wani ne ya amsa mishi da cewa " a'a ranka shi dade , babu wanda zai yi wa aurensu kallon auren yarjejeniya ........... "
bai qarashe maganarsa ba su ka jiyo sallamar mutum cikin fadar
a tare duk su ka juya su na kallon Prince tsaye bakin kofar Fadar
cikin rudu Al-Sayid ya ce mishi ya karaso
ba musu ya karaso tsakiyar fadar ya tsaya , ya dan sunkuyar da kai ya na fadin " ina mika sakon gaisuwata ga shugaban wannan kassar mai Albarka , tare da dukkanin mazaunan wannan wajen "
daya da ga cikin su ne ya amsa mishi da cewa " A gaishe ka dan Saurayi , me ya kawo ka gaban Al-Sayid ? "
cikin girmamawa Prince ya ce " ranka shi dade sunana Prince , ina neman Alfarma wajen shugaba "
" Alfarma kuma ? ka fadi abun da ya kawo ka " fadin Al-Sayid
" ranka shi dade , wani littafi na ke nema a kan tarihin tsohuwar Yemen , na je library da dama amma sai a ce min duk littafan tarihin masarautar Yemen , su na a cikin Libraryn Daular , ranka shi dade zan so a ba ni dama na duba Littafin in har ba damuwa "
wani dan karamin murmushi Al-Sayid ya saki kafin ya ce " Na ji dadin ganin har yanzu akwai matasan da su ka damu da sanin tarihin Tsohuwar Yemen , Allah ya yi maka Albarka yaro , Allah ya kara Basira "
a tare duk su ka amsa mishi da Ameen kafin Prince ya daura da cewa " Godiya na ke ya shugaba "
" Za ka iya zuwa ka duba duk littafin da ka ke so , na ba ka izini "
dan rinsinwa Prince ya yi ya na fadin " Godiya na ke ya shugaba , Allah ya ja zamanin mai martaba , Allah ya kare ka da sharin makiya "
da Ameen yanzu ma duk su ka amsa mishi , da ga nan ya juya tare da wani dogarin da zai raka shi libraryn su ka bar wajen
cikin nitsuwa ya ke tafiya kai a sunkuye ya na latsa wayarsa cikin filin masarautar
cen kawai na ga ya tsaya Cak waje guda slowly ya dago kai ya kalli saitin hagunsa ta cikin Window din wani ginin
nan ya gan ta tsaye rike da sword ta na sanye da wasu fararen Tracksuit , ta daure gashin kanta a baya , sai wassan takobi su ke yi da wani dogarin da ga gani ta kware
tsayawa ya yi ya zuba mata ido ya na son tantance wani abu
ya yi wajen two minutes tsaye a haka kafin ya ga sun tsaya sai haki ta ke ta na sakin murmushi
a hankali ta juya dai-dai lokacin da ya ga ta biyun ta karaso wajen su na fuskantar juna
tak wadda ya gani a libraryn cikin gari , har kayanta
kenan in ya gane Twins ne ? shi ya sa su ke kasancewa waje daban daban lokaci guda
wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya ci gaba da tafiyarsa har su ka iso libraryn da ga nan dogarin ya juya ya kyale shi ya nemi abun da ya ke zo nema
U.S.A ( WASHINGTON DC ) โ
Yau Garin tun bayan sallar asubahi a ka fara ruwan sama cen zuwa yamma kuma ya koma snow , Malik Gaskiya ya so ya tafi Saudiya a yau amma a Airport sun kira sun ce jirgi ba zai iya tashi ba a irin wannan lokacin sai dai ya bari har gobe
ba dan ya so ba ya hakura
washe gari kuma a yin sallar Asubahi su ka nufi airport shi da Inaya da Princess
su na isa ko Jirginsu ya daga ya nufi Saudiya
MASARAUTAR SAUDIYA ๐๐ฅ
DAULAR SAUDIYA ๐ฅ๐
MALIKAT NESRINE ๐๐ฅ
A hankali ta ke takowa ta na rike da tray cike da fruits , duk yanayin ta a sanyaye kamar ba ta jin jikinta
a haka har ta karaso cikin parlourn part din su ta na sallama kassa kassa
a hankali Diya ya dago kai ya na amsa mata sallamar ta
