su a hankali ya na kallon ta
daga mishi gera ta yi ta na faɗin " tunanin me ka ke yi haka ? Allah ya sa dai ba tunanin Tsohuwar girlfriend ɗinka ka ke ba "
ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juyo ya kalle ta ya ce " no , just ba na jin jikina , like something na faruwa a gida "
" yaushe za mu koma gida ? , ni ma ina kewar Aleenah "
" har kin gaji da zama nan da ni ? " ya faɗa ya na miƙewa zaune
sai da ta girgiza mishi kai ta na murmushi ta ce " na ga abun da za mu yi a nan mu na iya yin sa a cen , kai ma na san ka na son ka koma ka ji wane hali su momy su ke ciki "
" haka ne , ina ji a jikina kamar wani mugun abu na faruwa , ina fatan tunanina ne kawai ba abun da ya faru "
" in sha Allah ba abun da zai faru ma , yanzu tashi ka shirya mana breakfast , gaskiya yau kai za ka yi mana " ta kai karshen cikin ƴar shagwaba
" ki fara ba ni nawa breakfast sai na je na shirya miki naki " ya faɗa ya na daga mata gera guda
da sauri ta tashi da ga saman gadon ta na faɗin " no , yau dai sai ka yi azumi " ta faɗa ta na juyawa za ta bar wajen
da sauri ya riko hannunta ya janyo ta , ta faɗo saman gadon , da sauri ya juya ya yi mata runfa da kirjinsa
" kin dauƙa za ki iya tsere min ? " ya faɗa ƙassa ƙassa
marairaice mishi fuska ta yi ta ce " haba baby , na gaji wlh ka bari na ɗan huta , jikina duk ciwo ya ke min "
" zan yi miki tausa "
" no , ba na so , haka jiya ma ka ce za ka yi min tausa amma ka danne ni , sai da na gaji da yi maka magiya ka kyale ni "
" shikenan , na ga ai Honey moon mu ka zo , kuma gobe za mu koma Saudiya , ki bari na yi na karshe mana "
" bari har zuwa dare , zai fi dadi , please baby " ta faɗa cike da shagwaba
a hankali ya sunkuyo ya manna mata kiss a forehead da kumatu sannan ya sauka da ga saman ta ya na faɗin " Je ki shirya zan kawo miki breakfast ɗinki Gimbiyata "
wani cool murmushi ta saki kafin ta mike zaune ta zuba mishi ido har ya baro bedroom ɗin Sannan ta tashi ta shiga dressing room
shiryawa ta yi cikin kananan kaya pink color ta karaso ta zauna gaban dressing mirror ta fara shafa lotion ɗinta
ta na zaune a haka ya dawo cikin bedroom din , rike da wani tray ya shirya mata breakfast
maimakon ya ajiye saman table sai ya ajiye saman dressing mirror a gabanta , ya tsaya a bayanta ya na kallon su ta cikin mirror
wani dan karamin murmushi ta sakin mishi kafin ta ce " lafiya ka ke min irin wannan kallon ? "
" nothing , just you look so beautiful "
" no , we look perfect "
" perfect ? "
" yeah , we are perfect , ko ba ka gani ba ne ? sai ma mun samu Baby , ma su kama da kai "
" ina fatan hakan ta kasance " ya faɗa ya na juyawa ya koma bakin gadon ya zauna ya zuba mata ido
ta na nan zaune a gaban dressing mirror ta fara cin breakfast ɗin ta na ce mishi " Honey , yanzu in mu ka samu baby wani suna ka ke son mu saka mishi ? "
sai da ya ja lokaci kafin ya bude baki a hankali ya ce " Nayab "
" wow , sunan ya na da dadi "
" yeah , sunan Little brother ɗina ne "
da sauri ta juyo ta na kallon shi , ita dai duk zaman da ta yi a Saudiya ko so guda ba ta ji an kira wani da Nayab ba , kuma bayan Princess ba ta ga wani mai kama da shi , dan in har little brother ɗinsa ne kamar yadda ya Ce tabbas sai ya yi kama da shi ko da ta jini ce
a sanyaye ta ce mishi " amma ba cikin masarautar ya ke ba ko ? "
