wani iska mai zafi ya furza da ga bakinsa ya na neman sanyaya zuciyarsa , ya san in ya biye mata gawarta ce kadai za ta bar Part din nan
share ta kawai ya yi ya shafa lotion din sa , ya shiga dressing room , jim kadan ya fito sanye da wasu kananan kaya kamar kullum , wandon jeans da t-shirt , ya daure farin gashinsa a baya , da alamun ya fara dawowa dai'dai dan da ga kassa ya yi black kadan
haka ya karaso wajen bedside drawer ya dauki wayoyinsa
da sauri ta ce mishi " baby ina kuma za ka je ? yanzu fa ka dawo " ta fada a sanyaye ta na marairaice mishi fuska
ba tare da ya kalle ta ba ya ce " zan je in da ba zan ga wannan face din taki ba "
da sauri ta sauko da ga saman gadon ta sa hannayanta biyu ta tura shi har sai da ya yi baya kamar zai fadi
a rude ya juyo ya na kallon ta ya ce " ba ki da hankali ? "
" Eh , ba ni da hankali , wai me ka ke tunani ? kawai dan ina son ka za ka tsaya ka na fada min duk abun da ka ga dama , kar ka manta , da ga gidan sarauta na fito ni ma bare ka ce ina son ka dan dukiyarka , asali ma lokacin da na kamu da son ka ko sunanka ban sani ba bare na san da ga ina ka ke , ni fa matarka ce , ko ba ka so na ya kamata ka nuna min respect , in kai ba za ka iya fadawa momynka ba , ni zan fada mata a raba auren nan tun da har ba ka so na " ta fada ta na kuka hawaye na zubo mata bibiyu
shi dai ya yi tsaye ya zuba mata ido sai balbale shi da fada ta ke ta na kuka
sai da ya bari ta gama maganarta , sannan ya matso a hankali ya rungume ta ya na shafa bayan ta a hankali cikin sigar rarrashi
neman kwatar kanta ta fara yi ta na fadin " ka kyale ni na tafi , ni gidan mu zan koma "
a sanyaye ya ce mata " sorry , stop crying please "
" why ba ka so na ? duk kokarin da na ke dan na faranta maka ba ka gani , ni gaskiya gidan mu zan koma "
a hankali ya tako bakin gadon ya zauna , sannan ya zaunar da ita saman cinyarsa , ya na kallon face din ta ya ce " ba za ki daina kukan nan ba ? na zata ke jaruma ce "
" ai ko wani Jarumi ya na da rauni , ni kuma kai ne nawa raunin " ta fada ta na sa hannu ta fara goge hawayenta
" shikenan , yanzu daina kukan nan "
a hankali ta mike tsaye
da sauri ya riko hannunta ya na fadin " ina za ki je ? "
ba tare da ta juyo ba ta ce " zan je na wanke fuskata "
sakin hannunta ya yi , ya zuba mata ido har ta fita bedroom din
sai da ta fita sannan ya ja wani dan karamin tsaki , kassa kassa ya ce " ni dai na shiga uku "
da ga haka ya mike tsaye ya dauki laptop din sa saman bedside drawer ya fito bedroom din
βͺIZZAT
tsaye ta ke gaban dressing mirror din bedroom din ta , sai juyi ta ke yi gaban Queen kamar kullum inuwarta kawai ya fito cikin mirror din
sai cen na ga ta koma ta zauna bakin gadon
muryar Queen na jiyo ta na fadin " sai da na ce miki ki daina zuwa wajen nan , yanzu ga shi Prince ya gan ki "
" momy , ni ma ban yi tunanin prince ya na wajen ba , na so na yi anfani da damar nan ne kawai na kashe Malik mu huta "
da karfi Queen ta ce mata " no , ki daina shirme ki yi abun da na saka ki kawai , ko ma wani ki ke son kashewa Malikat Inas za ki fara kashewa "
" why ? i think aikin zai fi sauki in Malik ya mutu ....... "
katse ta Queen ta yi da fadin " Izzat , Izzat , idan har ba za ki iya abun da na ce miki ba zan dawo da ke na je na yi aikin da kaina " ta na gama fadar haka ta bace da ga cikin mirror din
