x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 1 - NA KASA JUREWA book 1

  • 1 words
  • 3000 words
  • Out of 86738 words

Category: Love Stories

Views 115

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[7/12, 2:32 PM] Mom Islam: *NAKASA JUREWA*
🪻🪻🪻

Bismillahir rahmanir Rahim, Nagode wa Allah da ya bani rai da lafiya har na kawo muku wannan labari mai suna a sama, idan har kinga ko kaga yayi dai-dai da rayuwar ka/ki, arashi ne, banyi wannan labarin da inci zarafin kowa ba.

Free Book

Page 1_2
Cikin tashin hankali Ma'aruf ya fito daga side ɗin momy hannunsa riƙe da key car idanunsa sun kaɗa sunyi jajir, cewa yake "Saudart kin cuceni kin lalata mana zumunci kin tozartani a..." karaf a kunnen Anty Jamila, sam baiyi tunanin maganar zuci ta fito fili ba, a hankali ya ɗago kai ya kalli ƙwayar idanunta, sai kuma ya sunkuyar da kansa, dama yasan a wannan karon ma bazata yarda da abinda zai ce ba, wani irin kallo take binsa dashi kai kace taga mugun abu, daga ƙarshe tai ƙwafa tabar gurin, har tayi nisa sosai bai ƙara ko taku ɗaya ba, saima jingina kansa da yayi da jikin bango yana mai-maita innalillahi wa inna ilahir raji'un zuciyarsa kamar zata fashe.

A hankali ya janye ƙafafunsa yai side ɗin Hajiya mama, yasan ita kam zata duba damuwarsa,
Da sallama a bakinsa ya shiga, sai dai beji daɗin ganinta a yanayin da ya ganta ba,
Jiki na karkarwa ya ƙarisa inda take, yayiwa kansa mazauni a saman Capet, kasancewar ita tana saman kujera 2sitter.
Ya rasa da wace kalma zeyi amfani domin ta gane nufinsa.
"Ma'aruf"
Hajiya mama ta kira sunansa fuska babu walwala murya a dakile,
Sai da gabansa ya bada rass kafin, yaja gauron numfashi, sannan yace "na'am Hajiya"
"Wace tsiyar ka sake aikatawa ƴar mutane?"
Murya na rawa yace "Hajiya cewa nayi kawai taje gidansu, saboda daren jiya ko runtsawa banyi ba"
"Eh lallai biri yayi kama da mutum, wato gulmace-gulmacen da ake yi a kanka yana nema ya tabbata kenan?"
"Kiyi hakuri Hajiya wlhi zanyi miki bayani ɗaya-bayan...."
"Dalla can rufemin baki, duk ka susuce kana neman ka mayar da kanka magaukacin ƙarfi da yaji, nidai a iya sanina ban haifi mahaukaci ba, kuma kaf danginmu babu mahaukaci"
Tana rufe baki, Anty Jamila ta karɓe da cewa "hmm ai yanzu abinda ya dace kawai ya rubuta mata takardarta shine abu mafi sauki, haka kawai abu yaƙici
yaki cinyewa"
Sam ya rasa dalilin da yasa basa yarda da maganarsa, sai dai suyi amfani da maganar Saudart, wannan karon ma maganarta ce tayi tasiri a zuciyarsu,
"Jamila.."
"Na'am Hajiya mama"
"Shin kina ganin yaron nan yanada gaskiya kokuma dai sauden ce baya so a cikin rayuwarsa, anyi wannan rigimar karo na uku kenan?"

Sai da Anty Jamila ta numfasa kafin tace "nifa na ganewa idanuna, har dukanta yake yi da bulala, bayan nan ya tattakata harda furucin zai sallameta sannan..."

"Ya isheni haka"
Hajiya mama ta faɗa rai a ɓace.
Ya gaza sake furta komai, sbda sun mayar dashi maƙaryaci, har yanzu kansa a sunkuyar yana jiran hukuncin da zasu yanke.