ya na zaune saman sofa ya na sanye da kayan barci , duk ya rame har wani dan duhu ya yi da ga gani ciwo ya ke tsantsar shi
a haka har ta karaso gefensa ta zauna ta na fadin " bude baki na ba ka ! " ta fada ta na dauko barin apple guda ta kai mishi a baki
murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya ce mata " na ji ciwo na ke amma ai ni ba baby na ne , zan ci da kaina " sannan ya kai hannu ya karbi apple din ya kai a baki ya ci abu ne
dan sunkuyar da kai ta yi kafin ta dauki tray din ta ajiye mishi saman cinyoyinsa sannan ta mike za ta bar wajen
da sauri ya riko hannunta ya na fadin " Nesi , wai me ya faru ne ? kwana biyun nan na ga duk yanayinki ya yi sanyi ko magana na yi miki ba ki ba ni amsa kamar a baya , ko wani laifi na yi miki ? "
girgiza mishi kai ta yi a hankali ta na fadin " ba komai , kawai barci na ke ji "
a hankali ya sa hannu ya janye tray din saman laps din sa , ya ajiye gefe , sannan ya dafe forehead din sofar , ya fara kokarin tashi a hankali
ta na jin ya fara jan hannunta da karfi ta yi sauri ta juyo , ta taimaka mishi ya mike tsaye ta na yi mishi sannu
mikewa tsaye ya yi ya riko kugunta a hankali ya janyo ta jikinsa , cikin sanyin murya ya ce mata " haba Sarauniyar zuciyata , haba uwar y'ay'a na , ke ki na tunanin za ki iya boye min damuwarki ? please fada min , me ke damun babyna ? ko sai na yi miki kuka ? " ya qarashe maganar ya na marairaice fuska
murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta rungume shi , ta kontar da kanta saman chest din sa
cikin sanyin murya ta ce mishi " kawai har yanzu ina tunanin halin da ka ke ciki ne , ba dan ikon Allah ba da yanzu shikenan na rasa ka har abada , ba zan iya rayuwa babu kai ba , don Allah ko tafiya ka ke son yi ka bari na riga ka , yadda ba zan ji zafin rashin ka ? "
" ni kuma na ji zafin rashin ki ko ? ki daina jin tsoro , in sha Allah ba abun da zai raba ni da ke , mu na tare har abada "
gyada mishi kai kawai ta yi kafin ta matse shi tsam a jikinta
wata yar karamar dariya ya yi kafin ya ce " ki na tune haduwar mu ta farko ? "
" please wai me ya sa sai ka min wannan maganar kullum ? ya riga da ya wuce , ni ka daina ba na so " ta fada cike shagwaba ta na turo dan bakin nan nata
wata yar karamar dariya ya yi kafin ya ce mata " to ai ranar ce na kassa mantawa , har yanzu ganin nake kamar jiya ne haduwarmu ta farko , ina tune lokacin kin sauko da ga school , ki na tafe ki na faman turo baki , da ga gani yunwa ce ki ke ji , a ranar na dawo da ga Abuja cikin mota , kawai na tsaya na ce miki ki shigo na rage miki hanya , amma ina , madam na bude baki ta balbale ni da fada , kai kuma malam da ga ina ? dan yankan kai ne ko ? da wasu idaninka kamar na mujiya , to wlh babu inda zan je da kai , kuma wlh in ka sake ka biyo ni sai na fadawa yayana ya yi maka dan banza duka , mai kanta kai kawai " ya fada ya na kwaikwayon Muryarta
dariya sosai ta yi ta na bugun shi a kirji a hankali
haka shi ma dariya kawai ya ke dan har ga Allah ba zai taba manta wannan ranar ba , ranar da ya kamu da son ta , ita ba ta san wannan tsiwar da ta yi mishi ne ya sa ya kamu da son ta a lokaci guda , ga shi yanzu tsawan shekaru 30 da yin aurensu har da yaransu biyu
sai da ta gama dariyarta sannan ta dago kai ta ce mishi " na ji shikenan , yanzu mu je ka konta ka sha maganinka , ka huta "