wata yar siririyar kara Izzat ta saki ta na fadin " ni gaskia na gaji da wannan aikin , abun haushin ma wannan sakarar matar da ta makale min "
ai ko ta rufe bakinta ta jiyo Muryar Rianna ta na kiran Faaz
wani dan siririn tsaki ta ja kafin ta mike tsaye ta fara takowa a hankali ta nufi kofar fita
kafin ta iso wajen kofar ta koma Faaz , ya kai hannu a hankali ya bude kofar ya fito da dan gudu ya nufi Parlour ya na fadin " ga ni momy "
ya na isowa parlourn idanunsa su ka sauka saman Princess konce gefen Rianna ta tada kai da laps din ta
cak ya tsaya ya fara takawa a hankali
sai da ya karaso gaban Rianna sannan ya saki kukan shagwaba ya na fadin " momy ta tashi da ga nan , wajena ne ta ke konce "
wani dan karamin tsaki Princess ta ja kafin ta mike tsaye ta riko hannunshi ta na fadin " kai , momyna ce , ba taka ba , in ka ce za ka cika ni sai na sa an rataye min kai "
da sauri Rianna ta mike ta na fadin " Princess , please ki kyale shi , yaro ne fa "
" momy ki kyale ni na koya mishi zama , na ga alamun ya na neman ya wuce gona sa iri , nan ba gidansu ba ne bare ya ce abun da ya ke so za a yi , har ya isa ya ce min ina zan zauna "
kwace Faaz ta yi da ga hannun Princess ta na fadin " ke dai ba ki da kirki , Faaz let's go , kyale ta " ta fada ta na jan Faaz su ka koma cikin corridor din
wani dan karamin tsaki Princess ta ja kafin ta koma ta zauna , ta dauki wayarta ta fara latsawa
ta na zama Junior ya shigo ya na sallama
with a smile on her face ta amsa mishi , ta na fadin " Junior , yau ina ka shiga tun safe sai yanzu na gan ka ? "
murmushi shi ma ya saki kafin ya karaso gefenta ya zauna gefenta , sannan ya ce " Lafiya ki na nema ta ? ko kin yi kewa ta ? "
" Yeah " ta fada ta na wata yar karamar dariya
dariya shi ma ya yi kafin ya ce " mu tafi shopping bayan sallar isha ? "
noke mishi kafada ta yi kafin ta ce " No , ni dai na fi son ice cream , amma Cutie ta ce na daina shan ice cream cikin dare , zai sa ni ciwo "
" shikenan , mu tafi garden mu yi hira , ko kin fi son zama nan ke kadai ? " ya kai karshen ya na mika mata hannu
murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta daura hannunta saman nashi , su ka mike tsaye su ka baro part din
Allah ya sani bai san me ya sa duk lokacin da su ke tare ya ke jin wani bakon yanayi cikin zuciyarsa , ya san da wuya ta gane abun da ya sa ya ke wadanan abubuwan , kuma ba lalle ba ne ta kamu da son shi saboda kallon dan uwa ta ke mishi , amma zai ci gaba da nuna mata so ko watarana za ta amince mishi tun da aure bai haramta tsakanin su ba
βͺPRINCE π
MISALIN KARFE 12 NA DARE
zaune ya ke cikin parlournsa sanye da kayan barci ash color , da laptop saman laps din sa
ya na zaune a haka ya fara jiyo takunta a hankali ta fito corridor
slowly ya dago kai ya kalle ta
ta na sanye da wata yar karamar rigar barci pink color kamar yar baby doll haka , amma wannan simple ce ba ta da wani ado santala santalan cinyoyinta na waje , ta saki gashin kanta a baya ta na tafe ta na latsa wayarta
tun da ta fara takowa ya tsare ta da ido babu ko kiftawa , ita ko , ko ta kansa ba ta yi ba ta nufi hanyar fita parlourn ta fice
ya so ya taro ta amma ya ji harshensa ya yi mishi nauyi ya kassa cewa komai har ta sa kafa ta fita
wata boyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juyo ya ci gaba da aikinsa
