x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - NAYEL THE RETURN OF EXILED PRINCE

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 89550 words

Category: Love Stories

Views 411

14 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ko abinci ba su ba shi , kullum su na tsangwamar shi , shi ne kawai na ce ya zauna tare da ni , Faaz , wannan Auntynka ce , kanwata ce , ina fatan za ka girmama ta kamar yadda ka ke min ? "


gyada mata kai ya yi a hankali kafin ya matso a hankali ya mikawa Inaya hannu ya na fadin " ni sunana Faaz , za ki zama abokiyata ? "

kallon hannunsa ta yi kafin ta dago nata a hankali za ta riko nashi su gaisa
ko one seconde ba ta yi ba ta janye hannunta da sauri

cikin rudu Faaz ya ce " Aunty lafiya ? me ya faru ? ba ki son zama abokiyata ? " ya fada ya na marairaice fuska kamar zai yi kuka

da sauri RIANNA ta riko shi ta na fadin " no ba haka ba ne , na san ta gaji ne ta na son ta je ta huta , baby ya kamata ku je ku huta , zuwa yamma mun yi magana "

ba musu Inaya ta gyada mata kai kafin ta tako a hankali ta riko hannun Malik da ke tsaye tun dazu ya zuba mata ido
da ga haka su ka yi wa MALIKAT INAS sallama su ka fice part din

su na tsaka da tafiyarsu Malik ya ce mata " me ya faru na ji jikinki ya yi sanyi ? " ya fada dan ya lura tun lokacin da Faaz ya ba ta hannu su gaisa jikinta ya yi sanyi

wani cool murmushi ta saki kafin ta ce " ba komai kawai na gaji ne "

" na dauka yunwa ki ke ji ....... "

cikin nitsuwa ta katse shi da cewa " in yunwa na ke ji za ka shirya min abinci ? dan gaskiya ina dan jin yunwa " ta qarashe maganar ta na dan marairaice mishi fuska

sai da ya dan jinkirta kafin ya ce " no , amma zan ba ki madara ki sha , ko ba ki so ? "

wata yar karamar dariya ta yi ba tare da ta ce mishi komai ba
a haka har su ka karaso building din sa wanda marigayi Malik Hicham ya gina mishi
da ya ke dama MALIKAT INAS na sane da zuwan su , tun lokacin da su ka yi waya ta sa a ka gyara part din , duk da ma kullum a gyare ya ke
ko yanzu ma kayansu direct nan a ka yi da su

ko da su ka shiga part din kai tsaye floor na hudu ya wuce da ita
tun a parlour ya fara ya fara zuba mata love , har su ka isa bedroom din su
nan ma sai da su ka mori juna har sai da su ka gaji sannan su ka shiga yin wanka

( ๐Ÿ˜ด๐Ÿ˜ด Ni kuma na dauki takarduna na nufi Yemen dan na ga abun nan nasu ba me karewa ba ne )




MASARAUTAR YEMEN


DAULAR YEMEN ๐Ÿ‘‘๐Ÿ”ฅ




tafiya ya ke cikin harabar masarautar kai a sunkuye ya na duba littafin hannunsa , jiya da ya zo daukar wa Junior littafin da ya saka shi nema ya ga wani littafin da ya ja hankalinsa , shi ya sa ma ya dawo dan zai so ya karanta shi
ya na sanye da wasu suit khaki , ma su bala'in kyau sun yi mugun kabar shi kuwa

ya na a haka kawai ya ji ya bugi mutum har sai da book din hannunsa ya fadi
wani dan karamin tsaki ya saki kafin ya dago kai ,
nan ya gan ta tsaye , ta na sanye da wata gown white color da Alkyaba blue da ga sama , babu ko dan kwali a kanta , gashin kanta duk ya na waje ya bazun mata saman shoulder , ta dafe forehead da hannu guda ta marairaice fuska kamar za ta yi kuka

" ba ki kallon gabanki ne ? " ya fada ya na tsare gida

ba tare da ta bude idanunta ba ta ce " kai ma ba ka kallon gabanka ? dubi don Allah ka ji min a forehead , wlh sai na fadawa Daddy , na ce a rataye min kai " ta fada ta na kukan shagwaba

dan tabe baki ya yi ya na kallon ta wai a rataye shi , to shi in ya yi niyya har Daddy nata sai ya sa a rataye shi kuma a zaune lafiya bare ita karamin aiki , da hannu guda ma zai sa sai dai wata ba ita ba

sai da ya bari ta gama maganarta sannan ya ce " to Daddyn naki da kansa zai rataye ni ko kuma ke zai sa ki rataye ni ? "

