x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 12 - NA KASA JUREWA book 1

  • 33001 words
  • 36000 words
  • Out of 86738 words

Category: Love Stories

Views 124

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ya faɗo masa, da sauri ya nufi hanyar ɗakin Saudar ɗin,
Ko da ya tura ƙofa, cikin sa'a ya hangota, ta rungume Saudart kamar wata jaririya, sai da ya tsaya ya gama ƙare musu kallo basu sani ba, kafin ya ci gaba da tafiya a hankali ya shigo ɗakin, ciki-ciki yayi sallama inda babu mai jinsa, domin zuwa yanzu jikinsa yayi sanyi, hamdala yayi, da yaga Saudart ɗin ma tayi barci, ya matsa kusa da Momy kana ya ɗaga Saudart daga cinyar Momy ya kwantar da ita a saman bed, Momy dai bata ko ɗago kai ta kalleshi ba,  cikin tausasa harshe yace "dan Allah Zainab ki zo muje ɗakina ba danni ba dan Allah"
Yai maganar yana kamo hannunta, miƙewa tayi, har yanzu bata ce dashi komai ba, tana dai kallonsa kawai, sbda itakam yanzu mamaki yake bata gami da tsoro, sabda tsoransa takeji sosai.
Bayan sun shigo bedroom ɗinsa, ya zaunar da ita a saman bed kai kace ƙaramar yarinya, ya je yayiwa ƙofar key wai duk sabda kar ta fice, ya durƙusa a gabanta harda kuka ya fara magana "Zainab nasan kin rufa min asiri, inason ki sake rufamin dan Allah Zainab ki fahimceni, duk wata fafutuka da nakeyi domin muji daɗi nakeyi, Zainab idan har kika tona min asiri me kike tunanin zai faru, zagi zato fargaba, duka zasu shigemu, amma idan kika rufamin asiri tabbas nikuma zanyi miki halarcin da kaf maza kafin a samesu sai an tona, Zainab a yau ki faɗi duk wani abu da kikeso a duniya wallahi tallahi sai nayi miki shi, amma fa kiyi hakuri, yau bazan ɓoye miki komai ba, Zainab ko hakan zai zamo silar rabuwata dake" Momy ta fashe da kuka, sbda ji take kwanyarta kamar zata tarwatse tsabar tashin hankali, Dady ya ci gaba da cewa "Tabbas Anam bata gurina, tana gurin ƴar uwarta Hussaina, walhi Zainab na rasa mafita ne, kuma kinsan tun dama munyi alƙawarin idan kin sake aihuwa dole zan kai musu ya zama biyu, Zainab yanzu ko da kin sake aihuwa babu mai taɓa miki yaranki ko ɗari zaki haifa" da wannan kalaman ya sace zuciyar Momy ta biye masa, sannan ta share hawaye, ya rungumeta yana yi mata kiss, "akwai alƙawarin da nakeso kayimin Habiby, idan har ka cika min alƙawari, nima zan sirrinta komai naka, Na farko shine ka yarda bazaka yimin kishiya ba, na biyu kuma inaso a fasa auren Saudart da wannan tsohon" da sauri Dady ya ware idanu tare da cewa "Zainab alƙawari ɗaya zan iya yi miki, bazan ƙara aure ba har abada, amma batun auren Saudart wallahi bazan iya ce komai ba, saboda wallahi tallahi, wannan mutumin da kike gani ciniki mukayi dashi" momy ta tashi a firgice, tare da dukan ƙirjinsa idanunta sunyi jajir ta cakumoshi tana cewa "cewa za kayi itama saudart ɗin ka siyar da ita kenan?" Tai maganar tana sake bugar ƙirjinsa,  "da na siyar da ita ai da ban bawa wani aurenta ba"
Dady ya faɗa yana ƙoƙarin ƙwace riƙon da Momy tayi masa,
"Wannan duk shirme kake faɗi, karfa ka mance sukenan min Saudart da ƴar uwarta sai Anam, ga shi har yanzu Allah bai bani wani cikin ba, gaskiya ka cuceni walhi tallahi nayi nadamar aurenka, kawai ka sauwwaƙe min in tafi gidanmu momy tai maganar hawaye Masu zafi suna bin kumatunta, shiru yayi bai ce da ita komai ba, yana kasa yi mata bayani inda zata gane, daga ƙarshe dai yace "Zainab ki sakeni walhi tallahi yau ɗin nan bazan ɓoye miki komai ba" momy ta juye masa fur taƙi sakinsa tace "tun ɗazu kake cewa bazaka ɓoyemin komai ba, nifa yanzu tsoronka nakeji wataran ni zaka bayar a baka dukiya, kaga kuwa idan ina gidan iyayena babu abinda zai sameni,
