bai shiga tsakaninsa da matarsa ba " Fadin Queen , da ga haka ta bace bat lamps din dakin su ka kunnu baki daya
wata yar karamar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya janyo chair ya zauna ya buga uban tagumi ya na sauke nunfashi a hankali
cen sai ya ce " shikenan yanzu ba zan samu Prince ba ? da a ce Big bro bai min kallon kanwarsa da na so shi amma sister din sa ta jini ya dauke ni , Prince din ma da na yi tunanin zan samu wannan yar iskar ta zo ta kwace , ni zan so na ga wace mara sa'a ce ta shigo gona ta , in dai ina cikin masarautar nan ba zan taba bari ta mallaki zuciyar Prince " ya na gama fadar haka ya bushe da dariya shi kadai
( IN NA GANE KENAN KUJERAR MALIK SU KE HARI SU MA ? TO ALLAH YA BA DA SA'A , NI NA BI BAYAN INAYA πππ )
βͺINAYA ππ
da Sallama a bakinta ta shigo parlournsu da ke floor na uku , Malik na zaune shi da Diya su na hira cikin nitsuwa
wani dan karamin murmushi ta saki dan ba karamin dadi ba ta ji ganinsu a haka ba
karasowa ta yi ta na fadin " Malik yau kuma kai ne a part din namu ? "
wata yar karamar dariya Diya ya yi kafin ya ce " Babyn malam , ga wanda ya janyo ni nan cewa ya yi wai na daina zama a waje guda shi ya sa na biyo shi "
sai da ta karaso ta zauna gefen Malik sannan ta ce " ya yi gaskiya , in ka na takawa za ka ji sauki da maza , kuma kai ma za ka ji dadin hakan "
" hmmm , ki na dai son kare mijinki , shikenan bari na tafi " ya fada ya na kokarin mikewa
da sauri ta taro shi da cewa " a'a koma zauna ni ma shigowar tsaye ce na yi , ina son na je airport na tarbi Matar Prince "
ta fada ta na dawo da kallonta kan Malik da ya tsare ta da ido tun lokacin da ta zauna a wajen
_________________________________________
[ FREE PAGE ___ 15 ππβ€ ]
da sauri ta taro shi da cewa " a'a koma zauna ni ma shigowar tsaye ce na yi , ina son na je airport na tarbi Matar Prince "
ta fada ta na dawo da kallonta kan Malik da ya tsare ta da ido tun lokacin da ta zauna a wajen
sai da ya kare mata kallo da kyau kafin ya ce " ba tare Prince za su zo ba ? "
girgiza mishi kai ta yi ta na fadin " no , ya ce shi sai wajen karfe 10 zai shigo Saudiya , akwai aikin da ya ke son ya gama a cen "
" kira min shi " ya fada cikin tsare gida ya na matse gera
dafa hannunsa ta yi ta na fadin " please ka kyale shi , tun da ya ce zai zo ka bar shi mana , na ga ka na son matsa mishi dayawa "
" ba matsa mishi na ke ba , ba ya jin magana ne shi ya sa , ta ya zai raba yarinya da familynta sannan ya kassa kawo ta cikin tashin familyn da kansa , at least da sai ya biyo ta in ta sauka sai ya koma , ba ma ya tsoron wani abu ya same ta "
" in ya dawo ya san ba za ka bar shi ba ya koma "
" Cutie , na ga alamun ke ki goya mishi baya ya na duk abun da ya ke so "
" kamar kai da Princess ba " ta fada ta na ware mishi kananan idanun nan nata
wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya " na ji shikenan , amma zai dawo ya same ni "
dariya ta yi kafin ta matso a hankali ta manna mishi kiss saman kumatu ta mike tsaye ta na fadin " sai na dawo " ta kai karshen ta na fara takawa ta koma cikin lift
shi dai Diya ya yi zaune ya saka su a gaba ya na kallon dramar su gwanin burgewa da ga ji ka san su na son junansu fiye da komai
bayan ta baro part din part din MALIKAT INAS ta koma su ka ci gaba da hirarsu , After one hour Junior ya kira ta ya ce sun sauka
