x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 4 - NAYEL THE RETURN OF EXILED PRINCE

  • 9001 words
  • 12000 words
  • Out of 89550 words

Category: Love Stories

Views 402

14 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ya meda trouser din sa ya na fadin " Are you mad ? Get out ! ! ! " ya fada da karfi har wani runtse ido ya ke dan ba karamin haushi ta ba shi ba , at least da sai ta yi mishi knocking , da yanzu ya kai ga cire trouser din shikenan ta gama sanin sirrinsa


ko motsi ba ta yi ba da wajen ta sulale a kassa sumamiya

ya na ganin haka ya ja wani dan karamin tsaki ya juya ya nufi toilet

taku daya ya yi ya tsaya cak , ya na zaro idanu
lokaci guda ya juyo ya na zuba mata ido cikin rudu , ya kassa ganewa , ya a ka yi yarinyar da ya bari yanzu a kasuwa har ta riga shi zuwa hotel , Hotel din ma ba karamin Hotel ba a ce kuma server ce , to me ta ke yi a kasuwa cikin tsohin kayan cen ? abun ya tsaya mishi a kai

wani dogon tsaki ya ja kafin ya kai hannu ya dauki wayarsa ya fara latsawa na dan lokaci kafin ya tilla ta saman gadon ya juya ya shige toilet ya medo kofar

ya na shiga ko wani bodyguard ya shigo , ya na sallama
kai tsaye yarinyar nan ya nufa ya sa hannayansa biyu ya dauke ta ya saba a kafada ya fice


After one hour ya fito da ga cikin toilet din ya na Sanye da bathrobe white color , gashin kansa na jike da ruwa duk ya bazun mishi a saman shoulder

hanyar dressing room ya nufa ya shiga
jim kadan ya fito sanye da wasu Tracksuit ash color , babu takalmi a kafafunsa , ya daure wanan smooth hair din sa a baya sai tashin qamshi ya ke

kai tsaye bed din ya nufa ya na shirin zama dai-dai lokacin da wayarsa ta fara ringing
sai da ya zauna sannan ya kai hannu ya dauki wayar , ya dauki kiran ya kai wayar a kunne ya na sallama cen kassan makoshi

a daya bangaran Muryar wani saurayin na jiyo ya na amsa mishi sallamar
cikin nitsuwa ya daura da cewa " Prince , How are you ? "

a takaice Prince ya ce mishi " fine , ya ka ke ? ya jikin uncle ? "

" jiki da sauki , har ma mun medo shi gida , yanzu dai fada min yaushe za ka zo ? uncle ya ce gobe su na kan hanya "

wani dogon nunfashi ya ja ya na saukewa a hankali kafin ya ce " i think nan da one week , tukunna ba mu samu mun yi meeting din ba , may be Friday na dawo " ya ke fada cike da nitsuwa kai ka ce an yi mishi dole ya yi maganar

" okay , zan tafi ka kula min da kanka "

" in sha Allah , ka gaishe min da uncle , da Ammie "

" okay " ya fada a takaice kafin ya katse kiran

Prince na jin ya katse kiran ya sauko wayar a hankali kai tsaye ya ajiye saman bedside drawer , ya dauki laptop din sa da ke sama ya medo saman cinyoyinsa ya bude

ya na bude ta ko ta kunnu , sai saman pic din Inaya da Malik ya na rungume da ita sai murmushi su ke saki

a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya kai yatsunsa biyu saitin bakinsa kamar ya manna kiss saman ya sauko yatsun ya daura saman pic din
cikin sanyin murya ya ce " i really miss my pleasures , in sha Allah next week zan dawo , na san kuma ku na kewa ta sosai ,,,,,,,,,,,,,,, but ba laifina ne ba , aikin da na zaba ne ba ya bari na zauna tare da ku amma in sha Allah komai ya kusa kammala " ya na gama fadar haka ya shiga latsa laptop din sa



♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡



U.S.A ( WASHINGTON DC )


MALIK 👑



konce ya ke tsakiyar gadon su , da ga shi sai short da singlet , ya bubude hannayansa ya zubawa ceiling ido babu ko kiftawa

ya na a haka Inaya ta fito da ga cikin toilet ta na sanye da bathrobe sai wani dan karamin towel a hannunta ta na goge gashinta

idanunta na sauka saman shi ta san ya na cikin damuwa
ajiye towel din hannunta ta yi saman dressing mirror sannan ta tako a hankali ta zauna bakin gadon ta zuba mishi ido

a haka har su ka yi mintina amma sam bai motsa ba kamar ba ya nan
cikin sanyin murya ta ce mishi " Baby , tunanin me ka ke yi haka ? "

wata nanauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya lumshe idanunsa slowly ya bude su , sannan ya juyo ya kalle ta na dan lokaci kafin ya saki wani cool murmushi ya na fadin " Nothing my Cutie "


tsuke fuska ta yi ta na matse gera ta ce " ka san ba abun da za ka iya boye min ko ? fada min me ke damun ka ? "