Dady yace "wallahi tallahi Zainab tunda na aureki ban taɓa tunanin rabuwa dake ba, har yanzu ina sonki, duk abinda kikaga inayine saboda farincikinki, Zainab abinda baki gane ba, walhi kuɗi sune masu ƙarawa ɗan adam daraja kinga dole mu nemesu, ke kanki bazaki iya rayuwa a gidanku ba, a halin yanzu, bance baku da shi ba, kunada kuɗi dai-dai gwargwado sai dai bakai inda nakeda shi ba, inada tarin dukiya fiye da tunanin mai tunani, sannan a halin da ake ciki ma zaɓen da za'ayi insha Allah, zan tsunduma neman shugaban ƙasa saboda har nayi rijistar, momy ta waro idanu "sai kuma ta fara tunanin idan har ta sake ta rabu da Dady tabbas, bazata zamo First lady ba, lokaci ɗaya ta fara hasaso rayuwar da zasuyi a lokacin da irin muƙamin da Dady zai rike da kuma taurarin da zasu dinga samu idan har hakan ta kasance, kawai wata zuciyar ta faɗa mata ta rungumeshi, ai ko ta rungumeshi tare da sake fashewa da kuka, "Habiby kaine duk abin da kake yi baka yin shawara da kowa, amma nidai karka bari Anam taje gurinsu" Dady yace "kash Zainab da wane yare kikeson in dinga yi Miki magana ne? Anam tana gurinsu, amma insha Allah zan sanya a yi ta roƙon Allah har Hussaina duk zasu dawo, duk dai da wannan daɗin bakin ya gama yaudareta kana ya siye zuciyarta da maƙudan kuɗaɗe yace taje ta rarrabawa mata mazauna gida irin waɗanda basa sana'a, "wow ta faɗa idanu duk sun kumbura tsabar kuka, sai kuma tace "to maganar Saudart shiɗin dai zata aura ko?" Eh mana, biliyan goma ya bani, saboda yace yana mutuwar sonta fiye da tunani, walhi saudart zataji dadin zama dashi, ai bawai girmansa zata aura ba," momy ta sake rungume Dady sbda tsantsar so da ƙaunarsa tana daɗa ratsa zuciyarta.
Ni Ko nace kuɗi masu gidan rana🤔.
Bari mu waiwaya gurin haɗaɗɗen saurayi mai ji da naira.
Bashi da alaƙa da ita, dan haka ko da suka bar gidan bai cigiyesu ba, sabda dama ba ƙaunar zamansu yakeyi a gidan ba,
Zaune yake a office, yana shan ice cream da chocolate sai wani lumshe idanu yakeyi, ga dukkan alamu yana jin daɗin yanayin da yake ciki, nocking ɗin da akeyi ne ya sa shi ɗago kai tare da sake lumshe idanu, kafin yace "come in"
Muhammad ne ya shigo, yana sanye da shadda sky blue, sai zuba ƙamshi yakeyi, koda ya ja kujera ya zauna, ya zubawa Ma'aruf idanu cikin zolaya yace "yau kuma taka ƙaddarar anan ta sauka na shan kayan zaƙi?"
"Idan kai ka siya min ka kwashe mana"
Ma'aruf yai maganar cike da jin haushin Muhammad,
Shi fa ya mugun tsanar Muhammad saboda munafurcin da yake yi masa a faɗarsa, Muhammad yace "mai da wuƙar kaga dama nazo in gaya maka ne, next week aurena insha Allah, ma'aruf ya washe haƙora kai kace ba shine magana take gagararsa ba, sosai kyawawan fararen haƙoransa, masu kyau da ɗaukar hankali suka baiyyana, dimple's ɗinsa suka loɓa, ya miƙa wa  Muhammad hannu suka tafa, kafin yace "wai dama kana nan kana soyayya ko? ɗan yaronka da kai" Muhammad yace "to me zan jira nifa bazan iya rayuwa babu soyayya ba, malam soyayya duniya ce, kai daga ƙarshe ma idan banji Muryar ta ba bana iya barci itama haka"  Ma'aruf ya jinjina kai yana murmishi kana yace "kuma ka tabbatar da bata iya barci itama ɗin" eh mana" wato dai bakasan menene so ba, bakasan daɗinsa ba, sannan baka san zafinsa ba" Ma'aruf yace "duk daɗin soyayya bai kai ice cream da chocolate ɗin da nake sha daɗi ba...!

