x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 11 - NAYEL THE RETURN OF EXILED PRINCE

  • 30001 words
  • 33000 words
  • Out of 89550 words

Category: Love Stories

Views 391

14 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
da mai dakin yamma zan so ku shirya tarbar su , a gyara musu part gudu cikin bangare na , sannan kuma yaranku ku shirya su sannan ku koya musu yadda za su tarbi mazajensu , zan so a yi auren bi sa tsarin al'adun mu na Yemen , dan haka ku fara shirye shiryen "

a Sayida Ahlame da Sayida Fadwah su ka amsa mishi da cewa " in sha Allah ranka shi dade "

su na gama fadar haka su ka jiyo Muryar Aleesherh ta na fadin " zan iya tafiya ? " ta fada kai a sunkuye

" ban ida da ke ba , Aleenah ke dama kin ce ba ki da matsala da auren da haka za ki iya tafiya " fadin Al-Sayid

ba musu ta tashi ta fice parlourn dan ita ma ta gaji da zaman nan

sai da ta fita sannan Al-Sayid ya ce wa Aleesherh " ina boyfriend din da ki ka ce ku na soyayya da shi ? "

ba ta ji tsoron komai ba ta ce " babu shi , dama karya na yi maka saboda ba na son auren nan , amma yanzu na amince a yi auren "

murmushi mai dan sauti Al-Sayid ya yi kafin ya ce " Allah ya shirye ki , tashi ki tafi to "

ba musu ta tashi ta bi bayan Aleenah su ka koma part din su
sai da su ka bar wajen sannan Sayida Ahlame ta mike ta na fadin " ranka shi dade zan je na yi wa ma su kula da kitchen magana a kan abun da za a shirya musu gobe "

gyada mata kai kawai ya yi kafin ba tare da ya ce komai ba , ita kuma ta sa kafa ta fit

sai da ya fita sannan ya kalli Sayida Fadwah ya ce " Gimbiyata , me kuma ya faru ? na ga kwana biyu duk kin sauya "

kamar dama jira ta ke ya tabo ta kawai ta buda mishi wuta ta na fadin " to me ka ke so na yi ? na sani ba ni na haifi Aleesherh da Aleenah ba , amma ko ba komai ni Mahaifiyarsu ce , ina da hakki a kan su , ta ya za ka yanke irin wannan shawarar ba tare da ka sanar da ni ba ? ka na son nunawa Jama'a ni ban da hakki a kan su ne kenan ? tun yaushe na ke yi maka magana a kan Abdoul-Jalil ya ce ya na son auren Aleesherh , amma ka rufe ido ka ce a'a kawai dan ya na yaron babban yayana kuma ba a Yemen ya ke zaune ba , yanzu kawai ka tashi wani wanda ba mu san shi ba , ba mu san halayansa ba ko sunansa ma su sani ba ka bashi auren yaran nan , ka yi min adalci kenan ? "

shi dai ya yi zaune ya zuba mata ido ya na murmushi sai zuba ta ke , cike da bacin rai

sai da ta gama maganarta sannan ya ce " tun da kin fadi abun da ke cikin zuciyarki yanzu sai ki tashi ki je ki sa a shirya musu wajen da za su sauka " ya fada cikin tsare gida cike da izza alamun ba wassa

sai da ta ja tsaki sannan ta tashi ta fice parlourn ta koma part din ta



โ–ชALEESHERH ๐Ÿ‘‘๐Ÿ’ž



bayan ta baro parlourn Al-Sayid kai tsaye part din su ta koma
ko da ta koma ta tardo Aleenah tsaye saman gadon sai tsalle ta ke kamar wata karamar yarinya gashinta na tashi sama


ba ta bi ta kanta ba ta zauna a nan saman sofa ta fiddo wayarta ta fara latsawa

ta na zama Sayida Ahlame ta shigo ta na sallama
da sauri ta ce wa Aleenah " ke madam sauko kar ki ji ciwo "
ko sauraron ta Aleenah ba ta yi ba ta ci gaba da tsallen ta na dariya

murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta karaso ta zauna gefen Aleesherh ta na fadin " Alee , lafiya na ga kin sauya haka ? me ke damun ki ? "

" ba komai " ta fada a takaice cen kassa kassa.

hannu Sayida Ahlame ta kai ta kwace wayarta ta na fadin " fadin gaskiya , me ke damun ki ? "

sai da ta ja tsaki ta na fadin " momy Allah ba na son auren nan , amma....... "

" ba fa ke kadai za a yi wa auren nan ba , har da Aleenah amma duba hankalinta a konce ya ke "