" you , you , you are mad , sai na c......... " ba ta karashe maganarta ba sakamakon bude idanunta da ta yi , ba su sauka ko ina ba sai cikin nasa ko , nan take ta sha jinin jikinta ta fara muzurai da idanu

daga mata gera ya yi ya na fadin " uhm , sai kin yi mi ? ida maganarki "

wasu yawu ta hadiye ta na girgiza mishi kai alamun ba komai

" Ah Haba ? ki fadi maganarki , ko sai mun je gaban Daddyn naki na fada mishi abun da yarinyarsa ke yi a wajen Daular ? haka ki ke so ? "

da sauri ta girgiza mishi kai kamar za ta yi kuka ta ce " a'a , don Allah ka yi hakuri , don Allah " ta fada ta na marairaice fuska

" miko min littafina "

da sauri ta duka ta dauki littafin ta sa Alkyabarta ta goge shi sannan ta mika mishi ta na fadin " don Allah kar ka fada mishi , ka ji ? " ta fada ta na marairaice fuska

hannu ya kai karbi littafinsa , ya na shirin magana ya ga dayar ta iso wajen ta na tambayar lafiya dai'dai lokacin da idanunta su ka sauka saman Prince da ke tsaye ya tsare su da ido

nan take ita ma ta sha jinin jikinta ta na muzurai da idanu

a hankali ya nade hannayansa a kirji , ya matse gera ya ce " wacece cikin ku ta shigo min bedroom a hotel ? "

shiru su ka yi ba su ce mishi komai ba sai muzurai su ke da idanu

" ba za ku ba ni amsa ba ? " ya fada ya na matse gera

da sauri ta farkon ta nuna kanta ta na fadin " ni ce , don Allah kar ka fadawa Daddy " ta fada ta na marairaice murya

wani dan karamin tsaki Aleesherh ta yi ta na fadin " ke don Allah yi wa mutane shiru , ba abun da zai yi , wuce mu tafi " ta fada ta na riko hannunta

da sauri ta ce mishi " ka yi hakuri don Allah "

" Aleenah , ki daina ba shi hakuri ba abun da zai yi , wuce mu tafi " Aleesherh ta fada ta na jan Aleenah su ka raba ta gefensa su ka bar wajen
ita dai Aleenah sai marairaice fuska ta ke ta na tsoron ya fadawa Al-Sayid ta shiga mishi bedroom , har a hotel ma , ta san shikenan ta su ta kare ba zai kyale su ba
ita kuwa Aleesherh ko a jikinta ko hakuri ba ta ba shi , ta san barazana ce kawai ya ke musu dan ya ba su tsoro

ko sannu Prince bai ce musu ba ya ci gaba da tafiyarsa , har ya karaso parking space din masarautar , ya shiga motarsa ya fice masarautar, kai tsaye hotel din da ya sauka ya koma ,

ya na isowa bedroom din sa ya ga P.A din sa tsaye cikin bodyguards din sa
ko sannu bai ce mishi ba ya shiga bedroom din sa
bin bayansa P.A din ya yi , ya shigo ya na sallama kafin ya ce " Good morning sir "

" me ya kawo ka ? " Prince ya fada a takaice ya na cire sneakers din kafafunsa

cikin nitsuwa P.A din ya fara fadin " Sir maganar meeting din nan ne "

cikin nitsuwa ya katse shi da cewa " ku soke ta kawai har na samu dama , next week zan koma Saudiya , in na je cen zan san abun yi "

" amma sir tun last week mu ka shirya zaman nan ya za a soke shi lokaci guda haka ? "

dago kai Prince ya yi a hankali ya zuba mishi wadanan hazel eyes din nashi irin na Malik
ya dan dauki lokaci kafin ya ce " ku soke ta kawai na ce , ba shawara na ke ba ka ba , now get out please ina son na huta "

" okay sir , ku na bukatar wani abu na sa a kawo muku ? "

