x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 7 - NAYEL THE RETURN OF EXILED PRINCE

  • 18001 words
  • 21000 words
  • Out of 89550 words

Category: Love Stories

Views 412

14 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ina ya ke shi wanda ku ke soyayyar , ya sunansa ? a ina kuma ya ke ? " Al-Sayid ya jero mata tambayoyin

wasu yawu ta hadiye kafin ta kai hannu ta fara goge hawayenta , karyar da ta yi ta na neman ta juye mata , to ita ina ta san sunansa , bare wajen da ya ke zaune har in da ya ke aiki

ta yi nisa duniyar tunaninta ta jiyo Muryarsa ya na sake tambayar ta
wasu wahalalun yawu ta hadiye kafin ta ce " um Daddy , yanzu ba ya cikin masarautar , ya tafi UK wajen aikinsa , kuma bai fada min yaushe zai dawo ba "

" okay , ki fada mishi ina son ganin sa , in kuma Magajin Malik ya riga shi zuwa sai dai ku yi hakuri da ke da shi dukka ku "

da sauri ta gyada mishi kai ta na sakin wani dan karamin murmushi ta saki " Eh Daddy zai zo "

gyada mata kai ya yi kafin ya ce " shikenan , Aleenah , ke kuma fa ? akwai wanda ki ke so ko babu ? " ya tambayi Aleenah ya na kallon ta

girgiza mishi kai ta yi kafin ta ce " a'a Daddy babu " ta fada murya cen kassan makoshi

" okay , za ku iya tafiya , sai da safe "

" Sai da safe Daddy " su ka fada a tare kafin su yi musu sallama su ka tashi su ka koma part din su

kai tsaye part din su su ka koma sai sauri Aleesherh ta ke kamar za ta tashi sama

ko da su ka shiga part din su ta riko hannayan Aleenah ta na fadin " please Aleen , ki fada min a wane hotel ne ya ke zaune , wlh in ban samo shi ba Daddy auren dole zai yi min , ni kuma wlh ina son sa har cikin raina " ta fada kamar za ta yi kuka har ruwa ke cikowa cikin idanunta

kwace hannayanta Aleenah ta yi , cikin sanyin murya ta ce " ko na fada miki ba abun da zai anfane ki da shi , saboda ba son ki ya ke ba , ta ya ma za ki kawo shi gaban Daddy matsayin wanda ku ke soyayya ? ki na tunanin zai amince ? a ka je kuma akwai wadda ya ke so ? "

" ni dai don Allah ki fada min , ni na san yadda zan yi , kenan kin fi son ya aura min wani cen wanda ban sani ba ko son sa ba na yi ? "

" kin dai ji fa ni da ke ya ce , ba ke kadai ba ya ce "

" na sani amma ai ke ba wanda ki ke so , kuma ai Malik yaro guda ne da shi , please ki ceci rayuwar yar uwarki guda , wlh in a ka yi auren nan kashe kai na zan yi " ta fada murya a sanyaye kamar za ta yi kuka ta na marairaice fuska

shiru Aleenah ta yi ba ta ce mata komai ba , ta san tabbas Malik yaro guda ne da shi , kuma dole Al-Sayid babbar cikin su zai fara ba shi , in har Aleesherh ta samu abun da ta ke so to tabbas ita za a bawa yaron Malik , yanzu zaba za ta yi tsakanin rayuwarta da ta Aleesherh , tun da har ta ce sai ta kashe kanta in har a ka yi auren nan to tabbas sai ta kashe kanta dan ta san yar uwarta da cika magana


wani dogon nunfashi ta ja kafin ta ce " a Sheba hotel ya ke , floor na farko , VIP room 3 "

wani kyawatacen murmushi Aleesherh ta saki kafin ta rungume ta tsam ta na fadin " na gode sosai my lovely sister , that's why i love you so muchhhhh "

wani dan karamin murmushi Aleenah ta yi kafin ta rungume ta

sun dan dauki lokaci a haka kafin Aleesherh ta sake ta ta juya da sauri ta na fadin " ina uniform din ki ya ke ? "

dan zaro idanu Aleenah ta yi kafin ta riko hannunta ta na fadin " ke Aleesh , da hankalinki kuwa ? cikin wannan daren ki ke son tafiya ? in a ka kama ki fa ? please ki bari har zuwa safe "