"Ma'aruf.."
Ya amsa da "na'am Hajiya"
Jiki a sanyaye.
"Inaso kaje gidansu Saudart yau ɗin nan ka dawo da ita ɗakinta, wannan umarni ne kaji na gaya maka..!!
Dum!!! Dumm!!
Ƙirjinsa ya buga, yanzu ne ma ya gane tabbas a wannan karon ma Saudart ta sake yin galaba a kansa amma zeyi maganinta, dawowarta shi zai bashi damar horata,
"Banji kace komai ba?"
Hajiya mama tayi maganar a taƙaice.
"Insha Allah zan je amma sai gobe"
"Inaa!!, Wallahi ban amince ba, ina Abuja ina Keffi, yau ɗin nan nakeso kaje Keffi"
Babu inda ya iya dole hakan yabi umarninta, sosai yakejin zuciyarsa babu daɗi, ya miƙe zai fita, Anty Jamila tace "ayi maka rakiya ne kokuma kai kaɗai zakaje?"
Murya a daƙile yace "ni kaɗai zani"
Ya miƙe fuuu ya fice.
Kai tsaye gidansa ya nufa, gidan nasa yana kusa da na iyayensa, zamu iya cewa katanga ce ta raba, a hankali yai hannunsa jikin get ɗin milk color ya ƙwanƙwsa, Idi mai gadi dake ta rusa gyangyadi ya miƙe a firgice yana cewa "innalillahi ƙila ma me buga ƙofar nan ya jima yana bugawa" ya ajiye rediyon dake hannunsa yake bude ƙaramar ƙofar dake jikin get ɗin.
"Ahh Alhaji kaine ?"
"Eh matsa"
Ganin fuskar ubangidan nasa babu walwalah yasa shi yin tsit da bakinsa har Ma'aruf ɗin ya ɓacewa ganinsa.
Koda ya buɗe ƙofa kai tsaye bedroom ɗinta ya wuce, tafkeken frame na hotonta ya tsaya yana ƙarewa kallo, lokaci ɗaya ya runtse idanunsa tare da cije kyakkyawan pink lip ɗinsa, tura hannunsa yayi cikin sumar kansa, a fili ya furta kayun ɗan maciji, "wallahi tallahi na tsaneki na tsani komai naki mtsw" ya fice a bedroom ɗin nata tare da bugo ƙofa,
Ita ɗin ba ƙaramar bace komai nata tsaf-tsaf, kasancewarta mace mai tsafta, sbda haka nema ta hana a ɗauko mata ƴar aiki, amma wannan lefukan da ya kamata dashi ya goge duk wata kyakkyawar mu'amala da yayi da ita, sam zuciyarsa ta gaza yi mata uzuri, tunda abinda abinda ya gani ba shine na farkon ganinsa ba, ya shiga bedroom ɗinsa ya zauna saman gado zuciyarsa cike da saƙe-saƙe, hannunsa ya tura cikin aljihun wandonsa ya ciro wayarsa duba time, "ƙarfe hudu" ya faɗa a fili, ma miƙewa yayi ya rage kayan jikinsa ka na a ya shiga toilet, saida ya tara ruwa a bahon wanka, kafin ya shiga ciki ya daɗe sanyin ruwan na ratsa fatar jikinsa, kasancewar akwai zafi sosai a gari, idanunsa a lumshe yake hasaso irin zaman da zasu cigaba da yi a wannan karon saboda wallahi tallahi yakai maƙura bazai iya ba"
