sane sarai da shi amma su ke zuba soyayyarsu ko kunyar sa ba su ji
( hmmmm in dai Malik ne ba ka ga komai ba ๐คฃ )
โชWASHE GARI โ
โชMASARAUTAR YEMEN ๐
Zaune Aleesherh ta ke cikin parlourn su , sanye da wata tsadadiyar gown blue ta daura wata farar Alkyaba da ga sama , ta yi mata kyau Over duk da ba ta yi make up ko kadan ba , amma fuskar ta na a daure kamar wadda uwarta da ubanta su ka rasu
ta na zaune a haka Aleenah ta fito da ga cikin wardrobe sanye da kaya tak tak irin nata sai dai ita gown din ta white color ce , fuskarta babu yabo ba fallasa sai sha-aninta ta ke
su na a haka Sayida Ahlame ta shigo ta na yi musu waya da murmushi a face din ta ta ce " ku tasso mu tafi su na fadar Al-Sayid "
ba musu Aleesherh da Aleenah su ka mike su ka bi bayanta
a cen kuma Fadar Al-Sayid
zaune Junior ya ke cikin fadar ya na Sanye da wasu suit blue ma su mugun kyau kuma gaskiya sun kama shi
sai jan sa da hira Al-Sayid ya ke
su na a haka har Sayida Ahlame ta shigo rike da hannayan Aleenah da Aleesherh ta karaso cikin fadar ta zaunar da su saman chair din da ke fuskantar wadda Junior ke zaune , dama yau fadar ba mutane dayawa a ciki da ga Al-Sayid sai Sayida Fadwah da Sayida Ahlame sai kuma wasu biyun na hannun daman Al-Sayid wanda su ka kawo shawarar auren ma
bayan ta zaunar da su Sayida Ahlame ta koma saman chair din ta da ke gefen damar kujerar ta Al-Sayid ta zauna , Sayida Fadwah kuma ta na a gefen hagu
sai da ta zauna sannan Al-Sayid ya ce wa Junior " wadanan su ne yaran nawa , mai blue din riga ita ce babbar Aleesherh , dayar kuma sunanta Aleenah "
wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya ce " Amma ranka shi dade ba ni ne a ka aiko ya gan su ba " ya fada dan kar ma Al-Sayid ya yi mishi maganar ya zaba ya rasa amsar da zai ba shi
cikin rudu Al-Sayid ya ce " kamar ya ? ba kai ne Yaron Malik Nawfel ba ? "
girgiza mishi kai Junior ya yi ya na fadin " no , ni cousin din sa ne , amma wajen Malik na ke zaune , shi ya sa ma ya ce mu taho tare "
" to ina dan uwan naka ya yi ? "
" sorry uncle , ya na wani kira ne mai mahimanci amma yanzu zai shigo "
da to kawai Al-Sayid ya amsa mishi ya na kallon kofar fadar ya na jiran ya ga wanene zai shigo dan shi fa ko Malik din a Tv kawai ya taba ganin sa bare yaronsa da bayan familynsa ba wanda ya san sunansa
sun yi wajen two minutes zaune a haka ba wanda ya ce wa kowa ufan ,
Har Al-Sayid ya bude baki zai yi magana su ka jiyo Muryar Prince ya na sallama cike da nitsuwa
dam Aleesherh ta ji zuciyarta ta buga har sai da ta wani lumshe idanu amma sam ba ta yi kokarin dago kai ba bare ta ga in da gaske shi ne ko ba shi ba ne
cikin rudu Al-Sayid ya kare mishi kallo dan ya gane fuskarsa sarai , amma bai kawo komai a ransa ba kawai ya yi tunanin ko wani littafin ya zo nema a libraryn masarautar
ya na sanye da wasu suit white color shi kuma , ma su bala'in kyau kamar dai irin na Junior
sai da ya karaso wajen Chair din da Junior ke zaune ya tsaya ya na fadin " ina mika gaisuwata ga shugaban wannan kassar mai Albarka "