Kuyi hakuri jiya baku samu update ba.
Mom Islam
08141799224
*NA KASA JUREWA*
💋💋💋
💋💋
💋

_Mom Islam_


Follow me on TikTok 👇



Page 41-42

Muhammad ya kwashe da dariya, shikam har ga Allah Ma'aruf yana birgesa, saboda babu ruwansa da kula ƴan mata, gefe guda kuma ya fara tunanin kodai yana da wata matsar ne?,
Allah shi ya barwa kansa sani.
Sallama yayi masa kana ya wuce, bayan tafiyar Muhammad Ma'aruf ya fara tunani, "to ma meye abin so a rayuwarnan in banda kasuwanci?"
Yayiwa kansa tambaya, kawar da tunanin nasa yayi ta hanyar danna wayar tafi da gidanka, ɗaya daga cikin ƴan aikin Company ɗin ce ta shigo, cikin girmamawa ta gaishe shi, cike da shan ƙamashi ya amsa, kana ya miƙa mata cover shoe ɗinsa, already tasan me za'ayi dasu, tunda ƙa'idarsa ne, kullum 3:pm nayi zai sa akai a goge masa, tana fita daga office ɗin Ma'aruf sukayi kiciɓis da Layla, "Ah Sara ina zuwa?" Layla ta jefo mata tambaya,
Sai da Sara ta waiga taga babu mai tahowa, cikin ƙasa da murya tace "aikin da aka saba yi, gugan takalmi mtswww"
Layla ta karɓi takalmin kana tace "kinga koma gurin aikinki zan kai a goge sannan zan kai masa har office" Sara tace "kin tabbata?"
"Eh mana" Layla ta amsa mata.
Koda yaushe mai polish ɗin takalma yana zama a ƙofar get ɗin company, cikin amincewar shugaban Company wato Ma'aruf,