" na sani amma na ce miki ba komai My Cutie , kar ki matsa please "
turo mishi dan bakin nan nata ta yi ta na marairaice fuska kamar za ta yi kuka
wata yar karamar dariya ya yi kafin ya ce " shikenan , kar ki min kuka "

cike da shagwaba ta ce " to fada min me ke damun ka ? "

a hankali ya juya ya na kallon ceiling ya ce " ba komai , kawai ina tunanin halin da Diya ke ciki ne , har ya yi paralyze a kassa samun wanda zai kira na ya fada min , Cutie i think ban yanke shawara mai kyau ba dawowar mu US baki daya , ko ba komai da na tsaya ina taimaka mishi , in wani abu ya same shi gaskiya ba zan iya jurewa ba , shi kadai ya yi min saura a duniyar nan " ya fada murya a dan raunace

ajiyar zuciya ta sauke kafin ta riko hannunsa cikin nata , ta matse
cikin sigar rarrashi ta ke fadin " baby , duk shawarwarin da yanke duk ma su kyau ne , kawai ka yi abun da zuciyarka ke fada maka ya dace ne "

" No Cutie , da yanzu a ce shekarun baya ban sauka da ga kan kujerar Malik ba da Aymane ba zai taba hawan ta ba har ya yi abun da ya yi , a ce lokacin da mu ka samu cikin Twins ban matsa miki a zubar da shi ba na San da yanzu shi ma Nayab ya na tare da mu , ina sane da illar da stress ke haifarwa mace mai karamin ciki amma na yi ta jefa ki cikin damuwa , har ya yi sanadiyar Nayab tun kafin ya shigo duniya , da a ce ban nada Diya ba a madadi na da yanzu bai k.......... "

ba ta bari ya kai karshen maganarsa ba ta daura hannu saman bakinsa ta katse shi
cikin sanyin murya ta ce " ya isa haka baby please , ya isa , ka daina tuna abun da ya wuce , duk abun da ya faru kaddara ce , Allah ya riga da ya rubuta mana hakan , kuma in sha Allah ba abun da zai samu Diya , dan haka ka kontar da hankalinka please " ta karashe maganar ta na marairaice mishi fuska


bai ce mata komai ba ya fiddo tongue din sa ya fara yi mata tafiyar tsutsa a tafin hannunta

wata yar karamar dariya ta yi kafin ta janye hannunta ta na fadin " ya isa haka , yanzu konta ka yi barci ba ka ga dare ya yi " ta fada ta na kokarin sauka da ga saman gadon

da sauri ya riko hannunta ya na fadin " ke kuma ina za ki je ? "
" kaya zan je na saka "

a hankali ya janyo ta jikinsa kafin ya dago kai ya kawo fuskarsa dab da face din ta , cikin rada ya ce mata " yau ki ka saba kwana da bathrobe ? zo ki konta kawai "

murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta haye saman jikinsa , ta na faman turo dan bakin nan nata kamar ya yi mata dole

hannunsa ya kai cikin jelar gashinta ya fara yi mata wassa da shi ya na fadin " kin san wani abu ? gaskiya zan so mu sake samun Nayab "
noke mishi kafada ta yi cikin shagwaba ta ce " ummm ni ba na so , ka manta irin azabar da na sha kafin su shigo duniya ? kuma ko ka na so ni ba zan iya haihuwa ba a yanzu "

" in ji wa ? ai har yanzu ki na period kin ga mun iya samun Nayab , please my Cutie "

ba ta ce mishi komai ba ta sauka da ga saman kirjinsa , ta koma gefe ta konta ta juya mishi baya
haka shi ma bai ce mata komai ba ya zagayo da hannunsa a kugunta , ta yi tunanin janyo ta zai yi jikinsa kawai sai ta ga ya warware igiyar bathrobe din jikinta , ya yi kassa da ita , ya manna mata kiss saman shoulder
a hankali ta sauke ajiyar zuciya kafin ta juyo su na fuskantar juna , kawai ya cabko lips din sa ta fara kissing din shi , nan take ta gama birkice mishi lissafi kawai ya sake mata ragamar

