x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - NA KASA JUREWA book 1

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 86738 words

Category: Love Stories

Views 119

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
Allah dan Annabi Talatu kiyi haƙuri bazan sake ba, daga yau zan dinga ce miki abinnan da ƴan binni suke gayawa yayunsu, Antu yake ko meye ma? "In kinso kice gwaggo babu abinda yai tsalle ya wankan mari, kizo kawai mu cire raini, ta cukuikuyo mata wuyan hijabi, ƙara Gudidi ta tsanda wanda yaja hankalin malam dake biyawa ɗaya daga cikin ɗaliban karatu, da sauri ya tashi tsaye da zafgegiyar dorina yace...!




Page 7-8
"Wai ke wace irin sheɗaniyar yarinya ce?, a islamiyya ma bazaki rabu da wannan yarinyar da kika sa a gaba ba? kullum sai an rabaku faɗa kenan"

Haba ai tunda Gudidi taji malam yana yiwa Talatu gargaɗi, ta saki baki ta fara bashi labarin rashin jin Talatu, a take a gun ya tsula mata bulala har uku, sam batayi kuka ba, sai dai tayi ƙwafa, irin "zamu haɗu ɗinnan"
••••••••
SINGAPORE
Bulan Island
Wani haɗaɗɗen gida na hango wanda komai nasa da remote yake amfani, hatta get ɗin ya haɗu ya gama haɗuwa, kutsa kaina nayi ciki yayinda nake ta ƙoƙarin kwaso muku jawabi, ƙarewa farfajiyar gidan kallo nayi, wanda yai matuƙar ƙayatar dani, "Masha Allah" na faɗa a cikin zuciyata, gidane na gani na faɗa, gidane wanda idan ka shige shi zaka rantse waɗannan mamallakansa basu da labarin talauci a duniya, sosai yanayin tsarin shuke-shuken zai birge me karatu, hmm yo gini ne na turawa,
Wata matashiyar budurwa ce ta fito daga wata ƙofa, wacce na tabbatar da ta danna wasu lambobi ne yasa ƙofar buɗewa, a ƙalla budurwar zatayi 23yrs cikin shiga ta nuna tsaraici, daga ganinta kasan babu musulunci a tare da ita, riga ce a jikinta ƴar yaloluwa milk color, ko Cibiyar ta bata rufe ba, sai ɗan mini skirt ɗin dake jikinta pink color iya cinya, kayan sun matseta sosai, ƙafarta kuwa takalmi ne mai bala'in tsini, duk igiyoyi ne a jikinsa, hannunta riƙe da handbag, gashin kanta har gadon baya, fara ce tass kunsan dai fari irin na turawa, ita ɗin baturiya ce..
Batsha kenan yarinyar mai ji da kyau.
Ci gaba da tafiya tayi, inda ta iso parking space securities suna take mata baya, ɗaya daga cikin scuritin shine drivernta, bayan ta shiga back side shikuma ya shiga mazaunin driver, "Madam ina zamuje?"
Yai maganar cike da girmamawa,
Am sorry to say da yare suke maganar, mukuma zamu ci gaba da yarenmu na Hausa, lolx.
"Kaini Ariana hotel"
Okay scuritin ya faɗa cike da girmamawa,
Tunda suka iso Hotel ɗin na gama tsinkewa, saboda kai da kaga kyau da tsarin gini kamar ba da bulo akayi ginin ba, ga wasu flawoyi da walwali da gurin yakeyi, bayan an buɗe musu get ya kutsa motar ciki, a inda ake parking ya ajiye motar kana ya fito ya buɗe mata ƙofa, takai kamar 10mins bata fito ba, can sai gashi ta zuro kyawawan ƙafafunta wanda suka sha adon jan farce mai kwalliya, buɗe hand bag ɗinta tayi kana ta ciro wayarta ƙirar 💕 ta kara a kunnenta, "Hello Vijay ka gayamin number"
Daga can ɓangaren wanda ta kira da Vijay ɗin yace "144" ta katse kiran tana yiwa scuritin alama da ya tafi, girgiza kai yayi kana ya shiga mota ya wuce.
A hankali take takawa kai kace tana tsoron taka ƙasa, har ta isa cikin Hotel ɗin, my fans Ina baku labari wani sassanyar sanyi naji ya ratsa kowacce gaɓɓa ta jikina, tunda nikam ba saba zuwa nayi ba, amma anam zan barta,
Bayan tayi musu bayani, ba tare da ɓata lokaci ba kai tsaye ta wuce room ɗin, yana zaune saman bed ta sameshi daga shi sai boxer ƙirjinsa a cike da gashi,
Yana ganinta ya miƙe tare da hugging ɗinta ya manna mata kiss a kumatu yana cewa "i miss You pretty"
Wani farr da idanu tayi masa wanda ya daɗa sace zuciyarsa, ya wani rungume ta ya sinsinar wuyanta, my pretty wane irin turare kike using kowane time sai inajin shauƙi idan muna tare" rufe masa baki tayi da nata, kana ta kashe masa one eye tace "uhhh muyi selfie mana, two days bamu haɗu ba"
Kamar koda yaushe idan sun haɗu sai sunyi hoto, yau ma hakan ta kasance, tana rungume a ƙirjinsa shikuma babu riga ga shi ƙirjin nasa duk gashi yayi masa luff, ta wani kwantar da kanta a saman ƙirjinsa, sunyi kyau sosai, kamar koda yaushe idan sukayi hoton suna ɗorawa a media, haka yau ma ta kasance, duk wasu kafafe da suke yi sai da suka ɗora shi.