Wacece Layla?
Layla na ɗaya daga cikin ma'aikatan da ake ji dasu a wannan company, sosai take bada gudunmawa, hakan yasa take sake jajircewa, gurin ganin an samu sauye-sauye, hakan yasa ta samu shiga a gurin uban gaiyya wato Ma'aruf, duk da hakan ba wai ya sake mata fuska sosai bane, kawai yana yawan karbar shawarwarinta, idan har ya ga akwai nasara a ciki.
Sara kam bata kawo komai ba, sabda ita kam sam bata wani son shishigewa Ma'aruf, duba da irin halinsa na miskilanci, ita dama ba wata bace a Company face mai gogo-goge, Sara Christian ce ba musulma ba.
Cike da shauƙi Layla ta kai polish ɗin takalmin Ma'aruf, ko da aka gama, rungumesu tayi a ƙirjinta, ji takeyi kamar Ma'aruf ɗin ne yake tare da ita, tana tafe tana zancen zuci har ta kawo ƙofar office ɗinsa, lumshe idanu tayi tare da jan dogon numfashi, aduniya Ma'aruf yana birgeta ko wane namiji ta gani komai kyawunsa bazata iya haɗashi da na Ma'aruf ba, ko mai yasa oho, sai da ta kalli fuskarta a jikin wayarta kafin ta buɗe hand bag ɗin dake maƙale a kafaɗarta ta ciro powder ta sake shafawa, kana ta ciro lipstick shima ta goga a lips ɗinta, sannan ta ɗauko turare mai sanyin ƙamshi ta fesa, kafin ta mayar dasu jaka, bata sake gyara lips ɗinta, kafin tayi nocking tana waigen ko akwai wanda yaga time ɗin da take makeup, "yes come in" Ma'aruf ya bata izinin shiga duk da bai san cewar ita ce ba, a hankali ya ɗago idanunsa ya sauke su a na Layla, tana rungume da takalmansa har ta ƙaraso cikin faɗaɗa murmishinta tace "Sir Barka da wannan lokaci"
"Barka" Ma'aruf ya faɗa a taƙaice.
"Sir zan iya zama?" tai maganar cikin zaƙaƙa muryarta, "eh zaki iya"
Ta ja kujera ta zauna tare da zuba masa idanu, shigo gabaki ɗaya hankalinsa baya gurinta, sbda rubuce-rubuce yakeyi, sai da ya ɗau tsawon mintoci kamar 20mints kana ya ɗago yana kallonta wanda tayi nisa a hasashen da zuciyarta ke ƙirƙiro mata, "zaki iya fadar abinda ya kawo ki" Ma'aruf yai Maganar ya miƙa hannu zai karɓi takalman da ke hannunta, miƙa masa tayi tare da narkar da idanunta, lokaci ɗaya ta fashe da kuka tare da ficewa a office ɗin, sam baya ƙaunar jin sautin kuka ko wane iri ne, hakan yasa kukan da ta fara yi ya shige masa rai, yanada numberta, ya danna tare da cewa "mai yasa kika tafi baki faɗi abinda ya kawo ki ba?" marairace murya tayi, cike da shagoɓa kafin tace "uhm dama inason faɗa maka wata magana ne"
Ta ƙarashe maganar tana sake sakin kuka,
"Ya Salam" Ma'aruf ya ambata da daddaɗar muryarsa mai ɗauke da daɗin amo, kizo office yanzu sbda ina shirye-shiryen tafiya gida,
Dama wannan lokacin take jira,
Ta tattaro kayanta na tafiya gida, kai tsaye ta wuce office ɗin nasa, yana zaune a hakimce kamar ɗazu, ta ƙara so tana cewa "Barka Sir" gyaɗa mata kai yayi tare da yi mata nuni da gurin zama, koda ta zauna zuba masa idanu tayi, kamar ɗazu da ta shigo, dama shi kam ba ita yake kallo ba, sabda shi ɗin ba irin mutanen nan bane da zasu ƙurawa mutum idanu har su gano kyawunsa da muninsa,
"Ina jinki"
Ma'aruf yai maganar yana rufe files ɗin da ya kammala cikewa,
"Uhm dama..dama..."
Ta fara inda-inda kamar wata marar gaskiya.
"Dama me? kiyi magana kina ɓatamin lokaci!!"
Ma'aruf yai maganar cikin daka tsawa.
Sosai take jin tsoronsa, sai dai soyayyarsa ta rufe mata idanu,
Layla tace "Dan Allah kayi haƙuri Sir, kasan akwai wata halitta da Ubangiji yake jarabtar ɗan Adam da ita, Ubangiji yana sawa bayinsa wani abu..."
"Ke dalla ni kimin magana inda zan fahimta kin wani tsaya yimin wa'azi ko nace miki banyi islamiyya bane?"
Ya ƙare maganar yana wani haɗe rai alamun ransa ya ɓaci,
"Okay Sir, dama na jima ina ɗawauniya da doyayyarka, dan Allah ko baka sona kace..."
Tunda Layla ta cigaba da magana yake sauraronta, tunda yaga ta sauya layi ya sake daka mata tsawa a karo na biyu,
Cikin sexy voice yace "oh kema ashe irinsu ce?, gaskiya kin cini game da har na tsaya jin wannan labarin ƙanzon kuregen da kikeyi min"
Ya buga table da ƙarfi, kana ya sake cewa "tashi ki ficemin bana son ƙara ganinki a office ɗina"
Ko da yayi maganar tana zaune, ta ɗora gwaiwar hannunta a saman table ɗin, tayi tagumi, tana daɗa zuba masa idanu, bata ma san yana yi ba, belt ɗin wandonsa ya ciro, kana ya fara nannaɗewa, sai a lokacin ta ɗago kai, sam batayi tunanin komai ba, sai gani tayi yana shirin kai mata duka, ta miƙe tsaye, kafin ta kai ga guduwa ta faɗi a gurin timmm, duk da haka nufo inda take yakeyi, cikin zafin rai ya bita da gudu, amma ta tashi itama ta ari na ƙare, kayanta ko dama suna maƙale a jikinta, dama ta ɗibosu ne, idan zai wuce gida ya sauketa a anguwarsu tunda duk hanya ɗaya ce.