da ga nan ta tashi da kanta ta je airport dan tarbar sirikarta
bayan ta je airport a nan reception ta ci karo da su zaune saman chair su na jiran ta
Junior na ganin ta ya yi sauri ya mike ya rungume ta ya na fadin " momy "
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " sake ni na ga daughter di ta "
sai da ya yi dariya shi ma sannan ya sake ta ya dawo gefenta ya tsaya
kallon su da kyau Inaya ta yi cikin rudu , ita mutum biyu ta ke gani ya hakan ta kasance
amma sai ta shanye abun da ke cikin zuciyarta ta kalli Junior ta na daga mishi gera
a hankali ya kai bakinsa a kunnenta , cikin rada ya ce " sunanta Aleesherh , dayar twins din ta ce Prince ya ce mu taho da ita "
wani dan karamin murmushi ta saki sai yanzu ta gane abun da ke faruwa
cike da kula ta kira sunan Aleesherh
slowly ta dago kanta ta kalli Inaya
nan take Inaya ta ga hawayen da ke konce saman face din ta duk da ta wanke face din ta cikin jet
wani dan karamin murmushi Inaya ta saki kafin ta mika mata hannu
ba musu ta karaso ta riko hannunta
sannan ta kalli Aleenah ta ce " ke kuma ya sunanki ? "
ita ma kanta na sunkuye ba ta dago shi ba ta ce " Aleenah "
" Aleenah , yanzu mu tafi gida ko ? " ta fada ta na mika mata hannu ita ma
ba musu ta matso ta riko hannunta , da ga haka ta juya su ka baro airport din , su ka shiga mota guda ita da Aleesherh , Aleenah kuma ta shiga tare da Junior
saman hanyarsu Inaya sai bin Aleesherh da kallo ta ke yi , amma ta sunkuyar da kai ko sannu ba ta ce ba
wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta kai hannu ta riko hannunta , cikin sigar rarrashi ta ce mata " na san abun da ki ke ji , kar ki damu za mu kula da ke saboda ke ma d'iyar mu ce , ki kontar da hankalinki ba abun da zai faru da ke in sha Allah , ko akwai wani abu da ke damun ki ? " ta fada dan ta ga yanayinta sam ba ya kama da na yar uwarta ta na gudun wani abu Prince ya fada mata da ya karaya mata zuciya
gyada mata kai Aleesherh ta yi a hankali alamun Eh
cike da kula Inaya ta ce mata " fada min minene ? "
sai da ta hadiye yawu kafin ta ce " ku yi hakuri in har abun da zai fada bai yi muku dadi ba "
" kar ki damu fadi maganarki kawai "
" don Allah wacece Cutie a wajen Prince ? , ina so na sani in ya taba yin aure kafin ni "
wata yar karamar dariya Inaya ta yi kafin ta ce " me ya ce miki a kan Cutie ? "
" she is His first love ya ce min " ta fada idanunta na sake cikowa da ruwa
yanzu ma dariya ta yi kafin ta ce " kar ki damu , wassa ne kawai ya ke miki , Prince bai taba ko girlfriend bare aure , ba wani First love , na san ya fadi hakan ne kawai dan ya ga in ki na kishi ne ko ba ki yi , na kuma ji dadi da ki ka yi min wannan tambayar , hakan na nufin ki na kishin shi , kenan ki na son shi , right ? "
shiru Aleesherh ta yi ba ta ce komai ba , ita har yanzu ba ta samu amsar tambayarta ba , ba ta ji wacece Cutie ba , tun da har Prince ya bude baki ya ce ya na son ta hakan na nufin ta na mahimanci a wajen sa fiye da ita
ganin ba ta amsa mata ba kawai ya yi shiru , ba wanda ya ce udan har su ka iso cikin Daular Saudiya
ba karamin mamaki Aleesherh da Aleenah su ka yi ba ganin wannan uwar Daular , duk da Daular Yemen na da girma amma ta Saudiya ta yi ukun ta wajen Girma har kyau
kai tsaye Inaya ta kai Aleesherh building din su dan za ta so ta gabatar da ita ga Malik
