" ba abun da za su iya yi , ka manta su wa ke tare da familynka " ta na gama fadar haka na ga idanunta sun sauya kamar juyawar page su ka koma White , sannan su ka dawo dai'dai lokaci guda
murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya ce " tun da haka ne abun , yanzu ya za a yi da ni ? yunwa na ke ji My Cutie "
hararrar wassa ta yi mishi ta na fadin " tsakani da Allah baby ba yanzu mu ka yi diner ba ? kuma ka ce yunwa ka ke ji ? "
" Noooo ! ni fa ba irin wannan yunwar na ke ji ba , tun jiya fa ba ki kula da ni ba , ba dole na ji yunwa ba , yanzu dai ki san yadda za ki yi a kai "
bushewa da dariya ta yi kafin ta zagayo da hannayanta a wuyansa
kafin ma ta ce wani abu ya toshe mata baki da nasa bakin ya fara yi mata kiss
( πΆβοΈπΆβοΈπΆβοΈ Ni kuma na dauki takarduna na fice , wannan game din ba irin namu ba ne π€£π )
βͺALEESHERH ππ
bayan sun shiga bedroom din Princess , ta zaunar da ita bakin gadonta ta na fadin " zauna, bari na je na hada miki ruwa ki yi wanka "
da to kawai Aleesherh ta amsa mata , da ga haka ta juya ta shiga toilet
ta na shiga Aleesherh ta dago wayarta , ta shiga kiran layin da Prince ya kira ta da shi dan yanzu Muryarsa kawai ta ke da bukatar ji
ko ringing biyu kiran bai yi ba ko ya daga ya na sallama kassa kassa kamar an yi mishi dole
wani dan karamin murmushi ta saki ta na sauke ajiyar zuciya a tare kafin ta amsa mishi sallamarsa
cikin nitsuwa ya ce mata " har kin kammala diner ? "
" Eh baby " ta fada a sanyaye
" shikenan , yanzu tashi ki yi wanka sai ki kwanta ki huta "
" ba zan iya ba , ni so na ke kawai ka dawo , da yanzu wani abu ya same ka na san ba zan iya jurewa ba "
" na sani , that's why ma na kassa shiga jirgin ina na kokarin kiran ki na fada miki za ni dawo , da ba dan ke ba da na san yanzu wata maganar a ke daban , na gode da ki ke cece ni "
wata yar karamar dariya ta yi , kafin ta shagwabe fuska kamar ta na gabansa ta ce " na ji shikenan , amma da ga gobe in ka dawo ba zan sake barin ka ka tafi kai kadai ba , kullum tare za mu tafi ko ina ne ma "
" okay , I love you my Beautie "
" I love you too my Baby "
" okay now tafi ki yi barci , sai da safe " , ya na gama fadar haka bai jira amsarta ba ya katse kiran
sauko wayar ta yi a hankali ta ajiye saman bedside drawer
ta na ajiye ta ko Princess ta ce mata " shikenan ? har kun ida hirar ? ba irin wannan jan ajin ? ki dan ja shi da hira , ki na zuba mishi shagwaba , ki na kiransa da wadanan kananan sunayan like my Angel , My Chocolate , Sweet , Candy , Honey ya ji ba ya son kashe kiran ma ba ki daya kamar ya janyo ki ta cikin wayar ya rungume "
wata yar karamar dariya Aleesherh ta yi kafin ta ce " yanzu wannan da na yi bai isa ba ? "
" hmmmm , shiga ki yi wanka ki zo na gwada miki yadda a ke yi Mrs Prince " ta fada ta na karasowa bakin gadon ta zauna
ba musu ta tashi ta shiga toilet ta yi wanka
ta yi wajen 45 minutes kafin ta fito sanye da bathrobe , a lokacin har Princess ta fiddo mata kayan barcinta ta saka
karbar kayan Aleesherh ta yi ta shiga dressing room din ta , ta saka kayan
sannan ta fito , nan ta isko Princess zaune tsakiyar gadon ta na rike da wayarta ta na latsawa
karasowa ta yi bakin gadon ta zauna ta na fadin " me ki ke yi da wayata ? "
murmushi mai dan sauti Princess ta yi kafin ta ce " zuba ido ki ga yadda a ke yi "