" to ai momy Aleen ki ka ce ba ni ba , why Daddy zai yanke irin wannan hukuncin , na sani ba na jin maganarsa har na koyawa Aleen amma yi min aure ba ita Ce solution din ba , at least ku bari na kammala karatuna "

murmushi mai dan sauti Sayida Ahlame ta yi kafin ta ce " ba fa karamin mutum ne ba za ki aura , magajin kujerar mulkin kassar Saudiya baki daya za ki aura , ki yi tunani wane matsayi ne za ki samu , matsayin MALIKAT fa , in har Allah ya ba ku baby boy kin zama MALIKAT AL'UMU , babu wanda zai ba ki umarni bayan mijinki ko shi in ki ka mallake zuciyarsa sai kin dinga ba shi Umarni , ki tsaya ki yi tunani mai kyau, kin fi son ki auri wani dan kasuwa da it's not sure ya ba ki irin rayuwar da mahaifinku ya ba ki , kar ki bari zuciya ta debe ki ki yi babbar assara "

shiru Aleesherh ta yi na dan lokaci kamar mai tunanin wani abu

kamar da ga sama ta jiyo Muryar Aleenah ta na fadin " momy ba auren ne ba ta so , akwai wanda ta hadu da shi kuma ta kamu da son sa , amma ba ta san in da ya ke ba "


a dubu dari Aleesherh ta juya ta wurga mata wani mugun kallo
ta na shirin magana Sayida Ahlame ta ce " What ? Aleesherh maganar me ta ke ? "

" gaskiya ne momy , akwai wani wanda na gani kuma na kamu da son shi , lokacin da Daddy ya tado min maganar nan na yi kokarin yi mishi magana a kan abun da ke cikin zuciyata amma bai saurare ni ba , yau da safe na sake komawa wajen sa amma na tarda ba ya nan ya bar kassar , shi ya sa ma na hakura na karbi maganar auren "


" Alee , na san irin abun da ki ke ji cikin zuciyarki ba zan yi miki karya ba , ko ni a lokacin da na ke da shekarun ki akwai wanda na ke soyayya da shi , amma lokaci guda iyayena su ka ce za su aura min mahaifinku , da farko har kokarin kashe kaina na yi dan ba na son sa , amma bayan an aura auren Allah ya ba ni ku na ji ba wanda na ke so a duniyar nan sama da shi , ni wlh na ma manta sunan wanda na ke soyayya da shi da farko , may be ya na raye ko a mace Allah kadai ya sani "


" yanzu momy kun yarda na shiga gidan wani bayan kuma akwai wanda na ke so ? ki na ganin na yi mishi adalci ? ni ko ban samu wanda na ke so ba please a janye maganar in sha Allah zan fitar da mijin aure da kaina " ta fada ta na marairaice fuska kamar za ta yi kuka


hannu Sayida Ahlame ta kai saman kumatunta ta shafa cike da shauki ta ce " ki yi hakuri tun da har an saka rana nan da one week , kuma yanzu in mahaifinku ya ce wa Malik ya janye maganar wane irin kallo ki ke son ya yi mishi ? ba ki san yadda Ikon Allah ya ke ba , a ka je shi wanda za a aura miki ki kamu da son shi da kallo guda kawai har ki manta wancen "

wani dan karamin murmushi ta saki ta na kauda kai murya kassa kassa ta ce " hmmm har na fara ganin sa dai "


sarai Sayida Ahlame ta ji abun da ta ce amma ba ta tanka mata ba ,
ta juya ta kalli saitin kofar shigowa part din ta ce " za ki iya shigowa " ta fada da dan karfi

ta na gama fadar haka wata budurwa ta shigo wajen da ba za ta wuce 30 years ba rike da wani tray da wani dan karamin bowl a sama

ta karaso wajen su ta ajiye bowl din saman table kanta na sunkuye sannan ta juya ta fice

sai da ta fita sannan Sayida Ahlame ta kai hannu ta dauki bowl din

cikin rudu Aleesherh ta ce mata " minene wannan momy ? "

" scrub ne , zai gyara miki skin ta kara haske na dukka jiki ne , ki fara shi tun yanzu kafin Ammienku ta zo , in Aleenah ta farka sai ta yi ita ma " ta fada dan fa Aleenah barci ya riga da ya sace ta

gyada mata kai kawai Aleesherh ta yi tare da fadin " sai na cire kayana ? "

gyada mata kai Sayida Ahlame ta yi kafin ta kai hannu cikin scrub din
mikewa tsaye Aleesherh ta yi , ta zuge zip din rigarta ta yi kassa da ita ta fidda ta bar underwear kadai ko kunyar Sayida Ahlame ba ta ji ba , sannan ta daure gashin kanta a baya ta koma ta zauna

ta na zama Sayida Ahlame ta debo scrub din ta shafa mata a face , ta murza da kyau
sannan ya shafa mata a saman hannayanta duk ta bi jikinta ta shafa mata har saman wuya da cinyoyi

bayan ta gama shafa mata ta tashi ta shiga toilet ta wanke hannayanta ta kuma tara mata ruwan wanka da perfume da suaran su ta fito ta ce mata nan da 30 minutes sai ta shiga ta yi wanka