Daga ƙarshe yai wanka ya fito ɗaure da farin towel, ya rasa me zeyi sai juye-juye yakeyi, kiran wayar Anty Jamila ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi, har wayar ta gama ruri bai ɗaga ba, sai ma shiryawa da ya farayi, sai da ya shirya tsaf ya fito kamar sabon ango, ya Subhanallah "Ma'aruf ya haɗu iya haɗuwa, fari ne amma ba sosai ba, yanada tsayi da ƙiba, tsayin nasa sai ya ɓoye ƙibar tasa, yanada dogon hanci, da ƴan madai-daitan idanu, idan ka kalli pink lips ɗinsa wow, sai ya birgeka, kai kace na wata macen, hatta fatar jikinsa abin kallo ce, sbda sheƙi da sulɓin da take yi, shiɗin fa ya haɗu, bakinsa yana zagaye da gashi ba wani mai yawa ba, sumar kansa koda yaushe cikin gyara take.
Matsawa yayi gaban mirror ya kalli kansa a midubi, ya haɗe hannunsa guri ɗaya tare da ambaton alhmdulilah, kana ya ɗibi mukullin mota da wayoyinsa da duk abinda yasan ze buƙata ya fice.
Duk wanda ya kalli fuskarsa yasan baya cikin walwalah, har ya isa parking space, ɗaya daga cikin jerin motocin ya shiga wacce already a wanke take sai sheƙi take, black color,
Koda ya tada motar, ya danna horn sosai har sai da Idi mai gadi ya fito a guje ya buɗe masa, ya figi mota sai Keffi,
Tabbas in banda biyayya babu abinda zai sashi ya tafi Keffi,
Yana tafe yana saƙe-saƙe har Allah yayi isowarsa, a bakin wani danƙareren gida ya tsaya da motarsa, yana danna horn.
Gidane na gani na faɗa, kafin ka shiga cikin gidan zaka fara hasaso irin tsantsar kyawun gida, tsarki ya tabbata ga Allah, abinda na faɗa kenan yayinda na kutsa kaina ciki, babban gida ne wanda ya haɗa da garden da gurin lilo da sauran kayan more rayuwa,
"Anty Saudart ga wancan ɗan na cin can wallahi karki koma ko yazo, kawai ki bari goben mu wuce India tare, tunda an gama shirye-shiryen tafiyarmu"
Ƙala batace ba, ta ci gaba da danne-danne a watarta sam ta nuna bata ma san da maganar da Anam ɗin keyi ba,
"Assalamu alaikum"
Sallamarsa gami da tattausar muryarsa ta ratsa kwanyarta, ko ɗagowa batayi ba, sai dai ya samu albarkacin amsa sallama, shima ɗin ya iya ji da kai, ko ta kanta bai bi ba, ya nemi guri ya zauna a saman one sitter, "Ina wuni yah Ma'aruf"
"Lafiya lau Anam ina momy fa?"
Anam ta gaishesa fuska a sake kai kace ba itace ta gama ce masa Sarkin naci ba,
Yanayin inda ya amsa yasa Saudart ɗago idanunta karaf, suka sarƙe a na juna, fuska ba walwala yaci gaba da kallonta, zuciyarsa nayi masa ƙuna,
A maimakon yaji shigowar momy, sai yajie Muryar Dady yana cewa "ashe yaron nawa ya iso"
Gabansa ya bada dumm, sam ya rasa dalili, duk girman lefin da Saudart tayi masa bai hanasa ganin girman Dad ba, sosai yakejin nauyinsa har cikin zuciyarsa, koda Dady ɗin ya zauna Ma'aruf sauka ƙasa yayi saman Capet ya sadda kansa kasa kafin yace "Dady ina wuni"
"Lafiya lau yarona wlhi nayi farinciki da ganinka, ai nayita neman number Alhaji bukar bata tafiya amman dai lafiya ko?"
"Eh lafiya Dady, kasan bai cika zama a Nigeria ba yanzu yana Saudiyya aikin asibiti"