ba ta ce komai ba ta yi shiru ta zuba mata ido ta na murmushi
ta na a haka ta jiyo wayarta ta fara ringing da alamun kira ne ta ke
sai dai kiran ya katse ta sake yin wani , wannan karan bai yi ringing biyu ba Prince ya daga ya na sallama
amsa mishi sallamar Princess ta yi kafin ta ce " Prince , ka na lafiya ? ba abun da ya same ka ? tun dazu na ke kiran ka sai yanzu za ka dauka ? hankalina har ya fara tashi "
cikin nitsuwa ya ce mata " don't worry , na shiga wanka ne , ba abun da ya faru da ni "
" and Junior ? please ba shi wayar ina son na yi mishi magana " ta fada ta na marairaice murya
da okay kawai ya amsa mata , kafin na ji wajen shiru kamar ya na taku
a haka na jiyo Muryar Junior ya na fadin " Hello ! My Princess "
wani cool murmushi ta saki ta na fadin " Junior , ba abun da ya same ka ? "
" Hmmmm , ki daina kirana da Junior yanzu "
" na ji shikenan My Heartbeat , yanzu fada min , ya jikinka ? ba ka ji ciwo ba ? please ka yi sauri ka dawo " ta fada cikin yar shagwaba
" uhm , har kin fara kewa ta kenan ? "
" ba dole na yi kewa ba , rabin raina ya tafi ya bar ni , tun safe ba abun da na yi kawai ina kwance ina tunanin ka , kuma ka ce ba zan yi kewa ba , yanzu ni dai ka yi saurin dawowa gobe "
wata yar dariya ya yi sannan ya ce mata " ni fa ba gobe zan dawo ba , Prince ne kadai zai dawo gobe , ni sai Thursday "
" what ? sai jibi ? no gaskiya ban yarda ba , so ka ke a kwantar da ni jinya ? ko yanzu zazzabi na ke sai da Daddy ya ban magani na sha " ta fada cike da shagwaba har da turo dan karamin bakinta dama gwana ce
" shikenan , yanzu idan na dawo me za ki shirya min ? "
" ka fara dawowa , ba zan rasa abun da zan shirya maka ba , ko da kuwa kaina ne "
" Really ? " ya fada cike da zumudi
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " sai da safe ni barci na ke ji "
da sauri ya ce mata " no , kar ki kashe , please ki fada min mana , kin san yadda ki ka tayar min da hankali ? , yanzu kin sa dole gobe sai na dawo "
" idan ka na son ganin ko minene zan shirya maka , to gobe ka dawo , ina tabbatar maka sai ka mutu ba ka ji irin wannan dadin ba " ta na gama fadar haka ta katse kiran , ta mikawa Aleesherh wayarta
kafin ma ta kai hannu ta karba ta ji wani kiran ya shigo
cikin nitsuwa Princess ta ce mata " kar ki dauka , duk kiran da za a yi "
" why ? " Aleesherh ta tambaye ta ta na meda wayarta saman bedside drawer
ja da baya Princess ta yi ta jingina bayanta da forehead din gadon ta ce mata " just dan na yi excited din shi " ta fada ta na daga kafadunta alamun ba ta damu ba
( π€£π€£π€£ sannu da kokari , ai kam aikinki ya cika , kin samu abun da ki ke so )
*WANNAN LITTAFIN NA BIYA NE , WANDA YA SHIRYA BIYA ZAI IYA TABO WANNAN NUMBER +22795577612 , β¦500 NE KUDIN SHIGA PAID GROUP ΖIN*
*HAR ZUWA RANAR FRIDAY ZAI KASANCE β¦ 300*
β€β πππππββ€
THE BIGINING ππβ€
cikin rudu Aleesherh ta ce mata " Excited ? you are married ? "
" Yessss , we are married , tun lokacin da ku ka tafi honey moon a ka Ιaura mana aure , ni ma jiya ne Daddy ke faΙa min "
" Wow , congratulations , i wish you to stay together in love and peace "
" na gode , ke ma ina miki fatan hakan , ke da Prince , Allah ya ba babys dayawa "
da sauri ta katse ta da cewa " what ? babys dayawa ? no gaskiya , ni da ga Nayab ba zan kara wani babyn ba , da babys Ιin za na ji ko Daddynsu ? "
