu, tare da cewa "Aysha ga masoyinki ya kira, tayi kamar bazata karɓi wayar ba, ta miƙa hannu ta karba tare da karawa a kunnenta, "aslmu alaikum"
Tayi sallama,
"Wlkslm" Zayden ya amsa, daga jin muryarsa ma ta nuna yanayin damuwar da yake ciki,
Kafin yace "beauty dan Allah ina son in roƙeƙi wata alfarma, sannan inason ki gayamin iya gaskiyarki saboda bana son ƙarya.."
In Cold voice tace "ina jinka"
"Aysha kina sona, tsakaninki da Allah?"
"Tayi shiru, kafin tace "eh sosai ma"
Yace "good"
Ya sake cewa "Aysha bana son idan muna magana ki dinga katse min kira"
Cikin sanyin murya tace "bazan sake ba"
A karo na uku ya sake cewa "yanzu meye yake damunki?"
Ta marairaice murya tare da cewa "babu komai"
"Yaushe zamu haɗu"
Kai tsaye tace masa "ko gobe"
Yace "a ina zamu haɗu?"
Ta jujjuya idanu kafin tace "zan kiraka, ƙawata ce zatayi birthday"
Yace "okay, Allah ya kaimu"
Tunda ya katse wayar Aysha, tunani iri-iri ya dameshi, sakamakon sonta da yake neman zautar dashi, duk inda ya zauna sai ya yi maganarta har cikin danginsa da abokansa, shi kasansa ya kasa misalta son da yake yi mata, wanda bai taɓa yiwa wata mace a faɗin duniya ba"
Itama a nata ɓangaren haka ne, soyayyar Zayd ta fara nisa a zuciyarta.
Har Umaimah tayi barci tana rungume da wayarta...
Washe gari
Tun bayan da sukayi sallahar asbha suka fara aikace-aikace, daga nan sukayi wanka, already dama babu school sboda malamar su anyi wa wata Malama cs headmastern su shima yana Hospital,
A gurguje sukayi breakfast sukuma masu aikin sukayi moping,
Ƙarfe 9:am abinci ya kammalu aka jere a dinning, sai da suka shirya tsaf, cikin Abaya baƙaƙe, sunyi matuƙar kyau, saboda abayar ta amsa sunanta, duba da ƙyaleƙyalen dake jikinta, duk wanda ya kallesu tabbas sai ya sake kallo, saboda har wani walwali takeyi sukayi rolling veil ɗin a kansu, ba wani abinci mai yawa sukaci ba, tsabar ɗoki da murna, anty Tasneem ta kawowa Aysha wata haɗaɗɗiyar sarƙa mai zobe, da turare mai tsada harda su ribom masu kyau, Masha Allah sunyi kyau sosai, Aysha tayi godiya tare da cewa "anty bakice munyi kyau ba"
Anty Tasneem tace "wlhi kunyi kyau sosai, sukayi hoto,
Tare da yi mata sallama, kasancewar ko wacce ta fito da hand bag ɗinta, anty Tasneem ta miƙawa Umaimah 10k tace ko zasuyi siyi wani abun, sukayi mata godiya kana suka wuce.
Kai tsaye parking space suka nufa, sukayi wa driver kwatancen anguwar da zai kaisu, suka shiga backside yayiwa motar key bayan an buɗe masa get.
Cikin ikon Allah suka iso anguwarsu Laurat har ƙofar gida ya kaisu, suka gaya masa time ɗin da zai dawo ya ɗauke su, ya wuce.
Nocking sukayi a get na gidan, mai gadi ya leƙo tare da cewa "sannunku daga ina?"
Umaimah tace "nan ne gidansu Laurat?"
Da sauri mai gadi ya gyaɗa kai gami da cewa "eh nan ne, amma daga ina kuke, kuyi hakuri wannan tambayar da nakeyi muku tana ɗaya daga cikin sharuɗan shiga wannan gidan"
Aysha tace "babu komai, ta buɗe hand bag ɗinta kana ta ciro wata ƴar takarda sannan ta miƙa wa Umaimah, tace ta kira mata lambar, ringing ɗaya Laurat ta ɗaga tare da cewa waye?" Aysha tace "gamu a ƙofar gidanku"
Cike da murna Laurat ta katse kiran tare da fitowa harabar gidan tana yiwa mai gadi magana akan ya buɗe musu get, bayan ya buɗe musu suka shigo, wow, hmm masu karatu gidan fa Masha Allah komai yayi, hatta motoci biyar ɗin dake jere a gurin ajiyar motoci duk na yayi ne masu tsadar gaske, Laurat tana sanye da gown irin ƴar kanti, kanta yasha gyara sai sheƙi yake yi Masha Allah, daga nan tayi musu iso zuwa cikin gidan, babu kowa a gidan, saboda an ɗaga birthday ɗin, sakamakon Dad ɗin ta yace ta bari sai next week, Aysha kuma bata sani ba shiyasa suka zo, kai tsaye ɗakinta ta kaisu, ɗakine babba kai kace ɗakin wata macen, Masha Allah ɗakin yayi kyau, bayan sun shiga suka zauna a wasu ƙawatattun kujeru, Laurat ta fita zuwa kitchen, ta kawo musu sakwara da miyar egusi, da kunun gyaɗa mai ɗumi wanda ya ji coconut da milk,