ABUJA NIGERIA
"Saudart!! Saudart!! Saudart!!" firgit ta tashi daga barcin da takeyi, jiki na karkarwa sbda wannan kiran da yakeyi mata cikin ƙaraji yakeyi,
"Na am" tace, murya a sanyaye, tana takowa har inda yake,
"Saboda yawon dare da kike zuwa ne yasa baki tashi da wuri ko?"
"Yaya ban fahimci abinda kake cewa ba?"
Sai da Ma'aruf ya ƙare mata kallo up and down kafin yace "oky kinaso in baki labarin fitarki ta jiya ne?"
"Jiya kuma zuwa ina?"
"Zuwa gidan ubanki"
Ma'aruf ya faɗa ransa a ɓace, "are you nonsense?, me kike nema a duniya, Saudart na tsaneki na tsaneki har abada bazan sake sonki ba wallahi ki ficemin a gida, ya sanya hannu cikin aljihun wandonsa ya ciro bandir na ƴan dubu-dubu, guda biyu ya watsa mata tana durƙushe a gurin tana rusa kuka, hannunta na karkarwa da wayarsa a hannunta, ya fizge tare da shureta da ƙafafuwansa, har ya fara tafiya, sai kuma ya dawo da baya, ba tare da ya juyo ba, cikin kakkausar murya yace "zan shiga wanka, idan har na fito da ga wanka baki bar min gida ba sai kinyi nadama"
Ya ƙare maganar yana cigaba da tafiya.
Rushewa tayi da kuka mai tsuma zuciya, a fili ta dinga maimaita innalillahi wa inna ilahir raji'un, zafafan hawaye ne suke ta zarya a kumatunta,
Jiki babu ƙwari ta miƙe, a fili ta sake furta "na gaji da wulaƙanci da cin mutunci, cikin ƙarawa kanta ƙwarin gwaiwa tace "ko me za'ayi yau sai ya sakeni, idan ya sakeni shikenan, Dady bazai sake matsamin akan komawa gidansa ba"
Tayi maganar tana share hawaye,
Yaushe rabonta da ta shiga sashen sa, har ta manta,
Cike da ƙwarin gwaiwa ta ci gaba da tafiya har ta iso ƙofar ɗakinsa, inda kasan ƙwai ya fashe mata a ciki haka tayi, ƙirjinta sai dukan uku-uku yakeyi, da sauri ta sake ƙoƙarin kawar da tsoro, ta yi nocking da ƙarfi, sam beyi tunanin ita ba ce, sbda tunda waɗannan abubuwan suke faruwa ko inda yake bata zuwa, buɗe ƙofa yayi fuska a tamke, daga shi sai gajeren wando da farar singileti ya waro ido, sai kuma yaci magani yace "wa ya baki izinin zuwa bakin ƙofa ta?"
"Babu wanda ya bani izini tunda ba gidan ubana bane"
Sosai yayi mamakin zafafan kalaman da Saudart ta gaya masa,
Ya ɗaga hannu zai kai mata mari ta riƙe hannun cikin ƙarfin hali tace "a wannan karon na kasa jure wulaƙanci da tozarcinka, haba Ma'aruf, ko a bola ka tsintoni ai na ci darajar ɗan adam, bare a gidan iyayena ka auroni, ko dan kaga iyayena basu goyamin baya ba? to ka sani wallahi tallahi yau sai ka sakeni nagaji na gaji, NA KASA JUREWA wulaƙancinka, ta ƙarisa maganar hawaye na sake wanke mata fuska....!