sai da su ka iso bakin kofar part din sannan motarsu ta tsaya , ta sauko sannan ta zagayo da kanta ta bude wa Aleesherh ta na mika mata hannu
saukowa da ga cikin motar ta yi sannan ta riko hannun Inaya su ka shiga cikin part din , Aleenah kuma Junior ya tafi da ita part din MALIKAT INAS
sai da su ka shiga lift sannan Inaya ta sa hannu ta janyo hular Alkyabarta ta rufe mata kai
su na nan dai shi da Diya kamar yadda ta bar su
da sallama a bakinta ta shigo parlourn ta na janye da Aleesherh
a tare shi da Diya su ka saki wani dan karamin murmushin gefen fuska Malik ya na furta Alhamdoulilah cikin zuciyarsa
sai da ta karaso tsakiyar parlourn sannan ta ce " Malik , Baby , ina son gabatar muku da sirikarku , Aleesherh "
a hankali Malik ya mike tsaye ya karaso gabansu ya tsaya na dan lokaci sannan ya juya ya kalli Diya ya ce " Diya ka sa a fitar da one hundred million a yi wa mutanan gari sadaka "
da sauri Diya ya ce " ina ga sai dai two hundred million "
wata yar karamar dariya Inaya ta yi kafin ta ce " Aleesherh , wannan shi ne mahaifinki , ina fatan za ki girmama shi tamkar shi ya haife ki "
gyada mata kai Aleesherh ta yi a hankali ba tare da ta ce komai , ta na so ta dago kai ta kalle shi amma ta na kunya ta ji Muryarsa tak irin ta Prince ta na so ta ga in ya na kama da shi kamar yadda Muryarsu ta yi kama
ta na a haka ta jiyo Muryar Malik ya na fadin " Cutie , ki kai ta part din Ammie ta huta mana na ga alamun kamar ta gaji "
" na sani , kawai na kawo ta ne ku gan ta kafin na kai ta part din MALIKAT INAS "
" shikenan , za ku iya tafiya " ya fada ya na komawa ya zauna
ba musu ta ja Aleesherh su ka koma cikin lift
kafin kofar ta rufe ta yi sauri ta dago kai ta saci kallon Malik , kuma gaskiya ya na kama Tak da Prince har Hazel eyes din su , ba dan shekarunsa da sai a yi musu kallon Twins
da ga haka su ka baro part din su ka nufi part din MALIKAT INAS
lokacin da Aleenah ta shiga part din duk sun dauka ita ce matar Prince sai tambayar ta su ke in ta zo lafiya , ya sunanta da sauran su sai da Junior ya ce musu ba ita ba ce , matar Prince ta na tare da Inaya sun tafi wajen Malik , wannan Twins din ta ce
duk da hakan ba su hakura ba sai tarerayar ta su ke Tesnim har da fadin ta yi wa Autanta kamu , ita dai Aleenah ga na zaune ta na kallon ikon Allah
a haka har Inaya ta shigo parlourn ta na sallama ta na rike da hannun Aleesherh
nan ma duk su ka ga tarerayar Aleesherh har gift MALIKAT INAS ta ba ta , wasu bracelet na Gold da duwatsun diamond a sama ta saka mata su a hannu da kanta
sai da kyair Inaya ta kwace ta da ga hannunsu sannan ta ce wa Aleenah su tashi su tafi
ba musu ta taso ta na sunkuyar da kai ta bi bayan Inaya su ka shiga corridor din
cikin dayan bedroom ta kai su sannan ta ce " ku shiga ku yi wanka , za sa a kawo kayanku a nan , zan je na shirya muku abinci na San ku na jin yunwa "
ta na gama fadar haka ba ta jira amsar su ba ta juya ta fice
sai da ta fita sannan Su ka fara bin dakin da kallo
Aleesherh ta karaso bakin gadon ta zauna ta na kallon bracelet din da MALIKAT INAS ta saka mata , gaskiya sun yi kyau over
karasowa ita ma Aleenah ta yi ta zauna gefenta ta na fadin " gaskiya sun yi kyau sosai "
murmushi mai dan sauti Aleesherh ta yi kafin ta fiddo gudan na hannun hagunta ta mika mata ta na fadin " karbi ki saka ke ma "