" Aleenah ba zan jima ba , please ki kyale ni na tafi , wlh rayuwata ce ke cikin hatsari in har ban je ba "

wani dan karamin tsaki Aleenah ta ja kafin ta saki hannunta ta nufi hanyar dressing room
jim kadan ta fito rike da uniform din ta irin na ma su aikin Sheba hotel
ta mikawa Aleenah ta na fadin " rike , amma wlh duk abun da ya same ki ba hannun Aleenah a ciki " ta fada ta na komawa bakin gadon ta zauna ta na nade hannayanta a kirji ta kauda kai

wata yar karamar dariya Aleesherh ta yi kafin ta karaso gefenta ta zauna , ta na fadin " ba abun da zai same ni saboda kyakyawar Twins di ta ta na nan , ke za ki taimaka min na fita ba tare da kowa ya sani ba , yanzu in an tambaye ni ki ce ina barci , in ban dawo ba nan da one hour ki je nema na , byeeeeee " ta fada ta na mikewa da gudu ta shiga dressing room

da kallo Aleenah ta raka ta har sai da ta shiga sannan ta ce " Aleesherh sai kin sa an kashe ni wata rana , wajen neman soyayyarki yanzu za ki saka rayuwata cikin hatsari " ta na gama fadar haka ta saki wani cool murmushi ta ce " Allah ya sa ni ma na samu wanda zan iya jefa rayuwata cikin hatsari dan kwatar soyayyarsa , kyakyawa mai kyakyawar zuciya "


ta na zaune a nan ita kadai har Aleesherh ta fito sanye da uniform din , kuma gaskiya sun yi mugun zauna mata fiye da Aleenah dan ta fi Aleenah cika da shape abun dai Masha Allah bare da ta saki curly hair din ta har tsakiyar baya gaskiya ba karamin kyau ta yi ba

a haka har ta karaso gefen Aleenah ta manna mata kiss saman kumatu ta na fadin " sai na dawo "
ta na gama fadar haka ta nufi wani closet na books da ke cikin parlourn
ta na isa ta sa duk karfinta ta tura closet din
nan na ga wata yar karamar door a baya
bude door din ta yi ta shiga , duk da wajen duhu ne amma sam ba ta ji tsoro ba dan sun saba bi ta nan




SHEBA HOTEL 🏨


VIP ROOM 3



konce ya ke tsakiyar gadonsa , da Laptop saman laps din sa ya na faman latsawa
da ga shi sai short da t-shirt blue color , ya saki wannan smooth hair din nashi ya bazun mishi a shoulder sai tashin qamshi ya ke

ya na zaune a haka ya ji wayar landline din dakin ta fara ringing
hannu ya kai ya dauki wayar ya kai ta a kunne ba tare da ya ce komai ba
cikin nitsuwa ya nijo Muryar wani matashin ya na fadin " Sir , ga fruits din nan an kawo muku , za ku iya bude mata kofa ? "

" okay," ya fada a takaice kafin ya mayar da wayar , ya sauke laptop din da ga saman cinyoyinsa ya sauko kassa ya nufi kofar

hannu ya kai ya bude kofar sannan ya juya ya na fadin " za ki iya ajiyewa saman table " ya fada ya na nufar toilet

ba musu ta karaso cikin dakin ta na sallama da wata siririyar Muryarta
cak ya tsaya dan ko cikin duhu zai iya gane wannan Muryar
a rude ya juyo ya na zaro idanu ya na kallon ta tsaye tsakiyar dakin rike da tray din fruits