Please kuyi manege.

Mom Islam ce
Ayi following ɗina fisabilillah
*NA KASA JUREWA*
       🪻🪻🪻

       Mom Islam

Page 9-10

Cikin isa da jiji da kai ya furzar da isa mai huci kana yace "me kike nufi?,  ba dan an takura min ba me zan ci dake?, kinga ni sauƙi ma kika nema min kije na sakeki saki uku"

Kafar a kunnen Hajiya mama dake ta kwaɗa sallama tun daga parlo bataji motsin kowa ba, a take a gurin ta faɗi sumammiya, cikin azama Saudart ta taho da gudu zata taimaka mata, yai saurin dakatar da ita gami da cewa "idan har kika taɓa ta wallahi sai na illata ki"

Ko da jin haka ta miƙe zuciyarta fess dan har ta fara jin tausayin Hajiya, tunda ya gaya mata magana tayi ta kanta, cikin farinciki da samun ƙwarin gwaiwa ta harhaɗa komai nata, kuɗin da Anam ta turo mata ta sake dubawa, a fili ta tace "hmm wallahi bazan sanarwa kowa maganar sakin nan ba, amma fa dole in nemo sheda kodan kar Dady yace min ƙarya nakeyi.

Biro da takarda ta ɗauka zuciyarta fess ta wuce ɗakinsa, a bakin ƙofa ta sameshi yana yayyafawa, Hajiya ruwan sanyi, tace "yaya nazo ka rubuta min shedar saki"

Babu musu ya karɓa saboda har ga Allah ta zame masa tamkar gobara, duk da tashin hankalin da yake ciki na suman Hajiya be hanashi rubuta mata saki ba, ya miƙa mata tare da cewa "kafin inje asibiti in dawo kar in sameki anan"

"Ai bazaka sameni ba, yanzu kam meye haɗinka dani, Allah yabi bayan me gaskiya" ta faɗa tana wucewa abin ta,

Ko saurar ta beyi ba ya kin kimi Hajiya zuwa parking space yana ƙwalawa Idi mai gadi kira, da gudu Idi ya taho yana cewa "lafiya kuwa alhjaji?"

"Dalla can buɗe min get, lafiya ne zan dinga yi maka wannan kiran?"

Jikin Idi na rawa yai azamar zuwa buɗe masa get sbda yasan halin uban gidan nasa.

