musu breakfast dan shi ne ya kawo ta , ta na yi ta na jan su da hira , ko su sai da su ka yi mamakin hakan ganin yadda ta ke yi musu hira ta na dariya , sam ba ta da girman kai kamar wasu
bayan ta kammala ta shirya musu breakfast din saman tray ta dauki kayanta ta baro kitchen din ta bar su da aikin gyara
bayan ta koma parlourn , a nan tsakiyar parlourn ta ajiye tray din , sannan ta fidda After dress din ta ta shiga corridor kai tsaye bedroom din sa ta wuce
a hankali ta turo kofar dakinsa ta shigo ta na sallama kassa kassa
nan ta isko shi kwance saman gado da ga shi sai short , ya daura hannu guda saman forehead , da gudan kuma ya na rike da wayarsa ya na latsawa
wani cool murmushi ta saki kafin ta tako a hankali , kai tsaye ta Haye saman shi ta kwanta , ta lumshe idanunta
a tare duk su ka sauke ajiyar zuciya , sannan ya sauko da hannunsa da ga saman forehead ya daura saman bayanta ya fara shafawa a hankali
a sanyaye ta ce mishi " tashi mu je mu yi breakfast "
kashe wayarsa ya yi ya daura saman bedside drawer ya ce mata " okay , bari na je na saka kaya "
mikewa ta yi a hankali da ga jikinsa ta koma bakin gadon ta zauna
a hankali shi ma ya mike zaune ya sauko da ga saman gadon ya nufi dressing room ya shiga
ita dai ta yi zaune ta zuba mishi ido , da ga gani akwai abun da ke damun shi
ta na zaune a haka har ya fito sanye da wasu kananan kaya wandon Jeans da T-shirt
ya karaso bakin gadon ya mika mata hannu
da sauri ta sauko da ga saman gadon ta riko hannunshi su ka fito a tare
a nan parlourn su ka zauna su ka yi breakfast din , shi coffeen da ta hada mishi kawai ya sha dan shi kadai ya ke da bukata a yanzu
sai da su ka kammala ba wanda ya ce ko ufan , ta tattare kayan ta meda kitchen
bayan ta dawo ta isko ya na konce a kassa saman carpet , ya lumshe idanunshi , Tabbas ko bai fada mata ba ta san wani na damun sa dan ba ta taba ganin shi cikin irin wannan yanayin ba , ko dai bomb din da ya tashi da jet Ιinsa ne abun ya ba shi tsoro , ko kuma wani abun
a hankali ta karaso in da ya ke kwance ta haye saman shi ta zauna saman cikinsa
slowly ya ware idanunsa , sannan ya ce ta sauka ya zauna
ba musu ta mike tsaye , ya zauna ya ja da baya ya jingina bayansa da sofa , sannan ta koma ta zauna saman Thigh Ιinsa
zagayo da hannayanta ta yi a wuyansa ta ce mishi " Honey , me ya faru don Allah ? na ga duk ka sauya lokaci guda , ko ba ka jin jikinka ? "
sai da ya ja wani dan karamin tsaki kafin ya ce " Ba haka ba ne Beautie , just akwai abun da ya tsaya min a rai na rasa ya zan yi "
" ka fada min minene , may be ka ji sauki idan ka fada min , please " ta fada ta na marairaice mishi fuska
sai da ya share five minutes bai ce mata komai ba ya zuba mata ido , haka ita ma ta zuba mishi ido ta na jiran ta ji abun da zai ce mata
a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya bude baki ya ce mata " ni ma ban sani ba , may be idanuna ne su ka samu matsala , ko dai kama ce kawai "
cikin rudu ta ce mishi " ban gane ba Honey , me ya faru ? "
" i think , i saw Nayab "
" What ? " ta fada da dan karfi