da murmushi a face din sa Al-Sayid ya ce " ina amsawa , yau kuma me ya kawo Prince wannan fadar ? ko dai wani littafin ka zo nema ? "
da sauri Junior ya kalli Prince ya na zaro idanu , ya na tambayar kansa ya a ka yi Al-Sayid ya san sunansa Prince kenan dama ya taba zuwa fadar Yemen
girgiza mishi kai Prince ya yi kafin ya ce " zan so na fara gabatar da kaina , sunana Prince Nayel Hicam Bin Jaabar , d'a ga Malik Nawfel Hicham bin Jaabar , zan so na mika sakon godiyata kai tsaye ga Al-Sayid da wannan gayatar " ya fada cike da izza
baki sake Al-Sayid da sauran mutanan fadarsa biyu ke kallon Prince , kenan dama ya zo fadar ba su da labari
Junior kuma sai tabe baki ya ke jin kalaman Prince ya na fadin " sannu Prince , izzar taka a nan ma sai ka nuna ta ? zan yi maganin ka in ka koma "
cike da kula Al-Sayid ya ce mishi ya zauna
ba musu Prince ya zauna gefen Junior
ita dai Aleesherh ta na jin duk abun da ke faruwa amma ta kassa dago kai , ta na gudun ta dago kai ta ga ba abun da ta yi zato ba ne
ta yi nisa duniyar tunaninta ta jiyo Aleenah ta na bubuga cinyarta ta na fadin " Alee , Daddy na mike magana "
a razane ta dago kai dan ita sam ba ta ji abun da ya ke cewa ba
ta na dagowa ko idanunta su ka sauka saman Prince da ke zaune ya tsare ta da ido shi ma tun zamansa ya ke jiran ta dago kai amma ta ki
dama Aleenah karya ta ke mata dan ta lura da irin kallon da Prince ke yi wa Aleesherh , shi ya sa ta ce ta dago kai su ga juna
cikin nitsuwa Al-Sayid ya ce wa Prince " ya kamata ku tafi part din da a ka gyara muku ku huta , zan sa a kai muku abinci "
Junior ya amsa mishi da cewa " a'a Uncle , taf....... "
bai karasa maganarsa ba Prince ya katse shi da cewa " mun gode ranka shi dade , amma mun riga da mun kama bedrooms a hotel , so a cen za mu sauka "
wannan karan Sayida Ahlame ce ta karbi zancen da cewa " a'a , gaskiya ba za ku kwana a hotel ba , mun riga da mun shirya muku part , dan haka sai ku tashi ku tafi , Aleesherh ko za ki kai su part din ? "
gyada mata kai Aleesherh ta yi kafin ta mike tsaye a hankali ta na fadin " bismillah "
ba musu Junior da Prince su ka mike su ka yi wa Al-Sayid sallama sannan su ka bi bayanta su ka baro fadar
sai da su ka yi dan nisa da Fadar sannan Junior ya cewa Prince " lafiya ka ce za mu zauna ? Daddy fa ya ce da mun zo mu koma , ni gaskiya ba Niyyar zama "
wani dan karamin tsaki Prince ya ja kafin ya ce " kai don Allah yi min shiru , ba duk kai ne ka janyo min ba , da ba ka bawa Daddy wayar a lokacin da na kira ka ba da ba zai ce na dawo ba , dan haka malam sai dai ka yi hakuri har na yi sign din contract din da ya kawo ni Yemen , in ya kira ka ce mishi Al-Sayid ne ya matsa mu zauna "
" no , ni gaskiya ba zan yi wannan karyar ba , ka san halin Daddy "
" Junior ka san Allah na fi ka duk shirmen da ka ke ji , in har na rasa wannan contract a karo na biyu saboda kai , Allah sai na hana ka samun sukuni a rayuwarka "
bushewa da dariya Junior ya yi har da tapi , kafin ya ce " ba dan Daddy ya yi maka auren dole ba za ka sauke haushin sama na , da ga na fadi gaskiya "