โคโš˜ ๐๐€๐˜๐„๐‹โš˜โค
________________
แด›สœแด‡ ส€แด‡แด›แดœส€ษด แดา“ แด‡xษชสŸแด‡แด… แด˜ส€ษชษดแด„แด‡





THE BIGINING ๐Ÿ•Š๐Ÿ‘‘โค





๐Ÿ•Š๐Ÿ’ž ( ๐™ฐ ๐™ท๐™ด๐™ฐ๐š๐šƒ ๐šƒ๐™พ๐š„๐™ฒ๐™ท๐™ธ๐™ฝ๐™ถ ๐™ป๐™พ๐š…๐™ด ๐š‚๐šƒ๐™พ๐š๐šˆ , ๐š๐™พ๐™ผ๐™ฐ๐™ฝ๐šƒ๐™ธ๐™ฒ , ๐™ธ๐™ฝ๐™น๐š„๐š‚๐šƒ๐™ธ๐™ฒ๐™ด & ๐™ณ๐™ด๐š‚๐šƒ๐™ธ๐™ฝ๐šˆ) ๐Ÿ’ž๐Ÿ•Š






โค๐Ÿ‘‘ ๐‘ด๐‘จ๐‘ณ๐‘ณ๐‘จ๐‘ฒ๐‘ฐ๐‘ต.๐‘จ๐‘ด๐‘ฌ๐‘ฌ๐‘น๐‘จ๐‘ฏ ๐‘จ๐‘ฉ๐‘ซ๐‘ถ๐‘ผ๐‘ณ๐‘จ๐’€๐‘ฐ๐Ÿ‘‘โค
( ๐‘จ.๐‘ฒ.๐‘จ ๐‘ด๐‘ฌ๐‘ฌ๐‘น๐‘จ๐‘ฏ ) โค๐Ÿ•Š






TAP THIS LINK TO JOIN MY COMMENT SECTION
https://chat.whatsapp.com/JTfho9QngpG5Ax4LM4d4sK





_______________________________________________


โ–ช๏ธŽPAID BOOK N500




[ FREE PAGE ___ 10 ๐Ÿ•Š๐Ÿ‘‘โค ]







da to kawai Aleesherh ta amsa mata , da ga haka Sayida Ahlame ta sa kafa ta fice part din

ta na fita Aleesherh ta mike ta shiga toilet ta zauna bakin bath din ta na kuka kassa kassa
ita dai Aleenah ba ta ma san duniyar da ke faruwa ba sai barcinta ta ke cikin konciyar hankali har da wani dan karamin murmushi a face din ta
bari na koma Saudiya kafin su kammala to



โ–ชMASARAUTAR SAUDIYA ๐Ÿ‘‘๐Ÿ”ฅ



โ–ชMALIK ๐Ÿ”ฅ



zaune ya ke cikin parlourn part din sa a floor na uku , Prince da Junior su na zaune su ma kowane ya na rike da wayarsa sai saman latsawa ya ke

cikin nitsuwa Malik ya fara magana ya na fadin " Prince , ina fatan Junior ya fada maka sakon da ya iso mana da ga Daular Yemen ? " ya fadi hakan dan a lokacin da letter din ta iso gare shi Junior ya na wajen

nan take yanayin face din Prince ta ida sauyawa duk da ba wani murmushi ne a kai ba ,
kamar zai yi kuka ya ce " Daddy i'm sorry in hukuncin tafiyar da na yi ne ka yi hakuri ba zan sake tafiya ba , amma gaskiya ban shirya yin aure ba "

" okay , ka ba ni hujja uku da za ta hana ka yin aure a yanzu , in har sun gamsar da ni to zan janye maganar auren " Malik ya fada cikin tsare gida ya na matse gera alamun ba wassa

wani dan karamin tsaki Prince ya ja ya na kauda kai , shi gaskiya ba ya son auren nan specially ma da ya ji wacece a ka ce zai aura

ya na a haka ya jiyo Muryar Malik ya na fadin " Nayel , da kai na ke magana , ka ba ni hujjojin na ce "

murya cen kassan makoshi ya ce " babu " da kyair ma sautin ya fito , tun da ya ji Malik ya kira sunan shi kai tsaye to duk abun da zai ce ba zai iya kare kansa ba , maganar auren ta zauna kenan ba mai kwatar sa sai Cutie , ita kadai za ta iya shayo kan Malik ya janye maganar auren nan

shi ko bai san Cutien da ya ke cewa ita ta kawo shawarar auren ma

wani dan karamin murmushin gefen fuska Malik ya saki kafin ya ce " okay , ku shirya gobe za ku tafi Yemen kai da Junior , nan da one week za a yi auren kuma za a yi shi ne bisa tsarin al'adun masarautar Yemen "

da sauri Junior ya ce " Uncle ina da magana please "