" Nayab ? ina ki ka jiyo wannan sunan ? " Princess ta tambaye ta a sanyaye
" Prince ne ya fada min sunan dan uwanku ne , ya ce min shi ne ke tsakanin ku ke da shi , ina son na dawo mishi da Nayab cikin familynsa , i think shi ne kadai gift din da zan iya yi mishi a wannan duniyar " ta kai karshen ta na Ιaura hannu saman cikinta
" haka ne , Prince ya na son babys sosai , may be dan bai da babyn ne ba ki lura da hakan ba , ina tabbatar miki in har ku ka samu baby ba karamin farinciki zai yi ba "
wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta gyara kwanciyarta saman gadon ta na fadin " Good night , barci na ke ji "
da okay kawai Princess ta amsa mata kafin ta kashe musu lamps din dakin ta kunna bedside lamps , ba jimawa barci ya yi gaba
Aleesherh kuma sai muzurai ta ke da ido ba wani barci da ta ke ji kawai tunanin masoyinta ne ya hana ta sukuni
misalin karfe 12 na dare haka , ta yi nisa duniyar tunaninta kawai ta fara jiyo wayarta ta na ringing
hannu ta kai ta dauki wayar da alamun ta manta abun da Princess ta ce mata , kawai ta dauki kiran ta kai wayar a kunne ta na sallama kassa kassa
a daya bangaran , cikin nitsuwa ya amsa mata sallamarta kafin ya Ιaura da cewa " me ki ke jira ba ki yi barci ba ? "
wata yar karamar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta mike zaune ta jingina bayanta da forehead din gadon ta ce mishi " ni ma ban sani ba , na kassa yin barci ne "
" fadi gaskiya , tunani na ki ke yi ko ? "
murmushi mai dan sauti ta yi jin abun da ya ce , kenan ya san abun da ta ke yi , cikin yar shagwaba ta ce mishi " Yes , ina tunanin ka , that's why ma na kassa barci , amma tun da yanzu na ji Muryarka , cikin sauki zan yi kwana "
" muryata kaΙai ? shikenan kashe kiran bari na yi miki video call "
gyada mishi kai ta yi a hankali kamar ya na gabanta , sannan ta sauko wayar a hankali ta katse kiran
sannan ta sauko da ga saman gadon ta fara takawa a hankali ta fito bedroom din
a haka har ta karaso cikin parlourn ta zauna ta na jiran kiransa
ta na zama ko ta ga video call ya shigo
wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta dauki kiran
ya na zaune ya jingina bayansa da forehead din gado , babu ko riga a jikinsa ya saki smooth hair din sa , da wani dan karamin dress a forehead din sa da alamun ya ji ciwo shi ma
dan zaro idanu ta yi kafin ta ce " Honey , me ya ji maka a goshi ? shi ne ka ce ba abun da ya same ka ? " ta kai karshen kamar za ta yi kuka
bai ce mata komai ba ya kai hannu ya janye dress din , sannan ya ce mata " kin gani ? yar karamar buguwa ce na samu "
marairaice mishi face ta yi kamar za ta yi ta na turo dan bakinta
a hankali ya dan kashe idanunsa ya ce " yaushe ki ka zama mai rigima haka ? bari na dawo , wannan dan bakin sai na cinye shi , yanzu tashi ki je ki yi barci "
" ni gaskiya ba zan iya barci ba , hira za mu yi "
" hira ? hirar me za mu yi ? " ya fada ya na kwantawa ya rungume pillow a kirjinsa
kwantawa ita ma ta yi ta na fadin " hmmm ban sani ba , hirar me masoya ke yi ? "
" Sex ? " ya fada a takaice ya na janye pillown da ke saman kirjinsa
ya mike zaune ya ajiye wayar saman bedside drawer ya sake riko pillonsa ya rungume , da alamun akwai wani abu da ke takura mishi dan ya kassa samun sukuni