" fruits " ya fada a takaice kafin ya mike ya nufi toilet ya shiga
ya na shiga P.A din nashi ya fito bedroom din
ten minutes bayan fitar sa wani server ya shiga rike da tray din fruits, kai tsaye ya nufi table din gaban gadon ya ajiye kafin ya juya ya fice

after SOME minutes Prince ya fito da ga cikin toilet din sanye da bathrobe kai tsaye ya wuce wardrobe
jim kadan ya fito sanye da wani trouser three cuter da t-shirt , ya saki wannan smooth hair din nasa ya haye gadon kai tsaye ya yi rub da ciki , ba jimawa barci ya yi gaba da shi dan a gajiye ya ke sosai




DAULAR YEMEN ๐Ÿ‘‘



ALEESHERH โค๐Ÿ”ฅ



konce ta ke rub da ciki saman royal bed din ta , cikin wani makeken bedroom hade da parlourn baki daya ma dan cen gaban gadon na hango wasu tsadadun sofas irin na gidan sarauta har da Tv

ta na konce rike da wani book ta na zane , wayar ta na gefe music na tashi , ta na rera waka cikin konciyar hankali

cen na Hango Aleenah tsaye bakin gadon sai kai kawo ta ke yi , duk a tsorace ta ke kar a je Prince ya fadawa Al-Sayid

wani dan karamin tsaki ta ja kafin ta zauna bakin gadon ta kai hannu ta dan bubuga kafar Aleesherh ta na fadin " ke Aleesh , please ki tashi, wlh hankalina ya kassa konciya , kar a je ya fada wa Daddy, "

a takaice Aleesherh ta ce " ba abun da zai yi "

" why ? ba ki sani ba dai " Aleenah ta fada ta na marairaice fuska

" you know what ? i'm falling in love for him , he is so handsome , really i love him " Aleesherh ta fada cikin ko in kula

zaro idanu Aleenah ta yi ta na kallon ta , a rude ta bude baki ta ce " kin san abun da ki ke fada kuwa ? love fa ki ka ce ? how ? "

" Aleen i know what i say , wlh na kassa cire lokacin da na gan sa a kasuwa , kar ki so ki ga yadda ya taro ni , sai ki ce jarumin wani film " ta na gama fadar haka ta janyo pillow ta rungume ta na sakin murmushi

a hankali Aleenah ta kai hannu saman wuyanta , ta janye ta daura saman forehead din ta
cikin rudu Aleesherh ta ce mata " lafiya ? "

" dubawa na ke na ga in ba zazzabi ne ya kama ki ba "

wani dan karamin tsaki Aleesherh ta ja kafin ta sa hannu ta buge hannun Aleenah
janye hannunta Aleenah ta yi ta na fadin " ba ki da hankali wlh , mutumin da ko sunansa ba ki sani ba ki ce kin kamu da son shi "

" and so what ? i'm serious i love him , kuma ke za ki taimaka min na samu abun da na ke so "

" ni kuma ? " Aleenah ta fada cikin rudu

gyada mata kai Aleesherh ta yi ta na fadin " Eh , ke , yanzu fara fada min a wane hotel ya ke zaune ? "

da sauri Aleenah ta girgiza mata kai ta na fadin " nooooo , ba ruwana a cikin wannan maganar " ta kai karshen ta na kokarin tashi da ga saman gadon

da sauri Aleesherh ta mike ta bi bayanta ta na fadin " please my lovely sister , yanzu ba za ki iya taimakawa sister din ki ba ta samu abun da ta ke so ? kuma ai ba ke za ki tafiya ba , ni zan je please ki fada min "

a haka su ka shiga zagayen bedroom din , Aleesherh na rokon ta ta fada mata sunan hotel din
Aleenah kuma ta kafe ta ce ba za ta fada ba ta na tsoron ta janyo musu matsala , ita ko yanzu a tsorace ma ta ke

su na a haka wata mata ta shigo dakin ta na sallama
da gudu Aleenah ta gudu ta boye a bayanta ta na fadin " Anna , ki ce mata ta kyale ni tun dazu ta ke neman ta dake ni "

dan zaro idanu Aleesherh ta yi ta na kallon ta ta ce " ke dai yarinyar nan ba ki tsoron Allah , yaushe na ce zan dake ki ? "

wata yar karamar dariya Anna ta yi kafin ta ce " ya isa haka shikenan , yanzu ku je bangaran Mai dakin Gabas , mahaifinku na jiranku a cen "