"Ayya kasan najima rabon da mu haɗu, amma dai kazo ɗaukar matarka ne ku tafi ko?"
Jimm yayi bai ce komai ba.
Kasancewar Dady mutum ne mai tawakkali da hangen nesa yace "Ma'aruf kayi haƙuri da duk wani abu da ya faru dan Allah, duk da dai naso jin me ya haɗaku momynta tacemin wai faɗanku ne a tsakaninku, dan Allah kayi haƙuri ku zauna lafiya, a iya zaman da muka yi da Saudart batada abokin faɗa ko tashin hankali.."
"Ina never wallahi..!! na rantse da rabissamawati wal ardi babu inda ƴata zataje, haba Alhaji sai kace wata mara galihu?, koda ka fara bincike dalilin da yasa ban baka labarin abinda ya faru ba, saboda baka ƙasar ne, taɓɓ bazata koma yaci gaba da zargin taba"
Ta ƙare maganar tana janyo Saudart jikinta, kuka take yi sosai kamar ranta zai fita, shi ko Ma'aruf, addu'arsa bata wuce Allah yasa Dady yaki amincewa da komawar Saudart ɗin,
"Haba mom Saudart me yasa kike faɗin haka bayan an wuce wannan gurin?"
Dady yai maganar ransa a ɓace.
"Ni kawai kayi masa gargaɗin kar irin haka ta sake faruwa, idan ko har hakan ta faru to shida Saudart har abada".
Inda tai maganar momyn cike da ƙwarin gwaiwa, sanar ta nuna ko a jikinta.
Murmushinsu na manya Dady yayi gami da cewa "Ma'aruf ɗauki matarka ku wuce, zamu yi magana a waya"
Jin haka yasa Saudart miƙewa ta wuce ɗakinta da gudu tana kuka.
"Anty Saudart kiyi shiru, a tunanina karatun da kika yi ya isa ki koyar da Ma'aruf shiɗin ba komai bane"
Shiru tayi batace da Anam komai ba,
Anam ta sake cewa "shiɗin wa, dan ubansa, ki rikirkitashi wallahi"
Sai yanzu ta amsa mata da cewa "rikitawa fa kikace"
"Eh man, nifa anty Saudart na fara zargin Yah Ma'aruf ko dai, shine ma abin zargin?"
Saudart tace wa Anam "zargi name fa?"
"Bin mata"
Cewar Anam,
"Hamm Anam Allah ne kaɗai yasan gaibu, wallahi ko sau ɗaya Anam ban taɓa zargin Ma'aruf ba, amma ya ɗauki laifin duniya ya ɗora shi a kaina, menayi masa??!!"
Takai ƙarshen maganar tana sake fashewa da kuka,
Shigowar momy ne yasa ta miƙe da sauri ta rungume momyn tana cewa "shikenan bani da gata momy, nace masa bana yin facebook yace ba haka ba, wallahi duk wasu social nayi".
"Saudart ki kwantar da hankali, idan yanacin ƙasa ya kiyayi ta shuri, anzo ƙarshe, tashi ki shirya ku tafi"
Sam ta kasa haɗa kayan ta, sai Anam ce take ta ƙoƙarin haɗa mata kayan, koda Anam ɗin ta gama ta fito da kayan parlo time ɗin Ma'aruf ya fita shida Dady, dole takai mota, sam momy ta kasa yiwa ɗiyar tata rakiya ita kaɗai ta fito, ta shiga mota, lokacin Ma'aruf yana gidan gaba, itama nan ta shiga, Anam tayi musu sallama suka wuce.
Kasancewar already me gadi ya buɗe get na gidan, ya figi motar kamar ze tashi sama...!