dan lumshe idanunsa ya yi a hankali kafin ya sake bude su ya ce mata " Beautie , ban san ya zan fada miki hakan ba , Lokacin da mu ke airport za mu shiga Jet , na tsaya ina kokarin kiran ki na fada miki zan dawo , juyawar da zan yi kawai na ga kaina ina kokarin shiga wani jirgin , you know it is impossible a ce na ga kaina a waje biyu , yadda ki ka gan ni haka , haka ni ma na gan sa , ba abun da ya banbanta mu , na fada miki har wannan smooth hair din nawa , da yanayin jikina , tsayina , idanuna , lips Ιina , All , Beautie kamar ina kallon kaina ne cikin mirror haka na gan sa , na yi tunanin ko kawai ba na gani ne kyau na tsaya na zuba mishi ido har ya shiga jet din , ya tashi , ya na barin wajen ne Jet din mu ya tashi da Bomb "
( πππ€π€ Wata sabuwa kuma , Nayab dai wannan Nayab da kowa ke shaidar ya mutu , a ka je da gaske Prince Nayab ne ya gani ? π€π€ gaskiya akwai sauran labari )
a hankali ta matso kussan kirjinsa , ta kai hannu saman face Ιinsa , cike da kula ta ce mishi " Honey , please ba abun da ka ke tunani ba ne , kai fa da kanka ka ce min Nayab ya mutu tun lokacin da ya shigo duniya , ta ya za a ce ka gan shi lokaci guda haka ? "
" Beautie , ni ma na kassa yarda , hankalina ya kassa dauka " ya kai karshen ya na lumshe idanunsa
" dan haka kar ka ba shi damar dauka " ta kai karshen ta na janye hannunta da ga saman fuskarsa
slowly ya ware idanunsa ya fara ganin wani dishi dishi kafin ya fara gani dai-dai
a hankali ya ga ta yi sama yar t-shirt din ta , ta fidda ta ta ajiye gefe
zagayo da hannayansa ya yi a kugunta ya matse ta a jikinsa , a hankali ya kai lips din sa saman wuyanta ya manna mata kiss
a dai-dai lokacin ko Aleenah ta shigo musu parlourn ta na sallama da fara'a a face din ta
a tare duk su ka zaro idanu musaman Aleenah ba ta yi tunanin za ta tardo su cikin wannan yanayin ba
da sauri ta juya za ta bar wajen , ba ta yi taku daya ba Aleesherh ta tsayar da ita da cewa " kar ki tafi madam , dawo ai kin riga da kin ga komai "
a hankali Prince ya dago kansa , cikin rada ya ce mata " tashi na tafi , ina son na kwanta "
" please honey , ka zauna mu yi hira da ita " ta fada ta na marairaice mishi fuska
gyada mata kai kawai ya yi ba tare da ya ce mata komai
murmushi ta saki kafin ta sauka da ga saman shi , ta Ιauki rigarta ta saka
ta na sauka ya tashi da sauri ya nufi corridor ya shiga , gwara ya yi mata wayo ya san in ya biye mata za su yi ta jayayya ne , yanzu ga shi cikin ruwan sanyi ya kubce mata
cike da shagwaba ta shiga kiran sunansa ta na fadin " Honey , please ka dawo "
amma ya share ta ya ci gaba da tafiyarta
sai da ya shiga sannan ta kalli Aleenah da ke tsaye ta juyawa parlourn baya ta ce mata " to ke malama sai ki shigo , kin kore shi kin ji dadi "
wata yar karamar dariya Aleenah ta yi kafin ta juyo ta fara takowa a hankali ta karaso cikin parlourn ta na fadin " to ke madam , bedrooms din naku wani aljani ne a ciki da ba ku iya tsayawa a cen ? " ta fada cikin zolaya
hararrar ta Aleesherh ta yi kafin ta ce " wai me ma ya kawo ki waje na a wannan lokacin ? "
zama gefenta Aleenah ta yi kafin ta ce " nothing , just ina kewar ki ne , shi ne na zo ganin ki " ta kai karshen ta na rungumo ta
" to yanzu ga shi kin sa Honey ya tafi , ai da sai ki min text za ki zo , da yanzu naked ki ka tardo mu fa ? "
bushewa da dariya Aleenah ta yi har da tapi , sai da ta tsagaita dariyarta sannan ta ce " sannu Honey , shikenan bari na tashi na tafi in da na fito "
da sauri Aleenah ta riko hannunta ta na fadin " no , kar ki tafi , na ji dadin ganin ki , mun jima ba mu zauna ba haka , na yi kewar ki sosai "