" Daddy kuma ? " su ka fada a tare a dan razane

gyada musu kai ta yi ga na fadin " ku yi sauri ya na jiran ku " ta qarashe maganar ta na juyawa ta fice part din

kallon juna su ka tsaya yi su na zaro idanu
cen sai Aleenah ta marairaice fuska kamar za ta yi kuka ta ce " kin gani ko ? sai da ya fadawa Daddy , yanzu Allah kadai ya san abun da zai mana "

tsaki kawai Aleesherh ta yi kafin ta fara takawa ta raba ta gefenta ta wuce ta na fadin " tsaya nan , ni kin ga tafiyata "

da sauri Aleenah ta bi bayanta su ka fito part din
kai tsaye part din Mai dakin Gabas su ka nufa wato Sayida Ahlame wadda ita ce mahaifiyarsu kuma uwar gida ga Al-Sayid

da Sallama su ka shigo parlourn , murya a sanyaye kamar mutanan arziki

su na zaune ccikin parlourn , Al-Sayid ya cire Alkyabarsa , Sayida Ahlame kuma na zaune geffensa da Alkyabarsa saman cinyoyinta da alamar yanzu ya shigo wajen

sai da su ka karaso wajen sofar sannan su ka zauna saman guyiwowinsu su na fadin " sannu da hutawa Daddy , sannu da hutawa momy " su ka fada a tare cike da girmamawa

a takaice Al-Sayid ya ce musu " da ga ina ku ke ? "

" Daddy mu na part din mu mana , shi ne Anna ta je ta ce wai ku na neman mu " Fadin Aleesherh

" kafin nan ina ku ka je ?, da farko ta je amma ta ce min ba ta gan ku ba "

" Daddy da gaske ba mu je ko ina ba , na san lokacin da ta je mun tafi library ne shi ya sa "

gyada kai ya yi a hankali kafin ya ce " okay , kun san dalilin da ya sa na kira ku ? "

" a'a Daddy " su ka fara a tare

sai da ya dan dauki lokaci kafin ya ce " na kira ku ne dan na fada muku shawarar da na yanke a kan bayar da aurenku ga yaron Malik din Saudiya Nawfel Hicham bin Jaabar "

a dubu dari Aleesherh ta mike tsaye ta na zaro idanu , ita kanta Aleenah ba ta ji dadin wannan maganar ba amma ba za ta iya ja da mahaifinsu ba

โคโš˜ ๐๐€๐˜๐„๐‹โš˜โค
________________
แด›สœแด‡ ส€แด‡แด›แดœส€ษด แดา“ แด‡xษชสŸแด‡แด… แด˜ส€ษชษดแด„แด‡

THE BIGINING ๐Ÿ•Š๐Ÿ‘‘โค

TAP THIS LINK TO JOIN MY COMMENT SECTION
https://chat.whatsapp.com/JTfho9QngpG5Ax4LM4d4sK

_______________________________________________






[ FREE PAGE ___ 6๐Ÿ•Š๐Ÿ‘‘โค ]






Dum ta ji zuciyarta ta buga a dubu dari ta mike tsaye ta na fadin " Daddy , aure ? why ? ni gaskiya ba na so "

cikin nitsuwa Al-Sayid ya ce mata " koma ki zauna ! " ya fada cike da isa sam ba wassa a tare da shi

ba dan ta so ba ta koma ta zauna ta na sunkuyar da kai
" Aleenah , Aleesherh , ba shawara na ke ba ku ba , umarni ne , na riga da na turawa Malik Letter dangane da maganar , dan haka ku jira amsar sa sati me zuwa ki fara shirye shirye "

nan take Aleesherh ta saki kuka ta na fadin " amma Daddy me ya sa za ku yi mana haka ? ni ban shirya aure ba gaskiya , kuma kuma.......... "

katse ta Sayida Ahlame ta yi da fadin " kuma me ? Aleesherh na lura ke sam ba ki jin magana , ki na neman ki fi karfin mu , dubi Aleenah ko kalma daya ba ta ce ba , kenan ke ki ke da bakin magana ? gwara ki tafi gidan mijinki ko shi zai iya gyara miki zama "

kuka Aleesherh ta saki ta na fadin " amma Daddy akwai wanda na ke so , akwai wanda mu ke soyayya da shi , don Allah Daddy ka janye maganar nan , wlh ba zan iya rayuwar aure in ba da shi ba " da alamun ta manta gaban wa take dan duk abun da ke cikin zuciyarta kawai ta ke fada

kallon juna Al-Sayid da Sayida Ahlame su ka yi kafin su juya su kalli Aleesherh cike da rudu

"
End Ads