after some minutes ta dawo parlourn rike da wani plate da fruits a ciki , ta na rike da fork ta na ci cikin nitsuwa , har ta karaso gefensa dan nesa kadan ta zauna
sai da ta zauna sannan ta mika mishi plate din ta na fadin " za ka sha ? "
girgiza mata kai kawai ya yi ba tare da ya kalle ta ba
dan daga kafadu ta yi alamun ba ta damu ba ta ci gaba da shan fruits din ta
sai da ta kammala sannan ta tashi ta ajiye plate din saman dining table , ta nufi corridor ta shiga ta koma bedroom din ta , ta haye saman gadonta ta konta , ba jimawa barci ya yi gaba da ita
shi kuwa , aikinsa ya ke cikin konciyar hankali har zuwa karfe 1 sannan ya tashi ya koma bedroom din sa ya konta
βͺAFTER SOME DAYS
da wassa wassa lokaci na tafiya har su ka share wajen sati guda a haka , yanzu Aleesherh ta daina sake mishi kamar da farko , kullum ta na cikin bedroom din ta ta na konce rike da waya , tun bai fara nuna damuwa a kai ba har ya fara nunawa ya na tambayar ta in ba ta da lafiya , amma ta ce mishi lafiyarta qlau , ba dan ya so ba ya shanye abun sa
lokacin da Malik ya fada mishi za su tafi honey moon bai ce mishi komai ba dan shi kansa ya san ya bukatar hutu a yanzu , ko ba komai zai samu ya dan huta
maganar Malik da Inaya kuma , har yanzu ba su sake komawa wajen duwatsun nan ba , kuma ba wanda su ka fadawa abun da ya faru
Princess da Junior kuma kullum sun tafi shan ice cream ko shopping , ko su na garden su na hira
Aleenah kuma , yanzu ta fara sakin jiki su na hira da Rianna , har ma da Princess , musaman da ya ke ta fi Prince sakin jiki , nan take su ka saba , su na hira kamar wasu friends , har shopping ta taba kai ta , tare da Azmat , duk da ba kullum ta ke zama ba , kullum ta na school ,
Malik kuwa ya yanke shawarar bayan dawowar Aleesherh za su koma school ita da Aleenah
Ranar Friday , Prince da Aleesherh su ka tafi Honey Moon din su , ba Aleesherh kadai ba har shi kansa Prince sai da ya yi mamakin irin wajen da Malik ya kawo su , ya yi mamakin irin dukiyar da mahaifinsa ya kashe wajen sayen wajen nan , har wajen gina gidan da za su sauka , dan ba karamin gida ne ba , duk wall din sa na zallar glass ne abun har mamaki ya ban , sai dai wani shirme da ya yi musu , duk irin girman gidan bedroom guda ce a ciki , floor na kassa duk parlour ne da kitchen da dining room , sai wani balcony bakin ruwa , floor na biyu kuma bedroom din ce baki daya
βͺISLAND OF THAILAND π
MISALIN KARFE 4 NA YAMMA β
βͺALEESHERH ππ
zaune ta ke a balcony saman wata lounge chair , da ga ita sai bra da wani dan wando kamar pant pink color , ta lumshe idanunta , wayarta na saman wata yar karamar table gefenta Music na tashi , da plate din fruits
ta na a haka ta ji kamar inuwar mutum a gabanta ya tare mata rana ,
slowly ta ware idanunta , ba su sauka ko ina ba sai saman shi , ya na tsaye gabanta da ga shi sai short , ya daure gashinsa a baya , yanzu ya dawo black din sa kamar da farko
a hankali ta gyara zamanta ta kai hannu ta dauki wayarta ta kashe Music din sannan ta kalle shi ta ce " me ya faru ka yi tsaye gabana ? ko wani abu ka ke bukata ? "
" Yeah , ina son magana da ke " ya fada a sanyaye kafin ya fara takawa ya koma cikin gidan
a hankali ta mike tsaye ta bi bayansa su ka koma cikin gidan , a nan parlourn ta gan shi zaune ya sunkuyar da kai
a hankali ta karaso gefensa ta zauna ta na ce mishi " me ya faru ? "
