Allah bai kaddara za ku kasance tare ba , ki yi hakuri , in sha Allah za ki samu wanda ya fi shi " Aleenah ta fada ta na son kontar mata da hankali , ta san yar uwarta ba karamin abu ba zai sa ta ce ta na son mutum , asali ma ko irin wannan friends ba ta da su , ko a school ba ta sakewa kowa fuska bare har a yi mata maganar abota , duk wanda ta bude baki ta na so har ta zubar da hawaye saboda shi ba karamar sa'a ya yi ba , ta so ta samu abun da ta ke so ko da wannan karan ne kawai amma Allah kadai ya san abun da ya shirya musu nan gaba , may be su sake haduwa may be ta hadu da wanda ya fi shi
a hankali Aleesherh ta mike tsaye ta nufi toilet ta shiga ta bar Aleenah zaune a nan
sai da ta shiga kawai na ga Aleenah ta fara zubar da hawaye , da sauri ta kai hannu ta goge hawayen kafin ta dauki wayarta ta ci gaba da latsawa
a haka har Aleesherh ta fito da ga cikin toilet din sanye da bathrobe ta nufi wardrobe ta shiga
mikewa ita ma Aleenah ta mike ta shiga toilet din ta yi wanka , ta fito sanye da bathrobe ita ma
nan ta isko Aleesherh zaune bakin gadonsu rike da wayarta ta na latsawa ta daure fuskar tamau
to fa na izzar sun motsa , Aleenah ke fada cikin zuciyarta
wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta girgiza kai ta nufi wardrobe ta shiga
▪ MASARAUTAR SAUDIYA 👑🔥
▪INAYA 👑🍃
zaune su ke cikin parlourn MALIKAT INAS , tare da RIANNA da MALIKAT INAS da Nesrine
Faaz ya na makale da RIANNA ko sakin ta ba ya yi kamar ita ce mahaifiyarsa , ita kuwa sam ba ta damu ba sai jan sa a jiki ta ke kamar yaronta na gaske, sai hira su ke cike da annashuwa sun saka Inaya tsakiya sai tsokanar ta su ke
su na a haka su ka jiyo Muryar Prince cen kassan makoshi ya na sallama
a tare duk su ka juya su ka kalli saitin kofar
a hankali ya shigo ya na sanye da wasu suit white color ma su mugun kyau ya daure gashin kansa a baya , amma ya sako wasu a gefen dama kadan rufe mishi ido
MALIKAT INAS na ganin shi ta mike tsaye ta na fadin " wayyo shalelena , zo na rungume ka " ta fada ta na bude mishi hannayanta
noke mata kafada ya yi ya na fadin " ni ba baby ba ne ku kyale ni , kuma duk fushi na ke da ku "
" fushi kuma shalelena ? me na yi ? " MALIKAT INAS ta fada cikin sanyin murya
" ba ku ku ka sa na dawo ba , ni gaskiya komawa ta zan yi ki cewa Daddy ya kyale ni na yi aikina "
wata yar karamar dariya MALIKAT INAS ta yi kafin ta ce " shikenan zan yi mishi magana yanzu dai zo rungume Ammien ka "
ba musu ya tako a hankali ya rungume ta ya na fadin " na yi kewar sosai Ammie "
" ni ma na yi kewar ka shalelena , fatan ka na cikin koshin lafiya ? "
" i'm fine Ammie " ya fada ya na raba jikinsa da nata
a hankali ta dago kai ta manna mishi kiss a forehead ta na murmushi
a hankali shi ma ya sunkuyo ya manna mata kiss saman kumatu
sannan ya kalli RIANNA , sai da ya ji zuciyarsa ta buga lokacin da idanunsa su ka sauka saman Faaz , ga shi ko shi ma ya tsare shi da ido kamar zai cinye shi
" momy , ba dai replaced di na ki ka yi ba da wannan abun ? " ya fada ya na nuna Faaz
wata yar karamar dariya RIANNA ta yi kafin ta ce mishi " kai ma ka sani ba zan iya ba "
" shi ne ki ka ki taho wa ki rungume ni ki na rike da Babynki ? shikenan ni ma da ga yau kar ki sake ce min babynki " ya na gama fadar haka ya nufi Nesrine ya rungume ta
da murmushi a face din ta ta ce " sannu da zuwa My Prince "