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " Honey , da alamun akwai abun da ke takura maka , na ga ka kassa zama waje guda "
" ba abu guda ba , abubuwa ma , i'm not feeling good here , ji na na ke duk a takure , specially ma da ba ki tare da ni " ya qarashe maganarsa ya na jan tsaki
" kar ka damu , gobe ka na tare da ni , ina rungume da kai tsam a jikina kamar haka " ta qarashe maganarta ta na janyo pillow saman sofar ta rungume shi tsam da dayan hannunta ta na sakin murmushi
a sanyaye ya ce mata " yi a hankali , za ki sa na fara jin kaina wani irin "
" shikenan , i'm sorry , yanzu fada min me ka ke so na shirya mana gobe ? " ta fada ta na ajiye pilon hannunta ta kwanta ta tada kai da shi
shiru ya yi bai ce mata komai ya zuba mata ido kamar ya janyo ta ta cikin wayar ya rungume ta ya ke ji
ita ma shiru ta yi ba ta ce mishi komai ba ta na sakin wani dan karamin murmushi ita kadai
sannu a hankali ya ga ta fara lumshe idanunta a hankali alamun barci ta ke ji
ya na kallon ta har barci ya yi gaba da ita da alamun ganin shi kawai ta ke son yi barci ya yi gaba da ita
kawai ya tsaya ya zuba mata ido har wajen two hours ba shi da labari har barci ya yi gaba da shi shi ma amma kiran bai katse ba
β WASHE GARI β
washe gari Misalin karfe 8 Malik ya tura Helicopter kassar UK dan dawo da su Prince
Misalin karfe 10 ba dan mintina Helicopter din da ya tafi dauko Prince da Junior ya sauka cikin Daular baki daya
ko da su ka sauka Prince kai tsaye part din sa ya nufa dan shi gaskiya bai iya wannan jajen ba kawai so ya ke ya huta
Junior kuma sai da ya fara biya fada wajen Daddynsa dan ya san a wannan lokacin ya na cen , ya yi sa'a ko ya tardo har da Malik
da ga nan ya juya ya koma part din shi , shi ma ya huta
βͺPRINCE ππ₯
da Sallama a bakinsa ya shigo parlourn part din sa , ya na tafiya kamar an zare mishi lakar jiki
ya na shigowa ya ga ta fito da ga cikin corridor ta na sanye da wandon Jeans blue da wata yar karamar T-shirt white color mai shilalen hannu , ta daura wata Afterdress white da ga sama
ta na ganin shi ta saki wani cool murmushi ta nufe shi da gudu ta fada jikinsa ta rungume shi tsam
rungume ta shi ma ya yi ya na sauke ajiyar zuciya , a sanyaye ya ce mata " Hi my Beautie "
" Na yi kewar ka sosai Honey " ta fada ta na raba jikinta da nashi ta na sakin murmushi
kallon ta kawai ya ke ba tare da ya ce mata komai ba dan ba ya da niyar magana a yanzu
daga mishi gera guda ta yi ta na fadin " Ka yi breakfast ? da alamun ba ka sha coffee ba "
gyada mata kai ya yi a hankali ba tare da ya ce komai ba
" shikenan , ka shiga ka yi wanka , zan je na shirya mana breakfast ni ma yanzu na ke shirin yi "
yanzu ma gyada kai kawai ya yi kafin ya fara takawa a hankali ya nufi corridor
da kallo ta raka shi har sai da ya shiga sannan ta saki wani cool murmushi ta juya ta fice parlourn
ko da ta fito Kitchen ta nufa ta shiga , nan ta tardo su Asmeet , sai aiki su ke yi cikin nitsuwa su na hira
su na ganin ta su ka yi tsit ko wace ta shiga gaishe ta cike da girmamawa
da fara'a a face din ta ta ce musu " Hirar me ku ke yi haka ? ku ba ni na sha ni ma "
Asmeet ce ta amsa mata da cewa " ba komai ranki ya dade , barka da fitowa ! "
" Barka , fatan kun tashi lafiya "
a tare duk su ka amsa mata da lafiya , da ga haka ta shiga aikin hada