dan zaro idanu Aleenah ta yi ta na girgiza mata kai ta ce " no , ke a ka bawa , ya ki ke tunanin kakarsa za ta ce in ta ga bracelet din a hannuna ? please kar ki janyo mana magana , na ga mutanan wajen duk su na kirki , ya kamata mu yi komai cikin tunani "
" na sani , kuma ba za ta ji zafi ba , please karbi ki saka "
girgiza mata kai Aleenah ta yi kafin ta tashi ta nufi kofar da ta ke tunanin toilet ce
ta na shiga ko wasu maids su ka shigo janye da trolley din su ta nufi dressing room su ka gyara musu kayan cikin closet su ka fito su na tambayar Aleesherh in ta na bukatar wani abu
girgiza musu kai kawai ta yi ta na murmushi
haka ta zauna jiran Aleenah sai da ta yi wankanta da kyau sannan ta fito , ita ma Aleesherh ta tashi ta shiga toilet din ta yi wanka , sannan ta fito ta shiga dressing room ta shirya cikin wata Abaya white color ta fito , ta dauki wayarta ta haye saman gadon ta fara latsawa , ita kuwa Aleenah tuni barci ya yi gaba da ita
AFTER SOME HOURS
a takaice dai inin ranar Aleesherh da Aleenah duk cikin bedroom din su ka share shi , sai dai Inaya ta shigo ta na tambayar su in su na bukatar wani abu , ko kuma ta kawo abinci da kanta
Prince kuwa, kamar yadda ya yi alkawari 10 na dare ya shigo cikin garin , ba karamin fada ya sha hannun Malik sai da Inaya ta kwace shi , da ga haka kuma ya koma part din da Malik ya shirya mishi
MISALIN KARFE 11 NA DARE
a hankali ya ke fitowa da ga cikin corridor din part din sa , ya na sanye da wasu pajama white color , ya daura gashin kansa a baya , ya na rike da waya kamar kullum sai aikin latsawa ya ke
a haka har ya karaso cikin parlourn ya zauna ya ci gaba da aikinsa
ya na a haka Inaya ta shigo parlourn ta na sallama ita kadai
ba tare da ya dago kansa ba ya amsa sallamar
karasowa gefensa ta yi ta zauna , da murmushi a face din ta ce mishi " sannu agogo Sarkin aiki , kai kullum ka na rike da waya ? ba ka gajiya ? "
" to Cutie in ban yi aiki ba me za ni yi ? kuma na ga ba na takurawa kowa "
" haka ne , amma yanzu ya kamata ka rage tun da ba kai kadai ba ne , ya kamata ita ma ka ba ta ko da rabin lokacinka ne "
" wa kenan ? "
hannu ta kai ta kwace wayarsa ta na matse fuska ta ce " ba na son shirme ka san sarai a kan wa na ke magana "
marairaice fuska ya yi ya na fadin " i'm serious momy , ban san a kan me ki ke magana ba "
" a kan matarka na ke magana , ka san Allah Prince ? kar ka ce za ka yi wannan wassan da ni dan ni na haife ka , dan haka tashi ka je ka dauko matarka ta dawo part din ka " ta fada ta na matse gera alamun ba wassa
cikin nitsuwa ya kai hannu ya karbi wayarsa sannan ya ce mata " me ya sa ba ki taho da ita ba ? "
" ce min ta yi wai su wajen su mijin da kansa ya ke tafiya dauko matarsa, dan haka tashi mu tafi "
wani dan karamin tsaki ya yi kafin ya ce " Cutie , wai............. "
katse shi ta yi da cewa " so ka ke sai Daddynka ya shiga maganar ? kai ma ka sani ba za ka ji dadi ba in har ya sa baki "
" shikenan let's go " ya fada ya na mikewa tsaye
wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta mike tsaye ita ma ta riko hannunsa su ka baro part din a tare
kai tsaye part din MALIKAT INAS su ka nufa
da sallama su ka shigo part din , babu kowa sai RIANNA da MALIKAT INAS
sai da su ka shigo cikin parlourn sannan ta saki hannunsa ta ce ya jira ta
ba musu ya tsaya sai tsuke fuska ya ke , MALIKAT INAS da RIANNA su na yi mishi dariya kassa kassa dan da ga gani bai ji dadin abun da a ka yi mishi ba