wani dan karamin tsaki Prince ya ja kafin ya juya ya na kallon gabansa
nan ya tuno ashe ta na a wajen
shi ko bai san duk maganarsu ta jiyo ta , kuma sun yi mugun tuno mata ita da Aleenah , haka su ke wannan jayayar in ta ce za ta yi wani abu
sai da su karaso bakin kofar part din ta sa hannu ta tura kofar sannan ta koma gefe ta tsaya kai a sunkuye ta ce musu " bismillah "
godiya Junior ya yi mata kafin ya shiga part din kai tsaye , shi kuwa Prince ya tsaya ya zuba mata ido
ganin har yanzu ya na tsaye a gabanta ya sa ta dago kai slowly , kai tsaye idanunta cikin nashi su ka sauka
kauda kai ta yi a hankali kafin ta juya za ta bar wajen
cikin nitsuwa ya taro ta da fadin " wa ya ba ki izinin tafiya ? "
ba tare da ta juyo ba ta ce " na ga wanda ya ba ni umarnin kawo ku wajen nan ba ya nan bare ya ce min kar na tafi "
" All right , za ki iya tafiya za mu hadu a gaba " ya na gama fadar haka ya fara takawa ya shiga cikin part din
ta na jin ya fara takawa ita ma ta ci gaba da tafiyarta , kai tsaye part din su ta koma
ko da ta shiga ta tardo Aleenah zaune bakin gadonsu
ba ta ce mata komai ba ta fiddo wayarta , ta sa music ta kai karar karshe sannan ta tilla wayar saman gadon
ta kai hannu ta cire Alkyabarta ta tilla gefen wayar
cikin rudu Aleenah ta tsaya ta na kallon ta ta na jiran ta ga abun da za ta yi
ba zato ba tsanmani kawai ta ga Aleesherh ta fara rawa har da kama sautin wakar ta na girgije wa da kyau
ita dai Aleenah ta yi zaune ta na kallon ikon God
su na a haka Sayida Ahlame ta shigo wajen
cak ta tsaya ta na kallon Aleesherh sai rawarta ta ke cikin konciyar hankali ta na murmushi
cikin rudu ta karaso wajen ta na fadin " Alee , lafiya ki ke rawa haka ? "
Aleenah ce ta ba ta amsa da cewa " momy , saurayin da ta ce muku ta na son shi , to shi ne Prince "
dan zaro idanu Sayida Ahlame ta yi ta na kallon Aleesherh sai rawa ta ke
wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta riko hannunta ta na fadin " rawar ta isa haka madam , zo zauna na yi miki magana "
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " momy i'm so happy , i can't imagine , don Allah ko mafarki na ke kar ku tashe ni "
hannu Sayida Ahlame ta daga za ta marin ta ta na fadin " ni zan tashe ki to yar rainin hankali kawai "
dariya kawai Aleesherh ta yi kafin ta zauna bakin gadon ta na kallon Sayida Ahlame
sai da ta zauna sannan Sayida Ahlame ta ce mata " yanzu an kawo miki scrub ki yi kafin ki shiga wanka , kuma Ammie ta ce ta turo miki perfume da wasu abubuwa ban San ko minene ba dan ba ta fada min ba , Al-Sayid ya ce next Friday za a yi auren in da rai da lafiya " ta na gama fadar haka ta juya ta fice
hannu Aleesherh ta kai ta boye fuskarta ta na murmushi kafin ta yi baya ta konta saman gadon zuciyarta cike da farinciki kamar ta tashi sama ta ke ji
Aleenah dai duk ta yi sanyi , sai latsa wayarta ta ke cikin konciyar hankali , ta ma rasa me ke yi mata dadi a duniyar nan ba ki daya , kuma ta kasa tantance abun da ke damun ta , ko dai kishi ta ke ?
๐ค๐ค๐ค TO FA ALEENAH ZA TA FARA KISHI DA ALEESHERH KO YA ?