" what are you doing here ? ! " ya fada da dan karfi har sai da ta saki tray din hannunta dan ba karamar razana ta yi ba , ga shi dama ba wani kayan kirki ne a jikinsa

wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya ce " please Get out ! "

wasu yawu ma su daci ta hadiye kafin ta bude baki murya har kerma ta ke ta ce " don Allah ka tsaya ka saurare ni , ina son mu yi magana , please "

cikin bacin rai ya tako gadan gadan gare ta
ta na ganin ya fara takowa ta fara yin baya ta na girgiza mishi kai har sai da ta kurewa bango

ya isowa ya kai hannu ya damko wuyanta , ya na kallon cikin idanunta ya ce " zan rufe ido , na kirga zuwa biyar , in har ba bude ido na gan ki cikin dakin nan , sai na yi miki abun da sai kin tsani kanki da kanki , sai kin mutu ki na nadamar hada hanyarki da ni , so get out tun kafin raina ya baci " ya na gama fadar haka ya saki wuyanta , ya kai hannu ya bude kofar dakin ya lumshe idanunshi ya fara kirge da ga 0

kuka ta saki hawaye na zubo mata bibiyu , kafin ta juya jiki a sanyaye ta fice dakin dai'dai lokacin da ya kai 5

ya na bude ido ya gan ta tsaye bakin kofar dakin ta juyawa kofar baya
da karfi ya meda kofar ya rufe ya na jan tsaki , kafin ya cusa hannu cikin gashin kansa dan ta na neman ta tayar mishi da hankali

wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya juya ya na kallon fruits din da su ka zube cikin dakin duk wajen ya baci

wani dogon tsaki ya ja kafin , ya karaso bakin bed din sa ya dauki laptop din sa , da wayoyinsa
sannan ya bude box din bedside drawer , nan na ga wajen cike da magnetic card har wajen goma ko fi
duba su ya fara yi daya bayan daya har ya samu wadda ya ke so , sannan ya dauka ya nufi kofar fita dakin ya fice

ya na fitowa ya nufi room din da ke fuskantar wadda ya fito ya na ce ma Bodyguards din shi " Gobe ku medo kayana cikin wannan bedroom din " ya fada dai-dai lokacin da ya shige cikin dakin ya medo kofar ya rufe



DAULAR YEMEN 👑



ALEESHERH 💋👑



ta na konce tsakiyar bed din su , ta yi rub da ciki sai kuka ta ke yi kamar ranta zai fita

ita dai Aleenah ta na tsaye ta zuba mata ido, tun dawowar ta ta ke kukan nan , ta tambaye ta lafiya amma ta ki fada mata

wata yar karamar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta zauna bakin gadon ta ce mata " ya isa haka kukan , ki fada min me ya faru a cen , ko bugun ki ya yi ? "

girgiza mata kai Ta yi a hankali ba tare da ta ce komai ba
" to minene matsalar ? sai kuka ki ke kamar wadda uwarta da ubanta su ka mutu " ta fada ta na dafa shoulder din ta

" Aleenah , i think i'm crazy " ta fada ta na kukan

a hankali Aleenah ta kai hannu ta tallabo ta , nan ta ga fuskarta a bushe ko digon hawaye babu

wani dan tsaki Aleenah ta ja ta na janye hannayanta ta ce " kin san Allah , in ba ki bude baki ki ka fada min abun da ke faruwa ba ba zan kara taimaka miki ba , sai dai ki san yadda za ki yi ke kadai "

wata yar karamar dariya Aleesherh ta yi har da daga kai sama kafin ta sauko shi ta ce " Aleenah , this guy is so handsome , Allah in ban same shi ba ina ga kashe kaina kawai zan yi , kin san yadda na ke , ba na saurin sakin wa mutum face , amma wlh lokaci guda ya tafi da zuciyata ban san ya hakan ta faru ba , ina jin sa har cikin zuciyata Aleenah "

tsaki kawai Aleenah ta yi , ita abun Aleesherh ya na neman ya ba ta haushi ma , sai ka ce a kanta a ka fara soyayya
mikewa tsaye ta yi ba tare da ta ce komai ba ta shiga toilet ta medo kofar ta rufe

ta na shiga Aleesherh ta saki wani cool murmushi ta dauki pillow ta rungume ta na fadin " minene sunanka ? zan so na san abun da ka ke boyewa bayan wannan zuciyar taka , ban san ya a ka yi na kamu da son ka lokaci guda haka , amma na san wani abu guda ,,,,, ina son kasancewa tare da kai , har abada har bayan mutuwa " ta karashe maganar ta na kara matse pillown a jikinta

( 😂🤔 to fa da Alamun wata ta fada tarkon Prince, yanzu ya za ta kasance tsakanin su ? za ta iya fada mishi abun da ke cikin ranta ? zai amince ko kuwa ? )