( 😴😴 a to ni na gudu da ga nan , abun ya fi karfina , sai mun hadu da safe )



❤⚘ 𝐍𝐀𝐘𝐄𝐋⚘❤
________________
ᴛʜᴇ ʀᴇᴛᴜʀɴ ᴏғ ᴇxɪʟᴇᴅ ᴘʀɪɴᴄᴇ





THE BIGINING 🕊👑❤





🕊💞 ( 𝙰 𝙷𝙴𝙰𝚁𝚃 𝚃𝙾𝚄𝙲𝙷𝙸𝙽𝙶 𝙻𝙾𝚅𝙴 𝚂𝚃𝙾𝚁𝚈 , 𝚁𝙾𝙼𝙰𝙽𝚃𝙸𝙲 , 𝙸𝙽𝙹𝚄𝚂𝚃𝙸𝙲𝙴 & 𝙳𝙴𝚂𝚃𝙸𝙽𝚈) 💞🕊






❤👑 𝑴𝑨𝑳𝑳𝑨𝑲𝑰𝑵.𝑨𝑴𝑬𝑬𝑹𝑨𝑯 𝑨𝑩𝑫𝑶𝑼𝑳𝑨𝒀𝑰👑❤
( 𝑨.𝑲.𝑨 𝑴𝑬𝑬𝑹𝑨𝑯 ) ❤🕊






TAP THIS LINK TO JOIN MY COMMENT SECTION
https://chat.whatsapp.com/JTfho9QngpG5Ax4LM4d4sK




_______________________________________________







[ PAGE___ 4 🕊👑❤ ]









MASARAUTAR YEMEN 👑❄




a hankali ya ke tafiya cikin wata makekiyar library , ya na sanye da wasu suit white color ma su bala'in kyau da tsada , ya na tafiya a hankali da waya a kunnensa da alamun kira ne ya ke

sai da ya karaso wajen wani closet sannan ya tsaya ya na fadin " Junior , ka na son ka ba ni aiki wlh , ina zan samo wannan littafin don Allah ? "

" please Bro , ka duba na san za ka same shi a nan saboda marubucin na nan kassar Yemen ne , ka duba mana pleaseeeee " ya fada ya na marairaice murya

wani dan karamin tsaki Prince ya yi kafin ya sauko wayar ya meda cikin aljihunsa , ya kai hannu ya zaro wani book , dai-dai lokacin da a ka zari book din da ke gefensa ta daya bangaran


idanunsa ba su sauka ko ina ba sai cikin nata su ka yi ido hudu
a rude ya zuba mata ido ya kasa gasgata abun da ya ke gani
ta na sanye da wata tsadadiyar Gown irin wannan mai budewar nan da ga kassa , ta yafa wani dan karamin veil fari a kanta amma jelar gashinta duk a waje ta ke , duk da ta yi simple make up hakan bai hana shi gane ta ba , kai ka ce ita ce diyar Sarkin Yemen din baki daya


a hankali ta juya ta bar wajen ba tare da ta ce mishi komai ba ta na sunkuyar da kai

shi kuwa tsaki ya ja kafin ya meda book din , ya bar wajen shi ma , kai tsaye wajen librarian din ke kula da libraryn ya koma

murya kassa kassa ya yi mata sallama da kyair ma ta iya jiyo ta
da fara'a a fuskar ta ta amsa mishi ta na tambayar ta wacce hanya za ta taimaka mishi

wayarsa ya fiddo , ya fara latsa screen din na dan lokaci kafin ya mika mata ya na fadin " wannan littafin na ke nema "

ba musu ta kai hannu ta karbi wayar ta na kallon sunan littafin
bayan ta karanta ta mika mishi wayarsa ta na fadin " i'm sorry Sir , but duk wani littafi da ya shafi tarihin masarautar Yemen a libraryn Daular a ke kai shi , ba za ku iya samun shi a ko ina ba sai a Daular , i'm sorry "

wani dan karamin tsaki ya ja ya na meda wayarsa cikin aljihu ya ce mata " Thanks " a takaice kafin ya juya ya fara takawa zai bar wajen

har ya iso bakin kofar fita idanunsa su ka sake sauka saman ta
ta na zaune saman chair ta na rike da book kamar wata mutuniyar kirki

a hankali ya juya ya fara takawa ya nufi in da ta ke
babu ko sallama ya ce " me ki ke yi a nan ? ko yanzu ma kin zo yin satar ce a nan ? "