A guje ya fice daga gidan kamar wanda zai tashi sama, cikin ransa ya dinga mai-maita innalillahi wa inna ilahir raji'un, har suka iso (Mai tama District Hospital)

Emergency room aka wuce da ita, inda aka bata taimakon gaggawa,

Duk wanda ya kalli fuskar Ma'aruf ko ba'a gaya masa ba yasan yana cikin matsanancin tashin hankali, adu'arsa bata wuce Allah yasa babu abinda ya sami hajiyarsa ba, idan kuma ta kamu da wani ciwon ta sanadinsa fa?"

Gaskiya bazai yafewa kansa ba.

Duk wani likita me shige da fice a ɗakin da aka kwantar da Hajiya, sai ya bishi yana cewa "likita dan Allah ya farfaɗo? likita tana magana?,

Inda kasan zautacce haka ya koma, wayarta dake hannunsa ya kalla, a sanadin faɗuwarta, duk ta farfashe, ya kawar da kallon wayar da yake sakamakon rurin da wayar ta farayi,

Sunan Anty Jamila ya gani yana yawo a fuskar wayar, sosai gabansa ya bada rass, lokaci ɗaya zufa ya fara karyo masa, be san amsar da ze bata ba, ƙarfin hali yayi ya ɗaga a ɗarare yace "As...asalamu a.."

"A'a Ma'aruf yakuke ina Hajiyar?"

Shiru yayi bai bata amsa ba, jin shirun yayi yawa, ta katse kiran ta sake kira, dolensa ya ɗaga, duk girman kansa da jan ajinsa baya yiwa mutum biyu, idan ka cire mahaifinsa da ya rasu, wato Hajiyarsa da Anty Jamila ƙanwarta kenan.

"Kayi magana mana, wai meke faruwa ne Ma'aruf?"

"Hajiya na hospital"

Kalmar da ya iya gaya mata kenan ya katse kiran.

Sosai hankalinta in yayi dubu ya tashi, ta fara harhaɗa kaya,

ƘAUYE

Ko da aka tashi daga islamiyya kowa ya watse amma Talatu bata matsa ko nan da can ba, sbda tun kafin a tashe su malamin ya fita, anyi masa kiran gaggawa,  ɗaya daga cikin manyan ɗaliban ne ya yi musu addu'a kowa ya watse, har lungu Talatu taja wuyan hijabin Gudidi, mutane biyu ne a biye dasu,  ɗaya sahura ce ƙawar Gudidi, ɗayar kuma Lantana sunanta ƙawar Talatu,

Rawa suke tiƙa sunayi musu waƙa suna cewa ...

"🎺A casu mata a casu, ku casu ba me rabaku araba ace anyi cuta, a zamanin nan na yanzu"

Sosai suke tiƙar rawa, kan kace me har Talatu tayiwa Gudidi lilis, babu mataimaki sai Allah, duk su biyun ƙawayen nasu basu isa suja da ƙarfin Talatu ba, sosai ta haɗawa Gudidi jini da majina, kafin faɗan ya ƙare, Gudidi na tafiya tana ɗingishi, tace "Hegiya maiyya jaka me ƙarfin Allatsine me kai kamar na duwatsun murhu"

Talatu ta biyota da gudu, itama gudun takeyi tana ɗingishi har ta ƙarisa gidansu,

Tana shiga ta samu Tabaiyye da malam sai uban musayar yawu suke yi, ita kuma ta shigo tana kuka babu wanda ya saurareta,

Wucewa tayi ɗakin Tabaiyyen ta kwanta a ƙasa ko zataji sassaucin mutsikar da tasha gurin Talatu.
Malam ya gyara zaman babbar rigarsa kana yace "Wallahi wannan hine gargaɗi na ƙarhe idan kika sake ragemin hatsi  kowa ze kama gabansa"
Cikin masifa Tabaiyye tace "yo in kama gaban nawa mana, ka gayamin me na tsinana tunda na aureka, kaf kiwon da iyayena suka haɗoni dashi sun ƙare, me kake dashi da zan ɗin ga ɗiba? ta gyara ɗaurin zaninta taci gaba da cewa "ko yanzu na fita a gidanka zan samu saurayi sabo fil gada gau me jini a jika"
Tun da ya ji ta faɗi haka, ya wuce ƙofar ɗakinsa kana ya ɗauki buta ya kuskure bakinsa, har ya nufi hanyar zaure ya juyo  yace "Tabaiyye kiji ta tsoron Allah karki ragemin masara"
"Da tsoronka nakeji mtsw"