DAULAR SAUDIYA 👑🔥




MALIK 🔥




zaune ya ke cikin parlourn part din Diya , ya na Sanye da jallabiya white color ya daure smooth hair din sa a baya duk da ba wani yawa ne da shi ba a yanzu
Diya na zaune gefensa , ya na sanye da jallabiya shi ma amma darck blue , ya na rike da wayarsa sai faman latsawa ya ke

cikin nitsuwa Malik ya ce mishi " please sauke wayar nan ka ci abinci nan ka sha magani "

murmushi mai dan sauti Diya ya yi kafin ya ce " ka ga ni fa ba yaro ba ne , ka kyale ni "

" na sani , amma na zo nan ne dan na kula da kai , ba zan bar wajen nan ba sai ka cinye abincin nan ka sha magani ka konta sannan zan tashi na tafi "

dago kai Diya ya yi ya kalle shi ya marairaice fuska ya ce " please i'm not a baby , tafi ka kula da Cutien ka , ni fa i'm okay "

tsuke fuska Malik ya yi ya ce mishi " za ka ci abincin nan ko sai na yi maka da karfi ? "

wata yar karamar dariya ya yi , ya na shirin magana wani saurayi ya fito da ga cikin corridor din part din , ya na sanye da Short da t-shirt ash color ma su kyau , ya na kama tak da Diya kamar an tsaga kara kuma ya na jinin Nesrine sosai , a shekaru zai kai 30 haka ko fi ma , ya na murdaden jiki

a haka har ya karaso cikin parlourn ya mikawa Diya wasu drugs ya na fadin " Daddy , please ka cinye abincin nan ka sha magani , dubi har ya yi sanyi fa "

matse gera Diya ya yi kafin ya dago kai ya kalle shi ya ce " kai Junior ni tsaran wassan ka ne , ka koma in da ka fito da maganin nan ba abun da zan sha , ku kyale ni don Allah kun wani saka ni a tsakiya sai ka ce baby , ni yanzu aiki na ke ku bari har na kammala "

marairaice fuska Junior ya yi kafin ya ce " Daddy , i say please , wai me ya ba ka damu da lafiyarka ba ne ? in ba ni ko momy mu ka ba ka magani sam ba ka damu ka sha ba , so ka ke mu koma Asibiti ne ? "

hannu Malik ya kai ya kwace wayar Diya ya tilla saman sofar bayansu ya ce mishi " Diya , ci abincin nan , now ! "

tsaki Diya ya ja , kafin ya kai hannu ya dafa sofar ya na neman tashi
amma ina kawai sai komawa ya yi ya fadi
da sauri Junior da Malik su ka kai hannu su na neman taro shi

" please ku bari , i'm okay na ce muku " Diya ya fada ya na tare su kafin ya koma ya zauna ya na sauke ajiyar zuciya

cikin bacin rai Junior ya watsa drug din hannunsa a kassa ya na fadin " okay , na kyale ka , yi yadda ka ke so " ya na gama fadar haka ya nufi kofar fita ya fice

da sauri Diya ya shiga kiran sunansa , sarai jiyo shi amma ya share shi ya sa kafa ya fice
sai da ya fita sannan Diya ya kalli Malik ya ce mishi " please je ka yi mishi magana "

gyada mishi kai Malik ya yi kafin ya mike ya na fadin " zan dawo gare ka " ya fada ya na takawa ya bi bayan Junior

a cikin Harabar part din ya tardo shi zaune saman wata chair ya na rike da wayarsa ya na latsawa

cikin nitsuwa Malik ya karaso wajen ya dafa shoulder din sa ya na kiran sunansa
ba tare da ya dago kai ba ya amsa mishi

" me ya faru ka ke fushi ? "

" nothing uncle " ya fada a takaice

a hankali Malik ya zauna gefensa ya na fadin " Nawfel , please tell me , ko sai kai ma ciwon zuciyar ya kama ka na yi jinya biyu ? "

" uncle ka na fa ganin abun da Daddy ke yi , sam ba ya kula da kansa ka duba fa abinci ma ya ki ci bare ya sha magani , ta ya zai warke a haka ? "

" please ka daina tada hankalika
End Ads