dago kai ya yi slowly ya kalle ta , cikin sanyin murya ya ce " Eesherh , please in wani abu na yi miki ki fada min , tun lokacin da mu ke Saudiya ki ka daina yi min magana , yanzu kwana biyu mu ka yi a nan amma ko so guda ba ki min magana ba , wlh ba na jin dadin hakan cikin zuciyata , in laifi na yi miki ki fada min na ba ki hakuri "
wani dan karamin murmushi ta saki , tarkonta ya yi kamu , dama Inaya ta ba ta wannan shawarar na ta kyale shi ta daina kula shi , ta san halin yaronta , kuma ta tanka dai'dai ga shi yanzu da kansa ya yi mata magana
hannu ta daura saman nashi ta ce " ni ba ka yi min komai ba , ba kai ka ce ba ka son hayaniya ba , shi ne kawai na daina takura maka "
riko hannunta ya yi cikin nashi , ya dago a hankali ya manna mishi kiss ya na fadin " i'm sorry , ni ban ce kin takura min ba , just ban saba zama da mutane ba ne , amma zan koya ko dan saboda ke "
" da gaske ? " ta fada ta na sakin wani dan karamin murmushi
gyada mata kai kawai ya yi alamun Eh
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta matso ta rungume shi
a hankali ya zagayo da hannayansa a bayanta ya rungume ta shi ma , ga shi ko ba wasu kayan kirki ne ba a jikinta , lokacin da hannayansa su ka sauka saman lalawsar fatar jikinta ba karamin shock ya ji ba , har mikewa gashin jikinsa ya yi , nan take ya ci gaba da shafa bayanta
wata yar karamar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta sake shi a hankali ta dago da ga jikinsa amma har yanzu bai sake ta ba
wani dan karamin murmushin gefen fuska ta yi kafin ta ce " sake ni na koma balcony "
bai ce mata komai ba ya matso a hankali ya kai lips din sa saman nata ya manna mata kiss dan shi kadai ne abun da ke yawo a brain din sa a wannan lokacin
ita kuwa ta na jin saukar lips din sa saman nata ta ji zuciyarta ta yi wata wawar bugawa ta na zaro idanu
ba ta gama shan mamaki ba sai da ta ji tongue din sa cikin bakinta ya na neman cabko tongue din ta , ya fara tsotsayar tongue din ta kamar ya samu sweet
ita dai ta yi zugum ta zuba mishi ido , ya lumshe idanunsa , duk ta ji ta kassa wani kwakwaran motsi
sai da ya yi wajen five minutes rike da ita a haka kafin ta ji ya sauke wata doguwar ajiyar zuciya sannan ya saki tongue din ta , a hankali ya zame bakinsa da ga cikin nata , sannan ya ware idanunsa a hankali , kai tsaye cikin nata su ka sauka
a hankali ya janye hannayansa da ga bayanta , a sanyaye ya ce " i'm sorry , ban san me ya shige ni na yi hakan ba "
gyada mishi kai kawai ta yi kafin ta mike tsaye a hankali ta ke takawa har ta koma balcony , saman lounge chair din ta , ta zauna ta saka Music ta saki wani cool murmushi ta ci gaba da shan iskanta , ranta fari kal kamar an yi mata albishir da gidan Aljannah
β€β πππππββ€
THE BIGINING ππβ€
*WANNAN LITTAFIN NA BIYA NE , WANDA YA SHIRYA BIYA ZAI IYA TABO WANNAN NUMBER +22795577612 , β¦500 NE KUDIN SHIGA PAID GROUP ΖIN*
_______________________________________________
[ FREE PAGE ___ 23 ππβ€ ]
β ISLAND OF THAILAND π β
βͺPRINCE ππ₯
kwance ya ke tsakiyar bed Ιinsu , da ga shi sai short ya zubawa ceiling ido kamar mai tunanin wani abu
ya na kwance a haka Aleesherh ta fito da ga cikin toilet sanye da bathrobe
sai da ta karaso wajen dressing mirror za ta shafa lotion Ιinta sannan ta lura da shi ta cikin mirror
slowly ta juyo ta kalle shi da alamun akwai abun da ke damun sa
takawa ta yi a hankali ta zauna bakin gadon , ta yarfa mishi ruwan gashinta