Bayan ta ajiye musu a saman table ta koma ta zauna, kafin suka fara gaisawa, nan take gaya musu ai an ɗaga birthday ɗin, Aysha ta ciro kayan da Anty Tasneem ta bata ta miƙa mata, sosai Laurat tayi farinciki da wannan tsaraba, saboda a halin yanzu sun shaƙu da Aysha sosai,
Basu wani ci abincin sosai ba, Laurat ta ƙurawa Aysha idanu, A'isha dai da ta gaji da kallon da Laurat keyi mata tace "ke ya dai lafiya?"
Laurat ta sauya mood zuwa na damuwa, kafin tace "Ƙawar Aysha Please sunanki fa?" Umaimah tayi murmishi kafin tace "sunana Umaimah, ni ƴar uwarta ce" Laurat tace "alhmdulilah"
"Dan Allah Umaimah ki taimakeni akan manufata Please ku fahimceni dan Allah"
Sosai ta jefasu cikin alhini duk da basu ji me take son cewa ba,
Laurat ta sakko ƙasa tare da durƙusa guwaiwoyinta ƙasa, ta haɗe hannayenta kafin tace "dan Allah Aysha kiyimin wata alfarma dan Allah"
Aysha tace "Laurat wace irin alfarma ce hakan, da har kika durƙusa min?"
Laurat ta shiga gallery na wayarta ta nuno wani kyakkyawan hoto, wanda wani matashi ne a jikin hoton, shi ɗin ba fari bane, baƙi ne, sannan baƙinsa ba mai muni bane, yanada gashin baki mai kyau, sannan ya gyare sumar kansa, ta nunawa Umaimah, kafin tace kinsan wannan?"
Umaimah ta gyaɗa kai, tare da cewa "wannan ai yayi ambassador a ƙasar waje, kuma har yanzu ana damawa dashi dan na gaban goshi ne, ga kuɗi kamar zai kasheshi" dukkansu basu san me take nufi ba, tace "kuyimin alƙawarin duk abinda nace zaku amince" a tunaninsu wata maganar ko neman shawara takeyi, cikin haɗin baki suka amsa da cewa "zamu amince"
"Laurat tace "Aysha dan Allah ki auri Dad ɗina, shine a jikin hotonnan, ni kaɗai nake zaune a gidannan sai masu aiki, sannan shi bai cika zama a Nigeria ba, sannan yana dawowa Nigeria baya cin abincin waje ko na masu aiki nice nakeyi masa, tun bayan rasuwar mahaifiyata, tana aihuwata ta rasu, wlhi tallahi Aysha baki da matsala da Dad, ƴan uwansa sunyi masa maganar aure har sun gaji dan Allah ki taimakeni"
Laurat ta ƙarshe maganar tana, sake cewa "karki manta keda Umaimah kunyi min alƙawari, sannan Ubangiji yana girmama alƙawari"
Kuka take yi sosai, yayinda Aysha ta daskare a gurin, Umaimah kam ta kasa koda motsa bakinta ne, tsabar firgici, saboda basuyi tunani ko tsammanin jin waɗannan zafafan kalaman daga bakin Laurat ba, ta sake fashewa da kuka tana cewa "Please nasan zaki iya kinada hankali nutsuwa tausayi da duk wani hali na gari da namiji ya kamata ya samu gurin mace, Please say something...!

Tofa, 2days nayi talauci, rashin data yasa banyi muku posting ba, kuyi hakuri dan Allah.

Mom Islam ce 08141799224

*NA KASA JUREWA*
💋💋💋
💋💋
💋
          Mom Islam



Page 61-62

"Innalillahi wa inna ilahir raji'un"

Hajiya Lubabatu ta ambata, cikin yanayi na damuwa, kana ta ci gaba da tafiya tana jimamin Gudidi, babbar damuwarta ina zataje..sannan da su wa zata hadu...a wane hali zata kasance?"
Har ta iso gurin get ɗin gidanta tana ci gaba da tunaninta,  nocking tayi mai gadi ya buɗe mata, kana yayi mata sannu da dawowa ta amsa tana shigewa ciki, tun kafin ta kai ga shiga cikin gidan ta fara ƙwalawa Rukaiyya kira, amma shiru, kamar babu kowa a gidan, sosai ranta ya ɓaci ta shiga ɗakinta tare da duba ko ina babu Rukaiyya babu alamarta, wasu kaya
End Ads