" baby , duk fa karfe 1 na rana , haba ku na neman ku saka ni a prison , duba fa har fada kun hana ni zuwa , at least ku bar ni na sarara "
" please baby , mu shiga da ga ciki magana , zan yi maka tausa in mu ka je " ta fada mishi cike da shagwaba ta na kashe mishi ido
wata yar karamar dariya ya yi , ya na shirin magana ya jiyo Muryar Malik kamar an koro shi ya na fadin " Diya , where are you ? "
a tare shi da Nesrine su ka juya su na kallon kofar shigowa parlourn dai'dai lokacin da Malik ya shigo shi da Inaya
wata yar karamar kara Nesrine ta yi kafin ta saki Diya ta nufi Inaya da gudu ta rungume ta ta na sakin kuka
haka shi ma Malik da sauri ya nufi Diya ya rungume shi
a tare su ka sauke wata nanauyar ajiyar zuciya , duk da su na ganin juna ko wacce shekara kuma su na waya amma a yanzu ji su ke yi kamar sun yi shekaru dubu ba su ga juna ba
sai da su ka gaji da rungumar sannan Malik ya dago da ga jikin Diya , ya daura hannayansa biyu saman face din sa , a rude ya ke fadin " Ya jikinka ? How ? ta ya haka ta faru ? kuma a ce ba za ka iya kira na ka fada min ba ? yanzu da wani abu ya same ka fa ? shikenan na rasa dan uwana tilo da na ke da shi ? me ya sa za ka min haka ? at least da sai ka kira ni ka fada min tun kafin abun ya tsananta , amma sai da ka gama samun lafiya za a sanar da ni , ko ka na tunanin ba ka da mahimanci ba ne a waje na ? haba Diya ? "
" za ka yi shiru ko sai ka saka ni kuka ? " Diya ya fada cikin sanyin murya idanunsa na cikowa da hawaye
da sauri Malik ya kara rungume shi ya matse shi tsam ,
a kunne ya ke ce mishi " I'm sorry , na so na kasance a tare da kai lokacin da ka fi bukata ta , i'm so sorry , I promise ba zan sake rabuwa da kai ba , ko da kuwa mutuwa ce ta zo shiga tsakanina da kai ba zan bari ta raba ni da kai ba , i'm back my bro , i'm back "
wata yar karamar dariya Diya ya yi kafin ya rungume shi tsam , kamar zai yi kuka
kar ku tambaye ni ina su Inaya , tun lokacin da Nesrine ta rungume ta ba su saki juna ba sai kuka su ke yi kamar za su hadiye juna , musaman Nesrine dan sai da Inaya ta dinga rarrashin ta kamar wata baby
a hankali Diya ya raba jikinsa da na Malik ya na fadin " now je ka huta , na san kun gaji , zuwa yamma na tarda ka "
" no , mu je na raka ka ka konta kafin nan " Malik ya fada ya na riko hannunsa , ya fara jan sa a hankali su ka nufi corridor
" zan iya tafiya da kaina , ka tafi kawai "
ko sannu Malik bai ce mishi ba su ka ci gaba da takawa har ya kai shi bedroom din shi , ya kontar da shi saman gadonsa , ya rufe shi da duvet sannan ya juya ya fito
TAP THIS LINK TO JOIN MY COMMENT SECTION
https://chat.whatsapp.com/JTfho9QngpG5Ax4LM4d4sK
_______________________________________________
[ PAGE ___ 5๐๐โค ]
ya na fitowa parlourn ya tardo Inaya da Nesrine rungume da juna
a hankali ya karaso wajen ya na fadin " Cutie , mu tafi zuwa anjima sai mu dawo "
a hankali ta raba jikinta da na Nesrine , cikin sanyin murya ta ce mata " je ki kula da shi , zuwa anjima na dawo "
gyada mata kai kawai Nesrine ta yi kafin ta juya ta nufi corridor ta shiga Inaya kuma ta bi bayan Malik dan tun lokacin da ya yi maganar ya fice
ta na fitowa ta hango shi ya na takawa a hankali ya nufi part din MALIKAT INAS