wata yar karamar dariya Aleenah ta yi kafin ta ce " na zata kin manta da ni , ki na nan rungume da Honey "
" hmmm , ke ma kin sani duk abun da zai faru ba zan iya mantawa da ke ba , ke ce dai ganin ki ya zama kallon rana , kullum ki na ciki sai ka ce amaryar , ki dinga fitowa may be ki hadu da naki Prince din " ta fada cikin zolaya ta na wata yar karamar dariya
murmushi mai dan sauti Aleenah ta yi kafin ta ce " in sha Allah , watarana zan hadu da shi , amma ba yanzu ba , yanzu dai tashi ki je ki kula da Honey , ni na tafi "
" no , gaskiya babu in da za ki je , yau tare za mu zauna mu yi hira " Aleesherh ta fada dan gaskiya ta jima ba ta zauna da yar uwarta haka ba , su ka yi hira
ba dan ta so ba ta zauna su na zuba hira da dariya
Prince kuwa ya na cen Bedroom din sa tunanin duniya ya yi mishi yawa , ya na tunanin abun da ya gani a airport ya kassa yarda da hakan , ta wani bangaran kuma ba ya tunanin gaskiya ne tun da har ya na da tabbacin Nayab ya rasu , amma minene tabbacin nasa ? Malik da Inaya su ka ce mishi ya rasu , a ka je su ma ba su da tabbacin ya rasu ? , gaskiya dole ya yi investigation in har da gaske Nayab ne ya gani to dole ya shiga neman dan uwansa ko da ya na bangon duniya
a takaice dai haka su ka share inin ranar a haka ,
Aleesherh da Aleenah su na a parlour su na hira , sai da lokacin sallat ya yi sannan Aleesherh ta ja su ka shiga bedroom din ta su ka yi sallat
Prince kuwa , ya na bedroom din sa har lokacin Sallat ya yi
ya tashi ya shiga wanka , ya yi alwala ya fito ya shirya cikin wata jallabiya white color ya baro part din ba tare da su Aleesherh sun sani ba
shi ma bai neme ta ba ta na cen tare da sister din ta ta manta da shi
bai baro Mosque ba sai da ya ga rana cen ta fadi saura kadan a yi Magriba sannan ya koma part din sa , Allah kadai ya san abun da ke damun sa a wannan lokacin dan duk yanayinsa ya yi sanyi
ko neman Aleesherh bai yi ba ya shiga bedroom din sa ya medo kofar
haka ita ma yau duk ta manta da shi ta na tare da Aleenah sai hira da dariya su ke , abun da su ka jima ba su yi ba , zama haka su na hira tun lokacin da su ka baro Yemen , yau kuma sun samu dama duk da cikin gidan guda su ke
*WANNAN LITTAFIN NA BIYA NE , WANDA YA SHIRYA BIYA ZAI IYA TABO WANNAN NUMBER +22795577612 , β¦500 NE KUDIN SHIGA PAID GROUP ΖIN*
*HAR ZUWA RANAR FRIDAY ZAI KASANCE β¦ 300*
β€β πππππββ€
THE BIGINING ππβ€
zaune ya ke cikin parlourn part din sa , ya na sanye da kayan barcinsa blue , da laptop a gabansa da wasu uban takardu da alamun aiki ya ke yi
kamar da ga sama kawai ya ji an rufe mishi idanu
a dan razane ya dago kai dan shi bai ji shigowar mutum cikin wajen ba tsananin ya yi nisa cikin aikinsa
tun kafin ya ce wani abu ta riga shi cewa " aikin me ka ke yi haka ? na shigo tun dazu ina sallama ka kyale ni "
wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya daura hannu saman hannunta da ke saman idanunsa ya ce mata " sorry my baby , ban ji ki ba ne "
a hankali ta janye hannayanta ta zagayo gabansa ta zauna , ta kwashe takardun baki daya da laptop din ya ajiye gefe
ta na shagwabe mishi fuska ta ce " ni fushi ma na ke da kai yau , tun da ka dawo ba ka neme ni ba , kenan ba ka yi kewa ta ba ? "
" to ba ga shi yanzu ke kin neme ni ba ? " ya fada ya na kashe mata ido