Tai maganar tana yatsina masa fuska.
Hankali kwance Talatu ke tafiya har ta iso gida, tunowa da babbar baƙuwar da Inna ta gaya mata zasuyi ne yasa ta washe haƙora, a fili tace "na rantse da Allah ina son ganin ƴan binne" da gudu ta shige tana cewa "Inna dan Allah ki biyoni ban ɗaki da buta tsuuuuu (Gudawa) nakeyi"
Sam bata ma ga Anty Jamila dake zaune saman tabarma ba, cikin ɗaga murya Inna tace "Talatu zanci mutuncin ki", tana ƙare maganar ta miƙe takai mata buta,
"Yauwa Innata idan nai aure zanyi kewarki"
Ko ƙala Inna batace mata ba ta dawo gurin Anty Jamila.
Murmishi Anty Jamila tayi kafin tace "wallahi A'isha tana birgini"
Inna tace "taɓɓ bakisan waye A'isha bane"
"Haba Inna ai Kowane yaro da ƙuruciyarsa"
"Hakane kam"
Inna ta faɗa tana dariya.
Bayan ta fito daga banɗaki ta ware idanunta, fess ta ɗora su kan Anty Jamila, washe jajayen haƙoranta tayi kafin ta taho da sauri tace "ahe kin ƙaraso Inna Jumai?"
"Na ƙaraso A'isha, amma sau nawa zan ce miki bana son ki dinga ce min jummai?"
"To kiyi hakuri yasin mancewa nakeyi, amma dai kinzo kiyi mana wata da watanni ne ko?"
Anty Jamila tai dariya kana tace "a'a yanzu ma daga Madobi nake gobe insha Allah zan koma Abuja"
Zaro idanu Talatu tayi sai kuma ta matso kusa da Anty Jamila tace "dan Allah ina Hajiyar nan da take zuwa tana raba mana hinkafa?"
Anty Jamila tace "Hajiya tana gida, sbda rashin lafiyarta ne ma zan koma gobe"
"Ahe bata da lafiya?"
Talatu ta faɗa tana ƙara tattaro nutsuwarta, kai kace dagaske,
Ita ko Anty Jamila duk tambayar Talatu tayi mata sai ta bata amsa.
Koda Inna tazo ta samesu sunata hira, abin yai mata daɗi,
Tace "Jamila kuna zantawa ne da ƴar taki?"
Anty Jamila tai murmishi.
Jollof ɗin dawa da wake Inna ta kawo wa Anty Jamila, ayko taci sosai ba laifi dan kaɗan ta rage tasha ruwa,
Wayar Anty Jamila ta fara ringing,
Ganin sunan Ma'aruf yana yawo a kan screen ɗin wayar yasa tai saurin ɗagawa, tare da cewa "my Son ya akayi?"
"Anty Jamila Hajiya fa bata magana kwata-kwata"
Cikin firgici Anty Jamila ta fara mai-maita "innalillahi wa inna ilahir raji'un"
Kana tace "son kayi haƙuri yanzu dare ya fara tunda ana shirin kiran sallahar magriba, insha Allah gobe ƙarfe huɗu zan taho, Allah ya bata lafiya"
Sosai hankalin Anty Jamila ya tashi, sanda a iya saninta Hajiya ba ta taɓa irin wannan ciwon ba.
Nan ta labartawa Inna abin da ke faruwa, Inna tace "itama zata bi Anty Jamila su tafi tare"

Talatu tace "taɓɓ wallahi he anje dani kawai ki tafi har binni ki barni hu'um"
"Ba fa wani abin daɗi ne ze kaini can ba, rashin lafiya ne, kuma befi in ɗauki kaya kala ɗaya ba"
Da ƙyar da lallashi dan sai da Anty Jamila tayi mata alkawarin zata turo me mota ya kawo ta Abuja sannan ta amince,
A daren Inna ta haɗa mata kayanta a bako sbda kafin su wuce zata kai ta gidan mahaifiyar babanta.