da sauri ta kamo shi ta riko hannunsa , ta na fadin " shi ne za ka taho ka bar ni ? "
" ba na son takura miki ne shi ya sa " ya fada ba tare da ya kalle ta ba
murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta kontar da kanta saman shoulder din sa su ka ci gaba da tafiyarsu a haka
duk inda ya wuce sai dogarai sun gaishe su cikin girmamawa , wasu har rako su su ke yi dan ba karya su na jin dadin ganin Malik cikin masarautar kowace shekara
wani abu da ban fadi ba , bayan mutanan da ke cikin Daular Saudiya , duk mutanan masarautar ba wanda ya san Diya ne a kan kujerar Malik , kowa a tunaninsa Malik ne , dan duk lokacin da za su yin wani taro inda a ke bukatar Malik da Rawani Diya ya ke tafiya , kuma wani lokacin ya na sanye da medical glass shi ya sa su ka kassa gane shi
da sallama a bakinsu su ka shigo parlourn MALIKAT INAS
su na zaune ita da RIANNA , cen na hango wani dan karamin yaro da ba zai wuce 8 years ba , ya na zaune gefen RIANNA da tray din fruits a gabansa
cikin nitsuwa shi kuma ya karaso cikin parlourn ya na kallon yaron dan shi a iya sanin sa RIANNA ba ta taba haihuwa ba to wanene wannan yaron ?
da sauri ita ma RIANNA ta mike ta nufi Malik ta rungume shi ta na fadin " na yi kewar ka sosai Akhie "
" ni ma na yi kewar ki over " ya fada ya na rungume ta shi ma , a haka har MALIKAT INAS ta mike ta rungume su a haka
sai da su ka gaji sannan su ka raba jiki MALIKAT INAS na ce wa Malik ya zauna
" a'a Ammie , zan wuce part di na , na gaji sosai wlh " ya fada murya a sanyaye
" shikenan " Fadin MALIKAT INAS a takaice kafin ta juya ta na kallon Inaya da ke tsaye ta zuba wa yaron ido
wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " to ba za ki gaishe ni ba ? wai tsaya ma , ina ku ka baro min Twins di na ? "
Malik ne amsa mata da cewa " Princess ta na US , exams gare ta shi ya sa ba ta biyo mu ba , amma in ta kammala za ta taho , Prince kuma......... ni kaina ban san inda ya ke ba "
a tare MALIKAT INAS da RIANNA su ka zaro idanu , har su na hada baki su na cewa " kamar ya ba ka san inda ya ke ba ? "
" Ammie , Aunty RIANNA , Prince fa ba baby ne ba , ya na da hankalin kansa , kuma na san duk in da ya ke ya na cikin koshin lafiya " Fadin Inaya da ke tsaye a bayansu
cikin rudu MALIKAT INAS ke cewa " ni fa ban gane me ku ke nufi ba , ina Prince di na ya yi ? "
" Ammie na fada miki , ni kaina ban san in da ya ke ba , wajen three months rabon da na saka shi a idona , ni ko waya ma ba mu yi , Sai dai ya turo mana letter ya ce wai ya na cikin koshin lafiya , yanzu dai zan tafi , Cutie let's go " ya fada ya na mikawa Inaya Hannu
ta na tsaye ta zubawa yaron nan ido babu ko kiftawa , shi kuwa sai sunkuyar da kai ya ke ya na ja da baya
a hankali ta dago kai ta kalli MALIKAT INAS ta ce " Ammie , wanene wannan yaron ? "
wani kyawatacen murmushi RIANNA ta saki kafin ta koma ta riko hannunsa , ta mikar da shi tsaye ta na fadin " sunansa Faaz , last month ne security su ka kama shi cikin kitchen din Daular , ya na satar abinci , za su hukunta shi ne na iso wajen , na ce su kyale shi yaro ne , kuma yunwa ya ke ji , da ga nan na sa a ka ba shi abinci , bayan ya ci na ke tambayar shi ina ne gidan su a mayar da shi , ban ya ke ce min wai da ga gidan marayu ya gudo , kuma ba zai koma ba saboda ba su da kirki wai