TAP THIS LINK TO JOIN MY COMMENT SECTION
https://chat.whatsapp.com/JTfho9QngpG5Ax4LM4d4sK
_______________________________________________
โช๏ธPAID BOOK N500
[ FREE PAGE ___ 11 ๐๐โค ]
MISALIN KARFE 8 NA DARE
โชPRINCE ๐
a hankali ya ke tafiya cikin harabar masarautar , ya na sanye da trouser white color da t-shirt blue , ya na rike da wani file a hannunsa ya na dubawa
ya na tsaka da tafiyarsa ya ji karar sword kamar a na wassan takobi
a hankali ya dago kai ya kalli saitin da ya ke jiyo karar
nan idanunsa su ka sauka saman ta , ta na sanye da wasu Tracksuit pink color , ta daure gashin kanta a baya , ta na rike da sword su na wassa ita da wani dogari , ba karya kuma gaskiya ta iya
Aleenah ta na zaune saman wata chair ta na kallon su
haka shi ma ya tsaya ya zuba musu ido ya kassa janye idanunsa ya rasa dalili
a hankali ya rufe file din sa ya fara takawa cike da izza ya nufe su
ya na isowa ya mikawa Aleenah file din
cikin rudu ta kai hannu ta karba ta na kallon shi , shi kuma ya na kallon su Aleesherh
cikin nitsuwa ya katse su da cewa " ina son na gwada ni ma "
cak su ka tsaya su ka juyo ita da dogarin su na kallon shi , ta na ganin sa ta kara tsuke fuska
ba musu dogarin ya karaso ya bawa Prince sword din hannunsa
karba Prince ya yi ya karaso wajen da ya baro su na fuskantar juna shi da Aleesherh
" ina fatan kin iya kare kanki dan ba zan raga miki ba "
" hm " ta fada cen kassan makoshi kafin ta kai mishi hari
da sauri ya dago takobinsa ya kare kansa , da ga haka su ka shiga wassan a tare cikin kwarewa dan Prince ma ba baya ba ya iya wassan takobi dan tun lokacin da ya fara tasowa ya ke yi
mu dai ni da Aleenah mun yi zaune mun zubawa ikon God ido , kamar ba su gajiya yaran nan
su na cikin wassan nasu ya samo ta a damtse har sai da ta yanke jini ya fara zuba
a tare shi da ita duk su ka saki sword din su , ita ta na dafe hannu
shi kuma ya nufo ta ya na fadin " i'm sorry , ba ki ji ciwo sosai ba ? " ya fada ya na shirin taba ta
da sauri ta ja da baya ta na fadin " don't touch me ! " ta fada cikin tsare gida
" why , we'll Get married soon , i think i have the right to touch you "
" no , Daddy bai ce ni za ka aura , ba ka tunanin da Aleenah zai hada ka ? ka zo kuma ka taba ni , ba na bukatar taimakon ka "
hannu ya kai ya riko damtsenta da ya yanke ya janyo ta dab da shi , sannan ya sake ta , ya kai hannunsa a bayan aljihunsa ya na fadin " ya ba ni auren ku , kuma na karba dan haka ba shi da ikon zaba min wace zan aura cikinku , wadda na zaba ita zan aura " ya fada ya na fiddo wani farin hanckie , ya daure mata wajen yankar da shi
sannan ya ce mata " in kin shiga ki ce a yi miki dress a wajen " ya na gama fadar haka ya raba ta gefenta ya nufi Aleenah ya mika mata hannu alamar ta ba shi file din sa
ba musu ko ta ba shi file din ya sa kafa ya bar wajen
sai da su ka yi nisa sannan Aleenah ta karaso gefen Aleesherh ta na fadin " ni akwai wani abu da ban gane ba , ki na son shi amma sai nuna mishi ki ke kamar kin tsane shi , why ? "
wata yar karamar dariya Aleesherh ta yi kafin ta ce " ba ki ga yanayinsa ba ne ? , da ga gani ya na da takama da izza , in na tunkare shi kai tsaye na ce ina son shi zai ce ba ni da kamun kai , kawai ina nuna mishi ne ni ma ina ji da kaina kamar shi , za ki gani sannu sannu shi da kansa zai bude baki ya ce na burge shi , amma da yanzu da ina biye da shi ina rokon shi ya so ji zai yi ma ya tsane ni saboda na takura mishi , ki jira ki gani , da sannu tsintsu ke yin gidansa , ni kuma zan mallake zuciyarsa " ta fada cike da kwarin guyiwa alamun ta san abun da ta ke
ita dai Aleenah ta yi tsaye ta na kallon ta dan kaifin tunanin Aleesherh ya ninka nata sau uku ba biyu ba , da ita ce ba za taba tunanin yin wannan abun ba , yadda ta ga Aleesherh na kuka saboda son shi , da ita ce kai tsaye kawai za ta fada mishi abun da ke cikin zuciyarta , amma ita Aleesherh sai ta zagayo ta wata hanyar daba dan ta fara mallake zuciyarsa kafin ta fada mishi abun da ke cikin ranta
( ๐๐ NI DAI INA TEAM PRINCE , GWADA KI GANI YARINYA , KO KALLO BA KI ISHE SHI BA , ๐๐ KO DA YA KE YANZU YA FARA NUNA DAMUWA A KANTA , PRINCE KAR KA BAN KUNYA PLEASE ๐ข )