#Cin amana
#Zalunci
#Badda kama
#Rayuwar gidan yarin
#Hassada
#Zazzafar soyayya
#Nadama


Idan har naga anyi sharing insha Allah zaku dinga samun update any time.

Ga number WhatsApp please ga duk meson shiga channel ɗina

08141799224

Page 3-4
Ganin shiru yayi yawa, ta buɗe hand bag ɗinta ta ciro wayarta ta fara game, sosai take jin daɗin game ɗin sbda har wani murmishi takeyi,
Tayi nisa sosai, dan batajin ko ƙarar tafiyar da suke yi a motar, ta ɗan kalli gurin zaman Ma'aruf taga babu shi babu alamarsa, juyawa tayi ta kalli inda suke kafin tace "hmm ashe mun iso ne, yafi ƙarfin yace min munzo"
Sai kuma ta fara tunani ya akayi sun iso bata sani ba?"
Kawar da tunanin nata tayi ta hanyar bude murfin ma motar ta wuce ciki.
Koda ta shiga parlon bakinta ɗauke da sallama tsit babu motsin kowa, to ina ruwanta ma, kamata yayi ta wuce bedroom ɗin ta kawai, duk wannan tunanin tayi shi ne a lokaci ɗaya,
Sam zaman gidan ya isheta, tunda tazo gidan Ma'aruf wata uku tayi da farinciki, meyasa bata da gata ne?"
Tunanin wace shawara ya kamata ta yanke ta farayi.
Ta daɗe tana tufka da warwara daga ƙarshe dai ta wuce kitchen lokacin ana shirin kirin sallahar magriba,
Kasancewar duk wani abu da zata buƙata akwai shi a kitchen ɗin yasa ta dafa indomie jollof, parlo tazo ta zauna sbda ta tabbatarwa kanta akwai mutum a gidan ko ya fita"
Har aka kira sallah aka shiga bataji motsin kowa ba, ta miƙe ta koma ɗakinta, bayan takai plet ɗin kitchen.
Toilet ta shiga ta ɗauro alwala, ta shimfiɗa sallahya ta kabbara sallah, tana kan sallayar tana rokon Ubangiji, har aka kira sallahar isha'i, sai da tayi kafin ta kwanta.
Rurin neman agajin da wayarta keyi ne yasa ta ciro wayar a hand bag ɗinta, "momy" ta faɗa a fili tana murmishi.
"Hello momy kuna nan lafiya mun iso gida lafiya"
"Saudart ki sanar dani idan akwai abinda ya shige miki duhu"
"Lahh momy babu komai wallahi"
Daga nan sukayi sallama ta ajiye wayar.
Lumshe idanunta tayi, lokaci ɗaya rigimar da suke yi da Ma'aruf ta dawo mata sabo fil, tunani ta farayi, anya Ma'aruf bashi da taɓin ƙwaƙwalwa kuwa?" Yo inba taɓin ƙwaƙwalwa ba yace wai itace take posting ɓatattun hotuna a social, da yaushe ma ta fara? ita da ba wani shige shige takeyi a madia ba, to inko haka ne akwai lauje cikin naɗi, yace hotonta ne a profile ɗin da yake zargin itace, waye yake neman ruguza mata farinciki,
Inko haka ne, zatasan inda zatayi domin ta ganewa idonta waye yake aikata wannan abin yake fakewa da ita, sbda a kwatancen da yakeyi kamar su ɗaya da wacce yake gani.
Kyakkyawa ce ta bugawa a jarida, sbda kyawunta ya ishi duk wani mai tunani misali, fara ce tass ga dogon hanci, gashinta baƙi ne siɗik har gadon baya, tanada zara zaran gashin ido, ga dogon hanci, bugu da ƙari doguwa ce bata da jiki ga diri kai kace kwalbar lemu lolx, a takaice kamar ita tayi kanta don kyawu, Saudart kenan, nasan zakuce me yasa Ma'aruf yake wulaƙantata? muje zuwa yanzu wasan ya fara.
Har dare yayi sosai bataji alamar shigowarsa ba, har bacci yayi awon gaba da ita,
A cikin barcin nata ne tayi wani irin mafarki, wata budurwa take gani idanunta a rufe tanayi mata dariya hannunta rike da wuƙa suna kokawa,
Kiraye-kirayen sallahar asbha da ake yi ne yasa ta farka daga wannan mafarki, da sauri ta dinga mai maita innalillahi wa inna ilahir raji'un, ga wani dukan uku-uku da ƙirjinta yakeyi, a hankali takai hannunta ta mutsike idanunta tare da zuro ƙafafun ƙasa ta wuce toilet,
Alwala tayi tai raka'atanil fijir, kafin ta kabbara sallah.
Bayan ta idar da sallah ta daɗe tana kwararo adu'oi na Allah ya tona asirin koma waye, domin kuwa abin ya shige mata duhu, a iya rayuwarta bata da wani saurayi bata da ƙawa wace ta wuce mahaifiyarta, ba fita takeyi ba, ko zuwa makaranta ne kawai yake fitar da ita daga gida, sam iyayen nata basa bari ta leƙa ko ƙofar gida.
Daga
End Ads