bai amsa mata ba ya dago da ga jikinta
" haba my Baby , yanzu fushi za ka min ? " RIANNA ta fada cikin sanyin murya
" ba kin yi sabon baby ba , ni kyale ni mun bata "
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta kalli Faaz ta ce " Faaz sake ni one minute "
ai ko kara matse ta tsam ya yi ya na fadin " no , ni sai dai mu tafi tare , ba zan sake ki ba "
wani dan karamin tsaki ta ja kafin ta juya ta kalli Prince ta na marairaice mishi fuska
kauda kai ma ya yi kamar bai gan ta ba ya nufi Inaya da tun lokacin da ya shigo ta tsuke fuska
A hankali ya tsugunna a gabanta ya riko hannayanta ya na kallon face din ta , ita ko ta kauda kai gefe
murya a sanyaye ya ce " momy , ba za ki kalle ni ba ? "
kwace hannayanta ta yi ta na fadin " tashi ka koma in da ka fito tun da ni ban da mahimanci a wajen ka "
" haba momy , ta ya za ki ce haka ? kin san yadda na yi kewar ki kuwa ? yanzu na dawo kuma kin juya min fuska "
" to ni na ce ka tafi ? da ka na so na da gaske kamar yadda ka ce da ba za ka yi wannan tsawan lokacin ko kira na ba ka yi , ni kyale ni na yi fushi da kai , kuma ko hakuri ka ba ni ba zan hakura ba "
riko kunnuwansa ya yi , ya yi Kneel down , ya na fadin " I'm sorry my Cutie , please forgive me , ba zan sake ba , ba na jin dadin fushin da ki ke min "
" Zan yi hakuri amma da sharadi " ta fada ta na dawo da kallon ta gare shi
da sauri ya ce " Eh na yarda ko ma minene "
wani dan karamin murmushi ta yi kafin ta nuna mishi gefenta da hannu
a hankali ya mike ya zauna geffenta
hannu ta kai saman face din sa , ta dago kai ta manna mishi kiss a forehead ta na fadin " ka sani ba ka da kirki ko ? ka san yadda Daddynka ya yi kewar ka kuwa ? kullum sai ya kira lambarka ya na sa ran za ka dauka , amma shi ne za ka gudu ka bar mu "
" I'm sorry Cutie , i promise ko zan sake tafiya ba zan wuce one week zan dawo "
" you promise ? " ta tambaye shi ta na murmushi
gyada mata kai ya yi a hankali ba tare da ya ce komai ba
kara fadada murmushinta ta yi kafin ta matso a hankali ta rungume shi ta na fadin " na yi kewar ka sosai my baby "
" ni ma haka Cutie " ya fada ya na kontar da kansa saman shoulder din ta
su dai MALIKAT INAS da sauran sun zuba musu ido gwanin burgewa
TAP THIS LINK TO JOIN MY COMMENT SECTION
https://chat.whatsapp.com/JTfho9QngpG5Ax4LM4d4sK
_______________________________________________
_ PAID BOOK N500
[ FREE PAGE ___ 9 🕊👑❤ ]
sai da su ka dauki lokaci a haka kafin su raba jiki , Inaya ta ce mishi " tashi ka tafi wajen Daddynka , ya na part din Uncle "
yamutse fuska ya yi ya na fadin " no Cutie , gaskiya a gajiye na ke zan so na tafi na yi wanka na huta "
" ka na so kara wa kanka laifi , amma ba ruwana tashi ka je " ta fada mishi
ba musu ya mike ya fara takawa zai fita
da sauri RIANNA ta ce mishi " yanzu kenan Prince ba za ka rungume ni ba ? "
ko sannu bai ce mata ba ya sa kafa ya fice parlourn
sai da ya fita sannan Inaya ta ce mata " sorry Aunty RIANNA , kin san halin yaronki da mugun kishi , may be dan ya ga Faaz ne a jikinki ne ya sa ya miki fuska "
kallon Faaz RIANNA ta yi ta na cewa " yanzu ka yi min adalci , ka hana ni tarbar babyna ? "
cike da shagwaba ya ce mata " momy kenan ni ba babynki ba ne ? " ya fada kamar zai yi kuka
wani dan karamin murmushi ta yi kafin ta ce " no , kai ma babyna ne , just na jima ban gan shi ba , na yi kewar sa sosai , amma ka ga saboda kai ya min fushi ko kula ni bai yi ba "