Bayan sallahar isha'i, suka wuce gidan Kaka, da sallama Inna ta shiga kafin tace "zauna mana ai dai kya gaihe ta"
"Ina wuni"
Talatu ta faɗa tana turo baki, "lafiya lau ƙawata na ganki da jakar kaya?"
Inna tace "wallahi na kawo ta ne zamu wuce Habuja gobe saboda Hajiya Habiba babu lafiya"
"Ash sha, Allah ya bata lafiya, zaki daɗe ne?"
"A'a kwana ɗaya zanyi"
Inna taba kaka amsa, kaka tace "to ki ja mata kunne banda rahin kunya, dan ba kowa bane ze ɗauka"
Sosai Inna tayiwa Talatu faɗa kana tayi musu sallama, bayan ta miƙa wa Talatu ɗari biyu taba wa kaka ɗari uku,
Kaka ta washe haƙora tana cewa "Allah ya tsare, "maiyyar kuɗi" Talatu ta faɗa tana hararar kaka"
"Nayi ɗin naga uwarki ce ta bani ko?"
Koda taji barci kaka ta hanata hawa gado wai kar tayi mata fitsarin kwance, sai da Talatu ta bari kaka tayi barci kana ta lallaɓa ta kwanta can gefenta,
Kaka dai tasan ta hana Talatu hawa gado, gashi fitila ta mutu, tunda su basa ganin wutar lantarki, cikin ihu da kururuwa take cewa "ke Talatu tahi ki gani kwarto"
Tunda Talatu taji kaka ta faɗi haka, ayko ta kunce zanin kaka ta cukuai kuyeshi, ta janyo hannun kaka kiiiii ta janyo ta ƙasa, ta haye gadon daga can inda take ta sauya murya tace "ke ƴar tsohuwa jiya naji kina adu'ar Allah ya baki miji hine nazo mu shirya"
Haba kaka ta sake rikicewa, bakinta na rawa tace "nifa tsohuwa ce haba kai kuwa baka ga jikina duk a tamushe ba, na roƙeka nidai ban ce haka ba"
"Zo nan"
Talatu ta faɗa cikin daka tsawa, ganin kaka ta rikice sosai yasa ta koma kan gadon ta kwanta tunda tasan bazata taba komawa ta kwanta acan ba.
Ƙarfe huɗu na asbha Anty Jamila ta farka, dan ba wani barci me nauyi tayi ba, ko wanka batai ba, ta shirya cikin leshi Black anyi masa ado da zare golden color me adon duwatsu farare, mai kawai ta mutsika, tayi tunanin Inna tana barci sai taga itama har ta gama shiri, kasancewar basu da wani kaya me nauyi suka fita neman me mashin, sbda masu mashina ba kasafai suke yawo ba, kasancewar ƙauye ne sosai, idan kaga mashin sai na masu zuwa gona, can maƙotansu Inna taje ta roki alfarma, tai sa'a yaron gidan na nan, ya fito da mashin ɗinsa suka hau zuwa tasha,
Sai da suka ƙarfe shida kafin motar ta cika, sannan suka fara tafiya...!

Ayi haƙuri jiya baku ga posting ba, wallahi kuna raina kunsan weekend mutum ba shi da wani hutu sosai.

Mom Islam ce 08141799224
*NA KASA JUREWA*
       🪻🪻🪻

       Mom Islam






Page11-12

Kai tsaye asibitin suka wuce, koda suka iso
End Ads