girgiza mata kai ya yi a hankali sannan ya ce " he is die tun lokacin da mu ka shigo duniya , na so na tasso tare da shi , mu yi karatu tare , mu yi wassa da dariya , ina tunanin ya rayuwata za ta kasance in da yanzu ya na raye "
ba karamin sanyi jikinta ya yi ba jin abun da ya ce ga shi ko yanayinsa duk ya yi sanyi ,
a hankali ta mike ta karaso gefensa ta zauna ta kontar da kanta saman shoulder din sa , a sanyaye ta ce " i'm sorry my baby "
zagayo da hannayansa ya yi a bayanta ya rungume ta ya na sauke ajiyar zuciya mai nauyi
a takaice haka su ka share yinin ranar manne da junansu , ta na zuba mishi kalaman soyayya da shagwaba , shi kuma ya na biye mata , har dare ya tardo su a haka , da ga nan kuma labarin ya sauya , ni dai ina gefe ina kallon su dan al'amarin nasu ya fi karfina , da alamun shi ma Prince ya gado Malik dan dare su ka bi su na aiki guda har barci ya dauke ni su na kan aiki
washe gari misalin karfe 10 na safe Helicopter ya zo daukar su , sai da su ka rufe gidan da kayan abincin da su ka zo da su dan kar su baci , su ka gyara komai yadda su ka tardo shi sannan su ka baro Island din
☆ MASARAUTAR SAUDIYA 👑🔥 ☆
yau dai masarautar duk cikin grief su ke , mutuwar MALIKAT INAS ba karamin girgiza masarautar ya yi ba , duk wata masarautar da ke karkashin Saudiya sai da Sarkinta ya turowa Malik sakon gaisuwa , har da Al-Sayid
Malik dai tun lokacin da a ka yi jana'izar MALIKAT INAS , a ka kai ta gidanta na gaskiya , ya juya ya koma part din sa , a floor na hudu ya wuce dan kar a takura mishi , duk wanda ya zo gaisuwa da ga wajen Diya ya ke tsayawa
Inaya kuma ta na part din MALIKAT INAS tare da RIANNA , Tesnim da Nesrine , da Princess , ta na kwance ta tada kai da cinyar Inaya
su na zaune ba me ce wa kowa ufan , idanunsu duk sun yi jazir sun kunbura
su na zaune a haka Prince da Aleesherh su ka shigo da sallama a bakinsa , ya san a wannan lokacin momynsa na wajen MALIKAT INAS , shi ya sa kawai ya wuto , ga shi ko tun lokacin da ya shigo masarautar ya ke jin zuciyarsa ba dadi , ya wuto nan dan ya tabbatar kowa ya na lafiya
Princess na jiyo Muryarsa ta tashi da gudu ta nufe shi ta rungume shi ta na sakin kuka
ba karamar faduwa gabansa ya yi ba jin kukanta , musaman yanayin face din da ya ga mutanan wajen
da sauri ya ɗago ta da ga jikinsa ya na faɗin " Cutie , momy , Princess , what happened ? me ya faru ? " ya fada hankali a tashe
a hankali Inaya ta mike tsaye ta ce wa Aleesherh " Alee , shiga Wajen Leenah "
sai da ta juya ta kalli Prince a sanyaye , sannan ta fara takawa ta shiga corridor ɗin
ta na shiga Prince ya nufo Inaya ya na faɗin " Cutie , me ya faru wai ? ya na ga duk ku na cikin damuwa ? please ku fada min , hankalina duk ya tashi , tun jiya na ke jin zuciyata wani iri , please ku fada min abun da ke faruwa "
Princess ce ta amsa mishi da cewa " Prince , Ammie is die , tun bayan tafiyarku ta kwanta ciwo , jiya kuma ta tafi ta bar mu , Akhie , I miss Her " ta faɗa ta na kuka
shi dai Bawan Allah ya yi mutuwar tsaye , shi dama ya ji jikinsa ba lafiya ba , amma bai yi tunanin Ammie ce ba , tun ya na karami ba karamin so ta ke nuna mishi ba , duk ita ta sangarta shi lokacin da ya ke karami har ya ke yi wa Malik jaraba , duk yawancin shawarwarin da ya yanke cikin rayuwarsa da sa hannunta , ko auren nan nashi da Aleesherh , ita ta kwantar mishi da hankali ta ce ya yarda cikin kankanin lokaci zai shaƙu da ita , ga shi ko maganarta ta tabbata , yanzu kuma a ce ta tafi lokaci guda