" yi hakuri momy , bari na je na ba shi hakuri " ya fada ya na raba jikinsa da na RIANNA ya tashi da gudu ya fito part din
ba ta yi kokarin tsayar da shi ba sai ma murmushin da ta ke yi
sai da ya fita sannan Nesrine ta mike ta na fadin " Ammie zan koma part di na "
gyada mata kai MALIKAT INAS ta yi ta na fadin " shikenan , ki kula da mijinki , sannan ki tabbatar ya sha maganinsa "
wata yar karamar dariya Nesrine ta yi ta na cewa " Ammie wlh ina fama dan kamar karamin yaro ya ke , magani ma sai na matsa mishi ya sha "
" sai kin hada da hakuri " MALIKAT INAS ta fada a sanyaye
murmushi kawai Nesrine ta yi mata ta fara takawa ta nufi kofar fita
har ta karaso bakin kofar Faaz ya shigo da gudu ya na kuka ya dafe kumatunsa na dama da hannu
kai tsaye RIANNA ya nufa ya fada jikinta
cikin rudu RIANNA ta shiga tambayar shi lafiya ya na kuka
cikin kukan nashi ya ce mata " momy , Uncle ne , na je na tambaye in zai zama abokina kawai , kawai sai ya mare ni , momy uncle ba shi da kirki , he is wicked "
rungume shi RIANNA ta yi ta ma rasa abun da za ta dan ta rarrashe shi
ba ita kadai ba har MALIKAT INAS da Inaya
musaman Inaya , ta san halin yaronta ya na da zuciya kuma ba ya son takura amma abu me wuya ne ya ce zai daga hannu ya bugi mutum , bare ma dan karamin yaro kamar Faaz , gaskiya zuciyarta ta kassa yarda da Prince ya mare shi
a hankali ta mike tsaye ta na fadin " Ammie ina zuwa "
da sauri MALIKAT INAS ta ce mata " no , koma zauna kyale shi zai dawo ya same ni "
" No Ammie ba wajen sa zan je ba , yanzu ina zuwa " ta fada ta na nufar kofar fita ta fice ta bar RIANNA da MALIKAT INAS su ka shiga rarrashin Faaz
▪PRINCE 👑
bayan ya baro part din MALIKAT INAS kai tsaye part din Malik ya nufa dan dama cen a ka kai kayansa
ko da ya isa a floor na uku ya wuce ya shiga bedroom din sa , ya sa hannu ya fara rage kayan jikinsa , sai da ya rage da ga shi sai short sannan ya nufi toilet
sai da ya yi wajen one hour a ciki kafin ya fito daure da towel a kugunshi , ya karaso wajen dressing mirror
daukar lotion din sa ya yi ya fara shafawa , bayan ya gama ya shiga dressing room
jim kadan ya fito sanye da kayan barcinsa white color ya saki wannan lalawsan gashin kansa irin na Malik , kai tsaye gadon ya nufa ya Haye ya konta rub da ciki kafafunsa ko ida Hayewa gadon ba su yi ba , a haka har barci ya yi gaba da shi
▪INAYA 🕊
bayan ta baro part din MALIKAT INAS kai tsaye part din Diya ta nufa dan ta san Malik na cen a wannan lokacin
ta ko yi sa'a , su na zaune a harabar part din , har da Abdoul
wani cool murmushi ta saki kafin ta karaso wajen ta na yi musu sallama
a tare duk su ka amsa mata , har Abdoul ya bude baki zai yi magana wata kyakyawar budurwa ta fito da ga cikin parlourn Diya
ta na sanye da wata gown pink color babu ko veil a kanta , ta saki wani golden hair din ta mai mugun laushi kai da ga gani ka san a na kashe mishi kudi
ta na kama tak tak da Junior da Diya , a shekaru za ta kai 18 years haka , fara kal da ita jinin larabawa kamar ka taba jini ya fito , Azmat kenan , autar Malik Diya
karasowa ta yi wajen babu ko sallama ta ce " Daddy , ka cewa Big bro ya ba ni bank card di ta , shopping na ke "
dafe forehead Diya ya yi ya na fadin " Ya Salam , wai da wane zan ji ?rigimar Junior ko taki ? tafi bedroom di na ki dauki tawa bar shi wannan "