Rai a ɓaci ya dawo ya zauna sai huci yakeyi, a fili yace "wai ma raini ne yasa wannan shegiyar yarinyar shigomin office tana gayamin maganganun banza ko ya akayi?"
Tunani ya farayi, duk rashin kula ƴan mata da bayayi sai da aka sami mara kunya ko?,
Time bai ƙarasa ba, ya haɗa kayayyakinsa, already ya danna wayar tafi da gidanka, Sara ta shigo tayi masa Barka, ya miƙa mata kayayyakin da zai tafi dasu, ta kai masa mota, kana shiga ya fito, cikin takunsa na ƙasaita,
Wacece Layla?
Alhaji Adam shine mahaifin Layla, Hajiya Rashida ita ce mahaifiyarta, Layla na kiran mamanta da Mamy, baban kuma tana ce masa Abbie, iyayenta sun kasance masu rufin asiri, sai dai wata jarabawa ta sami Abbie, bashi da dukiya kamar da, filayen da ya mallaka duk sun dulmiye, ada yana sana'ar siyarda motoci, Allah ya kawo tsautsayi ya gifta, yanzu dai yana sana'ar siyarda biredi, wato rarrabawa mutane biredi kama daga masu shayi da masu shaguna,
Ta haka yake ciyar dasu Layla harma da tufafin da kuma uzurorin rashin lafiya,
Layla tayi karatu sosai inda ta karanci business, alhmdulilah shine taimakonta, a koda yaushe tana tura takardar neman aikinta a website, cikin hukuncin Ubangiji Allah ya taimaketa, Muhammad ya gani, wato abokin Ma'aruf, sai da yayi mata magana kana suka tattauna, sannan ya zo ya sami Ma'aruf, cikin tausasa kalami, domin Muhammad ya tausayawa Layla sosai da sosai, ko da Layla ta zo tayiwa iyayenta albishir da samun aikinta, duk da a zahiri bata tabbatar ba, sukayi ta addu'a akan Ubangiji ya taimake su, cikin hukuncin Allah, sai ga Muhammad yayi mata albishir da Ma'aruf ya amince, sosai tayi murna tayi tsalle tsabar jin daɗin albishir ɗin da Muhammad yayi mata,
Dalilin da yasa ta samu karɓuwa a Company shine, tanada tunani mai kyau tare da iya sarrafa computer cikin sauƙi tare da binciko muhimman abubuwa,
Tunda tayi tozali da kyakkyawar fuskar Ma'aruf ta rasa tunaninta, duk da cewa kwata-kwata bata wuce 6months a Company ɗin ba, abubuwan da suke yi a Company sune.
Sarrafa Taliya
Macaroni
Shinkafa
Gishiri
Sannan kuma sunada gidajen abinci a Abuja har ma da Legos Enugu da Hotel babba a nan Abuja da Kano,
Sunan da suke amfani dashi a duk wata kafa tasu shine, M.M Food delivery service) shine sunan gidan abincin su, hotel kuma M.M Central hotel, company ɗin su kuma F.D INDUSTIRIES,tun bayan rasuwar mahaifin Ma'aruf ya ƙudurce wa kansa riƙe muƙamin da mahaifinsa ya riƙe, ta fannin kasuwanci da tattalin dukiyarsu, lokacin da mahaifinsa ya rasu F.D INDUSTIRIES company, ne kawai suke dashi, amma yanzu sunada hotel's da food delivery shima har biyu, bayan nan sunada filaye da gidaje, har da wasu masana'antun ma a ƙasar waje.
Driving yakeyi, ransa a ɓace, wannan yarinyar ta ɓata masa rai, ga shi be iya fushi ba, ko da ya iso bakin get da ƙarfi ya danna horn, mai gadi ya buɗe cikin girmamawa yana ɗagawa uban gidan nasa hannu, gyaɗa masa kai Ma'aruf yayi, kana ya shige ciki, bayan yayi parking ya fito tare da ɗibar kayansa ya wuce ciki, a hankali ya tura ƙofar door ɗin parlor kana ya kutsa kai ciki bakinsa ɗauke da sallama, kai tsaye upstairs ya hau yana ɗan gudu gudu, har ya iso ɗakinsa, ƙare wa ɗakin kallo yayi, kafin ya nemi guri saman beautiful couch ya zauna, "ya Allah" ya ambata jikinsa duk gajiya, hamma ce ta taso masa mai cike da ma'anoni iri-iri, ga yunwa ga barci ga gajiya, saboda tsabar gajiya, yana jin Bama zai iya shiga kitchen ba, shawarar samo ƴan aiki yayi wanda zasu dinga yi masa girki gyaran gida da wanki sabda wanki a washing machine ɗin ma wahala yake bashi, da wannan tunanin ya ɗan gyara zama kana ya kwanta saman couch mai zaman mutum uku, nan da nan barci mai daɗi ya ɗaukesa,
Tun 5:pm yake barci har aka kira sallahar magriba bai san an kira ba,
A hankali ya fara jin sanyi na shigarsa, sabda iskar da akeyi, tashi ɗaya gari ya haɗa hadari da alamun ruwan sama zai sauka, sosai gari yayi sanyi lokaci ɗaya ya fara ƙudundunewa, a hankali ya buɗe idanunsa, da sauri ya tashi zaune yana mutsike idanu, agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya kalla yaga har ƙarfe 7:40pm, cike da mamaki ya kunce agogon tare da wucewa toilet, yai alwalah kana ya fito, a parlonsa ya shimfiɗa sallahya kana ya kabbara sallah, bai tashi a gurin ba har sai da akayi sallahar isha'i, kana yayi addu'oinsa kafin ya ninke sallahyar sannan
End Ads