ya yi nisa duniyar tunaninsa ya jiyo Muryar Inaya ta na fadin " Prince , ya kamata ka tafi wajen Daddynka , na san zai ji sanyi idan ya gan ka , ya na Floor na hudu "
gyada mata kai kawai ya yi kafin ya juya ya fice ya na taku kamar an zare mishi lakar jiki
ya na fita Inaya da Princess su ka koma su ka zauna
bangaran Aleesherh kuma kai tsaye bedroom din Aleenah ta wuce ta na yi mata sallama
ta na zaune tsakiyar gadon idanunta sun yi jazir da alamun kuka ta sha
cikin rudu Aleesherh ta karaso wajenta ta na fadin " Aleen , lafiya na ga idanunki sun yi ja haka ? " ta kai karshen ta na zama bakin gadon
wani dan karamin murmushi Aleenah ta saki kafin ta ce " Amarya , sai yau ki ka yi niyar dawowa "
" please Aleenah , ki ba ni amsar tambayata , me ya faru ne ? na ga kowa yanayinsa kamar sun yi kuka "
" Kakar mijinki ce ta rasu Jiya "
" innallillahi wa'ina illaihi raji'un " Aleesherh ta faɗa a dan razane ta na zaro idanu
shi ya sa ta ga duk mutanan wajen sun yi sanyi , kamar an aiko musu sakon mutuwa ashe mutuwar ce a ka yi , ta san yanzu Prince ɗinta ya na cen cikin wani hali dan ya faɗa mata yadda ya ke son Ammiensa , ta so ta na kusa da shi ta kwantar mishi da hankali
a hankali ta kwanta ta ɗaura kanta saman cinyar Aleenah ta lumshe idanunta
wani ɗan karamin murmushi Aleenah ta saki kafin ta kai hannu saman kanta ta fara shafawa a hankali
☆ MALIK 👑 ☆
zaune ya ke tsakiyar gadonsu , ya daura Pillow saman cinyoyinsa , hannayansa na saman pillown , ya zubawa waje guda ido , idanunsa sun yi jazir har sun kunbura da alamun ya sha kuka ko ya sha hawaye
a hankali Prince ya turo kofar dakin ya shigo ya na sallama cen ƙassan maƙoshi
ko motsi Malik bai yi ba , ko sallamarsa cikin zuciyarsa ya amsa mishi ita , ba ya jin ya na da karfin yin wani motsi a yanzu
a hankali ya karaso bakin gadon ya tsaya ya na kallon Malik ya ce " Daddy ? "
wata doguwar ajiyar zuciya Malik ya sauke kafin ya kauda kai gefe , ya kai hannu ya goge ruwan da su ka tarun mishi a ido
sannan ya juyo ya kalli Prince ya saki wani cool murmushi ya ce " ya ? har kun gama honey moon ɗin ? na zata sai na tafi cigiya da kaina "
zama ya yi bakin gadon sannan ya ce " ba kai ne ka ba mu One week kaɗai ba , da ma two weeks ka ce , ni gaskiya wannan Honey Moon ɗin ba ta ishe ni ba "
" hum, amma ai da farko ce wa ka yi ba ka so "
hannu ya kai ya fara sosa bayan keyarsa ya na kauda kai
murmushi mai dan sauti Malik ya yi kafin ya lumshe idanunsa
ya na a haka ya ji Prince ya kwantar da kansa saman shoulder din shi
a sanyaye ya ce " Daddy , I'm sorry , na san ka yi kewa ta sosai tsawan shekarun nan da ba na zama tare da kai "
" na yi kewar ka sosai , amma hakan ya sa na ji irin kewar da Daddyna ya ji lokacin da na nan , da sauki ni na san halin da ka ke ciki , shi ko bai da ma tabbacin in ina raye , na sani ba laifinka ba ne , kuma ni ba na fushi da kai tun da ga shi yanzu ka dawo "
" I love you my Daddy " ya faɗa ya na zagayo da hannayansa a kugun Malik ya rungume shi ta gefe , ya lumshe idanunsa
sai da ya saki wani dan karamin murmushi sannan ya juyo ya manna mishi kiss a forehead ya na fadin " I love you too , my baby "
shiru Prince ya yi bai ce mishi komai ba , ajiyar zuciya kawai ya saukewa ƙassa ƙassa