daga kafa ta yi ta buga a kassa ta na fadin " No ! ni tawa na ke so , ka ce mishi ya ban abuna tun da ba shi ya ban ita ba " ta fada cike da shagwaba
a hankali Inaya ta matso in da ta ke tsaye ta daura hannu saman kanta ta na fadin " Azmat , har yanzu ke ma ba ki daina wannan rigimar ba ? shikenan mu je na karbo miki "
" yawwa momy mu je ki ja mishi wadanan manyan kunnuwa nashi " ta fada ta na jan hannun Inaya su ka koma parlourn tare
sai da su ka bar wajen sannan Abdoul ya ce wa Diya " Diya ina ga ya kamata ka yi wa babynka aure yanzu "
" ko na ce na yi mata ita da momynta ba za su yarda ba , sai da na yi mata maganar amma ta ce wai mu bari har ta kammala karatunta "
haka dai su ka ci gaba da hirarsu har zuwa lokacin da su ka fara jin kiran sallat Malik da Abdoul su ka tashi su ka nufi part din su dama Inaya ta jima da tafiya
Malik Kuwa a floor na uku ya tsaya ya nufi corridor ya shiga
har ya wuce kofar bedroom din Prince ya tsaya ya juyo a hankali dan ya ga haske na fitowa
a hankali ya shiga bedroom din ya na sallama kassa kassa
nan ya ga Prince konce rub da ciki sai sharar barci ya ke
gaskiya ba karamin sanyi ba ya ji cikin zuciyarsa ganin yaronsa har wani cool murmushi ya saki kafin ya tako a hankali ya zauna bakin gadon ya kai hannu saman kansa
wani dogon nunfashi Prince ya ja ya na mika sannan ya ware idanunsa slowly , sai saman Malik ko su ka sauka
" sannu agogo Sarkin aiki , sai yanzu a ka samu lokacin hutawa ? " Malik ya fada cikin sigar zolaya
a hankali Prince ya matso ya kontar da kansa saman laps din Malik ya na fadin " Daddy , tun yaushe ka ke nan ? "
" yanzu na shigo , tashi ka yi wanka mu tafi Mosque lokacin sallat ya yi "
" uhm " ya fada a sanyaye kafin ya sauke kansa da ga kan laps din Malik
ya sauko da kafafunsa kassa ya mike tsaye sai tangal tangal Ya ke kamar zai fadi
mikewa tsaye Malik ya yi ya riko hannunsa ya na fadin " what happened ? "
" nothing Daddy " ya fada ya na kai hannu saman ido ya na murza wa
wani dan karamin murmushi Malik ya saki kafin ya fara jan hannunsa ya nufi toilet da shi kamar wani karamin yaro
sai da su ka iso bakin kofar sannan ya saki hannunsa ya ce " shiga ka yi wanka ina zuwa " ya kai karshen ya na juyawa zai bar wajen
da sauri Prince ya ce " Daddy ? "
cak Malik ya tsaya ya juyo a hankali ya na daga mishi gera alamun minene
kawai rungume shi Prince ya yi ya na fadin " na yi kewar ka sosai Daddyna "
rungume shi tsam Malik ya yi ya na sumbatar kumatunsa , sai da su ka dan dauki lokaci a haka kafin Prince ya raba jikinsa da na Malik kawai ya juya ya shiga toilet ba tare da ya ce mishi komai ba
haka shi ma Malik juyawa ya yi ya fice ya shiga bedroom din sa
ya na shiga nan ma ya tardo Cutien sa , konce saman gado sai barci ta ke , bai yi kokarin tashe ta ba kawai ya shiga toilet
▪MASARAUTAR YEMEN 👑
▪AL-SAYID 👑
zaune su ke cikin parlournsa tare da familynsa, Sayida Ahlame da Sayida Fadwah su na zaune saman sofa guda
Aleesherh da Aleenah kuma su na zaune a kassa saman carpet sun sunkuyar da kai
cikin nitsuwa Al-Sayid ya ce " abun da ya sa na kira ku nan , a kan maganar auren ku ne da na bawa Malik din Saudiya , kuma ya karba hannu bibiyu ya kuma ce in sha Allah gobe yaronsa za su zo nan masarautar in ya so Next week a yi auren , mai dakin Gabas da ke