" wace magana ? " Malik ya fada ya na tsare shi da ido

sunkuyar da kai ya yi ya na fadin " umm Uncle , ni dai ba zan iya karbar auren nan ba , saboda akwai wadda na ke so "

dan tabe baki Malik ya yi ya na kallon shi ya ce " really ? wacece ? zan je da kaina neman maka aurenta sai a yi auren rana guda da na Prince "

sunkuyar da kai Junior ya yi ya fara wasu dan kame kame ya kassa fadawa Malik Abun da ke cikin zuciyarsa , ya na jin kunyarsa gaskiya

su na a haka Inaya ta shigo cikin parlourn ta na sallama da murmushi a face din ta kai tsaye ta nufi gefen Malik ta zauna
ta na fadin " hirar me ku ke yi haka ? "

Malik ne ya ba ta amsa da cewa " hirar auren yaranki , Junior ya ce akwai wadda ya ke so ba zai karbi kyautar Al-Sayid ba "

" Masha Allah , Junior ka fada mana wacece sai mu fara shirye shiryen auren a yi shi tare da na Prince " ta fada ta na kallon Junior

Prince kuwa ya na jin ta kira sunansa ya dago kai a dubu dari ya na kallon ta kenan ta na sane da maganar auren ya , ke tambayar kansa

shi dai Junior sai sosa bayan keya ya ke da hannu ya kassa fadin maganarsa kamar an rufe mishi baki ya ke ji

wani dogon tsaki Prince ya ja kafin ya ce " Cutie , Princess ce ya ke so "

a tare duk su ka juya su ka kalli Prince har shi kansa Junior
pillow ya dauka ya kai mishi bugu a baya ya na fadin " me a ba ka gane ba cikin sirri ? "

" wait ! Junior da gaske Princess ka ke so ? " Malik ya jefo mishi tambayar

wasu yawu Junior ya hadiye kafin ya ce " um , um uncle , dama da..... "

" ban ce ka yi min wani kame kame ba , Eh ko A'a za ka ce "

gyada mishi kai kawai Junior ya yi dan ba zai iya bude baki ba

wani cool murmushi Malik da Inaya su ka saki a tare , Malik har da wata yar karamar dariya ya na fadin " to ai faduwa ta zo dai'dai da zama , ta na dawowa za a daura auren "

marairaice fuska Junior ya yi ya na fadin " Uncle , it's not sure ita ma ta na so na "

Inaya ce ta amsa mishi da cewa " Kar ka damu , ba za mu fada mata an yi auren ba sai ka shawo kanta , kuma kai ma ka san halin Princess ta na da saukin kai , cikin sauki za ka shayo kanta "

wata yar karamar dariya Junior ya yi ya na sunkuyar da kai

Prince kuwa tsaki ya ja ya na fadin " Fine , da alamun hade min kai ku ke son yi yau "

" Kai malam aure ne dai sai ka yi shi sai dai ka mutu "

" yanzu Cutie ba za ki ce wani abu ba ? " ya fada ya na kallon Inaya

daga mishi kafadu ta yi alamun ba ta sani ba
bushewa da dariya Junior ya yi har da tapi

hararrar shi Prince ya yi ya na fadin " yi min shiru kai kuma ko na shake ka wajen nan "

" Ba ni na karto man ba , rataya a ka ba ni " ya fada ya na mikewa tsaye ya nufi lift da gudu ya na dariya

da sauri Prince ya mike ya bi bayansa sai dai kafin ya riko sa har kofar lift din ta rufe

wani tsaki ya ja kafin ya juya ya koma cikin parlourn
ya na dawo da kallonsa kan Malik da Inaya kawai ya gan su rungume da juna ya na yi mata magana cikin rada

" Daddy , da mutum fa a wajen " ya fada ya na dan zaro musu idanu

hararrar Malik ya yi kafin ya ce " in ka ji haushi sai ka yi aure kai ma , My Cutie , tashi mu tafi na yi miki tausa "

cike da shagwaba Inaya ta ce mishi " Baby ni gaskiya yunwa na ke ji "

kiss ya yi mata a forehead ya na fadin " don't worry , tashi mu tafi "

ba musu ta tashi shi ma ya mike tsaye ya riko hannunta su ka nufi lift su ka shiga, su ka bar Prince zaune a nan ya na kallon ikon Allah su na
End Ads