ya na a haka ya ji Malik ya zagayo da hannunshi a bayansa ya na fadin " Ba ka fada min ya Honey moon ɗinku ta kasance ? "
" So Sweet " ya fada a takaice da alamun ya manta da wa ya ke zaune
dan zaro idanu Malik ya yi jin abun da ya ce ko kunyar sa bai ji ba , shi kuma ya ci gaba da tambayar shi ya na fadin " kenan yarinyar mutane ka taɓa ? "
" na ga ai Mallaka min ita a ka yi , har gaban Allah tawa ce " da ga haka ya ware idanunsa ya na kallon Malik , ya ci gaba da fadin " amma ka san wani abu Daddy ? ban taba jin irin wannan dadin ba , Allah Daddy sai da na dinga ganin wasu stars "
Bushewa da dariya Malik ya yi har sai da idanunsa su ka ciko da ruwa bai da labari , amma Allah Prince ya cika dan Duniya , ko kunyar Malik bai ji ya fadi wannan abun , ai da farko da a ka ba shi auren ce wa ya yi ba ya so shi ya sa Malik ya bushe da dariya , yanzu ya fara jin dadin d'iyar mutane har da ganin wasu taurari
sai da ya gama dariyarsa sannan ya ce mishi " ka na ji , idan ka kai makura ba stars kadai za ka gani ba , sai ka ga universe din ma baki daya , Allah ya sa dai ba ka takura mata "
" to ba ita ta ce za ta iya ? dole ta yi hakuri tun da ta lasa min zuma "
" hakan na nufin you love her ? "
" Yes Daddy , ina son ta , fiye da yadda na ke jin ina son kaina , but I love you more than her " ya fada ya na kara matse Malik
wata yar karamar dariya Malik ya yi kafin ya rungume shi tsam shi ma , a haka har barci ya yi gaba da su
☆ AFTER SOME HOURS ☆
▪ INAYA 👑
a hankali ta turo kofar dakin ta shigo ta na sallama a sanyaye
ta na shigowa idanunta su ka sauka kan Malik da Prince kwance , Prince na kankame da Malik kamar wani ya ce zai kwace mishi shi
har sai da ta saki wani cool murmushi ba ta da labari dan ta manta last time da ta gan su manne da juna haka
a hankali ta ci gaba da takowa bakin gadon , ta sa hannu a hankali ta janye hannun Malik da ke saman bayan Prince
sannan ta dan bubuga kumatun Prince , kassa kassa ta ce mishi " Prince , ba za ka je ka yi wanka ba ? "
cikin magagin barci ya ce mata " please Baby , barci na ke ji "
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta murde kunnesa ta na fadin " wake up , ba ita ba ce , Maza tashi min da ga saman gado "
cikin wata siririyar murya ya ce mata " ashhh , Cutie da zafi fa "
" sauko to " ta fada ta na sakin kunnensa
a hankali ya tashi da ga jikin Malik ya sauko da kafafunsa kassa ya zauna bakin gadon ya na kallon ta ya na yamutse fuska
hararrar shi ta yi kafin ta nuna mishi kofar fita da hannu
bai ce mata komai ba ya juya ya manna wa Malik kiss a kumatu , sannan ya mike tsaye ita ma ya yi mata kiss a kumatu kafin ya sa kafa ya fice, ya baro part din baki daya
sai da ya fita sannan ta saki wani dan karamin murmushi , ta tako a hankali ta kwanta in da ya tashi , ta rungume Malik
kawai sai jin saukar hannunsa ta yi a bayanta , ya juyo su na fuskantar juna ya bude idanunsa a hankali , dama ba barcin ya ke ba , tunanin MALIKAT INAS ya hana shi barci
a sanyaye ya ce mata " me ya sa za ki korar min babyna ? ba ki ga barci ya ke ba ? "
cikin shagwaba ta ce mishi " ni kuma fa ? ni ma barci na ke ji "
wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya matse ta tsam a jikinsa ya lumshe idanunsa
ita ma lumshe idanunta kawai ta yi ta na sauke ajiyar zuciya
▪IZZAT
zaune ta ke gaban mirror din bedroom din ta , ta buga wani uban tagumi , tun safe ta ke