" haka za ka ce ? shikenan , na koma in da na fito " ta kai karshen ta na mikewa tsaye za ta bar wajen
taku biyu kawai ta yi ta ji ya riko hannunta
da sauri ya juyo ta , su na fuskantar juna , ya zagayo da hannayansa a kugunta ya janyo ta jikinsa
murya a sanyaye ya ce mata " haba my baby , da ga wassa ? wai me ya sa rigima ta yi miki yawa ne ? "
" ba wata rigima , ni kyale ni na tafi " ta fada ta na neman raba jikinta da nashi
ba tare da ya sake ta ba ya ce mata " kenan ba za ki kwana tare da ni ba yau ? ni da na shirya miki surprise , shi ne za ki tafi "
" surprise ? wace irin surprise ? "
" no , ba zan fada ba yanzu , sai kin amince za ki kwana a nan tare da ni "
" na yarda amma ba a bedroom guda ba , yanzu sake ni akwai maganar da na ke son mu yi "
ba musu ya sake ta ya koma ya zauna ya na nuna mata gefensa alamun ta zauna
ba musu ta karaso gefensa ta zauna ta na fadin " dama a kan investigation din da za mu yi ne a kan Faaz , Aleenah ta tambayi Momy ta fada mata gidan marayun da Faaz ya baro , ta kuma turo pic din shi da ta dauka ba tare da ya sani ba yadda za yi kwatancen shi cikin sauki "
wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya mike tsaye ya na fadin " please Baby , ki bar maganar nan , yaro ne fa ? wane mara imani ne zai yi anfani da karamin yaro kamar shi dan cutar da wani ? "
" kai fa ka yi min alkawari za ka taimaka min mu gano gaskiya a kansa , idan ba mu tabbatar da maganata wlh zai iya cutar da mu , please baby ba zan iya yin wannan abun ni kadai ba " ta fada ta na marairaice mishi fuska kamar za ta yi kuka
ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce mata " me sunan gidan marayun ? "
" Ekhaa charitable fondation for orphans care "
" ki na nufin orphanage din Ekhaa ? " ya fada dan ya san gidan marayun , su na da tsari da kula sosai a kan marayu musaman kananan yara kamar Faaz , da wuya a ce su zauna baki sake har ya baro gidan marayun ba su saka an fara neman shi ba , hakan na nufin tabbas fito da Faaz a ka yi , amma gwara ya biye mata su yi investigation din a ka je ta na da gaskiya Faaz da niyar cutar da su ya zo ?
ya yi nisa duniyar tunaninsa ya ji ta na kyasta mishi yatsunta saitin fuskarsa
a hankali ya dawo hayacinsa ya na fadin " me ya faru ? "
" ina yi maka magana ka kyale ni " ta fada cikin shagwaba
wani dan karamin murmushi ya saki kafin ta kai hannu saman face din ta ya na fadin " sorry my baby , ina tunanin wani abu ne , bari na je na kawo mana fruits , za ki sha ? "
girgiza mishi kai ta yi kafin ta matso a hankali ta rungume shi ta kontar da kanta saman chest Ιinsa dama ya fi ta tsayi amma kadan ya yi saura kanta ya tabo shoulder din sa
wani dan karamin murmushi ya saki kafin ya zagayo da hannayansa a bayanta ya rungume ta shi ma
kamar ya na yi mata rada ya ce " ya kamata mu shiryawa tafiya Honey moon mu ma , ko ya ki ka gani ? "
wata yar karamar dariya ta yi ba tare da ta ce mishi komai ba , sai kara matse shi ta ke yi kamar za ta shige jikinsa baki daya
" shikenan , yanzu sake ni ki shiga ki yi wanka zan dauko miki kayan barcina ki saka "
ba musu ta raba jikinta da nashi , ya riko hannunta su ka shiga corridor
βͺALEESHERH ππ
a hankali ta turo kofar bedroom din Prince , ta shigo ta na sallama kassa kassa , da ga ita sai Towel a kirjinta , da alamun yanzu ta fito da ga wanka