slowly ta dago kai ta zuba mishi ido ba tare da ta ce komai ba
sai da ta dauki wajen one minute kafin ta ajiye book din hannunta saman table din , a hankali ta juya ta fara takawa ta nufi hanyar fita ta fice ba tare da ta ce mishi komai ba

da kallo ya rakata har sai da ta fita ya kuma kassa ce mata komai
a haka har sai da ta fice sannan ya yi saurin bin bayanta dan ya na so ya san ya a ka yi jiya ta riga shi komawa Hotel , me ta ke yi a cen ma bayan yanayin da ya gan ta sam ba ta yi kama da me aiki a irin wannan hotel ba , yanzu kuma sai ka ce ita ce diyar Al-Sayid , ko dai aljana ce ke bibiyar ba shi da labari

da wannan tunanin ya fito libraryn
amma wani abun mamaki ya na fitowa ya neme ta sama da kassa ya karasa
a gaban idon shi ta fito ko ten secondes bai yi ba ya biyo bayanta shi ma ya a ka yi ta bace mishi in one seconde haka , ko dai aljana ce ?

( 🤔🤔 ni ma abun nan ya fara damu na , ko dai aljana ce ? duk in da ya je sai ya gan ta , ni dai abun nan ya fara ba ni tsoro )

wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya ci gaba da takawarsa ya nufi motarsa ya shiga su ka bar wajen




DAULAR YEMEN 👑


FADAR AL-SAYID ABDOUL-MUEED



Fadar babu kowa a ciki kamar an yi busa , bai su wuce mutum goma
cen na hango Al-Sayid zaune saman kujerarsa , fuskarsa babu yabo babu fallasa , kai da ga gani ka san zai yi fara'a

sai tattauna su ke da mutanan fadarsa cikin nitsuwa
su na a haka na ga wata mata ta shigo fadar ta na sanye da wasu kaya farare , a shekaru za ta kai 40 haka ko fi ,

da gudu ta karaso tsakiyar Fadar ta Zube saman guyiwowinta
ta sunkuyar da kai ta na fadin " Gaisuwa na ke ya ke shugabana , ranka shi dade akwai matsala , na duba part din yan biyu ban gan su ba ranka shi dade , na duba hart part din mai dakin gabas da mai dakin yamma amma duk sun ce tun jiya cikin dare ba su gan su ba "


wani dogon nunfashi Al-Sayid ya ja kafin ya daga mata hannu a hankali ya na fadin " za ki iya tafiya ba sai kin damu kan ki ba "

ba musu ta tashi ta fice Fadar

ta na fita daya da ga cikin mazauna fadar ya ce " ranka shi dade , Gimbiya Aleesherh da Gimbiya Aleenah ba su cikin Daular nan fa , kuma ka ce ta tafi kar ta damu kanta , in wani abu ya same su fa ? "

wani dan karamin tsaki ya ja ya na fadin " to ya ke so na yi ? yaran nan ne sam ba su jin maganata , ban san ya a ka yi su ka gano hanyoyin sirrin Daular nan ba , tun da ga lokacin shikenan sun samu hanyar fita , su na cen cikin masarautar su na shirme , ni ban ma san ya zan yi da su na "


" ranka shi dade tun da ka kassa , me zai hana ka aurar da su ? "

" aure kuma ? to wa ma zai auri wadanan yaran ? yara a ce ba ku da aiki sai wassa , ni da na Samu wanda zai aure sun ni da kyauta ma zan ba shi , saura kadan su saka min hawan jini dan jaraba "


a tare duk mutanan Fadar su ka yi dariya , sun san halin Shugaba nasu da yaransa , su kadai Allah ya ba shi , tun su na yara ya yi mugun shagwaba su , ya ke tarerayar su kamar Egg , ai dole yanzu su gagare shi


cen sai daya da ga cikin su ya ce " ranka shi dade me zai hana ka bawa yaran Malik Nawfel Hicham Bin Jaabar auren su ba ? a tarihin masarautar Saudiya ba a taba samun Malikat da ga masarautar Yemen ba , me zai hana su kasance na farko , hakan zai kara gyara alakar kasuwanci da ke tsakanin Saudiya da Yemen , ko ya ku ka gani ? " ya fada ya na kallon sauran mutanan fadar


wanda ya yi magana da farko ne ya karbe zancen da cewa " haka ne ranka shi dade , ina ga hada Zuri'ar ka da ta Malik Nawfel Bin Jaabar ba karamar daukaka zai janyowa Masarautar Yemen "


" in na gane kamar auren yarjejeniya ne za a yi musu ko kuwa ? "
End Ads